RUFAFFEN DUMA

chapter 17

by @khairatup01

RUFAFFEN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)

Karamci Writers Associations.

Wattpad:Khairi_muhd.
Arewabooks:Khairatup01.

17.


Washegari Alh.Danzaki da Alh. Shehu suka yi kyakywan kari da shafin Maryam Kabir. Ko ba  kama sunayensu ba sun san da su take. Suna da labarin an kama yaransu kuma basu je ba saboda ba sa son a gansu sai dai alamu sun na nuni da cewa Maryam ta san wani abu akan lamarin satar yaran da aka yi. 

Danzaki ya maimaita saƙon ya kai sau biyar yana share gumi. Kowa yayi zagi a kasuwa ya san da wa yake.

"An binne gaskiya da kuɗi sau da dama. Amma,wannan karon gaskiya za ta fito fili.Dukiya ba zata iya sayen shiru ba."

Saƙo na biyu kuwa cewa tayi;

"Idan ƴan kasuwa sun zama shugabannin laifi,alƙalamin jarida ya zama takobi. Muna bin sawunan kuɗi ,kuma ba da daɗewa a za a san waɗanda hannuwansu suka wanke...."

Ana ta kwament a fallasa ƙwan kowa ya huta da wari. Abubuwa kala-kala dai.

Danzaki ya ɗauko wayar sa da sauri ya danna kiran Shehu.

"Ka ga yarinyar nan ko?"

"Shehu akwai matsala fa ba kaɗan ba. Yarinyar nan muna mata kallon ƴar ƙaramar tsakuwa ashe ƙaton dutse ce da zata zame mana ciwo ido."

"Ni fa da girmana ba zan yarda abinda ya faru shekara huɗu baya ya faru da ni ba. Me amfani gwamnatin da take a aljihun mu in har ba zasu kare mu ba."

"Ka bar zancen a wurina.Zan aika yara kawai a ƙadamar musu a can a kashe su ba sai in suna nan za ayi kamen ba har aje kotu hr sirrin ya tonu ba?"

"Hakan zai fi amma yaya kake gani idan Boss ya san mun yanke hukunci ba tare da sanin sa ba?"

"Kai in muka biyewa Boss ɗin nan mu zamu kwana a ciki."

"Shi kenan ayi abinda ya dace."

"Hakan za ayi."

Da wannan suka ajiye waya.

*

Shiru kake ji babu wani motsin mutane. Aka ce dare mahutar bawa. Iska na kaɗawa, gari yayi shiru. 

Wasu mutane ne cikin baƙaƙen kaya sun kewaye caji ofis ɗin ƴan sanda inda aka ajiye ƴan bindiga. Ɗaya daga cikinsu ya katse wutar ofis ɗin ko ina ya yi baƙiƙirin.

Masu tsaro suka miƙe  tsaye, ƙoƙarin kunna fitilar wayarsa yake yi amma kafin ya kunna aka maka mai abu a tsakar ka ya sulale ya faɗi a wurin ya suma.
Ciki suka kutsa ga mamakinsu babu mutane ma a ciki. Da mamaki suke kallon junansu sai dai kafin su gane me yake faruwa suka soma jin jiniya daga waje. 

Motar jami'an operation Puff Adder ta iso.Tuni suka soma harbin na waje kafin suka kutsa ciki. Na cikin ma maida martanin wuta suke yi. Ofishin ya haustine,amma fa jami'ai sun shirya saida rayukansu amma ba zasu bari mugwaye su yi  nasara a kan su ba.

Jami'an basu yi ƙasa a guiwa ba sai da suka yi nasarar kama waɗanda suke da rai. 

DSP Hamza ya tsaya a tsakiya,ya duba waɗanda aka kama. 
Ya sarawa tunani da ƙwaƙwalwar Maryam shawarar ta tayi gashi sun samu nasara. Wannan ba ƙarmin ci gaban bincike ba ne. Ya kalli ogan maharan yace "Zamu ga inda wannan igiyar zata tsaya. Sai dai wannan karon ba za  a binne gaskiya da kuɗi ba."

