15
by @mommuhseen
*_NAYI SAKE....!_*๐
๐ '''DA DAMA TA'''
Free Book one.
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
Mrs Bb
Mom muhseen.
Wattpad name
Humaira3461
๐ ฟ๏ธ.......27&28
Jinai kamar an rik'e mun kwayar idanuna daga barin kallonsa shima kuma sai ya tsare ni da nashi kaifaffun idanun da suke huda har fatar jikina, ban san ya akai ba don hankalina bai kai ga wanda yake tare dashi ba saida naji muryar Amnat cikin kunnuwana tana cewa,
"Maah Ashe bakida lafiya, Abby ne yake gaya mana tazun nida Ammi, maah sannu minene yake maki ciwo?"
Ganin Amnat sai ya sake tado mun da wani irin rauni a zuciyata,nai saurin jawota jikina na rungume ina hawaye da shashshekar kuka k'asa-k'asa, lamo tayi jikina haka na cigaba da kukana a hankali har tace "Maah ki daina kinji ko, zaki warke nima danayi ciwon ciki na warke ko Abby?"
Ta jefa mashi tambaya yana tsaye rungume da hannuwan sa,Husna na gefensa lumshe idonsa yai yana jin jina kai kurin, ahankali na cirota jikina muna zama bisa gadon sai naji wani irin sassauci azuciyata, kuncin da nake ta fama dashi yana raguwa, k'in sanyin magana da nakeji sai naji inaso nayi da amnat, ahankali cikin wata sabuwar murya wadda naji kamar ba tau ba,saboda sanyin ta da sirantar ta.
na ce masu "sannunku da zuwa"
Matar tasa kad'ai ta iya bani ansa wadda ko kallonta bana sonyi tana cewa "yawwa sannu, ya jikin?"
Ba tare dana d'aga kaina na kalleta ba na ansa k'asa-k'asa "da sauk'i"
"Allah ya sawak'e"
Na ansa da "Amin"
Su umaimah suka hau gaida su ni kam Amnat sai zuba mun surutu take saidai na d'aga mata kai kurin, umaimah suka fita falo suka barmu nan araina naji haushi ainun da shariyar da yake mun, sai kace nace dole sai yazo, da yake tare yake da matarsa dole zai wannan miskilancin, Amnat ce ta katse shirun da cewa, "Abby ka banni in kwana da maah kaji don Allah,Ammi kice masa zan kwana da maah"
Kallon sa Husna tayi kad'an ita kad'ai tasan wutar kishin dake azalzalarta acikin zuciyarta tun daga sadda yafurta zuwansu zuwa yanzu, danne wa tayi tana cewa "zai ma barki ai shalelen Abby"
Saida ya gama danne dannen wayarsa sannan ya d'an tsaya daga d'an nesa kad'an yana mun magana hankalin sa akan waya still,
"Ya jikin, ina ganin za'a iya sallamarki zuwa yanzu,in kuma akwai wani abun da kikeji ki fad'a"
Hannun Amnat nake wasa dashi inajin wani irin yana yi yana ratsani wanda har kwalla tana son dizgani gaban waccen matar, nai saurin maida su amma muryata duk da haka zaka iya fahimta acikinta.
Tsawon lokaci sai yau nayi doguwar magana cikin jin wani irin yana yi da ni kadai nasan ya nakeji nake bashi ansa,
"Bana jin komi,Koda ma inaji nasan na lokacine zan warware"
Har sanan bai kallan ba ya sake cewa, "Allah ya sawaqe, ya kiyaye gaba"
Can k'asa na ansa da "Amin"
Dr saheeb ne ya shigo ganin su yai cirko cirko Amnat tai zak'al tana cewa "Maah wannan ne likitan dake dubaki?"
Kai na d'aga mataa kurin,Dr ne ya iso wajen mu yanaa mata murmushi ya ce "little angel how fa?"
Yana mik'a mata hannun sa ta anshe tana washe baki tace "I'm fine uncle, ba kayi ma Maah d'ina allura ba dai ko?"
Ban san sadda murmushi ya kubce mun ba saboda dai ita aduniya ba abunda bata so irin allura, shiyasa ko wani za'ai mawa kuka take masa, daidai sadda nake murmushin muka sake had'a ido dashi saida gabana ya buga, nai saurin dauke kaina.
Ina ma Dr magana da yake tambayata ya jikin, silently na ansa shi da cewar "na samu sauk'i muna iya tafiya gida ko?"
