12
by @mommuhseen
*_NAYI SAKE....!_*๐
๐ '''DA DAMA TA'''
Free Book one.
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
Mrs Bb
Mom muhseen.
Wattpad name
Humaira3461
๐ ฟ๏ธ.......21&22
Rayuwa babu daddy tamkar cin abincin da babu magi da gishiri ne aciki, saidai kaci don yunwa badan dadi ba to haka rayuwar tazo mun, tun daga sadda kunnuwana suka riski wadannan munanan kalaman daga bakin dr van sake sanin inda kaina yake ba, sati na guda akan gadon asibiti ban sanin wanda yake zuwa yana tafiya, Dr tsaye yake kaina bakin iyawarsa amma har yanzu ba alamun farfadowa.
Allurai ne aketa zuba mun acikin drip din dake shiga jikina da taimakon Allah da taimakonsu rannan na farfad'o,sakina na fara gani zaune gabana kafin na fara karewa d'akin kallo idona ya sauka akan umaimah.
Na dad'e ina kallonta ina son hasaso meya faru dani, menakeyi akan gadon asibiti muryar sakina naji cikin kunnena tana cewa, "Alhamdulillah, kinga umaimah ta farfad'o maza jeki kira Dr"
Saboda sauri har tana bugewa da k'ofa ta fice, idona na sauke akan sakina kafin cikin disasssar murya na ce mata, "meya sameni?"
Kwalla nagani idonta amma tai saurin sharewa tace, "ba wani babban abu bane yanzu ma za'a sallamemu.........dr da umaima ne suka shigo cikin sauri, na juya garesu ina kallon su tambayata yake ya nakejin jikin, ba inda yake mun ciwo dai ko?
Tsaresa da ido nai na tsayin lokaci kafin cikin yan seconds nazabura na diro daga gadon na rik'e Dr saheeb da karfin gaske ina cewa, "kaine kace Daddy ya mutu ko? Kaine ko? Karya ne bai mutu ba, Daddy na bazai mutu yabarni ba mugu kaine zaka kashe shi..............sai na tafi luuuuu na zube a sume, a sukwane ya taro ta shida sakina suka dorata bisa gadon, umaima kuka take sosai.
Sakina tace, "Dr meke shirin faruwa da Bahiyya?kardai rad'ad'in mutuwar nan ya tab'a mata kwalwarta"
Gyara drip din da aka sanya mata yake fuskar sa cike da damuwa ainun, yace "hakan ba zata faru ba insha Allahu"
Ya fice da sauri yabarsu nan, office d'insa ya wuce cikin damuwa da tunanin ta yadda za'a shawo kan lamarin nata,kwana bakwai kenan shida manyan likitocin asibitin suke tsaye kanta, da fatan in tafarka ba zatai irin wannan abun ba, don yana daga cikin rikicewar tunani mai alamar hauka,jikinsa a mace ya soma Kira awayarsa.
"Idan ka samu lokaci anjima ka shigo inason ganinka pls"
Ya sauke wayar,ya koma dakin ya duba daidaituwar numfashinta da bugun zuciyarta,sannan yace da sakina.
"Komi normal in sha Allahu,kina iya tafiya umaima zata zauna da ita muna fatan zuwa gobe komi zai daidaita"
Ta rausayar da kai cikin damuwa, "shikenan Dr, ubangiji ya bata lfy"
Sakina tatafi shima ya wuce office dinsa ya cigaba da aikin dake gabansa, amman rabin hankalinsa yana akan bahiyya.
**********
Sallama tayi cikin sassanyar muryarta bacin taga alamun ya ansa sannan ta shiga, yana cikin saka links fuskar nan d'inke cikin damuwa, ya dan kalleta kadan yana cigaba da saka links din, yace "Husna lafiya kuwa?"
Gefen gadonsa ta zauna itama fuskar da damuwar tafara magana tana rausayar da hannu, "Abbyn Amnat magana zamuyi, kuma naga kana shirin fita bacin baka zuwa ko ina irin wannan lokacin"
"Fitar ta dole ce, kifadi abunda ketafe dake ina jinki"
"Maganar da tsayi zanjira ka dawo,inhar ba zaka dad'e ba"
"Nima ban sani ba kozan jima, amman koma na jima din Koda safe ai sai muyi koko?"
Ta jinjina kai kurin tana binsa da kallo, ya wuce hanyar fira yana cewa saiya dawo.
