RAMIN ƘARYA...

Chapter 91-92

by @amanarcool323

💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫



_WRITING BY AMANARCOOL_✍️



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



Page 91&92


__________Afnan ta ja su Mama zuwa ɗaki ba tare da sun lura da sauyawar da fuskar Umma ta yi ba. Da ƙyar Umma ta gaishe da Hajiya da ke tsaye tana kallon ta.

Amsawa ta yi cikin sakin fuska.

Umma ta ce ta shigo daga ciki ita ma. 

Hajiya ta ce "Am ina neman wata alfarma dan Allah ina tare da baƙi ne, kuma ina son ki ba ni dama na shigo da su. Sannan in da wani ɗaki sai mu shiga mu yi magana a ciki saboda naga wannan da baƙi a ciki".

Haka kawai Umma ta kasa yi wa Hajiya musu, ta ce "To shikenan su shigo bari sai mu shiga ɗakin Haidar".

Hajiya ta ji daɗin karamcin da Umma ta nuna mata. Godiya ta yi mata sosai tana ƙoƙarin juyawa ta kira su Dady Haidar ya fito daga ɗakinsa, turus ta yi tana binsa da kallo, shima kallon ta yake yi da mamaki wace ce wannan mai kama da shi?.

Hajiya ta ce "Kai ne Haidar halan?"

Haidar ya ce "Eh ni ne".

Ta ce "Allah mai iko, wato Allah ya na so ya ƙara nuna mini ikonsa a kaina sai ka biyo ni sak".

"Ban gane me ki ke nufi ba, Umma ban fahimci maganar ta ba". Haidar ya yi maganar ya na kallon Umma da ta duƙar da kai ƙasa.

"Ai ba za ka gane ba jikalle na, ka je ƙofar gida ka shigo mutanen da nake tare da su". Gaba ɗaya Haidar ya kasa gane inda wannan tsohuwar ta dosa, amma sai ya fita domin ganin su waye baƙin. 

Umma ta kai Hajiya ɗakin Haidar, sannan ta fito ta tafi in da su Mama suka ƙara gaisawa tare da yi mata ya jiki, ta amsa musu cikin sakin fara'a da sakin fuska.


Umma ta ce "Afnan kawo musu ruwa kafin a kammala abinci". Ta dubi su Mama ta ce "Dan Allah ku ɗan yi haƙuri ina zuwa, baƙi ne suka zo suna magana da ni, ba daɗewa zan yi ba yanzu zan dawo" . Suka ce ai babu komai ta wuce kawai.

Haida ya fita ƙofar gida nan ya ga ashe mutane nan ne, cikin mutuntawa ya gaishe su, sannan ya ce su shigo, ya yi gaba suka bisa a baya, ya na shiga ɗakin sa ya kai su Hajiya na zaune akan tabarmar da Umma ta shimfiɗa mata, ita kuma tana zaune bakin katifa. Zama suka yi Dady sai binta ya ke da kallo. Haidar ya ja ya tsaya ya na kallon su.


Abba ya ce "Nemi wuri ka zauna mana".


Ya na ƙoƙarin zama ne Umma ta ce "Ka je ka gaida surukan ka mana ko baka ji shigowar su ba ne?". 


Haidar ya ce "Haba dai ai ban san su ba ne, shi ya sa ina banɗaki na ji ta fita da gudu". Fita ya yi ya shiga ɗakin Umma da sallama. Gaba ɗaya suka juyo suna kallon sa.


Ya duƙa har ƙasa ya gaishe da su Mama, suka amsa masa cikin sakin fuska. Maryam ta ce "Mama shi ne fa mijin Aunty".


Kafin Mama ta yi magana Inna Bilki ta ce "Dan Allah dai Maryam da gaske? Kai Alhamdulillah ma sha Allah, lallai Afnan kin yi dacen miji na nunawa sa'a yaro sai ka ce shi ya yi kansa tubarkallah". Murmushi Mama ta yi cikin jin daɗi ta ce "Kai Bilki ba ki rabo da abin dariya".


Haidar dai sai murmushi yake yi, daga bisa ni ya tashi ya fita a ɗakin, fita ya yi ya je bakin shagon dake ƙofar gidan su, ya siyo ruwa da lemu hadda su Abba ya siyo wa, ya dawo ya fara kaiwa su Mama sannan ya nufi ɗakin sa da sauran. Ya shiga ya ajiye musu ruwan da lemu ya nemi guri kusa da Umma ya zauna.


