Chapter 111-112
💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫
_WRITING BY AMANARCOOL_✍️
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*
Page 111/112
__________Ganin da ta yi Karima ta mayar da ita ƴar banza ya sa ta juya fuuu ta bar wajan, tana danasin barin ɗanta da ta yi ya aureta.
Karima kuwa waƙarta take sha hankali kwance, tana yi wa Hajara iskanci kala-kala
Hajara da takaici ya yi mata yawa shiga ɗakinta ta yi ta ɗakko wayarta ta kira ƙawarta Larai, tana ɗauka ko sallama ba ta tsaya yi ba ta fara magana "Ni dai an haɗa ni da jaraba da bala'i, Sanusi ya cuce ni ya auro mini ƙaddara, cikin abin da bai fi kwana biyu da zuwanta gidan nan ba an mayar da ni kamar shara? To wallahi ba zan yarda ba, dole na ɗauki matakin da ya dace, babu wata matar da ta isa ta shigo mini gida kuma ta ce za ta mulke ni". Ta ƙarasa maganar cikin masifa da kumfar baki.
Larai ta ce "Me yake faruwa ne?"
Hajara ta shiga labarta mata abin da ke faruwa tun shigowar Karima a gidan.
Wata uwar ashar Larai ta yi ta ce "Akwai wadda ta isa ta yi mana wannan tsiyar kuma mu zuba mata ido muna kallonta? Ai babu ita, lallai dole ne na zo mu ɗauki mataki akan wannan ƴar banzar amaryar taki, ita inda mun san da zancen auren tama isa ta shigo gidan balle har ta yi wannan iskancin?".
Nan Larai ta shiga masifa, suka tsayar da shawarar zasu je gun Malami ayi musu maganin Karima.
Har la'asar su Afnan na gurin Ammi, sun ji daɗin zaman gidan domin Ammin sakin jiki ta yi suka sha hira, Afnan ma ta ɗan saki jiki, Maryam bini-bini tana tuna gayen nan daya tambaye sunanta. Duk da bai jima da barin gidan ba.
Haidar ya dawo ɗaukar su, tsaraba sosai Ammi ta haɗa musu suka yi sallama da ita suka tafi.
Zuwan Afnan gidan ba ƙaramin daɗi ya yi wa su Ammi ba, musamman ma ita, sai ta jita wasai duk wata damuwarta ta gushe, ta saki jiki ta kuma normal, Abba sai da ya yi mata tsokana da tunda yau ta ga ƴarta shi ne ta saki ranta.
Sadik ya koma gida, Hajiya Maimuna take tambayarsa ina ya je yau shida baya son yawo ko da ya fita baya daɗewa yake dawowa? Ya ce "Hajiya yau gidan Abba na je, a can na wuni". "Ma sha Allah ka ko kyauta, lafiya ka baro su? Ya jikin Zainab ɗin?".
Ya ce "Suna lafiya, Hajiya wannan yarinyar da ta zo gidan ma".
Ta ce "Wa kenan?".
"Wannan ƴarta ɗin mana, Afnan".
"Haba dai? Shi ne ba a sanar da ni ba? Ko da yake nima zuwan kaina za ta yi mini".
Sadik ya yi murmushi sannan ya kuma cewa "Hajiya kuma tare da wata yarin suka zo black beauty, gaskiya yarinyar nan ta yi sosai Hajiya..." "Yaya kodai kana ciki ne?" Ummie ta yi saurin katseshi da tambayar tana dariya.
Murmushi ya yi ya ce "Sister baki ganta ba ne, yarinyar ta yi ne sosai, ban taɓa ganin yarinyar da ta burge ni kamarta ba, sai da na tambayi sunanta ta ce Maryam". Dariya Ummie ta yi ta ce "Lallai bamu nesa da shan biki kenan? Zan so naga wannan yarinyar da ta yi saurin saka yayana sabbatu haka". Murmushi ya yi, Hajiya ko da kallo take binshi. Lallai tunda har Sadik ya yi magana akan wannan yarinyar babu tantama sonta yake yi, wanda baya son zancen ƴan mata ko kaɗan, kuma baya so ayi masa zancen aure, amma shi ne yau da wannan maganar? Idan ko har haka ne da zata fi kowa farin ciki, kuma ba za ta bari a ɗauki lokaci ba ayi auren nan ba, za ta kira Zainab ta ji wace yarinya ce Sadik ya gani a gidan tare da Afnan, can ta tunna yarinyar nan ƙanwar Afnan kuma kamar Maryam ta ji an kira sunanta, tabbas ma ita ce don yarinyar nada black ce amma irin kyawawan nan. Murmushi ta yi a fili ta ce "Allah ya tabbatar mana da alkhairi, Sadik Allah yasa son yarinyar nan kake yi".
