RAMIN ƘARYA...

Chapter 83-84

by @amanarcool323

💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫



_WRITING BY AMANAR COOL_✍️



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



Page 83&84


__________Akan katifarsa ya zaunar da ita, kallon fuskarta ya yi da ke ɗauke da damuwa.

"Bab lafiya dai? Wannan damuwar ta meye?".

"Ya Haidar yanayin da naga Umma ne a ciki kamar tana cikin damuwa, kuma gashi ba lafiya ce da ita".

Saƙala hannunsa ya yi a wuyanta, ya saka ɗayan hannu ya tallafo fuskarta, ya tsura mata ido ko ƙiftawa baya yi. Sai da ta ji ta tsargu da irin kallon da yake yi mata ɗin, kafin ta ji ya ce "Kar ki damu, ta ji sauƙi sosai, in sha Allah za ta dawo normal". Ya yi maganar ya na haɗe fuskokinsu.

Afnan ta yi ƙoƙarin janye fuskantar ta ce "To Allah ya ƙara ba ta lafiya ingantacciya mai ɗorewa".

Ya amsa da Amin, ya na kuma kai hannunsa ya zagaye ƙugunta, ji ta yi ya sassauta ɗaurin zanin da ta yi ya tura hannunsa a ciki ya na wasa da jigidar ƙugunta.

Shiru ta yi masa kamar ba ta ji me yake yi ba

Jin da ta yi ya na ƙoƙarin wuce gona da iri, ya sa ta ce "Am Ya Haidar bari na zuba maka ruwan wanka, kaga yamma ta yi ba a nesa da kiran magariba".

Shiru ya yi mata, domin gaba ɗaya yanayinsa ya fara sauya, ci gaba da yin lalubensa ya yi tana jinsa ta kasa ce masa komai, sai dai gabanta na dukan uku. "Ya Haidar wai meye haka ne? Umma fa ba ta da lafiya, kuma idonta biyu, sannan kaga lokacin sallah na gabatowa".


Ƙala bai ce mata, sai hannunta da ya riƙo, ganin inda yake ƙoƙarin ɗora hannun nata ya sa da sauri ta ƙwacen hannunta. Dariya ya yi ya zo daidai saitin ƙunnenta ya na yi mata wasu surutai, lokaci ɗaya tsikar jikinta ta shi. 


Ida janyo ta saman katifar ya yi.


"Ya Haidar wai me ka ke ƙoƙarin yi ne?".


"Aikin lada mana, ko ba kya so mu samu ladar ne?". 


"Hmmmm" kawai ta ce


"Kinga ki saki jiki mu samawa jununmu farin ciki, kuma ga taren lada da zamu samu, ko da yake ma naga kina son abin kema, kawai dai kina ja mini aji ne, yanzu idan na ce ma ba zan yi ba sai kin damu ai".


"Ni wallahi ba na so, ba wani damuwar da zan yi, ka ma ƙyale ni ba na jin daɗi..." Ba ta gama rufe baki ta ji ya haɗe bakinsu guri ɗaya, tare da zuge zif ɗin rigarta.

Wasanni ya shiga yi mata, irin masu saurin kunna mutum da tsayawa a zuciya. Sai da ya tabbatar da ya kunnata matuƙa, babu yadda za a yi mai cikakkiyar lafiya ta iya jure wannan wasan ba tare da ta ji an ida isa zuwa matakin ƙarshe ba, sai ya mirgina gefe ya na mayar da numfashi, da ƙyar ya ce "Tashi ki zuba mini ruwan wankan da ki ka ce".


"Innalillahi wa'inna ilaihim raji'un, wannan wace kalar mugunta ce bawan Allah nan zai yi mini?". Afnan ta yi maganar ba tare da ta bari ya ji ba.


"Bab magana nake yi miki fa" ya yi maganar ya na dariyar ta ƙasa-ƙasa.

Haka kawai Afnan ta rasa me za ta ce masa, dan har ga Allah idan ya barta haka da ya kasaarata, kawai sai ta kama shishekar kuka. 


