NAYI SAKE DA DAMA TA

13

by @mommuhseen

*_NAYI SAKE....!_*πŸ’˜

     πŸ’˜ '''DA DAMA TA'''

Free Book one.

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

Mrs Bb

Mom muhseen.

Wattpad name

Humaira3461

πŸ…ΏοΈ.......23&24

"Sweet heart kwana biyun nan mataccen mijinki ya dameni amafarki na fa, duk akan ziyarar nan da nake kawo miki, in banda abunshi ai hakkina ne kulawa da iyalinsa koba hakaa ba"

Ya kwashe da wata irin kazantacciyar dariya yana sake rungumota jikinsa cikin bargo suna kwance a gado guda, itama dariyar take tana cewa,

"Wannan gaskiya ne honey, ai aduniya ba wanda ya dace ya kula Damu saikai kuma muna jin dadin hakan, Allah dai ya biyaka"

Suka sake sanya dariya cike da iskanci saida suka natsuwa sannan yace, "ya dace zuwa yanzu asan matsaya akan maganar gado, saidai naga alamar lauyan nan taurin kai gareshi, har yanzu mgnr Bahiyya yake akan saita farka za'ai rabon gadon to idan ya kaini bango shida ita duk zan turasu............."shiiiiiitt karsu b'ata maka ranka abanza barshi tatashin ai jira yake ta tashi daga jiyya ko? To barshi yaita jiran gawon shanu"

Suka sake fashewa da dariya mai cike da iya shege.

"Honey kabarni haka nan naje nai wanka"

"Sweet heart ked'ince kamar ba matar matacce ba komi zan zan"

Suka sanya dariya tace, "kasan munfi karfin wata shidda bama had'a shimfid'a yana ta fushi, nasan asannan duk yasan komi tsakanin ku, bakin cikine yake cinsa"

Yace"ai hakan yai mun dad'i sosai, tun daga sadda na rabashi da *SAUDIYYA* bai kara farin ciki ba, ni kuma daga lokacin nai bankwana da bakin ciki, gashi yanzu ina wanda k'a da iyalinsa sannan inyi da dukiyarsa woni d'an sa'a."

Tana saukowa daga gadon babu ko hankici jikinta tsirara haihuwar uwarta tana juya mashi mazaunai tace, "ai bansan haka plan d'inka zai kyau ba saida lokacin yayi, gaskiya honey kai din dan baiwa ne mai tarin basira,inama ace na riga k'awata samunka"

"Haba manta da Basira, koda ita ai kece tagaban goshina muuaahh"

Yana mata kiss ya hura mata, ta shige toilet tanaa dariya.

(πŸ€” Ohh ni yarsu, Allah ka sa mufi karfin zuciyar mu amin)

**********

"Mutanan nan fa Fa'iz sun so cutar mu Allah ne dai kawai ya taimake mu, nasan da kana wajen sai anyi rigima dakai, amma cikin siyasa na warware komi, yanzu suna barazanar janye hannun jarinsu dake cikin company, abunda zamuyi shine karmu nuna masu fargaba mu nuna masu kodasu ko babu su company zai cigaba da aiki fiye da da, don haka zasu sake dawowa nan da 2weeks dole zamu sake shiri"

Fa'iz idonsa ne kawai akan computer yana duba abubuwan da aka tattauna wajen meeting d'in da baya nan, kunnensa yana ga kamal dake masa bayani,amma rabin hankalinsa kwata kwata baya tare dashi har ya gama, tsawon minty biyar baice komi ba, kamal nazarinsa kawai yake kafin ya dan bugi table din yadda zai dawo hankalinsa.

