RAMIN ƘARYA...

Chapter 95-96

by @amanarcool323

💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫



_WRITING BY AMANARCOOL_✍️



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



Page 95&96


__________Mami na falo ita da Mudan Abba ya fito da sauri zai fita.

Ganin yadda yake saurin ne ya sa ta ce "Alhaji lafiya dai?".

Ya ce "Gurin ƴar uwarki zani yanzu ta kira ni ba ta jin daɗi". Daga haka ya buɗe ƙofar falon ya fita.

Tsaki ta yi ta ce "Aikin banza, zan yi maganin ki ne". 

Abba na fita ya na ƙoƙarin shiga sashen Ammi yaga motar Hajiya Maimuna ta shigo, tsayawa ya yi har ta fito ita da su Ummie yau hadda Sadik. 

Ƙarasowa suka yi inda yake, Abba ya yi musu sannu da zuwa. Suka ɗunguma gaba ɗaya zuwa sashen na Ammi.

Cikin sakin fuska Ammi take yi musu sannu da zuwa, Hajiya Maimuna ta ce "Ya ƙarfin jikin na ki Zainab?". "Da sauƙi Alhamdulillah" ta ba ta amsa.

Abba ya ce "Ya dai madam ko asibiti zamu tafi ne?". Ta girgiza masa alamar a'a.

Saddik ya kira Mudan ya tambaye shi yana gida ne?. Da yake suna ɗan shiri da shi

Mudan ya ce "Eh ina gida wani abu ka ke buƙata ne?". Sadik ya ce "A'a mun shigo gidan ne yanzu ni da su Momy, bari na zo ɗakin ka na same ka".

Abba ya yi saurin cewa "Ba inda za ka je, wato guduwa za ka yi saboda kar a dameka da surutu?". Mudan ya ji abin da Abba ya ce dan haka ya ce wa Sadik gashi nan zuwa shi.  

Mudan ya faɗawa Mami su Hajiya sun zo suna sashen Ammi, wani haushi ne ya kamata, ta san sanadiyyar cikin jikin Zainab ne ya sa Hajiya ke kula ta. Tashi ta yi tabi bayan Mudan da ya fita, ita ma ta tafi can a cewar ta gara ta je ta zauna a yi komai a gaban ta.

Koda ta shiga falon ya cika da jama'a, suka gaisa da Hajiya da sauran yaran ta nemi guri ta zauna. Abu kamar haɗin baki sai ga Alhaji Munir da Momy tare da Sharifa sun zo. Abba ya ce "Lallai yau gidan namu ya tashi da ni'imar jama'a sai ziyarar bazata ake yi mana?". Dariya suka yi gaba ɗaya. Nan aka fara hira, Mami dai na zaune ta ƙi cewa ƙala sai dai ta faki idon jama'a ta wurgawa Ammi harara.

Kamar wadda aka jefo ta shigo gidan. Mai gadi take tambaya ko Alhaji na gida?

Nan ya nuna mata sashen Ammi ya ce "Duka mutanen gidan na ciki". Ta tambaye shi har Mami? Ya ɗaga mata kai alama eh. Da sauri ta nufi gurin kamar mahaukaciya saboda abin da take ji a zuciyarta.


Babu sallama ta shiga falon tana faɗin "Ina ki ke baƙar munafuka algunguma wadda babu Allah a ranta ko kaɗan".


A firgice Mami ta kalli Turai dake cika tana batsewa.


Cikin hasala Hajiya Maimuna ta ce "Turai lafiya za ki faɗo muna cikin falo haka babu sallama sai muryar ki da muka ji tamkar saukar aradu?". 


"Ai dole ne ku ji ni fiye ma da haka, saboda abin da wannan matar da bata san hallaci da zaman tare ba, wallahi Saratu kin yi kaɗan da ki wulaƙanta ni, kuma ina mai tabbatar miki da cewar yau ranar tonon siririnki ce, ko ince asirinmu". Da sauri Mami ta tashi ta je gaban Turai cikin rawar murya da tashin hankali ta ce "Haba ƙawata kar mu yi haka dake mana, dan Allah ki yi haƙuri ki zo muje sashena?".