Hajiya ta yi gyaran murya ta ce "Amina gurin ki na zo, nasan ba sai na yi miki bayanin ko ni wace ce ba kin gane ni, saboda ba za ki taɓa mance fuskata ba a rayuwar ki, saboda abin da na aikata miki. Wanda dalilin hakan ne ya sa nayo tattaki na zo ƙafa da ƙafa domin na baki haƙuri tare da neman yafiyar ki. Kuma na nuna miki nadama ta akan abin da na aikata miki. Haƙiƙa naga ishara a rayuwata, kuma naga ne cewar duk abin da ka yi wa ɗan wani sai an yi wa naka fiye da abin da ka yi. Amina haƙƙin ki bai bar mu jin daɗin rayuwa ba, tun ba a je ko ina ba muka fara ganin ishara. Nayi baƙin ciki da takaici abin da na aikata, ta ƙarfi da ya na raba soyayyar da ban san abin da Allah ke nufi da ya ƙulla ta ba, na bi son zuciya da ya sa na raba ki da mijinki kuma hakan bai ishemu sai da muka mantar da shi ke a cikin rayuwarsa". 


Da sauri Umma ta ɗago da kai tana kallon Hajiya, Haidar ma kallon ta yake ko ƙiftawa ba ya yi.


Hajiya ta ce "Ƙwarai kuwa Amina mantar da Munir ke aka yi na tsawon lokaci ba tare da na duba jikinsa da ki ke ɗauke da shi ba. Shi ya sa bai neme ki ba, sai daga baya Allah warware masa komai". Nan Hajiya ta faɗa musu komai da irin asirin da aka yi wa Munir, sannan ta neme gafarar Umma.


Banda sharar ƙwalla ba abin da Umma ke yi, Haidar kuwa idonsa sun kaɗa sun yi jajur. 


Abba ya fara magana da cewa "Amina dan Allah ki yi haƙuri ki daina wannan kukan, abin da ya faru ya riga da ya wuce, ki yi haƙuri ki yafe musu tunda har sunyi nadama, kuma ta zo da kanta ta nemi gafarar ki, ko ɗan albarkacin wannan yaron dake tsakanin ki da su ki yafe musu. Dan nasan ko ba a faɗa ba ɗan Munir ne, saboda kamannin Hajiya ne a fuskarsa".


Da ƙyar Umma ta buɗa baki ta ce "Babu komai Hajiya Allah ya yafe mana gaba ɗaya".


Sai a lokacin Haidar ya yi magana yana kallon Umma "Umma dama mahaifina yana raye ki ka ce mini ya rasu? Me ya sa ki ka ɓiye mini wannan abin Umma?". 


"Haidar ina ga a gaban ka aka faɗi duk abin da ya faru, ba na son ina tuna abin ne a raina, sannan kuma ba na son kasan asalin dangin mahaifinka saboda ba ni da tabbacin shi ya na raye ɗin, kuma nasan ƴan uwansa ba sonka za su yi ba, shi ya sa na ce maka baya raye". Kallon Munir Haidar ya riƙa ya na tunanin yanzu wannan ne mahaifinsa? Dama ya na da uba a cikin duniyar nan?.


"Haidar zo nan, zo ka zauna kusa dani ɗana kai ma ka ji ɗumin mahaifinka". Tashi ya yi ya ƙarasa kusa da Dady ya zauna, Dady ya riƙe hannun Haidar ya na kallon sa. Sannan ya kalli Umma ya ce "Haƙiƙa Amina kin cika mace ta gari kuma wadda za a yi alfahari da ita, na ji daɗi kuma nayi farin ciki da abin da ki ka mini. Duk da taren laifina a gare ki bai sa kin hana a kira Haidar da sunana ba, kuma abin farin ciki ki ka saka masa sunan mahaifina wanda wannan shi ne burina a kullum idan na samu ɗa sunan mahaifina zan saka, ina godiya sosai Amina tare da ƙara baki haƙuri akan abin da ya faru da kuma halin da na saka ki, dan na san za ki fuskanci ƙalubale a wajan ƴan uwanki da kuma jama'ar gari, bayan da na dawo hayyacina kina raina, har ƙauyen ku na tura a yo mini bincike akan ki da nufin idan na ji labarin kina nan zanyi tattaki da kaina na je na baki haƙuri da kuma iyayen ki, sai dai abin baƙin ciki na samu labarin wai bakya garin ba a san in da ki ke ba, daga ƙarshe ma wani cewa ma ɗan aike na ya yi cikin shege ki ka da daɗewa aka kore ki daga garin. Na yi baƙin ciki jin wannan maganar, nan take na fahimci cikina ne ake kira da na shege. Na yi neman ki amma ban same ki ba, kwatsam sai ga likitana ya ce mini ƴata Sharifa sun kawo mara lafiya a asibiti, shi ne na je na duba waye suka kai ɗin, ni a tunani ko wani ta buge da mota ne, ina zuwa naga ke ce. Sai ki ka ƙi saurararmu daga ƙarshe guduwa ki ka yi. A ranar kasa bacci na yi saboda farin cikin ganin ki da na yi, sai dai kuma fargaba ta shige ni, na fara tunanin kada ya zan da auren wani akan ki. Ki yi haƙuri Amina ki yafe muna". Ya ƙarasa maganar ya na tsare ta da ido.


