Chapter 89-90
💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫
_WRITING BY AMANARCOOL_✍️
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*
Page 89&90
________Hankalin Dady ya ƙi kwanciya tunda suka dawo yake tunanin yadda zai ɓullowa lamarin nan ya samu Amina ta saurara shi, inda ya ka ƙara yi wa Allah godiya samun ta da ya yi ba a matsayin matar wani ba. Shi har yanzu ya kasa sanin abin da ya faru da shi har ya manta da ita na tsawon lokaci, ya san dai Hajiya ta saka ya sake ta. To tunda ga lokacin bai sake fahimtar komai ba. Ya na cikin wannan tunanin ne kiran Aunty Asiya ya shigo wayarsa, ya na ɗauka ta ce ya zo Hajiya na neman sa yanzu. Ya amsa da to.
Da ƙyar likitoci suka yi nasarar tsayar da jinin.
Kasancewar Mami a ruɗe take ya sa ba ta je asibitin da aka bawa Huda maganin zubar da cikin ba ta wuce asibitin da suke ganin likitansu.
Gwajin farko Dr ya gane cewar maganin zubar da ciki tasha.
A tunaninsa ba da sanin Mami tasha maganin ba.
Shi ya sa ya fara yi wa Mami bayanin sanadiyyar zubar da jinin ba wai miscarriage ne ta yi ba. Abortion ne. Kuma ta zubar da jini sosai saboda haka sai an yi mata ƙarin jini.
Mami ta nemi alfarmar da ya yi shiru kada ya faɗawa kowa abin da ke damun Huda kawai dai ba ta da lafiya ne. Ya amsa ta da to.
Ta kira Abba ta sanar da shi halin da ake ciki, ya ce gashi nan zuwa asibitin.
Hajiya ta dubi Dady ta ce "Munir ina son yin magana da kai ne, nasan za ka yi mamakin abin da za ka ji daga bakina. Da farko dai ina neman yafiyar ka akan abin da nayi maka a baya. Ko ina matsayin uwa a gare ka nasan na cuta maka ko ince mun cuta ma ni da ƴan uwanka. Nasan haƙƙin ku kai da yariyar nan ba zai bar mu ba, shi ya sa Allah ya nuna mini ishara akan nawa ƴaƴan. Asiya na son mijinta ya na sonta amma dangin sa suka saka shi yi mata kishiya daga ƙarshe kishiyar ta yi mata asirin da ta koma tamkar mujiya a cikin jama'a, ta saka mijin ya sake ta tare da yi mata korar kare, ita ma ɗaya ƙanwar taka mai binka, kana ganin yadda uwar miji ta hana mata zama a gidan tasa ya sake ta. Ga auta ko shekara ba ta yi da aure ba ta fara yin ya ji saboda rashin mutunci da miji yake yi mata. Nasan wannan ba komai ba ne face abin da na yi wa ƴar mutane ne aka yi wa nawa ƴaƴan, kana son matar ka muka raba ka da ita, kuma haka bai ishe mu ba sai da muka ga mun mantar da ita kai. Dan Allah Munir ka ya fe mana, wallahi na yi nadamar abin da muka aikata, gashi yanzu ba lafiya ce da ni ba, da zanga yarinyar sai na nemi gafarar ta. Duk da nasan yanzu ba lallai ne ma tana raye ba". Hajiya ta ƙare maganar tana matsar ƙwalla.
Aunty Asiya ma haƙuri ta bashi ita da sauran ƙannen shi.
Dady shiru ya yi yana bin su da kallo, ya kasa magana jin cewar mantar da shi Amina suka yi, kenan asiri suka yi masa?.
Hajiya ta ce "Munir ka yi magana mana".
"Hajiya me zance? Ke fa uwata ce. Duk abin da za ki yi mini ai babu rashin yafiya tsakanina dake, sai dai ita yarinyar da aka zalinta ɗin, in dai ta nine na yafe muku". Ya yi magana yana jin ɗaci a cikin zuciyarsa.
Ta ce "Munir ina zamu ga wannan yarinyar? Ai yanzu ba ma lallai ne tana raye ba, wai ni a lokacin ba cewa ka yi tana da juna biyu?".