"Allah ya tsare yasa Adawo lafiya"
Yace"Amin"
Tun daya fita ta buga tagumi afalo, tana kallon Amnat datai bacci akan three siter, bacin gaba daya hankalinta bama anan yake ba, ba zata iya tuna rabon da taga murmushin Fa'iz ba, ba zata iya tuna rabon ma daya nemeta ashimfida ba, ba zata iya tuna rabon daya zauna yai fira da ita ba, tayi dukkan tunaninta ta gama bata gano abunda tai masa ba, shima bataga alamar tayi masa laifi a fuskarsa ba, tayi tambayar duniyar nan ko baida lafiyane? Ko wani abune yake damunsa? Amma amsar daya ce watau aa babu komi.
To meke faruwa haka?bata son shigo da maman ilham aciki tana fatan ta daidaita gidanta kafin hakan, amman tayaya fa'iz ya canza kamar ba shiba.
Yau ko zai kai talatainin dare zata jirasa tagaji hakanan.
*******
Saida ya fito yake nadamar meyasa bai bari driver ya tukosa ba, kwata kwata babu kuzarin tukin tare dashi, hasalima tunda Dr ya kirasa natsuwarsa tabar jikinsa, a haka dai ya samu ya isa asibitin lokacin karfe takwas tayi.
Bai tsaya ko ina ba sai office dinsa, bai samai ba sai ya kirasa awaya.
"Nazo baka office,ok saika iso"
Ya sauke wayar yana zama bakin kofar office din inda aka aje kujeru na zaman jiran patient,bai dad'eba ya iso sukai musabaha sannan suka isa cikin office din.
Dr yai jimm dafe dakai k'asa baice komi ba na dan lokaci, Fa'iz hantar cikinsa ta d'an juya yace cikin rashin natsuwa, "ya kai shiru, ko ta mutu ne?"
Saurin dagowa yayi yana kallon sa yace, "fatan mutuwa kake mata ne?"
Kawar dakai yai gefe yace, "ba haka nake nufi ba, naga kayi shirune kamar akwai wani babban abu"
Isa Dr ya fesar yana cewa, "ehy babban abunne, saboda mutuwar Yallab'ai ta tab'a Bahiyya sosai, alamun rikecewar tunani da tabuwar kwalwa yana shirin kamata, dazun abunda tayi ya tada mun hankali, dole sai mun had'a da rokon Allah da kuma taimako na dangana da za'a nemar mata,don tunaninta ya juye sosai."
Shiru fa'iz yai wanda bazan iya gane meke cikin zuciyarsa ba akan abunda Dr ya fad'a, amman ga dukkan alamu shima abun ya dan tab'ashi don fuskarsa ta nuna.
"Idan kana ganin na takura maka ko, andora maka nauyi kabar komi hannuna"
Wani kallo yaima Dr,shima ya tsaresa da ido su kadai suka san kaallon me suke ma juna, kafin Fa'iz ya tashi yana cewa, "Alk'awari nane na riga na dauka kuma na ansa, cewa zai taimaka mata iyakar karfina har illa masha Allah,don haka karka sake gaya mun magana irin wanan pls, zuwa safe zansan yadda za'a, matsayinka na Likita kaima kanemi wata mafitar"
Ya juya ya fita yabarsa,bai ko nemi ganin ta ba ya shiga mota ya wuce gida, gaba d'aya maganganun sa sun b'ata masa rai, duk da yadda suke shida ita, ai baya mata fatan mutuwa,kuma shi musulmine dole duk mai imani ya tausaya ma halin da take ciki, kuma yana jin tausayin nata har cikin ransa, abunda ke tsakanin su kuma wannan daban yake.
Bai koma gida ba ya nufi wata unguwa can cikin geto side d'in cikin kano,yai samu wani waje yai parking sannan ya shiga wani dogon lungu kafin ya samu kofar gidan ya shiga yana sallama daga zaure.
Aka lek'o ana tambayar waye, yaron yana ganinsa ya washe fuska yana cewa ya shigo,alamun dai sun sanshi sosai.