"Babu komai Baban Sharifa Allah ya yafe mana".


Ba ƙara min daɗi suka ji ba, ganin ta sauko.


Dady ya kuma cewa "Amina sai ki shirya mu saka ranar da zamu je ƙauye na bawa su Baba haƙuri, kuma na faɗa musu gaskiyar abin da ya faru".


Nan take Umma ta ɗaure fuska ta ce "Ba in da zani ka rabu da su kawai".


Hajiya ta ce "A'a Amina ba a yi haka ba, ki yi haƙuri ai shi mai laifi ne a gurinsu, ki bari a je a basu haƙuri, kuma hadda ni za a yi tafiyar". Umma ba ta son yi wa Hajiya gardama ne ya sa ta amince.


"Yawwa Amina na ce na ji kina maganar Haidar ya je gun sirikansa, halan ya yi auren ne?" Cewar Abba. Ta ce "Eh ya yi aure ba da daɗewa ba". "Ah to ma sha Allah, ashe ɗan namu har ya zama babban mutum, ina ga kamata ya yi mu je mu gaisa da su, daga nan sai muga sirikar tamu". Ta ce "To bari na gaya musu". Ta miƙewa ta fita a ɗakin. Suma tashi suka yi suka bi bayan ta.


Koda ta zo su Mama sai fira suke yi, za ce "Dan Allah ku yi haƙuri na barku ku kaɗai iyayen Haidar ne suka zo, gasu nan shigowa ku gaisa". Suka ce ba damuwa ai, da sauri Afnan ta saka hijabin ta.


Shigowa suka yi suka gaisa, Abba ya ce "Ina sirikar tamu ne?".


Umma ta nuna masa Afnan, sannan ta ce "Ga mahaifiyarta nan wannan kuma ƙanwarta ce". Hajiya ta ce "Ma sha Allah ashe dai angon nawa ya iya zaɓe. Duk da haka dai nafi ta kyau". Dariya suka yi Abba ya nuna musu Dady a matsayin Baban Haidar, Afnan da su Mama mamakine ya kama su ganin iyayen Haidar daga ni kasan nera ta zauna musu, kuma a ce suna rayuwa a wannan gidan. 


Abba ya kuma kallo Mama dai ya kasa haƙuri sai da ya ce "Haidar ni fa kallon sani nake yi wa sirikar nan taka". Sai a lokacin Mama ta ɗago da kai ta kalle shi, kallo ɗaya ta yi masa ta shaida shi. Duk da shekaru sun ja. Murmushi ta yi wanda yafi kuka ciwo ba ta ce ƙala ba ta sunkuyar da kai. 


Haidar ya ce "Maybe kama take yi maka da wata daka sani ne".


"A'a Haidar ita ce dai wadda na sani, Munir ka tuna tsohon mai gadina Malam Abbakar". Dady ya ce "Eh na tuna shi". "To ai matarsa ce, ina tunanin ma matar Haidar ita ce yarinyar da aka haifa lokaci yake aiki a gidana, ashe ka ga da rabon zamu sake haɗuwa na yi nemansa bayan barinsa gidana amma ko ɗuriyar sa ban ji ba". Dady ya ce "Allah mai iko kuma sai gashi yanzu alaƙa mai ƙarfi ta haɗa mu da shi". Nan Abba ya tambaye Mama Abbakar ta ce masa yana nan ƙalau yanzu kasuwanci yake yi.


Sun daɗe a gidan kafin suka yi musu sallama, Haidar har bakin mota ya raka su, Dady ya ce zai sake dawowa, sannan idan ya koma zai aiko da saƙo a kawo.


Bayan tafiyar su ba da daɗewa ba su Mama ma suka yi musu sallama suka wuce, Afnan ta yi murna sosai da ganin Mama, kuma ta ji daɗin kayan da aka kawo mata, kayan kitchen ne masu kyau da zannuwan gado. Umma ta ce ta kai su can ɗakin Haidar tunda shima ɗakin babba ne kamar na Umma.


Alhamdulillah jikin Huda da sauƙi sosai, har an sallamo su daga asibiti, Abba na isa a harabar gidan ya tarar da Mudan na shirin fita. Nan yake shaidawa Abba cewar an sallamo su Mami daga asibiti. Kai tsaye Abba ya nufi sashen Mami ya ce Mudan ya biyo shi.


Amanarcool ✍️ 
***