11
by @mommuhseen
_*NAYI SAKE....!*_π
π '''DA DAMA TA'''
FREE BOOK ONE.
_*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*_
Mrs bb
Mom muhseen.
Watt pad name
Humaira3461
π ΏοΈ......19&20
Tunda na gama sallah nai azkar dina ina zaune gefensa na dora kaina gefe gadon idona rufe amma ba bacci nake ba, kaina ne ya cushe da tarin tunaanuka har basan wanda zan dauka ba, kamar wasa naji motsin Daddy hannunsa dake kusa da kaina naji yana motsi, nai saurin tashi cikin dan jin dadi ina kallon fuskarsa idon sa yake son bud'ewa ahankali, daker ya samu suka budu ya sauke su akai na, farin ciki ya cikani ainun, nace "Daddy ka farfad'o? Alhamdulillah Sannu Daddy ubangiji ya baka lafiya"
Lumshe idonsa yai ya bude alamun ansawa, nace "bari na kira Dr kila bai kai ga shigowaa ba"
Wayata na dauko har hannuna yana rawa na soma kiransa, kamar jirana yake kuwa ya dauka da sauri, "ya akai Bahiyya, lafiya dai ko?"
Kwallan farinciki suna zuba nace masa "Daddy ya farka yanzu Dr"
"Alhamdulillah, ina hanya ai nakusa isowa just give me some minutes"
Na kashe wayar na koma wajensa kallona kawai yake, ni kuma ina ta farin ciki na riko hannunsa ina sake masa saannu, da hannu yake nuna mun na cire masa oxygen din, duk da nasan ba dai-dai bane amma tunda yana so saina zare nasa shi yaja d'an numfashi kadan, wandaa har yanzu bai daidaita ba.
Magana yake yi mun saida na matsa sosai wajen bakinsa na kejin abunda yake cewa,
"Ki Kira mun Fa'iz"
Gaba na naji ya fad'i daya anbaci sunan sa, inkira masa Abbyn Amnat kuma? Kalon sa nake na rasa abunda zance masa saboda ni bazan iya tuna ranar ma danai waya dashi ba.
Nace"Daddy kayi hakuri kaida baka lafiya mezai xo yai maka?"
Ya sake cewa, "ki kira mun shi inason nai magana dashi"
Ganin yadda kirjinsa ke sama sa kasa wajen shakar numfashi dole na maida masa oxygen din, duk da ya nuna baya so.
Fitowa nai daga cikin dakin na zauna daga nan falon dakin cikin kujerun dake wajen na buga tagumi, bansan me yasa yace inkira masa shi ba, wayata nake kallo saboda no din tashi ma bana tunanin tana zuwa, saboda dadewarta a wayata da kuma rashin wayar da bamayi banida tabbacin cewa tana aiki.........Dr ne ya iso shida wasu nurse's na mik'e muka gaisa dashi, ya kalleni da alamun tambaya.
"Lafiya? U look so bad"
Sai kwallah sharrrr suka zubo mun, nai saurin sharewa nace "bakomi ka shiga ka duba shi"
Bai yadda ba amma bai ce mun komi ba suka shiga cikin, ba jima wa sauran Doctors din da suke dubashi tare suka iso,ni dai ina nan rik'e da waya a hannuna na kasa aiwatar da abunda yace, to idan nama sameshi a wayar mezan ce mashi? Fa'iz kazo Daddy na baida lafiya yana nemanka? Bansan amfanin kiran sa ba...........haka nan naji inata kuka kasa-kasa saboda rashin madafa, inama ace mahaifiyata tana nan! Ina ace bayan ni ta haifa mun kanne maza da mata da zan ringa shawara dasu,in ringa sharing damuwata dasu, hakika duk wanda ya rasa kulawar uwa yai kuka, wannan ciwon da radadin sai wanda bai tashi da ita ba kadai ya san shi,na jima Sosai ina kukan saiga Ammah nan sun iso ita da yaranta, ko kallonta banyi ba balle in sa ran gaidata, sun tura kofar dai sunga da likitoci suka dawo, umaima da Jalila suka gaisheni suna tambayata jikin Daddy, inata hawayena nace musu da sauki ba laifi, nan muka zauna dasu munyi jigum jigum, ga kwandon breakfast nan da suka zo dashi.
Kaina a soke kasa inata sharar hawaye naji kamar ankira ni............"MAAH"
kamar daga sama naga Amnat kusa dani, azabure na dago kaina aikuwa ita d'ince tsaye cikin uniform d'inta, saurin share fuskata nayi najawota na rungume da karfi inajin wata matsananciyar kewarta, da kaunar ta suna ratsa ni sai kukana ya dawo sabo, kamar daman jiran wani nake nayi ajikinsa, rungumar ta danai sai nakejin kamar na samu kwarin guiwa, banida wani dazan runguma nai kuka ya lallasheni, idan daddy yatai yabarni bansan inda zan saka kaina ba.
