NAYI SAKE DA DAMA TAFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

NAYI SAKE DA DAMA TA

  • 1views
  • 20chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · 1

*NAYI SAKE....!*💘    💘 '''DA DAMA TA'''   FREE BOOK ONE*** bbMom muhseen.Watt pad nameHumaira3461      🅿️.....1&2"Banga ranar da zan zo gidan nan bakiyi kuka ba, shin wai Fa'iz shi kad'ai ne d'a namiji a duniyar nan da har zaki karar da kuruciyarki wajen jiransa? Kukan ki ya isa haka nan akansa da ace kukan zai miki magani tun tuni da yai miki, tsawon wannan lokacin inda ko yaya yana jinki aransa bazai banzatar dake haka ba,to ya nuna maki karewa da karau ma ya furta maki da bakinsa,mace mai irin sunan ki ma baya marmarin sake Aure balle ke karan kanki, to dalili name ki tsawwala na rayuwarki, dubeki BAHIYYA kinbi kin lalace kinyi baki kin rame wallahi wanda ya sanki shekarun baya bazai ce kece a haka ba, nidai nayi lallashin duniyar nan akan kiyi hkr da fa'iz ki yafesa, ki fuskanci rayuwarki ta gaba shine zai fishsheki alkairi"Kuka kurin nake silently sai kana cikin dakin zaka iya jin sautinsa, na saka fuskata cikin ta fukan hannaye na ina tayi baji ba gani, sun dauki tsawon mintoci ba wanda ke magana banda sautin kukana, kafin na fara sassautawa ina kokarin dainawa nake magana cikin sassanyar muryarta data kara yin sanyi saboda kukan da nasha."Sakina duk abunda kike gaya mun nasan gaskiya kike nuna mun,da ace ina cikin ransa ko yayane tabbas zai waiwayoni ya yafe mun, ya mance baya ya maidani gidansa, amman yama riga yai aurensa tuni hakan ya sake nuna mun cewar Fa'iz da gaske yake ya yanke duk wata alak'a dake tsakaninnmu, bansan meyasa ko naji haushinsa araina sai indaina saboda dai babu irin damar da bai bani ba wajen gyara kuskurena, ba irin hakurin da bayyi dani ba alokacin da nakejin duniyar tana juyawa dani, nice na zubar da duk wani kimata ga idonsa nice najawo ma kaina duk wulakanci da cin mutuncin da yake mun, NAYI SAKE DA DAMA TA sakina, sannan nayi asarar miji irin fa'iz koda wani auren nayi nasan bazan tab'a samun mai hakuri irinsa ba, mai kawaici da kauda kai irinsa ba, kamar yadda kikace ya kamata ace na hakura dashi na fuskanci rayuwar dake gabana nida y'ata, duk da nasan watarana dole ya ansheta duka daga gareni."Wasu hawayen masu ciwo suka sake zubo man, sakina ta rik'o hannuna cikin tausayawa tana cewa,"Ki dauka haka Allah ya hukunta miki Bahiyya,ki cigaba da hakuri watarana saidai labari abunda zakiyi kiyi kokari daddy yabar fushi dake,zaki samu salama kota b'angarensa ne sannan inda zan gaya miki kiji ki maida masa yarsa zaki fi zama lafiya...............kiyi hakuri sakina ina masifar son Amnat nan da can bana son ta matsa daga gareni, bazan iya maida masa ita ba rabin jikina ce ita din""Shikenan Allah ya zab'a abunda yafi zama alkairi, amman ki dage da addua itace takobin mumini sannan kiyi nesa nesa da  Ammah kinfi kowa sanin s...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters20
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play