Ya yi dariya abin da bai cika yi ba ma, ya miƙe ya nufi ɗakinsa.
Maryam har ta kuma gida tunanin Sadik ya kasa barin zuciyarta da irin kallon da yake yi mata, tana zaune sai dai Mama taga ta yi murmushi. "Maryam wai lafiya ki ke kuwa? Tunda ki ka dawo daga gidan Afnan naga kina yin wasu abubuwan kamar mara gaskiya".
"Kai Mama babu fa komai" ta yi maganar
Mama ta ce "To ai shikenan" nan take sanar da Maryam batun komawarsu gidan Abba da zama, haka kawai sai Maryam ta ji ta yi farin ciki da jin wannan maganar, sosai fuskarta ta bayyana yanayin farin cikin da ta shiga, ta fara tunanin idan suka koma can za ta riƙa ganin gayen nan, kiran da Sharifa ta yi mata ne yasa ta daina tunanin da take yi ta ɗauki wayar.
****
Bayan kwana biyu duk wani shiri da su Haidar za su yi akan kumawa sabon gidansu sun yi, an yi karatun Quri'ani a gidan, Mama ta ƙara haɗawa Afnan tsaraba bakin gwargwado haɗe da kayan mata masu kyau, gaba ɗaya an kwashe kayansu a mayar da su wancan gidan, Abba ya kuma sai mata kaya na alfarma, amma Afnan ta ce kayan da Baba ya yi mata su za a saka mata a ɗakin da za ta fi amfani da shi, haka aka yi a can saman benen bedroom biyu da falo uku, sai bangaren Haidar, bedroom ɗaya aka saka mata kayan da Baba ya siya mata ɗayan kuma aka saka na Abba, sai nan ƙasa Abba ne ya saka komai a nan, Ammi ma ta yi mata siyayyar kayan kicin masu kyau, ta saka aka haɗawa wa Afnan kayan gyaran jiki da za yi amfani da su, ma sha Allah gidan ya tsaro ya yi kyau sosai. Umma ma ta sanar da can ƙauyensu batun tariyarta, Atika da ƙanwar Innarta sai suka zo domin rakata gidanta, Umma ta ce Dady ya yi haƙuri idan su Afnan suka tare yau ita kuma sai ta tare gobe, Haidar ya sanar da mai gidan da suke haya batun tashinsu, tare da yi masa godiya sosai. Dady da kanshi ya je gurin uban gidan Haidar ya yi masa godiya akan irin taimakon da ya yi wa Haidar ɗin, sannan ya mayar mashi da napep ɗinsa, ya ce ya yi haƙuri yanzu zai ɗora Haidar ne akan kasuwancinsa, amma hakan baya na nufin ya raba shi da Haidar ba. Duk lokacin da buƙata ta taso zai iya nemansa. Sosai ya yi murna da sauyin rayuwar da Haidar ya samu kuma ya yi masa fatan alkhairi.
Su Haidar sun tare a sabon gidansu, sai murna suke, barin ma Maryam har da rawarta, a daren Haidar ya shigowa da Afnan da manyan akwatina set biyu, kaya ne masu kyau a ciki, babu abin da ba'a saka ba, Afnan ta tambaye akwatinan waye? Ya ce nata ne, na lefe da baiyi mata ba, sosai ta yi mamakin yaushe ya haɗa wannan kayan hakan? Ya ce "Nasan za ki yi mamakin yaushe na haɗa lefen nan? Tun daga ranar dana fahimci ke ce matar da aka aura mini na fara tariyar kuɗin haɗa miki lefe, a ranar da Dady ya fara zuwa gidanmu bayan ya kuma gida washe gari ya kira ni ba tare da kun sani ba, yake tambayata akan irin rayuwar da muke ciki? Nan na gaya masa komai, hatta yadda aka yi aurenki sai da na gaya masa, nan ya karɓi kuɗin dana fara haɗawa na lefen ki ya cika ya haɗa mini wannan kayan" shiru ta yi tana kallonsa idonta cike da ƙwalla rungumi shi ta yi tana yi masa godiya. A daren haka Haidar ya kuma jinsa kamar sabon ango.