"Maah ki daina kuka kinji, me akeyi asibiti? Anty jalila meya samu maah take kuka, Ammah ce ta doketa ko?"
Isowa wajenmu jalila tayi tana durkusawa kusada ita tace, "Aa baby,babu wanda ya doki maah dinki, Daddy ne bashida lafiya"
Banyi tunanin ashekarunta zatai wannan abum ba,ta janye jikinta da sauri tana zaro idonta, "Daddy baida lafiya? Yana ina Anty Jalila inaso in ganshi"
Sai ta kama kuka ta juya inda ubanta ke tsaye ya rungume hannuwa, inajin suna gaisawa da Ammah yana mata yamai jiki,su Umaima duk suka gaidashi banji khaleesat tayi magana ba.
"Abby Daddy baida lafiya, inaso inganshi don Allah Abby, kace Maah ta kaini wajensa don Allah kaji Abbyna"
Sosai yarinyar take kuka kamar me, ya durkusa ya rungumeta yana lallashinta, "in kina kuka ba za'a barki ki ganshi ba, don haka oya keep quiet stop crying zakigan shi yanzu"
Tai lub ajikinsa tana shashsheka,kafin ta sakeshi taho wajena na dauketa na dora jikina ta kwanta kan kirjina mukai shiru, nidai bance masa ina kwana ba haka shima bai ce mun komi ba, balle ya mai jiki.
Haka mukai ta zaman kurame har Dr saheeb ya fito yana mun magana, "kin kira shi kuwa?"
Nasan kan maganar sai bance komi ba na nuna inda yake tsaye, ya juya wajensa sukai musabaha yana masa yamai jiki, yace "tunda ya farka kai yake nema, so inba damuwa muje ka ganshi pls"
Dirkowa Amnat tayi da sauri, "nima zanje likita"
Yai murmushi yace, "ok baby, no noise no cry OK?"
Ta daga kanta sannan suka shiga suka barmu anan, wani dogon tsaki Ammah taja tana cewa, "wannan ai rainin hankali ne, ya zamu zo mu iyalinsa ba abarmu mun shiga ba sai wani bare,wannan ai wulakanci ne"
Bansan ma sadda nake bata ansa ba, "Baren dai shi ya nema wata kila iyalin nashi basuda wani muhimmancin shiga wajensa, in banda ciwo babu abunda zasu kara masa."
Jinai tace, "keeee!,dawa kike? Allah yasa ba dani kike maida magana ba, kinsan da wa kike magana kuwa?"
Wani irin karfin zuciya yazo mun,ji nake zan iya tashi na lakad'a mata dukan bala'i a yadda bakejin kaina, na wurga mata wani jahilin kallo nace, "wanda ya tsargu to dashi nake,kuma magana nasan da wadda bakeyi ba bakuwata bac............Yaya Bahiyya karfa kice agabanmu zaki zagi uwarmu, don ba d'aga miki zamuyi ba akan me iye?"
Cewar khaleesat ina tashi duk wani zafin raina da wutar cikina akanta na sauketa na wanketa da mari, nace "Bismillah shege ka fasa, zoki dakeni ko kuma ki rama mata, don kutumar uwarki har an haifeki da zakina maida mun magana.........kikamareta Bahiyya?"
Cewar uwar tata a tunzure nace, "ehy, na mareta kuma zan kara daga sadda ta sake tsomo bakinta cikin maganata, bama ita ba ko waye ya nemi yi mun iskanci zan mareshi koma fiye da haka...........Subhanallahi meke faruwa hayaniyar miye kuke anan, kunsan kuwa halin da yake ciki baya son hayaniya, please idan har zaku kawo mana matsala kuna iya tafiya."
Cikin fushi Ammah tace, "zaku barmu muganshi ko aa?"
Hanya ya bata yace, "five minutes please"
Daidai sadda Fa'iz ke fitowa kamar wanda aka zarewa duka lakkar jikinsa, fuskar sa kad'ai ta isa ta sanar dakai yana cikin tsananin tashin hankali,bai tsaya nan falon ba kofar waje ya fita.
Bayansa nabi da kallo zuciyata na bugawa, ganin sa kadai yasa zuciyata wani irin yana yi, bansan me sukai magana akai da daddy ba, amman zuciyata tana son sani.
Tashi nai nashiga cikin dakin na iske yaran sai kuka suke Ammah ta rik'e hannun sa tana hawaye, hankalina yai kololuwar tashi da gudu na isa inda yake, sai naga ya bude idonsa naja ajiyar zuciya, daker ya iya furta cewa.
"Kice ta sake ni Bahiyya"
Cikin zafin ciwo da rad'ad'i yai maganar, ai basan sadda na buge hannunta ba, ina ta zubar kwallah nace "pls kuje tunda kun ganshi, taya zakuzo ku sashi gaba da hayaniya"
Dr ya shigo shima yace duk su fita waje, jikin Ammah yai sanyi amman ni banga wani nadama tattare da ita ba, bakar munafuska.