Firgigi yai ya d'ago yana kallon sa shima kamal d'in kallonsa yake yace, "baka cikin natsuwar ka Fa'iz akwai abunda yake damunka, bama yau ba bazan iya tuna radda na ganka cikin walwala ba"

Yar ajiyar zuciya ya sauke yana maida hankalinsa kan computer d'in yana danne danne, muryarsa tai sanyi sosai yace "Bana jin dadin jikina ne kwana biyu"

Murmushi kamal yayi yace"tabbas bakajin dadi nima naga hakan,amma dalilin hakan shine ban sani ba, ban takura maka ka sanar dani ba amma kai kokarin dawo da walwalarka kodan mu da muke tare dakai, tunda bazaka iya sanar dani ba"

Shiru na wani lokaci baice komi ba sai caan ya nisa ya ce, "zan k'ok'arta inga nayi hakan"

Kamal ya d'age kafad'a yace, "alright"

Wayar Fa'iz d'in aka kira ya duba yaga Sagir ne abokinsa mijin Sakeena,ya rufe computer yana janyeta gefe sannan ya dauki kiran yana sallama.

"Aboki ya kake?"

Cewar sagir daga can bangaren, Fa'iz ya bashi ansa a natse "Ina lafiya, ya hashir da mamanshi"

"Lafiya lau suke, ashe Bahiyya bata lafiya tun rasuwar daddynta sai jiya dana dawo daga tafiya Sakeena take sanar dani halin da take ciki"

Cije lips d'insa yai na kasa kadan yana sassauta murya yace, "ehy amma da sauk'i ba laifi"

"To Allah ya karo lafiya yanzu naje na kai Sakeena asibitin mun iske tana bacci,Allah ya kara afuwa yaushe zamu had'u"

Ya dan ja iska yace, "ehy to, idan na samu lokaci i will contact u"

"OK ahuta lafiya"

Ya sauke wayar yana d'an luliya goshinsa kamar mai ciwon kai, kamal dai kallonsa yake kurin har yagaji ya  tashi yana cewa, "zan wuce gida sai goben kenan"

"Don Allah ko zaka sauke ni, bana jin driving din driver na baidawo daga tafiya ba shiyasa"

Kafad'a ya d'age kurin yace, "ka saman a wajen motar"

Ya fice kurin yabar sa nan tsaye.

Dan murmushi kadan yai yana nufar toilet yasan fushi yake dashi, ya zayyi baya jin zai iya sanar da wani makasudin damuwarsa, yana son ya samu mafita akai wadda tsawon sati biyu kenan bai samu mafitar ba,hakan na nufin yana bukatar abokin shawara, yasan ko kusa maman ilham ba zata ma sauraresa ba akan wannan maganar, amman kamal zai iya bashi shawara akai saidai bai shirya karb'ar kalmar amuncewa ba, tun daga sadda yaji batun yake fama da zuciyarsa akan ansar batun.

Tunda suka fara tafiya babu mai cewa komi saida yaga kamal din ya nufi hanyar gida yace dashi, "ANNUR HOSPITAL zaka kaini tukunnah"

Baice komi ba ya karya kwana ya dauki hanya still ba mai magana duk da Fa'iz dama can bamau surutu bane,Amma yau sai yaji shirun babu dad'i kamal mutumin kirkine zai iya cewa duk cikin abokan sa shine wanda suka fi d'asawa, kuma wanda yake jin dadin mu'amala dashi, kamal bai tab'a boye masa wani sirrin sa ba daya shafesa, haka inyana cikin damuwa zaizo ya gaya masa yana neman shawarar sa, amma sai gashi shi yau yana b'oyen sirrin sa ga kamal, hakan ba daidai bane shima ba dan yaso ba maganar mai matukar girma ce agaresa.

Har suka iso Fa'iz zancen zuci yake ya rasa matsaya,kin fitowa kamal yai yace yaje ya fito yana jiransa "ba zaka shigo ka duba mmn amnat ba?"

Kallon shi yai na wani lokaci kafin daga bisani ya bud'e motar yafito suka shiga tare.