Washe gari aka da yamma aka raka Umma gidan mijinta, su Aunty Asiya ne da ƙannin Dady suka tarbi amarya, Ammi ta so zuwa amma yanayin girman cikinta ya sa ba ta je ba, Momy ma ta danne duk wani kishi ta saki jiki aka yi wasa da dariya da ita, bayan kowa ya watse Dady ya tara su guri ɗaya ya yi musu nasiha sosai, ya nemi alfarmar da su bashi haɗin kai wajan wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu. Umma ta tabbata Dady ya yi kewarta sosai, domin kwana ya yi yin abu ɗaya har sai da ta ji ta gaji sosai mararta ta fara ciwo sannan ya ƙyale ta.
Ƙiri-ƙiri Sadik ya gayawa Hajiya shi fa son yarinyar nan yake yi kuma da aure, ta ji daɗi sosai. Ta yi wa mahaifinsa magana, da yake shi yana can ba da shi suka dawo ba, ya ce ta yi wa Abba magana shima zai yi masa, ta samu Abba da maganar Maryam ya ji daɗi sosai, ya ce zai yi wa Malam Abbakar magana, amma ta bari su tare nan gidan tunda sunyi kusa baifi kwana uku ba.
*****
Yau Monday aka tura su Mami kotu, ba tare da ɗaukar dogon lokaci ana shari'a ba ganin sun amsa laifinsu, ya sa aka yanke musu shekaru masu yawa a gidan gyaran hali, tare da ba da izinin a je asibitin da abin ya faru a nemo likitar da ta yi musu aikin, sai dai ita ba a same ta ba, ta daɗe da rasuwa sanadiyyar gobara da ta yi a gidanta, sunyi kuka sosai tare da yin nadamar abin da suka aikata, Abba ya gaya mata cewar ya daɗe da sakinta dan kar ma ta yi tunanin akwai aurensa akanta, haka aka tasa ƙiyarsu gaba zuwa gidan yari, Mudan da Huda sun yi kuka sosai, ganin basu da yadda za su ya sa suka haƙura, suna komawa gida suka fara haɗa kayansu domin barin gidan, Abba sun bashi tausayi sosai kuma ya na son yaran, ya ɗauke su tamkar ƴaƴan daya haifa, ya so su ci gaba da zama a gidan amma Hajiya Maimuna ta ce ba ta san zancen ba. Da ƙyar ya ba ta haƙuri ta amince akan zai bawa Mudan gida ya ɗaura musu aure shida Huda.
Huda ta koma gurin Mamarta da zama kafin lokacin aurensu da Mudan ɗin, shi kuma ya ci gaba da zama a gidan kafin lokacin, amma ba da son ran Hajiya Maimuna ba.
Gaba ɗaya Zaliha ta rame ta fita hayyacinta kocan ga wada jikin nata yake, indai farin ciki ne ba ta cikinsa a gidan Daudu, kullum bisa ga uzzura mata yake ga rashin mutuncin da yake yi mata, ƴan uwanshi ma wulaƙanci suke yi mata hadda mahaifiyarsa, idan kaga Zaliha sai ta baka tausayi.
Lokacin da Hajara ta samu labarin su Mama za su bar gidan, hauka ne kawai ba ta yi ba, abubuwa gaba ɗaya sun ƙara taɓarɓare mata, ga Karima ta sakota gaba, Sanunsi ya daina kulata ko magana baya yi mata, sunje gurin Malam kwana biyu da suka wuce amma aikin banza. Ga yanayin da aka gaya mata ƴarta na ciki, ji ta yi gaba ɗaya duniya ta juya mata baya.
