Episode 7
by @zahraroyal
*MUGUN ICCE*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO........*
PAGE 7
*Gwajawa Rimaye, Kankia LGA, Katsina state Nigeria*
Zaune take tana sauri saboda wayarta da take ta ji tana ƙara a cikin ɗaki. Wanke-wanke ne jifge a gabanta, taci rabinsa.
Tana yi tana tsakin tsaki kaɗan-kaɗan dan Allah ya sani bata son wanke-wanke ko kaɗan dan ya zame mata dole ne kawai.
Saura kwano ɗaya ya rage mata da sauri ta idasa ɗauresa tana ƙoƙarin miƙewa kawai batai aune ba taji an wargo mata wasu kwanukan har guda uku lokaci ɗaya.
Da wani irin sauri ta ɗaga kanta Safiya ce ta gani tsaye a kanta tana mata wani kallo.
Tashi Ummi tayi tsaye da sauri tana nuna kwanukan tana cewa.
"Wa kike so ya wanke su?"
"Ke kanki kin san kanki ai, waye yake aikin idan bake ba?"
Wani kyakkyawan mari ne Ummi ta ɗauke Safiya dashi, dan ranta ya kai ƙololuwar ɓaci, dan ita kam bata iya ɗaukar wannan rainin, jiya ma dan a gaban uwarta ne yasa bata ɗauki mataki akan Safiya ɗin ba, da tai mata rashin kunya.
Wani ub*an ihu Safiya ta saki tana sakin kuka iya ƙarfin tana nuna Ummi da yatsa.
"A'a a'a mi zan gani haka ke Safiya mike faruwa a nan?"
Wani kalar kuka ta ƙara saki tana matsawa inda Ammi take ta ce.
"Ammi wai fa daga na kawo kwanukan nan wadda Baba ya gama cin abinci shine ta ce wai bazata wanke ba, ni kuma na ce mata ai ita ke da aikin waye zai wanke idan ba ita ba?, shine kawai ta ɗaga hannunta ta sharara min mari"
"Gaskiya ne Ummi kin riƙa kin zama riƙaƙƙiyar kuɓewa, har kin isa a kin kai a kawo wani aiki a cikin gidan nan ki ɗaga hannu ki ce zaki mari Safiya. Wai idan kin gaji da aikin mi yasa bazaki fiddo da miji ayi miki Auren ki bar gidan gaba ɗaya bane?, ai shine kawai zaki daina aiki a cikin gidan nan idan kin tafi naki gidan, amma muddun kina zaune a cikin gidan kuwa dole ne kiyi kiyi aiki wallahi, idan fitsari banza ne Kaza tayi mana wai mu gani"
Wani baƙin ciki ne ya turnuƙe Ummi zatai magana sai kuma tayi shiru jin wani irin malolan baƙin ciki daya riƙe mata maƙoshi.
"Kiyi magana mana ai dai-dai nake dake a cikin gidan nan wallahi"
Ammi ta faɗa tana banka mata wani banzan kallo.
Tasan Mama tana jin komai amma bazata taɓa fitowa ta shigar mata ba, ta rasa wane irin hali ne da Mamar tasu.
"Wuce ki tafi kawai kuma dole ko taƙi ko ta so dole ta wanke kayan ub*an wani zaiyi mata aikin ne?"
Wucewa Safiya tayi tana juyowa tayi ma Ummi gwalo, kuma ta gani wani irin murmushin daya fi kuka ciwo kawai ta saki tana duƙawa ta wanke kayan kawai ta tashi bar tsakar gidan da sauri dan bata so wani abu ya ƙara haɗata da su Ammi ɗin.
Tana shiga taga Mama a zaune tana jan carbi, a hankali ta zauna a kusa da ita, tana ƙoƙarin shanye hawayen da ta riƙe tun a waje suka sami nasarar zubowa akan kumatunta, ta riƙe hannun Mama ta ce.
"Wai mi yasa hakan ke faruwa damu ne Mama?, muma fa ba'a son ranmu muka kai har yanzu ba bamuyi auren nan ba, wallahi Allah munfi ku so muyi mu matsa daga kusa daku"
Wani irin kallo Mama ta jefa ma Ummi daya sa Ummi yin ƙasa da kanta.
"Ke har kina da baƙin magana ne Ummi?"
"Amm.....
Ɗaga mata hannu Mama tayi tana sake kallonta sosai ta ce.
"Kin riga kin san babu irin damar dake baki samu ba a rayuwar nan, kin san irin Maza da yawa tun kan ki kai haka yadda suke mugun sonki da son aurenki, amma a can baya kikai ƙimeme kika hana, kika ƙi bawa kowa dama, ni ada can bayan ma na ɗauka ko aljanu ne dake, ashe iskaci ne kawai, ai dama wani lokacin shi Allah zaita baka dama ne kai kuma kana wasa da ita, yanzu ina Mazan suke Ummi?"
Kuka mai sauti kawai Ummi ta saki, domin gaskiya Mama ta faɗa, sosai tayi wasa da damarta, bata jin duk gidansu wani yayi farin jinin Samari irinta, a lokacin da tayi tashen samari baya ita duk gidan nasu, amma ta rasa miye ya shiga kanta tayi ta wasa da damarmakin da Allah yayi ta bata, ta samu dama ba ɗaya ba ba biyu ba.
"Hmm ai idan dai kuka ne Ummi yanzu kika fara ma, amma idan zaki tsaida hankalinki waje ɗaya ki fiddo da miji kamin Babanku ya fara gajiya da ku ya bada ku sadaka wallahi daga ke har Salma ɗin"
"Haba Mama kiyi mana addu'a kawai"
"Ai addu'a yadda nake maku ma ni banawa kaina bari kinji in gaya miki. Na dai gaya miki gobe-goben nan ki shirya zaki wuce Kano karma ki ce ban faɗa miki ba"
"Wai yanzu Mama dole sai naje Kano ɗin nan?, wallahi Allah bana son zuwa gidan nan na Aunty Binta"
"Kyayi da wani"
Mama ta faɗa tana miƙewa ta wuce ta, ta barta a nan.
