SANADIN MAHAIFINA

Page 2

by @sanazty

•••SANADIN MAHAIFINA•••

Wattpad@SaNaz_deeyah

Arewabooks@sanazty

Facebook@Habibtyn Habibi

YouTube: ***

Tiktok: ***

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[karamci tushen mu'amula ta gari]

```Shafi na 2```

Hannatu kuwa gaba ɗaya ta saki baki tana kallon Jannat. "Dama an kusa aurenki baki faɗa mana ba, mu tanadi wani abu" ƴar dariya tayi tare da faɗin "Haba Umma me zaku tanada, aini zuwanku kaɗai ya wadatar" Sa'ad kuwa gaba ɗaya jikinsa ya mutu, ya kasa cewa komai.

Umma ta lura da hakan, kuma ta tausaya masa amma sai ta share dan kada Jannat ta gane duk  sun shiga damuwa.

"To Hannatu wannan shine na ƴammata, ga na kamu, ga na dinner yanzu kin ga dole kije gidanmu ko?"

Murmushin ƙarfin hali tayi sannan tace "Ai zanzo kafin bikin ma. Yaushe ne bikin kuma nawa ne ankon?"

"Saura wata biyu bikin, anko kuwa kyauta nayi miki.Wannan ma Mommy ce tace a kawowa Umma ankon iyaye."

"Haba dai irin wannan wahala haka, ku bar mu kawai muyi da kanmu" Cewar Umma.

"Umma taya za'a bari kuyi da kanku? Gaba ɗaga ƴan gida kyauta aka musu anko, kuma kuna daga cikinsu"

"To mungode Allah ya saka da alkhairi"

"Amin Umma amma kunfi ƙarfin haka a gurina"

Godiya suka ƙarayi sannan ta miƙe tana faɗin "Umma ni zan wuce sai na ƙara leƙowa"

"To Jannat mun gode ki gaida ƴan gidan"

"Zasuji, ke kuma Hannatu, ina nan ina jira ki cika alƙawari, karki damu idan zanzo ai zan kiraki a waya"

"To shikenan." ta faɗa sannan ta saka kai ta fita. "Yaya ka bita ka faɗa mata kana sonta."

"Amfanin hakan ya wuce" Umma ta faɗa tare da cewa "Kaje ka rakata bakin mota mana."

Jikinsa gaba ɗaya ya mutu haka ya tashi ya fita. Tana ganinsa ta saki murmushi. "Naga duk jikinka ya mutu"

Ajiyar zuciya yayi sannan yace "Jannat yanzu idan kika yi aure shikenan ba zamu sake ganinki ba."

Dariya tayi tare da cewa "Oh wai wannan dalilin ne ya saka ka tashi hankalinka?"

"Eh mana domin na san ba lallai mijinki ya yarda ki riƙa zuwa ba"

Rufe baki tayi tana dariya "Dan Allah kada ka damu kanka kaji, kuma fa ƴan gida ne, kuma na san babu yadda za'ai Khalil ya hanani zuwa nan, domin kuwa ya san yadda na ɗaukeku, dan haka ka kwantar da hankalinka kaji, insha Allahu babu abinda zai rabani daku"

"Shikenan Jannat amma...." Sai kuma yayi shiru.

"Amma me? Dan Allah ka faɗa min abinda ke damunka domin nasan ba wannan kaɗai bane, kuma akwai abinda kake son faɗa min ka kasa"

"Babu komai Jannat kinsan babu ɓoye-ɓoye tsakani na dake"

"To Allah yasa da gaske kake, zan tafi domin su Safina suna jira na za muje gidan kakannin mu"

"To shikenan ki gaida ƴan gidan"

"Zasu ji" shiya buɗe mata ƙofar ta shiga ya rufe.

*Bayan Wata ɗaya da sati biyu*

Yana zaune a kan tabarma da aka shimfiɗa a tsakar gida, kallo ɗaya zaka masa ka gane akwai damuwa a tattare dashi. Hannatu tazo ta zauna gefensa tare da faɗin "Yaya dan Allah ka fidda soyayyarta a cikin zuciyarka tunda ka san bazaka taɓa samun ta"

Kallon ta yayi tare da cewa "Hanne ke yarinya ce baki san zafin so ba, domin baki taɓa yi ba, amma daga ranar da kika fara tabbas zaki san yanda yake"