Bayan anyi gaba da su ya kira Maryam ya gaya mata "Lissafin ki ya tafi daidai sun yi kuskuren kuma mun kama."

"Alhamdulillahi! Wannan ma nasara ce amma ba za muyi shagalinta da wuri ba sai mun jira an kama manyan. Zan shigo da safe."

"Allah Ya kai mu."

Washegari aka wayi gari da labarin farmakin da aka kai wa ƴan sanda daga alƙalamain Maryam Kabir. 

"Anyi yunƙurin kashe masu laifin da aka kama a caji ofis,amma ƴan sanda sun yi nasarar kare su kuma an kama maharan."

Su Shehu na cin karo da wannan labarin komai ya ɗauke musu. Tunaninsu ya cunkushe,sun gama yarda cewa daga yanzu komai zai iya faruwa da su.

A safiyar Maryam Kabir ta tafi caji ofis ɗin cikin nutsuwa amma zuciyarta na ta bugawa kamar gangar yaƙi. A hannunta wata ƴar ƙaramar jaka ce mai ɗauke da kayan aikinta na rubutu. DSP Hamza ya tarbe ta a bakin ofishin.

"Maryam mace mai azama da zafin nama, har kin iso kenan?"

"Ba zan iya zama ba ne."

"Mutanen da aka kama suna nan. Amma ki sani ba fa su shirya buɗe baki ba."

Maryam ta gyaɗa masa kai cikin ƙwarin guiwa  tace "Ni dai ina so in ji daga bakinsu. Idan sun san wata gaskiyar ta fito ta bakinsu."

"Ba matsala muje." Ya sa ta a gaba ya rakata ɗakin da aka tsare su.Ɗakin ƙamshin turɓaya yake yi. A ɗaure suke a  ƙasa idanuwansu zaka kalla ka gano zallar tsoro da fushi a cikinsu..

Wani saurayi daga cikinsu sanye da riga da jeans ya kalli Maryam yace "Wannan ai Maryam Kabir ce ƴar jaridar nan mai tone-tone."

"Ni ce."

"Kika saka aka ruguza rayuwar mu."

"Bani na ruguza rayuwar ku ba.Wanda kuke wa aiki shi ne ya ruguza rayuwar ku ,ya kuma jefa ku a cikin masifar da baku san iya zurfin ta ba."

Sai yayi shiru yana kallonta. Wani ne daga baya ya yi magana kana jin muryar sa zaka san dattijo ne. Da yawa-yawansu fa an jima ana harkar daba ne ko sata wasu kuma zafin talauci ne yake kai su ya baro su. Kujera ta ja ta zauna ta zaro littafinta da shuɗin biro ta ɗora akan tebur ɗin gabanta.

"Baba meye ribar ka a wannan aikin?"

"Yarinya mun miki kashedi tun farko ,amma baki ji ba."

"Ba wannan nake son ji ba. So nake ku kama min sunayen ogannin naku. Waye ya baku umarni kuma waye ya aiko ku? Ina buƙatar ƙarin bayani."

Dattijon yayi dariya yace "lallai kin cika mace mai jarumta. Mun haɗu da shi wanda ya bamu umarni a GRA ,sun bamu kuɗi, sun bamu mota sun kuma bamu makamai. Umarnin ɗaya ne mu kashe waɗanda aka kama kafin a je kotu."

DSP Hamza ya kalli yadda Maryam ke aikin da ya kamata su yi. 

"Maryam wannan zai zame mana hujja  kotu."

"Sunayen su zaka bani."

"Danzaki da Shehu."

Ta kalli DSP tace "Magana ta ƙare Yallabai. Shaidu uku kenan kuma kowa wannan sunan yake kamawa. A fitar da warrent a kansu kawai a kama su Yallabai tun kan su gudu." Miƙewa tayi ta fita daga ɗakin.

Bata kai ga fita ba ma aka turo mata saƙon barazana.

Maryam tayi murmushi ta kalli DSP tace 'Yallabai lamba ta fa ta fito."