Tunda na farka bance da kowa komi ba acikin jikina nakejin wani irin yana yi marar dad'i, saidai hawaye kawai dake zuba ba k'ak'k'autawa, sakeena da suka zo ita da Baban hashir har ya tafi k'ala bance ba, ni kaina bazan iya bayanin abunda nakeji a cikin zuciyata ba, inaji kamar infita inyita gudu har sai nai nesa da mutane, inajin kamar inyita kuka har illa masha Allahu, inajin na tsani komi da kowa bana son ganin kowa, amma bakina yai nauyi kalmar A bazan iya furtawa ba badan bana maganar ba, kawai haka nakejin kaina.

Umaimah tatafi gida saboda kiran da uwarsu keta mata akan ta dawo gida tunda ba uwartace a kwance ba, ba yadda ta iya dole tatafi tana kuka ina kallon ta na kasa ce mata komi, saidai bayan tafiyarta na saka kaina acikin guiwa ba abunda nake sai kuka, kuka mai tsuma zuciya da tab'a mai saurare Dr da sakeena ba irin lallashi da banbakin da basuyi mun ba amma kamar bana jinsu, jinake kukan kawai shine zai rage mun rad'ad'in da nakejin zuciyata tana yi mun, *DADDY* shine kawai nake tunawa shinake tuna irin bakin cikin daya kasance ciki tsawon shekaru, abubuwa suka shiga dawo mun kukana yana k'aruwa har takai ga numfashina yana neman d'aukewa, Dr yai mun allurar bacci dan danan ya kwasheni.

Ban farka ba sai wajen karfe takwas na dare sannan Sakeena tatafi nurse ce tare dani, taje ta kira Dr yazo da kanshi ya ban wani ruwa aroba nasha, yace na wanke fuskata da kaina duk nayi yadda yace, ya tambayeni meke damuna sai kawai na sake fashewa da kuka, dai-dai sadda su Fa'iz sukai sallama cikin d'akin.

Cirko cirko sukai bayan musabaha da sukai da juna, Dr ne yai karfin halin danne abunda ke taso mashi yake ma Fa'iz d'in bayanin cigaban da aka samu, saidai matsalar wannan kukan da take.

_Inhar sihirin ya karye zata ringa kuka akai akai, to kubarta tayi iya iyawarta shine zai sanya kuncin da ke dankare acikin ranta ya wanke, ahankali ahankali zata dayaye_

Fa'iz ya tuno kalaman baba malam a jiya kenan, ajiyar zuciya yaja yana furta, "Alhamdulillah"

Duk kallasa sukai saidai baice komi ba na wani lokaci, kafin daga bisani yaja iska yafesar yana kauda kai kamar baya son ganin Dr d'in yake ce masa,

"Daga yau zuwa gobe kana iya sallamarta zata ida warwarewa"

Wani kallo yake ma Fa'iz din akaikaice amma baice komi ba, ya gaji da tsayuwa ya fice daga dakin, takawa Yai har bakin gadon inda nake inata kukan wanda har yajawo muryata ta dishe sosai bakajin kukan sosai.

"BAHIYYA"

sautin kiran sunan da sunan suka dira acikin kunnuwa na, suka je inda wani waje yake wanda zuciya bazata mance dashi ba, anan take naji zuciyar ta soma bugawa da sauri da sauri, kukana ya tsaya cak kamar daukewar ruwan sama.

"FA'IZ"

na ambata acikin zuciyata kasa d'agowaa nai balle in kalleshi, sama-sama ina tuno abunda ya d'an faru wanda bazan iya tantance gaskiya ne ba ko akasin haka............"yajikin?"

Na sake jin muryar sa ta dirar mun yana tambayata jikina, anya kuwa gaskene?van iya cewa komi ba kamar yadda ban d'ago kaina ba.

"Amnat tana gaidaki.............azabure na ciro kaina daga cikin guiwata ina dire manyan idanuna da suka canza kala saboda kuka, lumshe idanun sa yai ahankali sannan ya jinjina kanshi alamun tabbatar wa.

