Chapter 105-106
💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫
_WRITING BY AMANARCOOL_✍️
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*
Not editing
Page 105&106
__________Sai yamma sosai suka iso cikin garin Kano, su Umma suka fara sauke wa a gida sannan suka ƙarasa gida suma. Haidar na lura da yadda Umma ke ta haɗe rai ba ta son ko magana a yi mata, hakan yasa bai yi mata magana ba ya shige ɗakinsu. Umma kuwa wani irin abu take ji a zuciyarta da ta kasa tantance farin ciki ne ko a kasin haka?.
A matuƙar gajiye Dady ya isa gida bayan ya sauke Hajiya a gida, Momy ta yi ƙoƙarin danne kishinta ta yi masa sannu da zuwa, Sharifa ta gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska. Kai tsaye bedroom ɗinsa ya wuce Momy ta bi bayan sa, yana zuwa ya tuɓe kayansa ya shiga toilet bayan ya yi wanka ya ɗauro alwalar magariba ya fito, tana nan zaune a bakin gado ta yi shiru, kallon ta ya yi ya yarfa mata sanyin ruwan dake hannunsa. Da sauri ta dube shi ya ce "Ya dai Maman Sharifa? What is problem?".
"Babu komai, me ka gani ne?"
"A'a da magana a bakin nan naki, bari na yo sallah akwai maganar da zamu yi da ke mai muhimmanci". Jinjina masa kai ta yi, sannan ya fice daga ɗakin, ita ma ta wuce domin gabatar da sallah.
Ammi ta kasa sakin jiki tun jiyan nan, Abba ya kalle ta ya ce "Maman biyu ina lura dake tun jiya kin kasa sakin jiki, ni sai na ga kamar ma kina jin haushina".
" Ka daina wannan maganar ni ba wani haushinka da nake ji, kawai ni dai an yi mini abin da ban ji daɗin shi ba ne".
Ya ce "Haba Gimbiyata ban san ki da wannan halin ba, wai ma tukuna yaushe muka fara haka dake ne? A sanin da na yi miki duk hukuncin da na zartar akan abu ba za ki taɓa yi mini musu ko ki nuna mini rashin amincewar ki ba, me ya sa za ki yi mini a wannan karon? Bayan ba raba ki da ƴarki na yi ba, kawai dai ina son nuna musu karamci ne".
"Ni fa ba musu nake yi da kai ba, amma ai kana ganin yarinyar ta nuna cewar ta fi son su akan mu, kamar ma ba ta yarda da abin da aka faɗa ba, yanzu idan ba mu shaƙu da ita ba ai ba za ta taɓa yi mana kallon iyayenta ba, ni gaskiya kasan yadda za a yi". Ta ƙarasa maganar idonta na cika da ƙwalla.
Shiru Abba ya yi yana kallonta, tabbas tunda har Zainab ta iya yi masa haka yasan abin ya dame ta sosai.
"Ki yi haƙuri Zainab, in sha Allah zan san abin yi, sannan kuma kada ki manta yarinyar nan yanzu matar aure ce, irin kusancin da ki ke so muyi da ita ba zai yiyu ba, sai dai ta riƙa zuwar mana ziyara".
"Duk da haka ni dai kasan abin yi". Ta kuma faɗa.
"To shikenan an gama ranki ya daɗi" ya yi maganar yana murmushi, sannan ya kuma cewa "Kinsan yau tafiyar da muka yi ƙauyen nan aka maida auren Munir da tsohuwar matarsa" . Sai da gaban Ammi ya buga da ƙarfi! Jin cewar an yi wa ƙawarta kishiya, tasan zafin kishi irin na Fatima. Duk da tana da hankali da haƙuri, kuma tana da ya ƙinin Fatima ba za ta iya cutar da kowa ba, amma tasan yau sai wani ikon Allah zai sa ba ta ɗagawa Munir hankali ba.
"Kin yi shiru baki ce komai ba?".