Yace"ehy in sha Allah,nama tura su umaima gida suje su had'o kayanku keda Jalila, yanzu binsu zanyi saboda gudun rigima"
Rausayar dakai kurin nayi bance komi ba,amnat ce keta surutun ta daker ya kubce ya fita yabarmu nan, jinai yana mata magana cikin kulawa "Husna please ki jirani a mota"
"OK" kurin tace masa tana juyowa kaina cike da basarwa tace, "maman Amnat Allah ya kara afuwa"
Still yanzu ma da "Amin d'in na bita"
Amnat na mata by by wai sai ta dawo, bayan fitar ta ya wani canza fuska yana sake had'ta yace "Baby taso muje gida haka nan kina da islamiya anjima"
Saurin d'ago kaina nayi ina kallon sa,amnat ta fara dire-diren k'afa zata fara kuka, ban fahimci me yake nufi ba, cikin karyayyyar muryata da bata dawo dai-dai ba na ce, "kutafi fa kace? Ba zaka barta ko kwana biyu tayi dani ba, hakan zai karfafa ni"
Abunda yake ji bazai barshi ya iya barin y'arsa agidan wani banza ba, duk da yana jin wata zuciyar na hana shi abunda yake niyyar yi amma baya jin zai barta.
"Y'ata ba zata biki gidan wasu ba, inda gidanku ne wannan kila na amince.........Abby don Allah zan zauna da maah,ka barni kaji Abby nah don Allah Maah zata kula maka dani"
Cewar amnat tana kuka tana rik'e hannuna, banda karfin da zan iya hayaniya dashi, banda kwarin guiwar cecekuce dashi akan Amnat, ba kuma zan rok'esa ba bazan kaskantar da kaina awajen saba kamar wancen karon, duk yadda yaso yayi da yarsa.
Wasu zafafan hawaye suka soma silalo man ban shirya ba,ga Amnat na kuka tana cewa ba zata bishi ba nama kasa lallashinta balle inyi wani abun,dawowar Dr yasa Amnat rugawa wajensa tana cewa "kace Abby karya tafi dani kaji unlce Dr, ni inaso na zauna Da maah"
Kallon Fa'iz d'in yai cikin wani irin yana yi muryarsa da zafi zafi yace, "dagaske ba zaka bar mata ita ba na wani kwana ki kodan halin da take ciki?"
Shima d'in fuskar nan tai jajir yace "bazan bari ba d'in, ince dai y'ata ce nina haifa abuna ina da iko da ita, don haka ba zan barta ba ko kana da yadda zakai?"
Wani murmushi Dr yai yanaa kauda kai yace "kayi gaskiya kam, yarka ce bama da wani karfi akanta, I'm sorry Angel Abbynki bazai barki ba kibar Maah ta tafi ita kad'ai, koda ke ko babu ke zata warware zatayi rayuwarta mai kyau in sha Allahu"
Kalaman bana amnat bane duk mun fahimta duk da bai fito ya fad'a ba, kuma naji dad'in fad'arsu dayayi, kaina k'asa yake hawayena keta zuba ba kakkautawa,fad'owa tai jikina tana kuka sosai wanda jinake kamar zuciyata zata fad'o, nai dakiyar share fuskata ina son lallashinta nace, "kibi Abbynki Amnat duk rintse watarana zaki zo gareni, ni mahaifiyarki ce duk duniya babu wanda ya isa ya goge hakan, kuma ba wanda ya isa ya canza miki ni a matsayin uwa, kije kinji Allah yai miki albarka"
Kafin ma na ida maganata yazo ya janyeta ya dauketa suka fice daga dakin, ka filo na dora kaina na fashe da kuka mai tsananin cin rai bansan me Fa'iz yake so dani ba, ban san ya yakeso ya ganni ba arayuwa na fahimci duniyar yake so yaga na bar mashi hakan zaifi masa dad'i arai, baida wani buri a rayuwa daya wuce ya k'untata ni,ya jefani cikin bakin ciki shin ashe bawa baya kuskure arayuwa kuma yai nadama ayarda dashi?............"please Bahiyya I'm begging u stop crying, u are not felling well karki biye zuciyarki ki sake shiga wani mawuyacin halin,tsawon lokacin da kika d'auka kwance ba k'aramin rud'ani na shiga ba.............dagowa nai na tsaresa da idanuna da sukai jajir dasu, ban fahimci maganarsa ba dafe kai yai yana cewa "I mean saboda amanar da marigayi ya bani na shiga rud'ani akan rashin lafiyarki, ina tunanin idan wani abu ya sameki ya zanyi"
Kauda kaina nayi kawai ina share hawayena, yaja ajiyar zuciya yana matsowa inda nake yana cigaba da magana, "ba zugaki nake ba zuwa yanzu ya dace ki d'aga mashi k'afa, ki hakura kibar masa ita ganin kin dora dukkan kaunarki akanta yasa yake baki wahala, kiyi hkr ki fuskanci rayuwar dake gaba"
Uffan bance ba ya sake yin shiru na wani lokaci kafun ya ce, "naje gidan don gudun faruwar wani abu, na iske mamansu tana ta dukan su saboda sunzo wajenki,daker na anshesu na sasu suka had'a miki kayan suna motata komi da kika buk'ata,saidai tayi rantsuwar cewar babu inda Jalila zata ba wanda ya isa ya raba mata kan y'ay'a"
Sai lokacin nai magana da shak'ak'k'ar murya, "wannan ne kuma tayi kad'an,don zaman jalila hannunta ba abunda xai haifar illa ya gurb'ata mata tarbiyya,kuma tunda Daddy ya bada amanarta yana gudunfaruwar wani abun, don haka ka kaini gidan please Dr"
Kallona yake wani irin kallo yana cewa "bana son kije ta b'ata miki rai, ta ja miki wata damuwar"
Kaudar dakai nayi bana son wannan kallon da yake mun, nace "ba wata damuwa yanzu da zata sake kwantar dani Dr, tun da Daddy ya tafi kuma najure hat gashi na tashi, bana jin akwai sauran wani abu dazai sake girgiza zuciyata irin haka"
"Shikenan muje na kaiki d'in"
A sannu a sannu na saka takalmin da ya ajemun na gyara mayafin abayar jikina muka fito muka dauki hanya har muka isa ba mai magana.