"Gafara can munafukar banza ni za ki yaudara? Bayan cin mutuncin da kuka gama yi muna ke da ɗanki, ai wallahi yanzu babu sauran wata alaƙa tsakanina dake". Gaba ɗaya jama'ar falon kallonsu suke yi da mamaki . Abba ya ce "Turai shigo ciki ki zauna, kema Saratu dawo ki zauna". Shigowa Turai ta yi ta zauna.

Mami kuwa kasa zama ta yi, saboda tashin hankali ga wani irin gumi da ya fara tsatsafo mata. Sai da Abba ya kuma yi mata magana sannan ta zauna jiki babu ƙwari kamar an sulala karas.


Babu kunya Turai ta dubi Abba ta ce "Alhaji ina mai baka haƙuri da kai da Zainab da ma sauran jama'ar falon nan akan abin da za ku ji daga gare ni, nasan zai girgiza ku, kuma ya ɗaga muku hankali, amma ku sani ba ni da laifi a ciki goyon baya kawai na bayar. Duk abin da zaku ji shirin wannan makirar ne". Ta yi maganar tana nuna Mami.


Hajiya Maimuna ta ce "Turai ki yi magana mana sai ƙunbiƙunbiya ki ke yi mana".


Ta gyara zama ta ce "Alhaji da farko dai zan fara da sanar da kai cewar duk cikin da Zainab ke yi yana zubewa ba aikin kowa ba ne Saratu ke zubar da shi ta hanyar asirin da muke zuwa gurin bokaye da Malamai ana yi. Da zaran ta gane cewar Zainab na da ciki yanzu nan za ta sa a zubar da shi, daga ƙarshe ma cewa ta yi a hana ta haihuwa gaba ɗaya, ko matsalar da ta kuma samu kwanakin baya na ɓarin ciki Saratu ce ta sa aka tura aljani ya shafeka a lokacin da ka ke saduwa da Zainab domin cikin ya zube, saboda ita Zainab ɗin asiri bai cika tasiri akan ta ba yanzu. Sannan tana yi maka asiri kaima akan ta mallake ka sai yadda ta yi da kai, wani lokacin tana yin nasara akan ka, kai hadda Hajiya Maimuna ta yi wa asiri akan ta mallake ta sai yadda ta yi da ita saboda taga kana jin maganar ta, sannan ita ce ta ƙara cusa tsanar Zainab a cikin zuciyarta".


Gaba ɗaya aka ɗauki salati a falon, kowa kallon Mami yake yi da mamaki, Ammi kuwa hawaye ne kawai ke zuba a idonta. Hajiya kuwa mutuwar zaune ta yi. 


Abba zai yi magana kenan Turai ta tari numfashinsa da cewar "Alhaji yi shiru ai da saurin rina a kaba, wannan ba komai ba ne akan abin da Saratu ta aikata muku, akwai abu mafi girma da tashin hankali da zaku ji yanzun nan. Alhaji ina fatan dai baka manta da wani mai gadi da ka taɓa yi ba mai suna Abbakar?". 


Kafin Abba ya yi magana da ƙarfi Mami ta ce "Turai kada mu yi haka dake, dan girman Allah ki yi haƙuri ki yi shiru da maganar nan".


Abba ya ce "Saratu kada na sake jin bakin ki a gurin nan, Turai ci gaba da maganar ki na tuna shi".