Dady ya gyara zama ya dubi Hajiya da kyau ya ce "Hajiya Amina na nan a raye, kuma a cikin garin nan take da zama. Sannan cikin da ki ke magana ta haife shi. Duk da ban tabbatar da hakan ba, amma a kamannin da na gani a fuskar yaron na san cewar ɗana ne, saboda gaba ɗaya kamanin ki ya ɗakko, kuma abin Mamaki sunan mahaifinmu ne da shi".
Da sauri Hajiya ta ce "Kai Munir ya aka yi kasan tana nan garin? Kuma har ta haifi cikin? Dan Allah maza ka kai ne inda take na roƙi gafarar ta".
Dady ya gaya mata yadda aka yi ya san Amina na garin. Da inda ya fara ganin ta, har zuwan da suka yi gidan. Bai ɓoye mata komai ba sai da ya gaya mata.
Ta ce "Ikon Allah dole ne ta ƙi saurarar ka Munir, kusan shekara ashirin da bakwai baka waiwayeta ba. Yanzu abin da za a yi ba dai kasan gidan ba? Sai na shirya da kaina muje tare, ina da tabbacin ni ba za ta ƙi saurara ta ba".
Jin abin da Hajiya ta ce ba ƙara min daɗi dady ya ji ba, nan ya yi zuba mata godiya.
Ya ce "Hajiya sai ki shirya gobe mu tafi".
Ta ce "To Allah ya kai muna rai" . Tana ƙara saka masa albarka.
Maryam yanzu hankalinta kwance ita da Mama, suna zaune Mama ta ce "Maryam tubda yanzu nasan inda ƴar uwarki take zaune. Zan kai mata sauran kayan ta dana siya mata, ɗazun nan ma aka ida kawo mini saura kayan da babu na ba da a sawo mata. Mahaifinku ma na ji yana maganar ya biya kuɗin gado, gobe zai tafi tare da ke sai a ɗauka a kai mata saboda shi bai san gidan ba".
Cikin Murna Maryam ta ce "Kai ma sha Allah amma na ji daɗin haka sosai, Mama yaushe za a kai mata kayan da ki ka siya mata ɗin?".
Ta ce "Na yi wa Bilki magana gobe idan Allah ya kaimu zamu je duba sirikar ta ta, daga nan sai mu wuce mata da kayan".
"To shikenan Mama Allah ya kai muna rai".
Ta amsa da Amin
Hajara tunda kawu Sanusi ya faɗa mata cewar Afnan na cikin garin nan da zama wani irin malolon baƙin ciki ya tokare mata zuciya, nan take ciwon hassadar ta ya motsa, ta fara saƙa mugunta kala-kala a ranta. Alwashin raba auren ta ɗaukar wa kanta, matuƙar ta gama magance wannan matsalar ta auren Zaliha da Daudu sai ta raba auren Afnan da wannan yaron.
Ango Daudu an fara shirye-shiryen aure yanzu kullum suna gidansu shi da abokansa, ana aikin gini, wani tsohon ɗakin ne a gidan ginar ƙasa ce, daya fara zubewa shine Daudu ya tada shida abokinsa suka ƙaro ɗibo ƙasa aka ta da gini. Ko filistar da suka yi irin ta jar ƙasar nan ce, sai ihu suke suna ganin sun burge.
****
Abba ya ƙarasa asibitin shi da Ammi, ɗakin da aka kwantar da Huda suka shiga, Abba ya ga lokaci ɗaya ta yi wata rama ta kuma fayau.
Ya dubi Mami ya ce "Me yake damunta ne haka ne lokaci ɗaya ta yi tashi wannan yanayin?".
Cikin alamar rashin gaskiya ta ce "Am am ni ma dai ban sani ba, sun ce dai ba ta da lafiya sai an yi mata ƙarin jini".
Abba juyawa ya yi ya bar ɗakin, kai tsaye ofishin dr ya je ya same shi, cikin girmamawa ya gaida Abba. Zama ya yi ya ce "Dr me yake damun Daughter ne da lokaci ɗaya za rame haka?".
Ya ce "Alhaji duk da Hajiya ta hanani faɗar abin da ke damunta amma kai ba zan ɓoye maka ba, maganar gaskiya Alhaji Abortion ne ta yi".
"What! Abortion Dr what do you mean?".
"Alhaji Huda ba miscarriage ne ta samu ba. Abortion ne ta yi".
