Chapter 85-86
💫 *RAMIN ƘARYA....*💫
_WRITING BY AMANARCOOL✍️_
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*
Page 85&86
Me so daga farko ya yi following ɗin channel ɗin nan ***
________Washe gari da ƙyar Afnan ta iya fitowa daga ɗakin Haidar saboda nauyin Umma da kuma kunyar ta da take ji. Shi kam gogan ko a jikinsa, shi ne ma ya takura mata akan ta dena wannan noƙe-noƙen dan yanzu Umma ta fahimci komai.
Ya ce "Ni ba na son wannan kunyar da ki ke nunawa, bayan kema kina son zama a nan ɗin, me ya sa jiya baki ji kunyar ba sai yanzu?".
Ita dai bata tanka masa ba, dan ta san so yake ta tanka masa, ya samu damar yi mata ɓarin zance. Ta fita domin ta je gaisheda Umma.
Da ƙarfe takwas Alhaji Munir ya kira Abba, bayan sun gaisa ne, ya ce "Musa ka shirya yanzu zan fito da Sharifa ba na son mu ɓata lokaci ne, shi ya sa, kar a samu matsala, ya je can ganin da ta yi mana ya sa ta yi ƙoƙarin ɓuya. Sai dai kuma ina cike da fargabar idan ba matar wani ba ce, Musa ina jin tsoron na tarar da wani ya aure mini Aminata".
Abba ya ce "Kai mutumena tun yanzun zamu fita ne? Ina laifin zuwa ƙarfe goma".
"Musa ba za ka gane ba, dan Allah ka shirya kar ka ɓata mini lokaci, ganin zuwa na ɗauke ka".
Ya ce "To shikenan sai ka zo ɗin". Kashe wayar Munir ya yi, ya kira Sharifa a waya tana ɗagawa ya ce "Ki zo ina neman ki".
Ta shigo ɗakin da sallama ta ce "Good morning Dady". "Morning Daughter how are you?".
"I am fine".
"Yawwa ki shirya yanzu zamu tafi, kuma kar ki gaya Momynki in da zamu ko da ta tambaye ki, ki ce mata baki san in da zamu je mu ba". "To Dady bari na je na shirya ɗin"
"Yawwa yi sauri Allah ya yi miki albarka''
"Ina zaku je ne yanzu Oga?" . Ammi ta yi tambayar tana kallon sa. "Zan raka Munir wani gurin ne" . Ya ba ta amsa. Ta ce "Ok to Allah ya kai ku lafiya" ya amsa da Amin, ya na kallon cikinta da ya fara fito. Hannunsa ya ɗora akan cikin ya ce "Ya Allah ka sanya wannan cikin rabonmu ne, Allah nuna mini ranar da za ki haifo mini baby mai kama dake, Ubangiji ya sauke mini ke lafiya shalelena". Ya ƙarasa maganar ya na sumbatar bakinta.
Ammi ta buɗa baki za ta yi magana kenan suka ji ana yi musu norking, sai da ya ƙara shafa cikin sannan ya tashi ya je ya buɗe ƙofar, Hajiya Maimuna ce tare da Ummie, sakin fuska ya yi, ya ce "Hajiya barka da safiya an tashi lafiya?".
Shigowa ta yi ciki tana amsa gaisuwar da yake yi mata, Ummie ta gaishesu. Ammi ta yunƙura zaune cikin jin kunyar ganin da Maimuna ta yi mata babu hijabi, saboda fitowar da cikin jikinta ya yi. "Barka da safiya Hajiya, ya gida ya iyali?". Ammi ta gaisheta.
Baki buɗe Maimuna ke bin Ammi da kallo ganin ciki a jikinta, nan take ta ji gwiwarta ta yi sanyi. Duk tijarar da ta tashi da ita yau sai ta ji ta karaya, abin da ta zo yi sai ta ji ba za ta aikata shi ba, dama rashin haihuwar Zainab ne ya sa take tsangwamar ta, da kuma soyayyar da ɗan uwanta ke nuna mata ɗin. "Hajiya ana gaisheki fa" Abba ya yi mata magana.
Sai lokacin ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, mun same ku lafiya?".
Ammi ta ce "Alhamdulillah".
Maimuna ta ce "Musa ashe matarka ciki ne da ita baka gaya mini ba?".
"Hajiya ki yi haƙuri, kin san ba a son yawan magana ne idan cikin ya samu har sai anga wada hali ya yi, shi ya sa ban faɗa miki". "Haka ne, to Allah ya raba lafiya ya bada marayi mai albarka, sai ka kula da ita sosai, ke kuma banda dogon motsi, ki riƙa lallaɓa jikin ki". Ammi ta ce "To Hajiya in sha Allah nagode sosai".