"Me zance ko? Allah ya basu haƙuri, shi kuma ya bashi ikon yi musu adalci". Da Amin ya amsa yana kallon ta gaba ɗaya ta birkice masa.
Bayan sallan isha Dady ya dawo gida, zama ya yi ya ci abinci sai da ya kammala, sannan ya maida hankalinsa ga Fatima ya ce
"Fatina"
"Na'am Dadyn Sharifa".
Ya ce "Magana nake so muyi da ke, ina fatan zaki fahimce ni, sannan duk abin da ki ka ji ban yi hakan dan in muzguna miki ba, kada ki kama ni da laifin rashin sanar dake da ban yi ba sai bayan faruwar abin, nima banyi tunanin haka za ta kasance yanzu ba..." "Alhaji ka fito fili ka gaya mini ba sai ka tsaya yi mini wani dogon bayani ba" Momy ta yi maganar tana tsare shi da ido.
"Dama ɗazu tafiyar da muka yi ƙauyen nan, to bayan komai ya wakana Hajiya ta neme alfarmar da a mayar da aurena da Amina, a taƙaice dai bamu baro garin ba sai da aka mayar da auren...." "Ta neme alfarma ko dai kai ka nemi alfarmar? Ai dama nasan za a rina, ina lura da take-taken ka, tunda ka ga matar nan gaba ɗaya hankalinka ya kasa kwanciya, ni ɗin ma bana gabanka a ƴan kwanakin nan, ka mayar da tunaninka da komai akanta, ai shikenan tunda an mayar da auren yanzu sai hankalinka ya kwanta, farin cikikin ka ta dawo''. Sakin baki Dady ya yi ya riƙa kallon Momy yadda lokaci ɗaya kishi ya rufe mata ido take gaya masa maganar da duk ta zo bakinta. Kasa ce mata ƙala ya yi, ya barta ta faɗi abin ke ranta wata ƙilan hakan zai sa ta rage jin zafin abin, sai da ta faɗi albarkacin bakinta sannan ta tashi ta bashi guri zuciyarta nayi mata zafi sosai, idonta sun kaɗa sunyi jajur saboda tsananin kishi.
A wannan daren da ƙyar Momy ta iya yin bacci saboda yadda take jin kishi na nuƙurƙusar zuciyarta.
******
Washe gari ya kama ranar auren Zaliha, Hajara na cikin baƙin ciki da ɓacin ran wannan auren, hakan yasa ba ta gayyaci kowa daga cikin danginta ba, daga Shafa ƙanwarta sai matar ƙaninta da kuma ƙawarta Larai sune kaɗai a gurinta suna ba ta haƙuri, Zaliha kuwa tun tana kuka yanzu har ta haƙura ta daina kukan.
Ɓangaren Gwaggo cike yake da jama'arta da kuma mutanen ƙauye, duk jama'ar dake gurin babu wanda bai san abin da ke faruwa ba na cewar Afnan ba ƴar Ɗanladi ba ce. Duk wanda yaji wannan abin sai ya yi Allah wadai da halin su Mami, ya ji tausayin Mama. Tare da jijinta lamarin, maganar tun jiya ta fara zagaya unguwar sanadiyyar Hajara da ta fara yaɗa maganar duk da tana cikin ta ta damuwar.
Afnan ta ɗan sakin jikinta ita da Maryam sai har kokinsu suke yi, suna ta ƙoƙarin ɗora girki, saboda wasu daga cikin mutanen ƙauye suna nan gurin Mama sai hira suke, ba laifi Mama ta saki jiki duk da cikin zuciyarta damuwa ce fal ranta. Inna Bilki ma suna gurin Bahijja na tare da su Afnan, gidan cike yake da jama'a sai hidima ake yi, ɓangaren Hajara ne kawai za ka ji shi shiru, idan mutane ma suka shiga wulaƙanci take yi musu.