Jiki a sanyaye Ummi tayi ƙasa da kanta tana ɗan zamewa a hankali ta kwanta a ƙasa tana zurfafawa cikin tunani akan rayuwarsu ta baya tada wuce.
***************"Kinga Aunty Ummi wallahi gayan nan yayi Over a dai yadda Ya Muhmd ke gaya min shi, dan Allah kar ki ce shima baki sonshi"
Gyara tsayuwarta Ummi tayi tana duban Salma ta ce.
"Nifa baiyi min ba Salma, idan har mijin nan nawa ya zo zanji fa ina sonshi amma wannan kam a'a gaskiya baiyi ba"
"Ikon Allah yanzu miye aibun Sadiq Aunty Ummi?"
"Bashi da wani aibu Salma bana son nashi ne kawai shikenan"
"Anya baki da motsi a saman kanki ba kuwa?"
Wani dukan wasa Ummi ta kai ma Salma tana gocewa da sauri ta miƙe daga inda take tana ƴar dariya ta ce.
"Ai gaskiya ce, ya za'ai ke kullum baki son kowa, to ma wai waye zaki so ne?"
Shigowar Mama yasa Ummi yin shiru.
Kallonsu tayi ta ce.
"Shima wannan ɗin da Yayan naku ya haɗaku baiyi miki ba ko?"
Juya ƙeya tayi tana turo baki ta ce.
"Haba Mama kin gansa kuwa da wani ƙaton ciki, ni gaskiya bana sonshi bai min ba"
"Hmm yayi miki kyau ai, amma wallahi ku duka ku sani idan har na gaji zan bar maku gidan ne, sai ku zauna ku tare kuda Mahaifin naku, dan naga shima shike ƙara ɗaure maku gindi ai"
Shiru sukai gaba ɗaya kansu a ƙasa tana gama faɗar haka ta wuce parlo ta barsu a ɗaki daga parlon suna jin yadda take mita tana ƙara cewa.
"Shi dai mutum idan har yayi wasa da damar shi ai zai gane kuransa, wata damar dai sau ɗaya a rayuwa take zuwarma mutum wallahi"
Su duka ba wadda yayi ƙoƙarin ƙara magana dan sun san Mama idan ta kama mitar nan sai Allah kawai.
Shigowar Ya Muhmd ne yasa ta ɗan yin shiru suna iya juyo muryarsa yana cewa.
"Wai yanzu tsakani da Allah Mama haka Ummi tayi ma mutunen wulaƙanci?, wai fa kai tsaye ta nuna masa bata ra'ayinsa fa"
"Yo ai Muhmd kamar baka son yaran nan ba ai basu da hankali da tunani, garama Salma, amma kaga Ummi, kwata-kwata bata iya tafiyar da mutum ba, ai ko baka son mutum ba ka sanar dashi a nan take ba, sai ka lallaɓasa ku rabu lafiya, amma da yake bata da wayo duk bata iya wannan ba ita"
Daga can cikin ɗaki Ummi ta kumbura fuska kamar zata saki kuka ta ce.
"To ni Mama kawai sai nayi ta yaudarar mutum da soyayyar ƙarya?, gara kawai na gaya masa a nan take karma yasa ka ran son nashi nake"
"Dalla gafara can rufe min baki, shashasha marar wayo, ai kinyi ma kanki wallahi"
"Hmm ai Mama wallahi ba ƙaramar asara tayi mana ba, Abuja fa zai aje ta Mama, harfa alƙawari aiki yayi min da anyi bikin nasu zai bani aikin, amma yanzu tayi mana baƙin ciki"
"Ai tayi ma kanta, ni wallahi dama ba ita ya ce yana so ba dama Salma ya ce yana so"
"Tabɗi jam ai wallahi itama haka zata ce masa, duk fa halinsu ɗaya Mama"
"Ai gara Salma nasan ita bazata gaya masa kai tsaye bata sonshi ba, zata lallaɓasa ne koda bata son nashi su dai rabu lafiya, amma fa ita Ummi kowaye ya ce yana sonta kai tsaye take sanar dashi itafa bata ra'ayinsa, wai a haukanta sai dai kawai a rinƙa gaisawa, ko suyi abota da shi, baccin kina hauka wata rana ma hatta mai abotar zaki nema ne ki rasa muddun bazaki shiga hankalinki ba wallahi"
Daga cikin ɗaki Ummi ta taɓe baki tana kamo hannun Salma ta ce.
"Ke yanzu nan sai ki yarda a ƙaƙaba miki wannan mutunan?"
"To Aunty Ummi miye ne dashi na abun ƙi wai?"
"Hmm lallai to in gaya miki duk yadda Ya Muhmd ke faɗa miki shi ba haka yake bafa. Wai kin gansa da wani ƙaton ciki gashi ance har aure garesa da ƴaƴa manya, ina zan kaisa ni?, inaaa wallahi bazan iya ba"
Jikin Salma ne yayi wani irin sanyi itama sai taji bazata iya auren nasa ba.
Suna iya juyo yadda Mama keta ruwan masifa Ya Muhmd na ƙara zuga ta......
*Wannan book ɗin na kuɗi ne Free pages zai tsaya daga na 10 insha Allah, zaki iya saka kuɗinki a turo miki complete nasa akan Naira ɗari biyar kacal #500*
Account number *** Fatima Rabi'u Opay Bank.
Shaidar biya ***