Abba ya ce "Wai ina Sadik ne? Tunda kuka dawo bai zo gidan nan ba".
Ta ce "Ai kasan halin Sadik da rashin son hayaniya, ya fi so kullum ya na ɗakinsa, sai dai abokansa su zo nan gida su same shi".
Dariya Abba ya yi ya ce "Sadik manya, matar shi za ta yi fama da shi akan rashin maganar sa, sai dai ta wanni fannin za ta more miji dan akwai shi da sanyi hali, shi har yafi mahaifinsa sanyin halin ma".
"Hmmm rabu da shi, mace za ta shi ya yi magana dan ubansa, ni bari na zo na koma gida, dama yau na tashi da kewar ku ne, shi ya sa kaga nayo muku sammako a gida". Ammi ta kalleta kawai amma ba dan ta yarda ba, ta san duk yadda aka yi akwai abin da ta zo yi sai dai in fasawa ta yi.
"Allah Sarki Hajiyarmu maganin kukanmu, muna godiya sosai, Allah ya barmuna ke. Yawwa da ma ina son gaya miki wata magana ne".
"To shikenan ina jinka" cewar Maimuna
Nan ya gaya mata abin da ke faruwa, akan zancen Mudan da Huda da kuma Hasina, da kuma rashin amincewar Saratu akan zancen auren Hasina ɗin. Sannan ya faɗa mata hukuncin da ya yanke.
Ta ce "Amma dai Saratu ta ba ni mamaki yanzu duk yadda take da Turai amma ta iya yi mata wannan rashin arzikin? Sai in ta san akwai wani abin da suke aikatawa wanda bai kamata ba take gudun a yi wa ɗanta, amma dai koma miye ni ka yi mini daidai tunda ita ba ta san ya kamata". Tana gama faɗar hakan miƙe tare da yi musu sallama ta fita, ta biya sashen Saratu ɗin suka gaisa kai tsaye ta so ta yi mata maganar sai dai kasancewar tana sauri ne ya sa ba ta tsaya ba, ta fito.
A harabar gidan suka haɗu da Mudan, ya gaishe da Hajiya sannan ya ce "Sannu Hajiya Ummie mai indomie ya ki ke ya kuma cin indomie ɗin?".
Dariya Ummie ta yi ta ce "Yawwa sannu ya Mudan cin indomie na nan muna yi, sai ka zo na dafa maka kai ma kaci ɗin".
Dariya suka yi, ya shige sashen Mami ita kuma ta shiga mota suka bar gidan.
Sharifa ta shirya ta ce wa Momy za ta fita tare da Dady ne.
Momy ta ce "Ina za ku je ne da sanyin safiyar nan? Ko da na so anjima ki raka ni na duba jikin Hajiya".
"Momy nima ban sani ba, kawai ya ce na shirya zamu fita ne, Momy kin san fa ko da ba fita zamu yi da Dady ba, ni ba zan raka ki wannan gidan ba, ba zan iya da masifar Mama Asiya ba, komai kayi laifi ne a gurin ta, kamar mu ne muka korota daga gidan aurenta, ga in da aka yi mata abu sai ta zo wanda bai ji ba bai gani ba tana huce haushi akan sa". "Sharifa yayar mahaifinki ce fa, ki daina wannan maganar akan ta babu kyau".
"Momy naga kema fa ba raga miki take yi ba, itama Hajiya ai yanzu ne ta daina masifa, haka kwana ki dana je na ji tana yi wa Mama Asiya magana akan wai haƙƙin yarinyar nan yake bibinyarta, ni dai ban tsaya jin zancen ba na bar musu gidan".
Momy ta ɗan ɓata fuska jin abin da Sharifa ta faɗa, ta ce "Na ji to wuce ki ba ni guri, faɗi ba a tambaye ki ba". Fita ta yi ta samu Dady da kanshi ya ja mota suka bar gidan. Ya biya ya ɗauki Abba suka wuce.
******
Yau iyayen Daudu suka kawo kuɗin auren Zaliha, aka saka nan da sati biyu kafin Baba Umar ya koma za a ɗaura auren, hadda kuɗin gaisuwar iyaye da kakanni, wanda wannan shirin Baba Umar ne, saboda ɗai Gwaggo ta bashi goyan baya, ya bada dubu hamsin ya ce gasu nan na gaisuwar kakanni ne suka bayar, nan Gwaggo hankali ya tashi anga kuɗi, tuni ta fara sakawa Daudu albarka tare da bada goyon bayan a yi auren, Hajara ba ƙaramar hauka ta yi ba, kuma hankalin ta ya tashi sosai, ta shiga gaya wa Gwaggo baƙaƙen maganganu akan ita ba wanda ya isa ya aurawa ƴarta wanda ba ta so. Zaliha ma kuka take yi sosai kamar ranta zai fita.