Sauke idona nai daga barin kallon shi don gani nake kamar mafarki, Fa'iz ne yake mun magana da sanyin murya? Fa'iz ne yazo dubani banda lafiya? Meke faruwa?

"Maman Amnat yajikin naki"

Kamal ya furta daga inda yake tsaye,jinjina mashi kai kurin nayi yace "Allah ya sawake ya sa kaffara ne"

Ciki-ciki nace "Amin"

Agogon hannunsa ya kalla sannan yace "zamu koma saida safe Allah ya sawak'e, kiyi Alwallah inzaaki kwanta inda hali kiyi shafa'i da wutri"

Uffan bance masa ba suka juyaa suka nufi k'ofa har yasa k'afa zai fice nace can ciki-ciki, "inason ganin Amnat please"

Juyowa yai muka had'a ido dashi, nai saurin sadda kaina k'asa ya ce "Zan biyo da ita nan da safe in Allah yaso"

Na d'aga kaina kurin yajuya yabi kamal suka fita.

***********

Suna cikin tafiya zuwa gida har sannan kowa yai shiru Fa'iz ya katse shirun da cewa, "kamal meyasa ka kasa tambayata?"

Bai kallai ba hankalinsa na kan titi yace, "na bari ne duk sadda kai ra'ayin sanar dani komi na maka tambayar"

Abun kwantar da kujera Fa'iz ya latsa kujerar tayi baya,ya shige ya kwanta yana yin filo da hannunsa cikin natsuwa da sanyin murya yake cewa.

"Sati biyu kafin rasuwar Daddyn Bahiyya nazo asibitin don duba jikinsa ba lafiya,na iske yana nemanaa akira masa ni, daidai nazo kenan muka isa nida Dr saheeb, Yace Dr ya bamu waje nida shi yana cikin halin ciwo Kamal haka ya rik'e hannuna cikin nashi, inajin hannun yana kerma ya dauki zafi yake rok'ona cewa idan har Ta Allah ta kasance gareshi in kula masa da y'ay'ansa Bahiyya da jalila, in zame masu yaya,uba,aduk sadda wani abu ya taso masu,daker yake maganar saboda yadda kirjinsa yake d'agawa, sannan ya ja numfashi ya sake cewa yana neman Alfarma wajena ya had'ani da Allah da manzon sa,ya rokeni kamar yadda almajiri yake rok'on abinci inyazo bara, yake cewa *INA SO KA MAIDA BAHIYYA DAKINTA DUK SADDA KAGA KA HUCE DAGA FUSHIN KA,* ba dan halinta ba kayi hakan don ni fa'iz ina jin tsoron wanda zata fad'amawa wanda bazai kyautata mata ba,Bahiyya abun tausayice ba uwa haka zaalika zata rasa uban da tajingina dukkan rayuwarta dashi, bance karka horata ba inyaso ko ka maidata ka cigaba da horata har sai ka tabbatar ta gyaru yadda kake sonta, don Allah Fa'iz kai mun wannan alfarma.

Tun daga wannan ranar walwalata farin cikina da komi nawa ya tsaya cak kamal,na farko kasan wacece Bahiyya na biyu kasan wuyar da ta bani,na uku na riga nayi rantsuwa akan nida sake zaman aure da ita har abadan, sannan Daddy ya wuce duk yadda kake tunani a wajena, ina kallon sa ubana ina mutunta shi ina girmamashi fiye da kima, yazo ya daureni da kalamansa bansan inda zan saka kaina ba, and mmn ilham!!! Ita kad'ai ma ba zata bari haka ta kasance ba,saboda bayan ni babu wanda yakaita tsanar Bahiyya bana jin zata sake mata kallon rahma, kaji halin da nake ciki daya canza ni daga Fa'iz din asali zuwa wannan,tsawon lokaci da kaji bance maka komi ba mafita nake nema Kamal,amman wallah har yanzu ban samu ba ya zanyi......ka taimakeni kamal."

Mom muhseen✍🏻