Misalin sha ɗaya na safe aka ɗaura auren Zaliha da Dawuda, sai kuma auren Sanusi da Karima, jama'ar gurin da dama sunyi mamakin wannan auren. Saboda babu wanda yasan da zancen auren sai yanzu. Lokacin da sanarwar ɗaurin auren ta isa cikin gida guɗa Gwaggo ta saka tana murna da shewar Allah ya nuna mata ranar da ɗanta ya fara ajiye mace biyu, saura Ɗanladi da Umar suma nan ba da jimawa ba za suyi nasu auren.
Lokacin da Hajara ta samu labarin ɗaurin auren dim! Gabanta ya ba da wani irin sauti, ƙin yarda ta yi. Duk da sautin lasifika ya shigo har cikin gidan. Cikin tashin hankali ta nufi gurin Gwaggo tana zuwa babu ko sallama ta ce "Gwaggo abin da na ji ana faɗa gaskiya ne?"
Ɗage ɗankwali Gwaggo ta yi ta ce "Ƙwarai kuwa Hajara gaskiya ne".
"Da saninka Sanusi ya yi mini kishiya?".
"Ƙwarai kuwa kina tunanin zai yi abu ba tare da nasani ba?".
"Gwaggo kin san waya aura kuwa? Yanzu ya rasa wa zai auren mini sai Karima mai bakin shan daɗi? Amma Allah ya isa ban yafe ba, wallahi duk wanda yake da sa hannu a wannan auren ban yafe ba". Nan Hajara ta shiga zubawa Gwaggo rashin kunya, sai da kowa ya yi ala wadai da halinta. Har wasu daga cikin ɗiyan Gwaggo na ƙauye suka nemi yin rigima da ita. Sai da Gwaggo ta hana su. Ta ce wa Hajara
"Ni yanzu na gama da baben ki Hajara tunda na gane baki da kunya, duk gidan nan babu wanda nake nunawa son da nake yi miki amma ki rasa wa za ki ciwa mutunci sai ni, saboda baki da kunya? Ai shi ya sa da Sanusi ya zo mini da zancen auren na amince duk da nasan cewar yarinyar da yake son aure ƴar duniya ce, sai naga ai ita ce daidai dake. Har cikin zuciyata ban so ya auri wannan yarinyar ba, amma saboda ke na amince da auren kuma na tursasawa ƴan uwanshi akan dole su basshi goyon baya akan yin auren".
Hajara ta bar gurin tana zage-zage ji take kamar za ta yi hauka, da ƙyar ƴan uwanta suka rartasheta, kuka take yi sosai na baƙin ciki biyu ya haɗe mata lokaci ɗaya, babban tashin hankalinta matar da ya aura, Karima mai bakin shan daɗi ba ƙaramar ƴar bariki ce ba. Duk unguwar ba wanda bai san halinta na iya duniyanci ba, duk gidan da ta shiga indai da wata matar a gidan to sunan ta sorry, wai wannan aka auro mata a matsayin kishiyarta? Sanusi ya cuce ta sai Allah ya saka mata. Surutu take yi sosai.
Lokacin da su Mama suka samu labari, duk mutanen dake gurin Mama ce kawai ba ta yi murna ba, ta ji tausayin Hajara na haɗa ta kishi da Karima. Duk da tasan aniyarta ce ke binta, amma ta tausaya mata, kowa dake gurin ya yi farin ciki da hakan barin ma Inna Bilki da Maryam hadda rawa suka yi.
Maryam ta kwashe da wata mahaukaciyar dariya ta ce "Kam bala'in nan lallai gidan nan zamu sha kallo, tabbas za a mutu, sai dake Kawu Sanusi namu mai lokaci, gaskiya yau ka biya ni, ka gama mini komai, ita ma waccan tsohuwar yau ina yinta over da ta bada haɗin kai gurin yin wannan auren. Inna Hajara daga yau sunan ki auduga, shegen bakin nan naki mai kama na saniya zai mutu murus". Ta ƙarasa maganar tana dariya. Mutanen gurin ma dariya suke yi sosai.