"Maryam, ki tsaya ki daina wannan binciken ,idan ba haka ba za ki bi sahun waɗanda suka ɓace a baya."

"Ba kya tsoro Maryam? Lamarin fa ya ɗauki sabon salo."

Murmushin ta kuma yi ta saɓa jakarta a kafaɗarta tace "Ina son gaskiya ko da kuwa ni ce ƴar farar ledar da zata rufe rijiya."

*

Alhaji Danzaki da Alh.Shehu zaune a gidan gonarsu. Abin duniya ya ishe su. Basu taɓa cin karo da yarinya irin Maryam ba. Bata da tsoro kuma bata da shakku bare kuma ta san da ja da baya. 

"Kai." Shehu ya faɗa yana jijigaa ƙafafuwansa. 

Danzaki yace "Wallahi yarinyar nan yadda ka san mayu ne suka yaye ta ko suka shayar da ita. Kai yarinyar nan da ace ƴar sanda ce da fa an samu matsala ta iya bincike da ɗana tarko kamar wata wadda ta karanci fannin crimes."

"Ni da ko ta gama goge min hadda."

"Ta goge maka ko ta goge mana?"

Wannan tattaunawar ta faru ne bayan kiran wayar da aka yi wa Danzaki aka sanar masa da an kama yaran da ya aika. Kuma har sun zanta da Maryam.Har ana ƙoƙarin zuwa wurin magistrate a fitar da warren a kansu. Wannan labarin ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba duk wata dabara ta ƙare musu. Babu saƙar da basu ƙulla sun warware ba.

Shehu yace "Har yanzu fa ƙungiya bata neme mu ba ,bayan na san duk abinda yake faruwa sun sani amma ba a kira zama ba."

"Ka tuna abinda ya faru shekaru huɗu baya? Ka ga ƙungiya ya kare su ne? Kana kallo fa muka kulle idanuwan mu muka bari aka kama su ,yanzu suna ina ba suna gidan yari ba? Mu ma daga nan sai can babu mai ceton mu."

Shehu ya sauke numfashi mai nauyi yace "Duk da haka mu samu Boss mu ji ta bakinsa. Tashi zaka yi ka zo mu tafi gidansa kawai. Ya kamata a turo mutane daga Abuja su zo su shafe shari'ar tun kan ta shiga kotu sunanmu da maratabar mu su zube."

"Boss ba ya ganin kowa a gidansa. Kawai mu aika saƙon gaggawa ga ƙungiya a haɗa meeting a daren nan."

"Ka yarda da ni mu gwada zuwa kawai."

Suna buɗe ƙofa kuwa suka ci karo da fuskar ankwa tana lilo a gabansu a hannun DSP Hamza.

Suka kalli juna suka sauke ajiyar zuciya....

Ta faru ta ƙare....


*

Unguwar Gwari!
(Kaduna)

*White hall*

A cikin wani babban falo,manyan fuskoki ne zaune,kowanne da na sa muƙamin. 

Kamar koyaushe idan za a ayi irin wannan taron na manyan mutane yan ƙungiya. Akwai manyan mutane sosai. Akwai ƴan sanda, akwai ƴan jarida masu matsayi ,akwai ƴan majalisa masu faɗa a ji.

Ɗakin da duhu kasancewar an kashe fitilar ɗakin. Kowannensu gabansu akwai kofunan shayi. 

"Danzaki da Shehu sun shiga hannu,kuma DSP Hamza yana ta ƙoƙarin sai ya gano duk masu hannu a cikin lamarin.Idan ba a ɗauki mataki ba za a iya samun matsala a gaba wadda ta fi wannan." Bala Gata ya faɗa.

"Wato yarinyar nan Maryam barazana ce garemu duka. Duk wani tsohon aiki da muka rufe tana bi lallai sai ta tone shi. Ina tsoro kar ta koma kan tsohuwar tashar jirgin nan. In ta je nan ko ta gano wani abu a nan lallai za a samu haɗari. Kowannenmu yana cikin matsala da tashin hankali."

"Shehnaz me kike ganin za ayi?"