"Rabu da ita, ai wallahi sai na faɗa. Duk ɗan da ya hana uwar shi bacci shi ma ba zai yi baccin ba. Yawwa ina fatan baku manta da ya taɓa ɗakko matarsa da tsohon ciki zuka zauna a nan gidan tare ba? A lokacin Zainab na da tsohon ciki ita ma, wanda babu yadda Saratu ba ta so salwantar da shi ba, Allah bai nu fa ba. Za ku iya tuna ranar wata juma'a bayan sallar isha na ƙuda ta kama matar Abbakar, wanda a lokacin itama Zainab naƙuda ta taso mata aka haɗa su gaba ɗaya aka yi asibiti da su, ina gida Saratu ta sanar da abin da ke faruwa ta ce nazo asibitin yanzu, babu ɓata lokaci na je, babu kowa a daga ni sai ita ne, Alhaji da Abbakar mai gadi suna waje, muna nan zaune Saratu ke nuna mini irin baƙin cikin da take ciki, har take ce mini da za ta samu da ma kashe abin da aka haifa ɗin za ta yi. Ni kuma a lokacin ƙara ingizata na yi tare da bata ƙwarin gwiwa. Muna nan zaune mun tsabbace kanmu a gefen barandar gurin muna jiran tsammani, sai guraren goma da rabi na dare likitar dake karɓar haihuwar ta fito. Da sauri muka nufe ta muna tambayar halin da ake ciki? Nan take sheda muna cewar gaba ɗaya sun sauka lafiya ɗaya ta haifi mace ɗaya kuma namiji ta haifa, sai dai namijin bai zo da rai ba, cikin sauri muka tambaye ta cikin su waya haifi macen da kuma wanda ya haifi namijin? ta faɗa mana cewar farar ce ta haifi mace ɗayar kuma namiji, nan take muka gane cewar Zainab ce ta haifi mace kenan matar Abbakar ce ta haifi namijin da bai zo da rai ba. Da sauri muka ce to zamu iya shiga mu gansu?.
Ta ce a'a ai ba a shiga, sannan gaba ɗaya matan basu dawo hayyacinsu ba, tana ƙoƙarin barin gurin Saratu ta ce tana son yi magana da ita, amma idan da hali mu samu wani gurin, matar ta ce ba damuwa muka keɓe da ita cikin wani corido dake gurin. Saratu ta ce dan Allah likita wata alfarma muke nema a gurin ki. Inda dai har ki ka yarda da abin da muka zo miki da shi.
Ki faɗa mana komai ki ke buƙata zamu baki matuƙar ki ka yi mana abin da muke so.
ta ce me kuke buƙata a gurina?
Saratu ta ce so muke ki yi mana musayar yaran nan, wadda nata bai zo da rai ba ki ba ta wanda ya zo da rai, ita kuma wadda natan ya zo da rai sai ki bata wanda bai zo da ran ba.
Sakin baki ta yi tana kallon kafin ta ce gaskiya bazan iya haka ba, wannan abin ya saɓawa ƙa'idar aikinmu, kuma cin amanar aiki ne, ku yi haƙuri bazan yi ba.
Likita zamu baki ko nawa ki ke so in dai za ki amshi buƙatar mu, ki faɗi duk abin ya yi miki zamu baki. Saratu ta kuma yi mata magana. Nima na ɗora da nawa lallamin, mun jima muna roƙon ta, tare da yi mata magiya akan ta taimaka mana.
Shiru ta yi na ɗan wani lokaci kafin ta sauke a jiyar zuciya ta ce na amince.
Farin ciki ne ya luluɓemu ganin mun yi nasarar shawo kanta. Ta ce mu koma barandar mu jira ta, saboda aikin akwai hatsarin a cikin sa, dole ne sai an yi taka tsantsan.
Misalin ƙarfe sha ɗaya na dare, sawun mutane ya fara ɗaukewa, kowa ya fara neman gurin da zai adana ransa da sama wa gangar jikinsa nutsuwa. A yayin da wasu lokacin ne, suke gudanar da harkokinsu.
Madaidaiciyar harabar asibitin, ɗauke da ababen hawa na ma'aikata da wasu daga cikin majinyata. Tsirari daga cikin majinyata, na kai wa na komowa a harabar asibitin.
Daga wata baranda kuwa, wasu mutane ne a tsaye, cirko-cirko fuskokinsu ɗauke da yanayi na damuwa, su na ta kai wa suna komowa a ƙofar wani ɗaki, da aka sanya alamar ba wanda yake shiga, sai iya ma'aikatan wurin.
Sannu a hankali take tunkarar ɗakin, gabanta na tsananta faɗuwa, tare da tunani a kan hukuncin da ta yanke, amma wata zuciyar ta ci gaba da bata ƙwarin gwiwa, da jin ba wani abu. Martabar fararen kayan jikin matar, ya sanya mutanen da suke tsaye a ƙofar ɗakin, suka fara yi mata sannu da aiki.
Cikin sakin fuska ta amasa musu da yauwwa sannunku, amma dan Allah ko zaku koma barandar ƙasa, ba ma buƙatar kowa a ƙofar wurin nan, idan muka kammala, zamu yi muku magana in sha Allah, sai ku zo ku gansu. Ta yi maganar cikin son su ɗaga daga gurin domin ta samu damar yin aikin ta ba tare da kowa ya sani ba.
Cikin girmamawa suka ce to babu laifi bari mu je, gaba ɗaya suka sauka, ya kasance babu kowa a wurin, ta saki ajiyar zuciya da jin, komai zai zo mata da sauƙi. Babu ɓata lokaci ta shiga ta yi musayar yaran, sannan ta yi muna magana akan aiki ya kammala. Nan take Saratu ta tura mata maƙudan kuɗaɗe a cikin account ɗinta wanda ya kusa zautar da ita, sai dai aka daidai ta komai sannan aka sanar daku haihuwar kai da Malam Abbakar, sosai ka shiga damuwa akan rashin zuwan da yaron ka bai yi ba da rai. A haka muka tattara cikin dare muka koma gida bayan da su Zainab ɗin sun dawo cikin nutsuwar su. Bayan kwana biyu da haihuwar ne sai muka fahimci jaririyar Zainab da aka bawa matar Malam Abbakar tana da wani shatin baƙi kaɗan a gefen wuyanta irin na Zainab, sannan kuma ƙaramin yatsanta na ƙafa shima ya na da shatin baƙi kamar na Zainab ɗin, sai muka ga hakan na iya zama barazana a gare mu idan Abbakar ya ci gaba da zama a gidan da tare da jaririyar. Hakan ya sa muka je gurin wani malami muka sa aka yi wa Alhaji asirin ya kori Abbakar kuma kada ya sake koda zancen sa ne, haka aka yi bayan kwana biyu ba tare da laifin komai ba aka kori Abbakar da matar sa daga gidan, wanda har yanzu ba mu koma jin ko da ɗuriyarsu ne ba".


