MUGUN ICCE

Episode 8

by @zahraroyal

*MUGUN ICCE*

*Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSO........*

PAGE 8

*UMMI POV*

"Wai Ummi baku shirya ba har yanzu?"

Da sauri Ummi ta shiga ɗaure kallabinta da yayi saura, tana ƙoƙarin saka gyale, tayi kyau sosai ta dubi Salma dake saka takalmi tana cewa.

"Wallahi fa Mama tun ɗazu ita nake jira"

"To ni nayi gaba ku iske ni bakin hanya, kuyi sauri kuma"

Mama ta faɗa tana ficewa daga ɗakin.

"Kiyi sauri dan Allah Aunty Ummi"

"Muje karki cinye ni ɗanya. Nifa da Mama ta biye min baza ni wani biki ba ni wallahi"

"Wai mi yasa ke baki son mutane ne?, komai akai miki ba'a iya ba"

"To ƴar iya, baki ji jiya ƙawar Mama ta kira ta ba suna maganar bikin nan na ɗiyar ƙawarsu a Kankia?. Harda gaya mata matsala ta, wai ta ce mata ta rinƙa tahowa damu wai ko za'a dace a wajan biki mu samu miji, jifa wata magana dan Allah?, nifa ko bana son haka wallahi, ita kuma Mama ta wani biye mata"

"To Aunty Ummi miye a ciki kika sani ma rabon samun mijin zai kai ki bikin nan, kin san wata ko wani a bikin wasu suke samun nasu abokan zaman ai"

Taɓe baki Ummi tayi suna idasa fitowa daga cikin ɗakin nasu. Suna fitowa suka iske Ammi da Safiya a tsakar gidan suna zaune.

Sunyi ma Ammi sallama a sama-sama ta amsa tana binsu da wani kallo, basu damu ba suka yi gaba dan sun saba da irin hakan daga gare ta dama.

"To wai su nan ina zasu je ne Ammi?"

Faɗin Safiya tana bin bayansu da kallo har suka ɓace ma ganinsu.

"Yo waye ma ya sanar masu ne?"

"Daga ganin wannan gayun dai ƙila biki ne zasu je"

"Hhhh to ikon Allah yanzu kuma ita Nadiya ta fara zuwa da ƴaƴanta biki kenan?, ko duk neman mashinshinin ne haka?"

"Lahh ai ko shine ma Ammi neman mijin aure aka tafi"

Faɗin Safiya tana riƙe baki.

"Hmmm ayi mu gani dai"

Kawai Ammi ta ce tana sakin wani maƙirin murmushi na gefen baki.

"Wai tunda muka fito baki ga Ammi yadda take jefa mana kallon banza bane Aunty Ummi?"

"To sai miye?, na gani man, tayi da wadda zata yi ai. Matar can fa munafuka ce, a gaban Mama karki so ganin yadda take mana, bata taɓa nuna komai sai ta rinƙa nunawa kamar ita ce ta haifemu, tana wani nunawa kamar duk ɗaya muke da Safiya a wajanta"

"Ni na san hakan kuwa Aunty Ummi, ai gida ɗaya fa muke zaune da ita, kinga ita da Aunty Murja na rasa gane waye yafi wani iya munafurci"

"Lallai ai ita Aunty Murja ƴar kai tsaye ce, nan take, take faɗar abunda ke cin ranta, itafa wannan baka taɓa gane inda ta dosa fa"

"Allah dai ya shiga tsakanin na gari da mugu wallahi"

Faɗin Salma dai-dai lokacin da suka ƙaraso bakin hanya inda Mama take tsaye da Ya Muhmd dake son tare masu Mota.

"Mi kuka tsaya yi ne a gidan?, shiru kunje kinyi wani zamanku Allah da an sami Motar da sai da kuji Mama ta tafi tabar ku"

Turo baki Ummi tayi tana magana ƙasa-ƙasa.

"Dama an samu ɗin wallahi kamin isowar tamu, da an hutar dani nikam"

Ta ƙare maganar tana wani juya ƙeya baya.

Girgiza kanta kawai Mama tayi dan tsaf taga bakin Ummi na motsi ta san kuma magana ce zata faɗa. Allah dai ya shirya mata Ummi, dama tunda ta nuna mata son zuwa bikin nan zata yi abunda yafi haka ne, bata son hayaniya kwata-kwata shi yasa sai baƙin rai take.

