17
by @oumfatima33
💓MATAR MANYA💓
By
OUM FATIMA
GAJEREN LABARI
PAGE 17
BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM
........"Assalamu alaikum." Na furta sallamar ina kallon Baba Mari dake jefa min mugun kallon dake bayyana tsananin hassadarta a kaina. "Ina yini Baba, na same ku lafiya?." Na faɗa ina ƙarasowa ciki tamkar banga kallon banzar da take min ba nayi gaba abina ba in gyara takuna don in ƙara tura mata baƙin ciki don duk magan-ganunta sun shiga kunnena.
Bayanta ta raka da mugun kallo tana jan dogon tsaki tace "Gayyar tsiya gayyar bariki kawai!." Ɗan dakatawa nayi na juyo na sakar mata murmushin rainin hankali nace "Na gode Baba, koba komai ai ni barikin ta min rana tunda na tuba akan lokaci kuma ban yi wulaƙantar da ake so inyi ba sai nayi aurena nake zaune cikin aminci." Ai kuwa maganar ta shigeta ba kaɗanba don dama akan tsini take tana jiran wanda zai taɓata ta shiga ɓaɓatu da masifa ni kuma nayi shigewata ɗakin Mama dake jin duk abinda ke faruwa.
"Sannu Salamatu, wato dai ke bazaki taɓa canzawa ba ko? Nace ki daina kulata idan tana abinta amma ba kya ji ko?." Mama ta faɗa tana watso min harara. "Allah ya baki haƙuri Hajiya Mama." Na faɗa ina cire ɗankwalin Abayar dana naɗe kaina da shi na zauna su Sagir suna ta murnar ganina.
Gaisheta na shiga yi cike da girmamawa ta amsa min da sakin fuska sosai tana jin daɗin sauyin da take gani a tare dani na nautsuwar dana ƙara yi, sosai rawar kaina ya ragu tamkar ba Salma matar manya ba. Hira mukaci gaba dayi ni dasu Sadiq cikin farin ciki Mama tana sa mana baki. Kora su Sadiq tayi bayan na basu tsarabar chocolate dana kawo musu tace suje wasan su bayan ta ɗebi tsarabar dana kawo ta basu su miƙawa Baba Mari.
Bayan fitarsu Mama ta dubeni a tsanake tace "Meke damunki ne Salmatu?." Ɗagowa nayi na kalleta ina jin rauni na lulluɓeni amma na danne nace "Ba komai Mama, me kika gani?."
"Nice na haifeki na kuma raineki, don haka nafi kowa saninki. Duk da canzawar da kikayi hakan baisa na kasa hango damuwar da kike ɓoyewa ba a tattare dake. Shin da Mijinki kike samun matsala koda yan'uwansa, ko Matarsa?. Ta ƙare maganar cikin damuwa don tasan halin Salma tana da rawar kai sosai amma sai dai tana da rauni sannan kuma tana da wasu halayen masu kyau na tausayi da jinƙan wanda tafi, abinda ya faru da ita ƙaddararta ce da Allah ya jarabce ta da ita. Amma ko ita zata bada shaidar cewa ta sauya sosai bayan faruwar al'amurran don haka take binta da addu'a da fatan alkairi akoda yaushe.
Ajiyar zuciya na sauke ganin Mama ta tsareni da ido alamar tana jiran amsa daga gareni yasa na sadda kaina ƙasa nace. "Ba komai Mama kawai kewar gidane da rashin sabo a can ɗin, amma Alhamdulillah yanzu ya samo min mai taya ni zama da aikace-aikacen gidan bayan haka babu wata matsala ki kwantar da hankalinki". Ba don Mama ta gamsu da abinda ƴar tata ta faɗamata ba kawai dai ta ƙyaleta ganin bata son faɗar sai ta bita da addu'a kwai da nema mata sauƙin ko mike damun nata.
Ranar a gida na ƙarasa yinina nida Mahaifiyata da ƴan ƙannena, yayinda baƙin ciki ya kusa kashe Baba Mari tayi ta harare-harare tana yada magana amma ba wanda ya kulata. Ko kayan tsarabar dasu Sadiq suka kai mata korosu tayi da zagi tamkar zata dake su, koda Baba ya dawo naje na gaishesa ya amsa min da sakewa wanda hakan yasa na ƙara samun natsuwa sosai a zuciyata.
Da dare bayan sallar isha'i Alhaji ya aiko direba ya maida ni gida cike da tsaraba da nasihar da Iyayena suka yi min harda ɗan kukana na roƙi Mama ta bani Sadiq in tafi dashi tace bada ita ba. Haka na tafi cike da kewar ahalina. "Allah Sarki gida mai daɗi." Na furta a hankali lokacin da muke tafiya zuwa gida.
Koda na koma wanka kawai nayi da yake naci tuwo a wurin Mama shi yasa banci abincin da Baba Attine ta gabatar min ba muka ɗan taɓa hira kawai kafin kowa ya shige ya kwanta.