Maryam da Bahijja suka koma sashen Inna Bilki suna dariya hadda shewa, saboda farin ciki Inna Bilki na taya su yi. Ta ce "Ai ni na ƙara ziga Babanku akan cewar ya dage sai an yi auren nan saboda haka suka yi wa Afnan sai bayan an ɗaura aure muka sani".
Dariya Maryam ta yi ta ce "Sai dai ke Inna Bilki tamu kina wuta ina biyarki da fetur, ai baki san me na yi masa a hanya ba da zamu je makaranta ni da Feena, muka ga ɗan iska shida zugar tambaɗaɗɗi irin sa, muka ƙare masa zagi ta uwa da uba, sai kin ga idon munafuki kamar agwagwa ta yi faci. Ai jin haushin hakan ne ya sa ya koma gurin Zaliha". Dariya suka yi gaba ɗaya Maryam ba ta rabuwa da abin dariya.
ita dai Mama ba ta ce ƙala ba, ta san Ubangiji ne ya fara turawa kura aniyarta, kukan da Hajara ke son ganin ta saka ta a ciki ne, Allah ya juya zuwa gare ta.
Afnan ta kasa sakin jiki da Umma saboda kunyar da take ji, ita kuma Umma ta yi kamar babu abin da ya faru, sai janta take yi da hira. A haka Haidar ya shigo da ledar da yayo cefane.
Zama ya yi ya ce "Umma hira ake yi ne? Lallai jiki ya yi kyau sosai, Allah ya ƙara lafiya mai inganci". Umma ta amsa da "Amin".
Ya ce "Ga cefane nan yau ina da waƴanda zan yi wa aiki, kuma da wuri zanje shi ya sa nayo muku abin ku da guri".
"Ok to shikenan Allah ya taimaka, ya bada sa'a, Allah tsare" . Ya amsa da "Amin". Sannan ya dubi Afnan ya ce "Madam zan wuce".
"Allah ya tsare ya kiyaye, a dawo lafiya".
"Amin ya hayyu ya ƙayyum" ya yi musu sallama ya fita, ya na fita ya ga mota na dunfaro ƙofar gidan, tsayawa ya yi ya na jiran su ƙaraso.
Suna fitowa daga motar kallo ɗaya ya yi musu ya gane su, sannan ga Sharifa da ya gani tare da Maryam, ƙarasawa ya yi cikin girmamawa suka gaisa, Alhaji Munir sai kallon Haidar yake yi, ya na ganin kamannin Hajiya a fuskarsa.
Abba ya ce "Ɗan samari ya gida? Ya kuma mai jiki da sauƙi?".
"Eh jiki da sauƙi Alhamdulillah".
"Ma sha Allah. Yau nace ba mai gidan ya na nan ka yi mana sallama da shi" cewar Abba
Haidar ya ce "Ai kusan ni ne mai gidan, daga ni sai Ummata da kuma matata ne a gidan".
Munir ya yi saurin cewa "Mijin Umman ka muke magana ka yi mana sallama da shi".
Haidar ya ce "Ai na ce muku mu kaɗai ne, ba ta da miji".
Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya Munir ya sauke, sannan ya ce "Dan Allah muna so kayi mana iso gurinta muna so zamu yi magana da ita" .
Haidar ya ce "To ba damuwa bari na je na sanar da ita, ke ina ki ka baro Maryam ɗin yau?".
"Tana gida" cewar Sharifa tana murmushi.
Haidar ya yi gaba Sharifa ta bi bayan sa. Su Umma suka ga Haidar ya dawo, Sharifa na biye da shi. Afnan ta yi tunanin hadda Maryam. Sai dai taga wayam. Sharifa ta yi wa Umma ya jiki, Afnan ta ce "Sharifa ke ce?"
"Eh Aunty an tashi lafiya?"
"Alhamdulillah".
Haidar ya ce "Umma kin yi baƙi, suna son ganin ki".
"Baƙi kuma su waye?"
"Mutanen da suka je asibiti ne".
Take annurin fuskarta ya ɗauke ta ce "Haidar ba na son ganin kowa, kar ka kuskura ka shigo mini da su a gidan nan" . "Umma dan Allah ki...." "Ka tashi ka bani guri Haidar". Umma ta faɗa da ƙarfi.
Amanarcool✍️
***