Gwaggo ma abin duniya ya isheta, tana ji tana gani ita da ɗanta amma yafi ƙarfinta, ga rashin mutuncin da Karima kiyi mata, ba ta ganin girmanta ko kaɗan, ko wace magana taga dama faɗa mata take yi.
Su Mama sun gama shirinsu gobe zasu tare a gidan, Abba ya sa an kwashe kayan Mami an kai mata can gidan Yayanta, ko tsinke nata bai bari a gidan ba, aka saka kayansu Baba a ɓangaren. Afnan ta yi farin ciki sosai da su Mama suka dawo kusa da su, yanzu gida ɗaya ne tsakaninta da su, su Mama suka dawo gidan, kowa sai murna yake, Ammi ba ƙara min daɗin hakan ta ji ba, Sharifa da Maryam Afnan hadda Feena duka suna gidan, ɗakin da Huda shi ya koma mallakin Maryam, sun ba je a ɗakin sa hira suke yi ko da suka ankare dare ya yi, Haidar ya zo ya tafi da Afnan da yake ita kusa suke Sharifa da Feena sai waya suka yi suka sanar akan sai gobe za su dawo.
Bayan kwana biyu da dawowar su, Abba ya yi wa Baba zancen Sadik akan Maryam, Baba ya ce "Ni ba ni da matsala zan bincike ta indai tana sonshi sai kuje gurin su Umar ku nemi aurenta a can".
Baba ya yi wa Mama maganar ya ce ta binciki Maryam ta ji, da Mama ta yi wa Maryam magana, tunda daga yanayinta ya sa Mama ta fahimci ta amince, ta sanar da Baba cewar ta amince, shiru Baba ya yi sai da Abba ya kuma yi masa magana sannan ya gaya mishi Maryam ta amince, basu ɓata lokaci suka sanar da su kawu batun zuwansu, ranar da suka zo neman auren a ranar aka saka sadaki da ranar aure wata biyu.
Maryam baki ya ƙi rufuwa, Sadik ya shirya zo zance, ya zo mata da waya mai kyau.
Sati ɗaya da kawo kuɗin auren Maryam Sharifa ma aka kawu kuɗinta da ɗan abokin Dadynta, lokaci ɗaya aka saka bikinsu da na Maryam hadda nasu Mudan aka haɗa.
Bayan wata ɗaya da sati biyu abubuwa da dama sun faru, masu daɗi da akasin haka, su Maryam da Afnan Umma rayuwa suke cikin farin ciki da jin daɗi, saɓanin su Gwaggo da Mami ƴan gidan gyaran hali, Karima ta uzzurawa Gwaggo da Hajara, shekaranjiya ma dukan tsiya ta yi wa Hajara da Gwaggo ta zo rabonsu ne ta bangajeta, ta faɗi akan hannunta nan take ta samu kariya a hannu, lokacin da su Baba Umar suka yi magana ta yi tsayinta akan Hajara ce, Gwaggo tana ihu aka yi mata gyaran hannu, Baba Umar ma shirye-shiryen tashi yake yi a gidan, saboda ya gama sabon gininsa. Gwaggo ta ce sai Sanusi ya saki Karima, amma ya ƙi ya nuna mata shi fa yana son matarsa, yanzu haka ma Hajara na zaune ta rafka uban tagumi sai ga Zaliha ta shigo mata fuska a kumbure, ƴan uwan mijinta ne suka lakaɗa mata shegen, kuma Daudu na dawo Mamarashi ta saka kuka akan Zaliha ta zage ta, bai tsaya bincike ba, ya ƙara mata wani dukan ya koro ta gida.
Hajara ta je gidansu Daudu ta riƙa masifar sai an sakar mata ƴarta, Daudu ya ce "Nima na gaji da wannan silin ƴar taki, babu komai a jikinta sai ƙasusuwa, kullum na shigeta ba na jin komai sai wani kashe dake ƙoƙarin nakasani ya mayar da ni mataccen namiji, amma wallahi ba zan sake ta ba sai an biya ni kuɗina dana kashe". Gaba ɗaya jama'ar gurin babu wanda bai ji kunyar abin da ya faɗa ba. Cikin takaici Hajara ta tambaye shi nawa ne kuɗin? Ya gaya mata, ta koma gida ta kira dillaliya ta siye kayan ɗakinta katifa ɗai ta bari. Duk da ba ita ta karɓi kuɗin auren ba gara ta biya a sakar mata ƴarta. Ta haɗa da sauran kuɗin da take da shi ta biya Daudu ba tare da sanin su Gwaggo ba, Daudu ya danƙarawa Zaliha saki biyu. A ranar Hajara ta saka aka kwaso kayan ɗakin Zaliha, sai lokacin mutanen gidan suka san abin da ke faruwa.