_____________&
Zaune ya sameta a bakin gadonsa sai cika take tana batsewa, a matuƙar fusace take da Alhajin don tunda suka fito shida shegiyar yarinyar da kallo ɗaya taji ta tsaneta. Hankalinta kasa tsayuwa wuri ɗaya yayi don haka bata wani daɗeba tayi musu sallama ta wuce ita kaɗai banda ƴanmatan da suka ce su ba yanzu ba.
Gida ta wuce kai tsaye tana ƙoƙarin kiran wayar Alhaji amma bata shiga don suna fitowa ya sakata a airplane mode don yasan dole sai ta kira saboda ya lura da yanda take watsa masa wani mugun kallo tunda ta ganshi da Salma. ai kuwa ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba don haka ta nufi gidan a fusace tana jiran dawowarsa ta sauke masa buhun tijarar data tanada masa.
Alhaji Murtala dala kuwa bai dawo gidan ba sai da dare yayi sosai kusan 11:00 sannan, sai dai yana buɗe ƙofar ɗakin nasa ya shigo da sallama yayi turus ganin Hajiya Fatsuma zaune saman gado tana kaɗa ƙafafu cike da fusata. Ƙin kwanciya tayi tace sai ya dawo ya faɗa mata me yake nufi a kan waccan yarinyar, ko su Malika da suka dawo har suka gama zaman kallonsu suka haye sama suka kwanta bata fito ba. Har su Taufiq dake kanann yaranta korasu tayi ɗakunansu tace suje su kwanta ita kuma ta zauna zaman jiransa don ta rantse ko ƙarfe nawa zai kai ba zata kwanta ba sai ta jira shi.
Dakewa yayi ya shiga takowa cikin palon yana ayyana cewar 'matar nan tana nan tana jirana tsabar masifa'. A zahiri kuwa murmushi ya ƙawata fuskarsa da shi ya nufe ta yana cewa "Maman yara har yanzu baki yi bacci ba?." A matuƙar fusace ta ɗago tana cewa.
"Oh dama jira kake sai nayi bacci ka shigo saboda ka san baka da gaskiya, to ina nan ina jiran ka kazo ayita ta ƙare don naga rawar kanka a kan yarinyar nan ta musamman ce!." Ta ƙare maganar a zafafe.
"Haba Maman yara ya zakice haka, kin san dai ba wata Mace da zan auro tazo ta fiki a wurina. Ai ke ta musamman ce ina aurensu ne kawai domin biyawa kai buƙata tunda Kinga ke ba iya jurewa kike yi ba." Yayi maganar cike da kwantar da murya da rarrashi.
"Kaga Alhaji ko mai zaka ce ba yarda zanyi ba kawai ka saki yarinyar nan don naga alama ita daban take da sauran yaran daka aura, don haka tun wuri ka sake ta ta ƙara gaba."
"To shike nan za'a yi yanda kike so, amma dai ki ɗan ƙara min lokaci in ƙara morar kuɗina sannan don ba ƙaramin kuɗi na kashe ba." Da haka da daɗin baki Alhaji ya samu ya lallaɓata ta haƙura ta ƙara masa lokaci kafin ta yarda suka kwanta, koda ya nemeta kuwa ƙiyawa tayi don tana cikin jerin matan da basa jurewa buƙatar Mazanensu amma sai azababben kishi. Haka dai ya haƙura ya kwanta yana mita a zuciyarsa da tunano irin abinda yake samu a wurin Salma.
____________★
Rayuwata taci gaba da tafiyar min a gidan Alhaji cikin godiyar Allah domin kuwa ba abinda ya canza daga dabi'ar Alhaji sai ma sabbi da nake gani kullum, sai dai nayi alƙawarin haƙuri da nuna juriya don ko Mama ban taɓa faɗawa halin da nake ciki ba. Ga azababbiyar Matarsa da yaransa da suka hana ni saƙat a gidan, don da gayya ƴanmatan suke shiryowa suzo har gidan suyi abinda suka ga dama ban isa in yi magana ba sai suce gidan Ubansu ne kuma shine ya sayi komai a gidan don haka ni ban isa hana su suyi abinda ransu keso ba.
Baba Attine ita ke tausata tana bani haƙuri a ko da yaushe, ranar da abin ya ishe ni nayi musu magana ranar naga tashin hankali domin kuwa rubdugu sukayi min Suda ƙawayensu da suka gayyato suka yi party a gidan, haka suka ƙure kiɗa a tsakiyar parlo suna tiƙar rawa sannan suka shiga kiching suka min kaca-kaca da Snaks ɗin da muka yi nida Baba Attine. Baƙin ciki yasa na kasa shanye wa na fito nayi musu magana shine fa suka min dukan tsiya sai da ƙyar Baba Attine data kira mai gadi suka ƙwaceni.
Itace ta taimaka min ta kaini sama bayan fitarsu nayi wanka ta gasa min jiki sannan na kwanta zazzafan zazzaɓi ya rufeni dole ta nemo paracetamol ta bani na sha. Koda Alhaji ya dawo ya sameni a haka ya tambaye ni abinda ke faruwa kuka kawai na saka masa don na san kona faɗa masa iyaka ya bani haƙuri tunda ba yau suka saba yi min ɓarnar ba na faɗa masa baya ɗaukar wani mataki, sai dai dukan da suka min yau shi yafi komai ƙona min rai.