"Ya Muhmd mun ɗan tsaya sallama da Ammi ne"

Salma ta faɗa.

"To yayi"

Ya faɗa dai-dai wata Mota ta zo giftawa ya tsaida ita, anyi sa'a kuwa har Katsina Motar hayar ta nufa dan haka Ya Muhmd ya ce Kankia za'a kaisu. Suka hau gaba ɗaya kamin ya wuce ya tafi wajan aikinsa, dama kuma daga can ya fito shan iska ya hango Mama a bakin hanyar shine ya tako ya zo yana tsaida masu Mota.

Har suka isa Kankia Mamar na ɗan basu labarin ƙawar tata wacce sukai Makaranta a tare Salma ta gane ta, ita ko Ummi tana dai jinsu ne a sama-sama.

Basu wani ja lokaci ba suka isa Kankia, ana sauke su suka gangara da yake gidan kusa da bakin hanya ne.

Sun samu tarba ta mutumici sosai ƙawar Mama ɗin uwar bikin kenan sai nan take da su sosai taji daɗin ganin Mama da ƴan matanta.

Dandanan aka cika gabansu da kayan ciye-ciye.

Mama dake zaune da ƙawarta uwar bikin ta ce.

"Ni kam sister wa'innan duk yaranmu ne suka girma haka?"

Mama ta kallesu tana murmushi ta ce.

"Wallahi fa kin dai gansu nan"

"Ai ko tubarkallah sun girma wallahi Masha Allah. Amma fa gaskiya babbar can Ummi sunanta ko?"

"Haba Salamatu harkin manta sunan ƴar taki, kin san sunan mahaifiyar Babansu taci Bilkisu shine ake ce mata Ummi, ita kuma ƙanwar ai nasan bakin mance da sunan nata ba tunda takwararki ce ai"

Dariya suka saki a tare Salamatu ta ce.

"Ya za'ai na mance da takwara ta kuwa?. Kinga ba wannan bama wallahi na fara sha'awar haɗa Ummi da ɗan waje na Al'mustapha, kin san har yanzu baida aure. To da can ya samo Mata a can Kano ni kuma gaskiya ban aminta da yarinyar ba, shine yasa ma ya ɗan takatar da maganar tata, ni kuma yanzu tunda naga Ummi naga kamar zasu dace da juna"

Wani irin daɗi ne ya rufe Mama zuciyarta kamar an mata albishir da aljanna haka taji tana murmushi ta ƙara maida hankalinta ga Salamatu ta ce.

"Kina ganin shi zai so ta ne?"

"Haba ai duk abunda na ce ma Al'mustapha ina so to tabbas shi zaiyi, karki wani damu, kawai ita a sanar da ita, ai dai nasan bazata ƙi jini na ba"

Ɗan shiru Mama tayi, mita tuna kuma ta saki murmushi kawai tana cewa.

"Karki damu insha Allah kawai Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, ki bani number nashi saina bata ko kuma shi idan kuka gama magana sai ki bashi number ta, idan ya so da mun koma gida zanyi mata maganar insha Allah"

"Yawwa sister shi yasa nake yi dake, ai ni yaron na ya sami kamar Ummi ai abun alfahiri na ne wallahi"

"Amma dai bata da wadda take so a yanzu ko?, ba wadda ya fito neman aurenta?"

Salamatu ta ƙara faɗa tana kallon Mama sosai.

Girgirza kai Mama tayi ta ce.

"Gaskiya babu kowa a yanzu, kuma ma koda akwai bai shigo gida ba, kinga kuwa ai ba an bawa na dawa na gida bai ƙoshi ba"

Dariya suka saki a tare harda tafa hannu.

Sun daɗe suna tattaunawa akan haɗa Ummi da Al'mustapha ɗin yadda zasu ɓillo ma al'amarin, bare Mama da take ganin sai ta miƙe tsaye sosai akan Ummi idan ba haka ba zata iya rusa mata komai, to ya zama dole a wannan lokacin sai tayi mata jan ido tukunna zasu shirya da ita......

*Wannan book ɗin na kuɗi ne Free pages zai tsaya daga na 10 insha Allah, zaki iya saka kuɗinki a turo miki complete nasa akan Naira ɗari biyar kacal #500*

Account number 8130479973 Fatima Rabi'u Opay Bank.

Shaidar biya ***