"Na fara mana, zafin sa ne ban sani ba, tunda ni ban shiga irin halin daka shiga ba, amma kada ka manta matsayinmu, kuma a yanzu daga ni har Umma kaine bango a garemu tunda Baba baya raye, me kake tunani idan muka rasa ka?" Baice mata komai ba sai kanshi daya kauda gefe. Ita kuma ta cigaba da cewa "Jannat a cikin garin nan take amma bayan ita babu wani nata daya taɓa raɓarmu, ko da a waya ne basu taɓa kira da zummar gaisuwa ba, sai dai fa idan ta zo tace mana sunce suna gaidamu, wataƙila ma kawai faɗa take yi"

"Ban damu da haka ba matuƙar zata soni"

"Aikuwa ba zata taɓa sonka ba, kama daina tunanin zata so ka, bayan sati biyu ya rage a kaita ɗakin miji." Umma ce ta faɗa lokacin da ta fito daga ɗakinta.

Zama tayi tare da cigaba da faɗin "Idan so kake ka mutu sai ka cigaba da saka Jannat a ranka. Haba Sa'ad nawa muka kashe a asibiti a satin daya gabata, mun kashe kuɗi kusan dubu talatin, kuma hawan jinin ka yana gab da komawa ciwon zuciya meya sa zaka bari ka cutu? Har kayi ciwon ka gama bata ma san kayi ba, rabona da Jannat nafi sati uku, to kaga ita kanta ta fara ja da baya damu"

"Ba haka bane Umma, ni nasan yadda sha'anin biki yake wata...." Bai ƙarasa maganar ba suka ji sallamar a cikin gidan.

Ita da Safina ne suka shigo. Umma kuwa murmushin dole tayi tare da faɗin "Wata sabon gani"

Hannatu ta miƙe tare da cewa "Bara a ɗakko tabarma"

  Bayan sun zauna Umma da kanta ta kawo musu ruwa tana ƙara yi musu sannu da zuwa.

Sa'ad kuwa ya ƙura mata ido yaga ta ƙara kyau sosai saboda ana mata gyara jiki, tayi wani haske mai sheƙi.

"Umma kuyi haƙuri banzo ba, wallahi abubuwa ne suka min yawa, ga gyaran jiki muna zuwa, ina ta so nazo amma sai yau na samu dama"

"Babu komai Jannat ai kina ƙoƙari ma, mu gashi har yau bamu samu munje ba"

"Umma ai Sa'ad ya wanke ki, Hannatu ce dai nake fushi da ita"

"Kiyi min afuwa Jannat insha Allahu zanzo"

"Mu dai fushi muke dake, kamata yayi ki haɗo kayanki ma mu tafi sai an gama biki ki dawo tunda next week za'a fara" Safina ta faɗa tana kallonta.

"Umma wannan itace Yayata Safina"

"Oh itace muke ta jin labarin ta"

"Eh itace, ni Mama ko dai Sa'ad bashi da lafiya naga duk ya rame?"

"Yayi jinya amma da sauƙi ma"

"Amma ba'a faɗa min ba"

"Babu komai karki damu Jannat ai hidima kike shiyasa ma nace  kar a faɗa miki"

"Duk da ina hidima da nazo, Allah yasa kaffara ne"

"Amin ya rabbi"

"Ga I.V na kawo muku" ta karɓi fancy bag dake hannun Safina ta ajje a gaban Umma.

Chewing gum da sweets ne masu tsada ko wanne leda 6 a ciki. Sai I.V guda uku.

"Biki ya matso kenan"

"Eh Umma, dani da Safina ne"

"To Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya, ashe tare da amare muke ba amarya ba" Murmushi tayi tare da sauke kanta ƙasa.

Sun fi mintuna talatin kafin suyi sallama su tafi. Sa'ad kuwa har bakin mota ya rakasu.

Kallon shi tayi lokacin Safina ta shiga mota "Ka faɗa min damuwarka dan Allah"

Murmushin yaƙe yayi sannan yace "Ni bani da wata damuwa"

"Hmmm! Akwai abinda kake ɓoye min ni na kasa gano ko menene, kuma lokacin dana shiga naga dukkanku fuskarku tana ɗauke da damuwa, ka faɗa min dan Allah mene matsalar?"

"Babu komai Jannat da da akwai ko ban sanar miki ba Umma zata faɗa"