Dr saheeb dani muka taimaka masa ya wanke bakin sa aka bashi abun kalaci, yasha magungunan shi sannan ya jingina na dan lokaci kafin akai masa allurar bacci don ya kara samun hutu.
Rik'e yake da hannuna yana alamun zai baccin yake ce mun, "Allah yai miki albarka Bahiyya, kiyi hakuri da Rayuwa aduk yadda tazo miki, ni nan babu irin wuya da kalubalen daban shiga ba kafin Allah ya zamar dani wani abu, wanda ta dalilin Zamana wani abun yajefa rayuwata ahaka, karki yadda dakowa sai kanki dr saheeb da Fa'iz zasu tsaya maki aduk abunda ya taso miki............kuka nake kasa-kasa saboda idan yana wasu maganganun gani nake mutuwa zai yabarni.
"Daddy meyasa sai Fa'iz? Daddy babu sauran abunda ya rage tsakanin mu, ko ina neman taimakon kowa bazan nemi nashi ba saboda bazai tab'a taimakona ba"
Murmushi naga yayi yace, "zai taimaka miki na rok'i alfarmarsa ya kuma ansa mun, kedai kiyi hakuri sannan kiyawaita adduar Allah ya bayyana miki mahaifiyarki, aduk randa kuka had'u kisanar da ita tayafe mun........."
Bacci yaci karfinsa dole na zare hannuna na barshi na fito, Jalila da Umaima kadai na iske sai amnat muka zauna kowa yai shiru kamar muna zaman makoki amnat tai lamo ajikina duk da tana yarinya ciwon Daddyn ya dameta.
"Yayah Don Allah ko kinsan wani abu daya had'a Daddy da Ammah? Wallahi hankalina baya kwance akan sabanin da suka samu, yanzu ma anan ciki dakin inaji yana ce mata in sha Allahu tun aduniya zata girbi abunda ta shuka, shidai bazai iya yafe mata ba, kukan da kika iske tana yi kenan muna taya ta, don tana ta bashi hakuri da kuma sanin metayi masa amma saidai yace, marawuyya bakida imani tun aduniya zaki gani, wannan maganganun sun tayar mana da hankali, sannan abunda ya sake d'imautani Yaya Bahiyya shine yace mana mu dauki kaddara aduk yadda tazo mana, domin kuwa uwarmu ta jefamu cikin halaka"
Umaima ce duk take wannan maganganun tana kuka Jalilaa nayi, shiru nai bayan na gama saurarenta saboda dai nasan inda duk maganganun sa suka nufa, kuma ita Ammah tunanin ta bai bata Daddy yasan komi akan abunda takeyi ba.
"Kubar wannan kukan, zafin ciwo ma ba abunda bai sanya mutum ya fad'a, duk da nasan sun samu matsala amma bazan iya cewa ga abunda ya hadasu ba, kuyita masa addua Allah ya bashi lafiya."
Muna nan har akai la'asar salla ke tada mu, muna dan lekashi koya farka amma baccin sa kawai yake, Dr ya bada aka yo mana take away amman daker naci abincin loma uku, don bakina babu dadi kamar yadda zuciyata take,har lokacin baba Badaru baizo ba bale iyalinsa, ganin baccin yai yawa yasa naje nace ma Dr kozai duba shi yaga lafiya dai ko? Saboda tun goman safe yake bacci har biyar tayi.
Tare muka fito dashi ya shiga dakin ni kuma na zauna, saiga Abbyn Amnat ya shigo da karfi zuciyata ta doka nai saurin kauda kai daga inda yake, alokacin dai na danne abunda ke nukurkusata nace masa, "ina wuni"
Shima sama-samaa yace "lafiya, nazo tafiya da Amnat ne tunda bata samu zuwa sch ba...........karar wata na ura mukaji wadda ke nuna ana bukatar likitoci, cikin minty daya sai gasu aguje, suka shigacikin dakin,jinai cikina yai wata irin kara zuciyata ta soma bugawa sa sauri da sauri, atare nida shi muka kalli juna ai bansan sadda na banka kofar na shiga ba, nurse ce ke rik'eni ina fixgewa saboda inason isa inda Daddy yake, sai jona masa shock ake alamun dai baya numfashi so ake ya dawo, amma babu alamar hakan, fizge fizge nake ina wani irin kuka ina kiran Daddy, su biyu suka fiddoni zubewa nai kasa kamar wata mahaukaciya ina kuka, su umaima nayi amnat ta fado kaina itama tana yi, isowar Baba badaru da iyalinsa fitowar Dr Saheeb daga dakin yana hawaye, kuka yake sosai yace "we are sorry, yallab'ai he dead...........wannan itace kalmar karshe da kunnena yaji mun na zub'e k'asa bansan inda kaina yake ba.........
Kulli nafsin za'ikatul mautππππ
Allah yajikan Daddyπππ»
Mom muhseenβπ»