Dariyar da Haidar ke riƙewa ce ta fito fili, Afnan jin ya na dariya sai ta ƙara sautin kukan dan ta san da gayya ya yi mata haka.


Bai kuma ce mata ƙala ba, ya janyo ta jikinsa. Ya suka lula duniyar shillalo, ko da suka ankare har magariba ta gota, cikin sauri ya shiga banɗaki ya yi wanka, tare da yin alwala ya fito, kayansa ya saka ya fita a ɗakin. Itama Afnan wanka ta yi ta fito, ta maida kayan da ta cire sannan ta fita, sai dai ta kasa shiga ɗakin Umma, sai yanzu take jin wata irin kunya na kamata.


Umma ta taga ta ga Afnan tsaye, ta kasa shigowa ɗakin, murmushi ta yi ta ce "Ai ƙarya ki ke yi, ba wata kunyata da ki ke ji, tunda har za ku iya rufe ƙofa da yamma nan". Ta yi maganar tana dariya ƙasa-ƙasa.


"Afnan tsayuwar me ki ke yi ne a waje? Ki shigo na tashi ai, tukuna ma kin yi salla ne?".


Kamar wata munafuka Afnan ta shiga ɗakin sai sinne kai ƙasa take yi, darduma ta shimfiɗa ta tayar da salla.


Maryam na isa gida, ta labartawa Mama abin da ke faruwa.


Mama ta ce "Subhanallah amma dai jikin nata da sauƙi ko?" 


"Eh da sauƙi".


"To Allah ya ƙara bi da lafiya, in sha Allah zan je na duba jinkin nata". Maryam ta amsa da Amin 


"Mama ina ta so na faɗa miki na haɗu da wannan yaron mai wuyan Raƙumi".


"Ke Maryam wane yaro ne kuma mai wuyan Raƙumi?".


"Wannan takwalin Daudi ɗin, ɗan iska barbaɗaɗɗe, zamuna makaranta ni da Feena muka ganshi, wallahi na karta masa rashin, ai shi ya sa ya zo ya ce ya fasa aurena, shege da wani baki nasa kamar gada ta karye".


Mama ta ce Maryam Allah ya shiya mini ke, wai ke ina ki ka koye wannan halin ne? Ko da yake ai ba sai na tambaya ba, gaba ɗaya halin Umar ne da ke, yanzu da ku ka yi masa rashin kunya, ba kwa jin tsoron ya dake ku ne?".


"Haba Mama haka kawai sai mu tsaya ya dake mu? Ai idan ya kuskura ya dakan sai na je har gidansu na yi wa Babarsa kwalalon maganin ɓera kowa ma ya huta".


Duk yadda Mama ta so fuskewa sai da ta dara, ta ce "Allah ya kyauta, yawwa ɗazu ko Babanku Umar ya dawo".


"Ma sha Allah amma ko na ji daɗi, Baba Umar namu, sai anjima zan je na gaisheshi, lallai Mama ki ce gidan nan akwai ya ƙi, ina roƙon Allah yasa iyayen Daudu su kuma zuwa da zancen Zaliha a gidan nan, wallahi da kaina zan gaya masa komai, kuma na san idan ya ji ko gidan nan zai kama da wuta sai an yi auren nan, kin san fa duk bala'in Kawu Sanusi ya na shakkun Baba Umar, Gwaggo ma da kanta wani lokacin tsoronsa take ji, Baba Umar nawa, kai ina godiya da Allah ya sa na ɗaukko halinka, ba ma son rai ni". Haka Maryam ta shiga zuba kamar kanya. Mama sai kallon ikon Allah take yi.


Nan Mama ta gaya mata abin da ya faru ɗazun bayan dawowarsa, aikuwa Maryam kamar za ta taka rawa dan daɗi, ta san tunda har ya furta hakan, babu wanda ya isa ya hana faruwar lamarin sai Ubangiji.


Hajara tunda ta fita a gidan sai yanzu ta dawo, jiki duk ya yi tsame, an je yawo gurin Malam ita da ƙawarta Larai, domin ganin an janye maganar auren Zaliha da Daudu an mayar kan Maryam. Zama ta yi cike da farin ciki, saboda Malamin da suka je gurinsa ya tabbatar musu da zai lalata maganar.