Bala'i ta shiga yi da kumburarren bakinta da Karima ta buge, ta ce "Ina fatan dai baki da cikin wannan barbaɗaɗɗen a jikin ki?" Ta yi maganar tana kallon Zaliha.
"A'a ni fashin sallah ma nake yi"
"Yawwa to Alhamdulillah"
Sosai Baba Umar ya yi faɗan kashewa Zaliha aure da Hajara ta yi, kawu Sanusi ma haka Karima ta ƙara ziga shi har ya ce sai Hajara ta bar masa gida tunda ta kashewa ƴarsa aure, da ƙyar ƴan uwanta suka bashi haƙuri ta zauna.
*****
Umma amarci ɗai ake gurza, kuma suna zaune lafiya ita da maman Sharifa, Afnan na yawan kai musu ziyara, har gurin Hajiya kakar Haidar tana zuwa, Aunty Asiya ta samu miji wani ne da matarsa ta rasu da yaransa bakwai ta aura. Umma ta shirya ita da Dady hadda Momy suka je ƙauye ziyara, su Inna sunyi murna sosai da zuwan su, sai yamma Abba da Momy suka juya, nan suka bar Ammi sai ta kwana biyu kafin ta koma.
An fara shirye-shiryen auren su Maryam, ana saura sati ɗaya ɗaurin aure Ammi ta fara naƙuda aka kaita asibiti, Abba da shida Hajiya Maimuna suka saka ido sosai akan likitocin duk da babu wanda zai cutar da su a yanzu ɗin, ba a ɗauki dogon lokaci ba ta haifo yaranta biyu mace da namiji, ma sha Allah yaran gwanin burgewa macen babu inda ta baro Afnan, namijin kuwa duk Abba ya ɗakko, nan familyn suka ƙara shiga cikin farin ciki, a lokacin Afnan tana fama da laulayi tun tana ɓoyewa har aka ganota, yanzu ta saki jiki sosai da su Abba har tana shiga ta yi duk abin da take so a gidan. Haka ta ci gaba da daurewa aka ci gaba da shirye-shiryen bikin aure da na suna da ita. Lokacin biki ya zo an sha shagali sosai ga bikin suna da aure, hadda auren Huda da Mudan aka yi, da auren Sharifa da angonta Kabir. Ko wace ta tare a gidan mijinta.
Bayan shekaru biyu, yaron Afnan wanda ya ci sunan Baba wato Abbakar ana kiran shi da Annur, har ya iya tafiya, shekararsa ɗaya Afnan ta kuma yin wani cikin ba dan ranta ya so hakan ba, dole ta haƙura, Maryam da Sharifa duka sun haihu ko wace ta haifi ƴarta mace, Huda ce dai shiru har yanzu rabon bai zo ba, ba laifi tana shiga cikin su Afnan duk da Maimuna ba ta son hakan. Haidar an zama babban mutum yanzu duk wasu harkokin kasuwancin Dady shi yake juyasu, kuma ya jawo abokinsa Faruk sosai a jikinsa tare suke yin wasu abubuwan, Baba ma haka kasuwancinsa ya ƙara bunƙasa. Faruk ne ya auri Feena ƙawar Maryam lokacin da suka zo gidan Afnan tare da Maryam, shi kuma ya zo a nan suka haɗu.
Gwaggo har yanzu tana fama da hannunta bai warke ba, kuma Karima ba ta fasa gana musu azaba ba ita da Hajara, gaba ɗaya sun fita hayyacinsu, ga kawu Sanusi ya zama abin tausayi, Karima ta mayar da shi kamar wani dolo sai abin da ta ce, ganin halin da Gwaggo take ciki ya sa Abba cewa Baba ai gara ya mai ita kusa da shi, Baba ya mayar da Gwaggo gidansu, a lokacin Gwaggo take kuka da roƙon yafiyar Mama akan abin da ta aikata musu ta san hadda haƙƙinsu ke bibiyarta.