Gaba ɗaya tsit falon ya kamar babu mutane a ciki tsabar kaɗuwa da jin maganar da Turai gama ɗin.


Ammi kuwa kuka take yi sosai na ji irin tsantsar zaluncin da aka yi mata na raba ta ƴar ta da aka yi, wanda a halin yanzu ba ta san inda suke ba, wata ƙila ma ba ta raye?.


"Allah ya isa tsakaninmu da ku Saratu wallahi ba za mu taɓa yafe muku ba, kun cuce mu, azzaluman banza, marasa jin tsoron Allah" Hajiya Maimuna ta yi maganar cikin hargagi da ɗaga muryar.


Abba kasa cewa komai ya yi, sai binsu yake da kallo.


Alhaji Munir ya ce "Ikon Allah lallai ɗan Adam abin tsoron ne, yanzu ke Saratu bakya ma jin tsoron haɗuwarki da Ubangiji? Irin wannan mugunta haka da rashin imani?". Hajiya ta ce "Ni wallahi ba wannan ba, damuwata a yanzu shi ne ina zamuga Malam Abbakar ne? Domin ya san da wannan maganar, kuma ina tunanin ta yadda zai karɓi lamarin". Ta ƙarsa maganar tana zubar da ƙwalla.


"Tabbas Hajiya maganar ki gaskiya ce abin akwai rikitarwa a ciki, rana tsaka a zo a ce masa yarinyar da yake wa kallon ƴarsa a ce ba tasa ba ce?". Daga ɗiyan Hajiya har Mudan da Sharifa sun tsorata sosai da wannan maganar.


"Munir babbar damuwar shi ne a ina za a nemo su yanzu?".


Dady ya yi murmushi ya ce "Ai kin san Allah babu ta yadda baya yin ikonsa, ki kwantar da hankalinki Malam Abbakar mun san inda yake yanzu haka, kuma har ma alaƙa mai ƙarfi ta haɗa mu da shi".


Da sauri Maimuna ta dubi shi tana faɗin "Kun san inda yake? Har alaƙa kuma ta haɗa ku da shi? To wace irin alaƙa kuma?".


Amanarcool ✍️ 
***