"Fa'izu kaine tafe adaren nan, sannu da zuwa ya gida ya iyalin"
Kanshi k'asa yana murmushi yake ansa mata, sannan yace "malam nazo gani ko yana kusa"
"Ehy baiyyi nisa ba, yanzu nan zaka ga yashigo, zauna ga tabarnan isuhu kawo masa ruwa..........wallahi inna na gode abar shi"
"Toshikenan, duk ya kuke fatan kuna lafya ai muhibba ma kwanan nan ta lekomu,harda abun arziki,mungode sosai fa'izu Allah yaima rayuwa Albarka"
"Kai Inna ba komi wallahi,ai duk daya ne adduarku kawai muke buk'ata a kodayaushe"
"Aikuwa kun samu,ba dare ba rana yimaku muke"
"To muna godiya..........malam din yai sallama yana cewa "ai ina ganin mota akasan layin nan nace yarona ne fa'izu, ashe kuwa hakan"
Murmushi fa'iz yake yana tashi ya risina suka gaisa yace, "aikuwa nine baba malam, nazo wajenka ne wallahi wata yar damuwace dani"
Yace"subhanallahi, to maza k'araso ciki mu tattauna"
Dakinsa suka shiga suka sake gaisawa sannan ya sanar dashi halin da Bahiyya ke ciki, kasan cewar yasanta yasan babanta kuma yasha taimakonsu ba kad'an ba, duk ta dalilin fa'iz kuma yasan tsohuwar matar sa ce, yace"Allah sarki baiwar Allah, dole ne ta shiga wannan hali amma in shaa Allahu da taimakon Allah zata dayaye, ahankali zata dawo daidai yanzu zan fara mata rubutu da iznin Allah, zuwa safe kafin ka wuce aiki kazo ka ansa kotana bacci ad'ura mata, aakuma ringa shafa mata ga fuska na kwana uku ne,inya kare sai asake ansar wani in sha Allahu komi zai wuce"
"Shikenan baba malam angode.......bana son jin wata kalmar godiya kana jina, ai kamar y'ata nai mawa don haka maza jeka ba komi ai"
Sukai sallama ya aje mai kudi,daker ya ansa sannan sukai sallama da inna ya fito ya tafi.
Sadda yazo gida sha d'aya ta wuce dakinsa ya wuce kawai ya cire kayansa ya shiga wanka, yana fitowa ya ganta vakin gado.
"meyasa baki kwanta ba har yanzu?"
"Najiraka ne ka dawo"
Girgiza kai yayi yana zama yafara tsane jikinsa yace, "inajinki"
Kamar zatai kuka ta fara magana, "Abbyn Amnat meyasa kake so ka canza mun,meyasa kakeson gidanmu yazama gidan makoki, kullum babu farin ciki amnat kanta korafi take akanka,baka wasa da ita baka doguwar magana da kowa me mukai maka har nagaji da tambayarka laifin da nayi, inkuma wata matsalarce ni matarka ce bazaka iya sharing damuwarka dani ba? Don Allah na rok'eka ka dawo yadda kake, ka koma ainahin Fa'iz d'in da kowa ya sani ba wannan ba."
Kwalla ta silalo mata zuwa sannan ya gama shafa man sa, ya taso ya jawota jikinsa ya rungume cikin lallashi yace "kiyi hakuri husna nima nasan canza war dake tana damunku, nima kaina tana damuna amma abun yafi karfina kiyi hkr bazan iya sanar dake komi ba, kidai yi mun adduar fatan alkairi kawai,kuma zan kokari inga na gyara abunda nake"
Tasan baya son gardama amma da ta nace masa saiya gaya mata, sai tabisa da to kurin ta tayashi ya sa kayan bacci suka kwanta, ranar an biya bashin kwanakin da aka baro baya ๐.
*********
Da safe ba laifi gidan fa'iz ansamu yar walwala saidai sama sama, haka amnat tai ta masa surutu saida ya ajeta makaranta ya samu sukuni, kamal na ta kiransa saboda yamakara office,saidai ya tura masa sakon uziri don saiya biya unguwar su baba malam, sannan ya wuce asibiti.
Zuwansa keda wuya ya iske wannan rikici, tun bayan da na koma wannan dogon baccin ban sake farkawa ba sai washe gari da asuba, tunda na farka naga umaima na fasak'ara na damk'eta ina kokowa da ita saita kirawo mun Daddy,hankalin kowa saida ya tashi Dr yana gida haka umaimah na kuka riris ta kirasa a sukwane ya taho, tun lokacin nake kuka ina kiran sai ankira Daddy duk wanda yazo saina cakumesa nace yaje ya kira Daddy inba haka ba in caka masa wani aalmakashi dake hannuna na rik'esa tam, ga Dr,ga umaima ga wasu nurses biyu,duk sunyi cirko cirko nesa dani abun yafi karfinsu, da akazo za'ai mun allura danben da akai dani ba karami bane, dole aka saurara mani.