Cikin ruɗani Abba ya ce "Dr kana mini zancen zubar da ciki, wai yaushe Huda take da ciki ne balle har ta kai ga yin Abortion?".
Dr ya ce "Alhaji kana nufin Hajiya ba ta sanar da kai ba? Ai kusan 2 week na je na duba jikin Huda da ba ta jin daɗi nan naga tana ɗauke da juna biyu, kuma tun a lokacin na sanar da ita".
Abba ya ce "Me yasa ni ba ka sanar da ni ba?".
"Alhaji na yi tunanin za ta sanar da kai ne".
"Ok to yanzu me ye abin yi?" Abba ya yi tambayar cikin damuwa.
Dr ya ce "Yanzu babu ciki ya fita, amma tana buƙatar a yi mata ƙarin jini saboda ta zubar da jini sosai".
Abba ya ce "Ok to shikenan sai a je a duba wanda ke yi mata a saka mata, kuma a tabbatar da lafiyar sa kafin a saka mata shi". Dr ya amsa to, sannan Abba ya bar ofishin ya koma ɗakin da Huda take.
Tunda ga yanayin kallon da yake bin Mami da shi tasha jinin jikinta, gashi tana cikin wani ruɗu na ganin kamar cikin ne a jikin Zainab. Shiru ya yi mata bai ce mata ƙala ba, aka sakawa Huda jini. Dr ya ce nan zasu kwana sai zuwa gobe.
Sai dare Abba da Ammi suka koma gida. Da Abba ya faɗawa Ammi abin da likita ya ce ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba, sai da ta yi ƙwalla na tausayin Huda da kuma wannan ƙaddarar data afka mata. A dare Dady ya kira Abba ya sanar da shi komai da suka yi da Hajiya. Abba ya jinjina girman al'amarin, sannan Dady ya kuma sanar da shi batun zuwan da Hajiya za yi gobe, kuma ya na son a yi tafiyar da shi, Abba ya ce "To ba matsala Allah ya kai muna rai".
Turai ta yi alkawarin matuƙar tana numfashi Huda ba za ta aure Mudan ba, wannan ma ai zancen banza ne. Wayar Malaminta ta kira sai dai ta ji wayar aka she, tsaki ta yi tare da ajiye wayar tana jin komai Saratu take ji da shi ba ta isa tasa Mudan auren Huda ba, kuma wallahi idan ta matsa mata sai ta tona mata asiri.
Washe gari misalin ƙarfe sha ɗaya Dady ya je ya ɗakko Hajiya, su Aunty Asiya sun so su bisu amma ya ƙi amincewa da hakan, ya biya suka ɗauki Abba a gida. Sai da suka fara biya wa asibiti duba jikin Huda, sannan suka wuce zuwa gidansu Haidar.
Mama ta gama shirin ta ita da Inna Bilki suka shedawa Gwaggo inda za su je, ta yi ta masifar basu tashi gaya mata ba sai yanzu, kayan gado ma da Baba ya sanar da ita masifa ta yi, napep suka tara aka saka kayan a ciki suka tafi tare da Maryam suke. Dan Baba cewa ya yi ta baɗa masa sunan unguwar kawai ta faɗa masa sannan kuma ya karɓi lambar Haidar.
A ƙofar gidan motar su Dady ta tsaya, fitowa suka yi, a daidai nan napep ɗin su Mama ta ƙaraso, suma fitowa suka yi mai napep ɗin ya sauke musu kayansu ya tafi. Mama suka gaisa da Hajiya. Maryam sai kallon Dady take yi ganin yana kama da Sharifa sosai, shi kuma Abba kallon sani yake yi wa Mama.
Maryam ta fara ɗibar kayan ta nufi cikin gidan da su, su Mama suka ɗauki sauran suka bi bayanta Hajiya ma ciki ta shiga
Maryam ta shiga da sallama Afnan na ɗakin Haidar ta ji muryam Maryam da sauri ta fito, Umma ma na ɗakinta ta fito, da murna suka tarbe su Afnan ta rungume Mama cikin farin ciki.
Gaban Umma ne ya yi mummunar faɗuwa ganin fuskar da ko a mafarki ba za ta taɓa mantawa da ita ba.
Amanarcool ✍️
***