Ya rage daga Hajara sai Karima a gidan da Zaliha dake zawarci, yanzu ta zanzare iskancin da Hajara take yi wa su Afnan fata shi Zaliha ke yi, babu wanda bai san halinta ba. Hajara ta yi biyar bokaye da Malamai akan Karima amma aikin banza, sai dai aci kuɗinta a banza.
Baba Umar na sabon gidansa hankali kwance, har sun aurar da Bahijja tana nan da tsohon cikin.
A gidan yari kuwa cikin shekaru biyu su Mami sun koma kamar basu ba, sun yanƙwane, ga ciwon zuciya da Mami take yi wanda har ya tsananta, ya kaita kwance, kuma tana fama da wani ƙurji a ƙafanta ya na fitar da ruwa, wani lokacin hadda tsutsa ke fita a cikinsa, a nan asibitin gidan aka kwantar da ita, sati ɗaya da kwantar aka ga ciwon babu sauƙi ana ƙoƙarin kaita babbar asibiti ne Allah ya yi mata rasuwa, Turai ta kaɗu sosai wanda hakan ya fara taɓa mata ƙwaƙwalwa ta kama abubuwa kamar na marasa hankali, mutuwar Mami ta taɓa Mudan da Huda sosai. Abba ma ya damu da rasuwarta, Mami ko hadda kukanta. Hajiya Maimuna "Allah ya jiƙanta" shi ne kawai abin da ce.
Gwaggo ta fara samun sauƙin hannuta, saboda yanzu tana samun kulawa sosai, ba kamar da ba.
Hasina ɗiyar Turai ma an yi mata auren, da ta je taga halin da Momynta ke ciki, ita ma ta yi kuka sosai, har ta je ta dawo Turai ba ta fahimce waye ita ba.
Haidar na zaune a falo Annur ya shigo mishi da kuka ya ce "Annur lafiya waya taɓa mini kai?".
Yaron ya ce "Ba Momy ba ce"
"Me Momyn ta yi maka?".
"Daga na ce ta bani wayarta na yi game shi ne ta kore ni" ya yi magana cikin gwarancinsu na yara.
Haidar ya ɗakko wayar shi ya kunna masa game, ya ce "Zauna ka yi bari na je na same ta".
Zama ya yi ya fara game ɗin, Haidar ya nufi ɗakin Afnan
Tana kwance cikin bargo ya ce "Madam me ya sa aka hanawa yarona waya ya yi game bayan kuma Babansa ne ya sayi wayar?".
Kallon Haidar ta yi ta ce "An hana shi, Baban nasa sai ya zo ya ƙwatar masa".
"Yanzu kuwa zan zo abin da ma ya fi ƙwatar waya zan yi". Ya yi maganar ya na dira saman gadon ya shige cikin bargon shima, dariya suka yi gaba ɗaya tare da rungume juna duk da jikin jikinta ya fara girma.
Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah a nan na kawo ƙarshen littafin Ramin Ƙarya na fara shi 20/5/2025 na gama 5/9/2025 Ubangiji Allah abin da na rubuta daidai Allah ka bani ladan faɗakarwa, akasin haka Allah ya yafe mini, ina fatan jama'a su ɗauki darasin dake ciki, kuma aiki da shi. Godiyata ba za ta taɓa ƙarewa ba a gare ki, abar ƙaunata Aysharcool haƙiƙa kin yi namiji ƙoƙari sosai wajan tallafa mini, ina godiya sosai da sosai Allah ya dafa miki akan dukkan lamuranki ya baki abokin zama na gari wanda zai kula muna dake cikin aminci da salama.
Masoyan wannan littafin ina godiya sosai da comment ɗinku da addu'oinku a gare ni, ina son fisabilillah, sai Allah ya sake haɗa mu a sabon book ɗina. Domin ba da shawara gyara ko ƙorafi za a iya mini magana ta wannan lamabar ***
Amanarcool✍️