Bayan sallar isha Maryam na zaune sai ga yaro ya shigo ya ce "Wai ana kira Zaliha inji Daudu". 


Da sauri Maryam ta ce "Wa ka ce ya na nemanta?".


Yaron ya ce "Daudu"


Ai Maryam ba ta san lokacin da ta kwashe da wata mahaukaciya dariya ba har tana riƙe ciki, ganin da ta yi Mama ta shiga banɗaki ya sa ta miƙe da ƙarfi ta ce wa yaron "Kai zo muje na nuna maka ƙofar su". Tana ji Mama na yi mata tare a banɗakin amma ta yi kamar ba ta fahimci komai ba ta fita.


Kai tsaye gurin Hajara suka nufa, Maryam na gaba yaron na biye da ita, suka shiga da sallama, kamar abin arziki Maryam ta ce "Inna ina Zaliha ne?" .


"Tana gurin Gwaggo lafiya ki ke neman da daren nan?". Hajara ta yi maganar tana hararar Maryam.


Maryam ta ce "Maida wuƙar Inna Hajara, ba rigima ce ta kawo ni ba, alkhairi ne yake tafe da ni, dama saurayin ta ne ya aiko kiran ta, shi ne yaron ya yi ɓatan hanya na zo na nuna masa, ashe ma ba ta nan, kai yaro zo na nuna maka in da take ka isar da saƙon".


"Ke tsaya wane saurayin ki ke magana?" Hajara ta tambaya, kafin Maryam ta ba ta amsa yaron ya ce "Daudu ne". 


Ya na faɗin haka suka yi gaba, Gwaggo na zaune, Zaliha na gefen ta, su Maryam suka shiga, Maryam ba ta ma tsaya bi ta kan Gwaggo ba, ta ce "Yaro gata nan faɗa gaya mata aiken da aka yi maka". Yaro ya ce "Wai ana kiran Zaliha inji Daudu". Ya na gama faɗa Maryam ta ce "Je ka ce masa gata nan zuwa". Juyawa ya yi ya bar gurin


"Gidan uwarki za ta je ne? Mara kunyar yarinya kawai, wato rashin kunyar ce ta ciyo ki shi ne ki ka zo za ki sai da halin ko? To ba za ta je ba".


"Ikon Allah yau ina ganin abin da zai kashe kakata, Gwaggo dan Allah zuwana gurin na kula ki ne? Ko kuma na yi miki rashin kunya ne? Ni fa gurin amaryar Daudu na zo, kuma wallahi maganar gaskiya bai kamata ki hana ta fita ba, wulaƙanci bai da daɗi, taya mutum ya zo gurin zinariyarsa a ce ba zai ganta ba?".


"Meramu ki fita daga idona" cewar Gwaggo 


"Haba Gwaggo ya za ki kira ni da wannan sunan? Gaskiya ba na so, ke kuma amaryar Daudus ki tashi ki je, ka da ki biyewa wannan tsohuwar ta ja miki asara, dan rasa saurayi kamar Daudus ba ƙaramar asara na ce". 


Kafin Gwaggo ta yi magana Baba Umar ya ƙaraso gurin. Cikin murna Maryam ta gaisheshi, ya amsa ya na sakar mata fuska, da tambayar ta ya karatu? Sannan ya dubi Zaliha ya ce "Ke Zaliha ba ki san kin yi baƙo ba ne? Gashi can a ƙofar gida ya na jiran ki".


Gwaggo ta ce "Ba inda za ta je".


"Akan me Gwaggo? Me yasa za ki hanata hita, ke tashi ki je ko yanzu na yi ball dake a gurin nan, kuma ki ka yi masa rashin kunya sai na zane ki". Tashi Zaliha ta yi tana jin kamar ta zunduma ihu, ta yi waje, Maryam ta juya ta koma ƙofar su.


Gwaggo na son yi wa Umar magana, amma ta san halin kafiyarsa ya sa ta yi masa shiru, har ya tafi ba ta yi masa maganar ba.