Tunda muka iso k'ofar gidan zuciyata kamar zata kece saboda tuno da Daddy da nai, kallon gidan nake kamar zan ganshi a ciki idona tab da kwalla sai su silalo ingoge har na iso cikin main falon, daman naga bakuwar mota a compound ashe shine?
Baba Badaru ne hakince cikin kujera an jera masa breakfast lafiyayye yana yi ga Ammah a gefensa kamar zataje gasar sarauniyar kyau,dududu Daddy satinsa cikin na uku ne da rasuwa me hakan ke nufi? Meke faruwa? Matsayinta na mai takaba wannan haramun ne,..........."Bahiyya"
Baban ya anbata cike da mamakin ganina ya juya yana kallon Ammah da itama ni d'in take kallo,
"Taya akai haka?"
Murmushi nayi nace "kai zaton nima mutuwar zan? Ko kai zaton bazan tashi ba? Ai ba abun mamaki a cikin lamarin ubangiji, alamun inada sauran kwana a gaba,kuma jinyar tawa Allah ya kawo karshenta,"
"Mekikazo yi gidana?"
Cewar Amma da tasha mur tana kallona, na auna mata wani kafirin kallo nace "gidanki? Tofah yaushe ya zama naki?asanina ba'a raba gadon ba saurin me kike? Hmm bar wannan maganar nazo tafiya da yar uwata gudan jinina Jalila"
Wata yar dariya tayi tana mik'ewa tazo inda nake"Y'ata babu inda zata,ai ni na haifa ko? Ba ubanda yai mun nak'udarta don haka Jalila na nan kofar takashi ba zata ba"
Na zauna cikin onesiter nace, "kinsan daga asibiti nake bana jurar tsayuwa, hmm yawwa kika ce me? Kinaso ne Allura ta tono galma?, kinaso ne garin kano ya d'auki sunan ki? Ko kinaso ne y'ay'anki su san su waye su? Su san wacece ke? Wace irin uwace Allah ya basu maha'inciya macuciya kuma azzalum..............jikinta na wani irin kerma kamar anjona mata shock ta rufe mun bakina tana waigen hanya arud'e, khaleesat ce tafito daga hanyar dakin su da air pies a kunnenta tana daddana wayarta kamar dai ba abunda ke damunta, kamar ba mutuwa akai mana ba mai zafi da gigita zuciya,koda yake ba abun mamaki bane tunda basu had'a jini dashi ba amman abun akwai daure kai.
Wani kallon izgili tayi mun tana wucewar ta,Baba Badaru kuwa mutuwar zaune yai don naga ya k'ame yana ta kallona.
"Idan kika sake kika furta wani abu ya shiga kunnen y'ay'ana saina hallakaki"
Dariyar dana jima banyi ba na saki ina cewa, "Au wai tsoro kikeji? Bakiso su sani kenan? To tunda bakiso su san komi ki kira mun Jalila tafito da kayanta mutafi"
Jikinta tsuma yake,tajuya tana kallon Baba Badarun shima ita yake kallo,uffan baice ba ya dauki hularsa ya mik'e yai hanyar fita daga gidan, nabisa da kallon wulakanci ina cewa, "Aa ha Baba ina kuma zakaje?na dauka kalaci aka shirya maka kuma zaka tafi baka gama ba"
Juyowa yai yana kallona wani kallo na auna masa yai saurin ficewa daga falon, itama ahanzarce ta fice na dafekaina cike da bakin ciki da takaicin wannan rayuwar, wad'adannan mutanen nayi alk'awari sai inda karfina yak'are wajen ganin sun anshi hukuncin su.
D'akin Daddy na wuce kafin zuwan Jalila.
Mom muhseenโ๐ป