A haka yai sallama dakin ya shigo, kamar jiransa nake na d'ago a hanzarce kamar mahaukaciya cak ya tsaya bakin k'ofa, dirowa nai aguje na cakumosa dakarfina shaddarsa na cukuikuiyeta nace, "ka kira Daddy na, ka kira mun daddy na yanzun nan, daddy na nakeso nagani kaje ka kirasa naceeeeee"
Na daka masa ihu,kowa saida ya tsorata banda addua babu abunda yake tofa min afuskata, mik'a ma Dr ledar hannunsa yai sannan ya rik'e dukkan hannuwana bai fasa adduar ba kamar yadda van fasa ihu da kururuwa ba, idona jagejage da hawaye harda majina jikina kamar mai karfin doki, cikin karfin Addua da danashi karfin yajani har bakin gado,har sannan ban barkiran Daddy ba inakuka, amma karfin kukan ya ragu.
Cikin karfin hali yace, "in kinason Daddy yazo kibar wannan ihun, ki natsu kiyi duk abunda nace miki"
Kamar jiransa nake na hau d'aga kaina ina cewa, 'to,to,to,zan daina ka kirashi yazo nan yanzu yanzu"
Wayarsa ya fiddo yana cewa "sai kin daina abunda nace sannan,"
Haki nake saboda karfina ya fara karewa, na daina kukan amman ina shashsheka cikin siyasa ya saka wayar a kunne yana magana, "hello Daddy ina kwana,ina ka shiga haka Bahiyya na nan na nemanka baka san tana asibiti ba, maza kazo yanzu yanzu,nemanka take ganinka kawai take sonyi, toshikenan saika iso"
Idanuna duka na kwallalo ina kallonsa har ya gama wayar,yace "kinji dai ko?to gashinan nan yataho don haka kafin yazo anshi wannan"
Ya mik'a hannu Dr yabashi ledar ya fiddo jarkar faro swan da aka zuba rubutun aciki,ya zuba cup ya bani yace "shanye sa yanzu nan kafin Daddy yazo"
Girgiza kai nake idona cikin nashi ko kyaftawa banayi, daure fuska yai yace "to bari na kirasa ince ya zauna karyaz............kafin ya rufe baki na kwacena shanye tass inazare ido, yazuba wani acup d'in ya kira umaima dake can rab'e sai rawar jiki take,yace "shafa mata afuskarta da kanta"
Sai kwallah sharrrrrr "Yaya bazan iyaba, duka take wallahi"
Rasa yadda zaiyi yayi sai yace Nurse din ta shafa mata, tunda na sha wannan rubutun nafara layim bacci,ana gama shafa mun na silale saida nurse din tai saurin kamani tana gyara mun kwanciya sosai.
Sannan kowa ya sauke ajiyar zuciya, ba abunda zuciyar Fa'iz keyi banda duka shi kad'ai yasan halin da yake ciki, fita sukai shida Dr zuwa waje.
Babu a bunda yake ma Fa'iz yawo akai illah maganar baba malam ta dazun dayaje ansar rubutun da yake cewa.
_"inhar kuka ga tasha rubutun bacci mai nauyi ya kwasheta to hakika ciwonta akwai sammu aciki"_
"A binciken da mukai daren jiya nida likitoci mun tabbatar kwalwarta lafiya lau take, ba wani abu da ya shafi kwalwarta,ta yuwu dai zafin mutuwar ne zai rikitata"
Cewar Dr saheeb,yana maganar baya duban inda Fa'iz din yake, maganar ta tsinke masa tunanin daya shiga. shima kuma kansa a k'asa yace "ciwonta bana asibiti bane, amman dole anan zata cigaba da zama har zuwa sadda zamuga yana yin jikinta, jikina bai bani amaidata gida yanzu ba."
Jinjina kai yayi Dr saheeb din yace, "haka ne, amman zanyi mamaki meyajawo haka?waye zai mata wani abun?"
Kafad'a ya d'aga kurin yana cewa, "Allahu wa'alamu, nizan wuce wajen aiki,akwai bukatar asaka ido kanta idan ta farka koma yaushe ne a sake bata tasha akuma shafa mata"
Sukai sallama ya fita jikinsa amace yaja motarsa ya wuce company.
Mom muhseen.โ๐ป