Zaliha na hita taga Daudu a tsaye ya cake, wandon atamfar roba ce a jikinsa da hula kalar wandon, sai ya saka rigar nan irin ta ƴan tauri, sai warin taba yake, ga tsamin hammata na tashi a jikinsa.


Cikin gabjejiyar muryarsa ya ce "Amarsuta barkar ki da dare".


"Yawwa". Ta amsa masa


"Yawwa na ce ba, ai an faɗa miki cewar ina sonki, dan ɗazu ma iyayena sun zo gidan ku har ance idan na shirya nan da sati biyu a yi aure, shi ne na ce bari na zo yanzu mu gaisa, kuma ina fatan zan samu karɓuwa a gurin Zalihatuna". Daudu ya yi maganar ya na yi mata dariyarsa mai kama da kukan jaki, shi duk a tunaninsa waye wa ce.


Zaliha banda hawaye babu abin da take yi, cikin tsiwa ta ce "Kaina ke ciwo bari sai jibi ka dawo". 


"Ashsha Allah ya ba ki lafiya, to ga wannan ko magani sai ki siya". Ya ɗakko ɗari biyu ya ba ta, ba tare da ta duba ba ta shige gida tana kuka. Hajara sai ganin ta ta yi kamar an jefo ta. "Ke lafiya kuwa?".


"Wallahi Inna ba zan aure sa ba, wai kinga yadda ya zo gurina kuwa?".


"Au wai dama shegeyar yarinyar nan da gaske take yi? Ni nazata tsokana ce ta zo yi, ai kuwa dai ki sha kuruminki in dai ina raye babu wanda zai aura miki wannan gantalallen yaron".

*****

Sharifa na kwance a ɗakin ta Dady ya shigo, gaisheshi ta yi tana jiran ta ji me zaice tunda Momy ta gaya mata cewar anci ta je asibiti kuma shi ne ya sanar da ita.


Zama ya yi a bakin gadon ya ce "Daughter"


"Na'am Dady".


"A ina ki ka san matar da aka kaita asibiti da ke?, ki faɗa mini gaskiya ba na son ƙarya".


"Dady na je gidan su ƙawata ne, shi ne ta ce na rakata gidan Auntynta, tom da muka je gidan ne na ganta a can".


"Ko da kuka je jinya take yi kenan?".


"A'a Dady muna shiga gidan tana ganin sai ta yi ƙoƙarin faɗuwa a gurin ta suma, shi ne muka kaita asibiti".


"Ok to za ki iya gane gidan?"

"Eh Dady"

"To ki shirya gobe mu je tare, kuma ka sa ki faɗawa Momynki".


"To shikenan Dady". Daga haka ya tashi ya bar ɗakin.


Haidar tunda ya fita bai dawo ba sai wajan ƙarfe tara da rabi, ɗakin Umma ya shiga ya yi mata sannu da jiki. Ta amsa masa, dubansa ya mai suwa gun Afnan da ta yi shiru saboda kunyar Umma take ji sosai, dan ta san sai dai shiru ne Umma ta yi musu amma ta fahimci komai, "Ke lafiyar ki kuwa?".

Shiru ta yi masa, dama ya san ba magana za ta yi ba. Dan haka ya ajiyewa Umma ledar da ya shigo mata da ita tare da yi mata sai da safe. Ya miƙe zai bar ɗakin kenan ya ji Umma ta ce "Afnan me ki ke jira? Ai sai ki tashi kibi mijin naki".


Afnan ji ta yi kamar ƙasa ta tsage ta shiga. Babu kunya Haidar ya ce "Ki tashi mana ana yi miki magana kin yi shiru".


Ƙin tashi ta yi

Umma ta kuma cewa "Afnan tashi ki wuce zan rufe ɗaki na ne".

"Umma a nan zan kwana" ta yi maganar da ƙyar.


Umma ta ce "Haba Afnan ai kin gama kwana a ɗakin nan, maza tashi ki bi shi".


Tashi ta yi cikin sanyin jiki. Haidar ya yi gaba ta bi bayan sa.

Umma ta yi dariya, ta ce "Marasa kunya kawai, ku je can ku ƙarata".


Amanar cool ce ✍️ 
***