Sai da ya matsa na faɗa masa abinda ya farun, sosai naga damuwa a saman fuskarsa sai dai iyakarta nan don na san ba abinda zai yi saboda tsoron Matarsa yake. Ai kuwa haƙuri ya shiga bani sannan yace in tashi ya kaini asibiti. Tashi nayi ba musu na zura dogon hijabi muka wuce Baba Attine na mana a dawo lafiya.
An dubani sosai an yi min duk abinda ya dace a asibitin sannan aka bani magani muka dawo gida zuciyata tamkar zata kama da wuta tsabar baƙin ciki.
Tun daga wannan lokacin na canzawa Alhaji fuska saboda naji matuƙar zafin rashin ɗaukar matakin da bai yiba akan abinda yaransa suka min saima matarsa da tazo har gidan tayi min tijara ta kuma jamin kunne akan shiga harkar yaranta akan ko mi zasu yi a gidan tunda gidan Babansu ne. Alhaji yana gidan lokacin da tayi wannan tujarar amma ya kasa yin komai sai haƙuri daya shiga bata abinda yayi matuƙar motsa zuciyata har na kasa daure wa na saki mugun tsaki na haye sama na barta tana ta bala'i.
Koda na shige cikin bedroom ɗina faɗawa nayi saman gado na fashe da matsanancin kuka wanda nake jin zafinsa a cikin ƙirjina tamkar zai babbake da wuta tsabar ɓacin rai. Wace iriyar lukutar masifa ce wannan? Wace irin rayuwa ce wannan na saka kaina a cikinta, nida nake hango tarin jin daɗi, farin ciki da tsan-tsar kulawa a gidan Alhaji amma tunda na shigo saɓanin haka nake gani. "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un! Allahumma ajirni fiy musibatiy wa akhlifni kairan minha." Na shiga mai-maitawa da ƙarfi har sai da na samu natsuwa. A can ƙasa kuwa ban san ya suka ƙareba don tun ina jiyo hayaniyarta har na daina jiyowa ban san yanda aka yi ya fitar da ita daga gidan ba.
Kwana biyu da yin wannan rikicin tafiya ta kama Alhaji zuwa Lagos don haka yace in shirya mu wuce tare. Ban yi musu ba na shirya muka wuce don har ga Allah zaman gidan ya isheni ina buƙatar matsawa in sha iska.
Ashe bada sanin Matarsa ya tafi dani ba don haka lokacin da ta gane tayi masifar shaƙa tayi ta bala'i ta kuma yi aniyar sai ya sake ni.
A can Lagos kuwa Alhaji shaƙatawarsa ya riƙa yi hankali kwance domin kuwa dalilin tafiyar dan ya huta sosai shi yasa ya taho da Salmar ba tare da sanin Matarsa ba, don ya san matuƙar ta sani bai isa ta barshi ya tafi da ita ba saboda da azababbiyar matace mai masifar kishi.
Satinmu ɗaya a Lagos na fara azababbiyar jinya irin wacce nayi a wan can lokacin dana samu ciki, don haka a wannan lokacin ma zuciyata ya zargi cikin ne dani saboda banga baƙon watana ba dama. Harga Allah nayi matuƙar farin ciki saboda haka kawai naji ina matuƙar son koma miye a cikin nawa, don haka koda Alhaji ya kira likita ya dubani ya tabbatar da zargina na cewar ina da cikine. Murmushi ne ya ƙwace min ba shiga furta hamdala a bayyane.
"Tambayar da Alhaji yayiwa Doctor ta cewar "Wane irin ciki kuma? Ba dai na haihuwa ba!." Ita ce tasa na É—ago na zuba masa ido zuciyata na tsits-tsinkewa da yanayin da nake hangowa a saman fuskarsa na tashin hankali da rashin jin daÉ—in labarin.
"Eh ƙwarai kuwa Alhaji da buƙatar ka kawo ta asibiti ayi mata scanning don sanin kwanakin cikin ma." Saƙare Alhaji yayi bai ƙara magana ba har likita ya gama abinda zai yi ya rubuta magun-gunan da zan buƙata ya tafi bayan ya mai-maitawa Alhaji cewar yafa kaini asibiti.
Jagwaf Alhaji ya zauna saman sofa ɗin dake cikin ɗakin da muke yana dafe kansa, ruɗu mamaki da tunanin yanda akayi na samu cikin bayan da kansa yake saka min ƙwayar hana ɗaukar ciki a abin sha kuma a gabansa nake sha. Kasa riƙe abin yayi a ransa sai da ya furta cewa "Taya aka yi kika samu ciki bayan ƙwayar hana ɗaukar ciki da nake zuba maki, kuma kike sha?."
A matuƙar zabure na miƙe zaune ina cire ƙarin ruwan da aka jona min nace. "Me kake faɗa haka Alhaji? Wace irin ƙwayar hana ɗaukar ciki nake sha? Yaushe? Kuma a ina?!.". Na ƙare maganar a haɗe kuma rikice.......