"Boss zan iya watsa labaran da take kawowa a matsayin ƙarya zan kuma iya karkatar da hankulan jama'a daga kan batun. Zamu iya cewa ma kamen Danzaki da Shehu kawa shiri ne irin na aikin siyasa da adawa hakan zai iya raba hankulan jama'a."

"Na san za ki iya

"Hon.ka ce wani wani abu mana tuntuni kayi shiru ka kame bakin ka ya kake ganin za ayi?"

"Ni a gani na kar ku nutsa kan batun fito da Danzaki ko Shehu. Saboda yin hakan zai saka shakku da alamar tambaya ga lamarin. Za a samu masu gaskiyar da zasu so tono abin daga tushe in kuwa aka samu idon wasu ko kuma aka samu mutane sun farga hankalinsu kuma ya dawo kan siyasar ƙasa za ku sha mamakin irin kayin da zamu sha."

"Kuma fa ka ce wani abu Hon. Ya kake ganin za ayi?"

"Kafin Paul akwai Abdallah yanzu yana ina? 

Akwai paul yana ina yanzu?

Akwai yaron da ya so ya kawo mana hari Yusuf yana ina?

Akwai smith shi ma yana ina?

To ku kwantar da hankalinku wacece wata Maryam? Bata isa ba Wallahi.Wannan fa labarin da jinin mutane bila'adadin fa aka rubuta shi. Ba zamu kashe ta ba amma zamu haɗa ta da wanda zai gama da ita cikin ruwan sanyi."

"Ta ya kenan?" Waziri ya tambaye shi.

"Rayyan! Ta hanyar Rayyan kaɗai zamu ci nasara a kanta. A saka shi ya cusa mata ƙaunarsa a ransa ta yadda zai yi mata illa a zuciya."

"Amma me yasa kake ganin soyayya zata saka ta karaya?"

"Idan kace zaka karya mace da ƙarfi sai ta koma maka jaruma sak. Amma idan ka karya zuciyarta,ka raba ta da ƴancin tunaninta ,ta zama tamkar tsuntsuwa mara fuka-fuki."

"Madallah da Hon. A takaice dai makircin soyayya ya zame mana makami."

Duka suka yi na'am da wannan zancen a haka aka tashi sun yarda sun yi sadaukarwar Danzaki da shehu.

*

Yana zaune cikin mota. Airport za shi duba wasu kaya da za a tura cin. Saƙo ya shigar mai ta wayar sa. Yana dubawa yaga hotuna ne na manyan ƙusoshi manyan mutane wanda dama ya san su. Amma bai san lamarin ya kai haka ba. Iska ya furzar a hankali ya maida wayar ya kulle. 

Fita daga cikin motar yayi. Ya isa kusa da wani  ba chana suka yi musabaha. Daga ƙarshe suka yi cike-cike suka a hannu suka kuma yin musabaha ciniki ya faɗa.

"Am. Mr. Hong ina neman wata alfarma ne a wurin ka." Muhammad Ya faɗa yana kallonsa. Da ke ya saka wannan machine ɗin a kunne wanda yake translating yaren mutane mabambanta.

"Ina jin ka Mr.Sageer."

"Akwai wani yaro da nake nema. Kuma an gaya mini yana ƙasar ku. Ko na ce magarƙamar ƙasar ku. Ina son a bincika min ko da gaske yana can."

"Ah! Don wannan ba wani abu ba ne, zan zuba yarana kan aikin sai dai ka sani zai ɗauki lokaci. Ka tura min bayanansa kawai zan duba lamarin."

Muhammad ya washe bakinsa yace "Thank you! Mr.Hong." 

Daga nan suka yi sallama ya shiga private jet ɗinsa ya tafi.

Muhammad ya zaro wata wayar daban ya yi danne-danne ya maida ta yana murmushi. A fili kuwa cewa yayi "Sauran ƙiris. Samun wannan shi ne zai samar min da matsugunni a cikin wasan yadda ya kamata.  Yana kuma ji a jikinsa lamarin ya zo ƙarshe."