Inna Bilki ta ce "Wannan gaskiya ɗiyata ta kaina, zamu ga yadda za a yi wannan zaman, Hajara bala'i da masifa ta iya su Karima ma gwanace a wannan fannin, lallai dole wayata ta kasance koda yaushe a cike saboda idan an fara nayi video na riƙa kalla wani lokacin".
Maryam ta ce "Inna Bilki raba kanki wannan kakarta ce a bala'i, Karima ko hanjinta gani take akan masifa, ai kawai Hajara sunan ta tuwon dawa da miyar kuka" suka kwashe da dariya har suna tafa hannu da Inna Bilki.
Mama ta ce "Haba Bilki ya za ki biye wa yara kuna wannan abin? Ai tausaya mata ya kamata kuyi".
"Waza a tausayawa Aunty? Ba dai Hajara ba? Tab ai Allah ne ya tashi kamata munafukar mata, indai makirci abin yi ne ai gashi nan ta gani ga rabon ta".
"Lallai kam dai yanzu sai abin da mai bakin shan daɗi ta ce za a yi, ni fa ko Gwaggo ina ji a jikina Karima sai ta gyara mata zamanta, sai ta san shayi ruwa ne" cewar Maryam tana dariya.
Shiru Mama ta yi ganin abin nasu ba na ƙarewa ba ne. Haka suka ci gaba da dariya Inna Bilki na biye musu.
Haidar ma ya zo ɗaurin auren, ya shigo suka gaisa da su Mama har inda Gwaggo sai da ya zo, ta shiga nunawa mutanen ƙauye shi, tana faɗa musu shine ɗan gidan Amina, bai wani daɗi ba ya tafi. Bayan ya gama yi wa Afnan magiyar anjima zai zo su tafi tare.
Haka aka yi bikin auren nan uwar amarya ba ra cikin daɗin rai, tunda safe da Sanusi ya bar gidan bai dawo ba har gashi ana shirin yin magariba, babu laifi an gyarawa Zaliha ɗakinta, itama an sai mata gado mai kyau duk da bai cimma na Afnan ba. Sai dai da ƙyar ɗakin ya ɗauki kayan saboda ya yi ƙarami.
Bayan sallan isha aka shirya amarya Zaliha domin kaita gidan mijinta, ta yi kuka sosai na rabuwa da Mamarta. Haka aka ɗauketa zuwa gidan Daudu ba tare da anyi mata duk wani gyara da ake yi wa amarya ba, sulmun gadinta aka kaita.
Ana fita kai Zaliha ƴan kawo amaryar Sanusi suka shigo, gurin Gwaggo aka fara kaita, tun daga yadda fuskar Karima take a buɗe tana kallon jama'a kasan kunya kam babu ita, nan Gwaggo ta fara shan jinin jikinta. Sannan aka ɗauke ta zuwa sashen Hajara, ɗakin dake kusa da ita aka buɗe babu dattin komai tsaf da shi, saboda jiya Sanusi ya share ɗakin ya goge komai, ita a tunaninta kawai gyarawa ne ya yi. Leda aka shinfiɗa sannan aka aza katifa tare da saka labule aka saka mata sauran kayanta a ciki. Yayar Karima ta ce "To zo akai ki gurin uwar gidanki ko, kafin ki fara shiga ɗakin naki".
Karima ta dubi ta ta ce "Wa ni Allah ya kiyaye ai ni ce uwar gidan, babu inda za ni, nasan abin da ta ƙulla akaina da zan shiga ɗakin, ni ku sada ni da nawa ɗakin kawai".
Shiru suka yi babu wanda ya kuma magana, dama sun san hakan za ta faru, dan haka suka kaita cikin ɗakinta, suka ƙara yi mata nasiha sannan suka bar gidan. Duk abin da Karima ta faɗa akan kunnen Hajara.
Amanarcool ✍️
***