"To shikenan. Next week wednesday za'ayi kamu a ina fatan dai zaka zo?"

"A'a amma dai na san tabbas Hanne zata zo"

Ɓata rai tayi tare da faɗin "Bikin nawa ne ba zaka zo ba?"

"Zanzo amma ɗaurin aure kaɗai"

"Tabɗi! To wallahi idan har baka zo ba, to nima ba zan zauna a wajen ba fita zanyi"

"Meyasa?"

"Saboda muhimmancin ka a wurin yafi na kawo, dan Allah kazo"

"Shikenan zanzo insha Allahu"

"Indai baka zo ba nima bazan zauna ba, i mean it" ta faɗa tare da buɗe murfin mota ta shiga."

Motarsu na tashi yaji hawaye masu zafi a kuncinsa, da sauri yayi gida.

Safina dake driving ta juyo ta kalli Jannat sannan ta cigaba da tuƙi. "Tunanin me kike haka?"

"Safina sai inga kamar ƴan gidansu Sa'ad suna cikin damuwa, amma na kasa gane dalilin haka."

"Nima na gane suna cikin damuwa, amma maybe akwai abinda ke damun nasu, kuma naga Sa'ad ya ƙura miki ido, baki tunanin shaƙuwar da Sa'ad yayi dake ta koma masa soyayya?"

"So kuma?"

"Na lura kamar yana sonki"

"Haba dai... Akwai wadda yace yana so fa, taya Sa'ad zai fara sona, ki daina wannan tunanin"

"To shikenan"

"Yanzu dai mu biya mu ɗauki Farhan maybe ta gama siyayyar da zatayi"

"Okay".

Dare

09:30pm

Tana kwance kan gadonta ta rungume tedy, Sai juyi take ta lulu duniyar tunani.

  Akwai yarinyar da nake so kyakykyawa ce dan ban taɓa ganin mai kyawunta ba.

     Ta kaini a kyau

Zakuyi ɗaya, ina sonta amma na kasa faɗa mata, ina tunanin taya zata karɓi soyayya ta.

  Kada kaji tsoro faɗar abinda ke zuciyarka, ka fito fili ka faɗa mata kana sonta koma wacece, barin abin a ranka shine zai iya haifar maka da matsala.

  Idan kuma tace bata sona fa?.

  Zaka jajirce ne, ai soyayyar ƴa mace ba cikin sauƙi ake samunta.

  Ina zulumi domin ɗiyar manya ce.

  Babu ruwan soyayya da kuɗi, kai da ka jarraba.

Tashi tayi zaune tare da yin tagumi. Maganganun  ta da Sa'ad take tunawa.

Na lura kamar yana sonki.

Ta tuno furucin Safina.

Dafe goshin ta tayi, ta tuna yadda yake ƙura mata ido da sukaje kai I.V, sannan yadda yake wasu abubuwan ma sai yau ta lura kamar yana  sonta.

Anya kuwa

Ta furta a ranta sannan ta janyo waya ta kira numbersa.

Tana shiga ya ɗaga. "Hello" yadda yayi maganar duk da a waya ne sai data fahimci lallai yana da damuwa.

"Sa'ad dan Allah ka faɗa min abinda ke damunka, wallahi na kasa samun sukuni na damu sosai"

Kece damuwata Jannat ya faɗa a zuciyarsa, a fili kuwa cewa yayi "Jannat kada ki damu kawai canjin yanayi ne."

Ƙara riƙe wayar tayi tare da faɗin "Wallahi kaima kasan bazan yarda ba, dan Allah ka daina ɓoye min"

"Ko da na faɗa miki babu amfanin da zai miki"

"Damuwarka ai tawa ce, ka faɗa min"

Shiru yayi har sai da tace "Ko baka jina ne?"

"Ina jinki"

"To faɗa min"

"Wadda nace miki ina so, to ita bata sona, ta faɗa min cewar anyi mata miji"

Gabanta ne ya faɗi, a ranta tace Kar fa maganar Safina ta zama gaskiya.

Ajiyar zuciya tayi sannan tace "To amma kai ka tabbatar da haka? Kasan mata fa idan basu son abu sai suyi ƙarya"

"Na tabbatar da hakan domin har an saka bikin" jin haka ya saka ta fito da idanunta waje, tamkar yana ganinta.

"Da safe zan shigo sai muyi maganar"

"Allah ya kaimu" ya faɗa tare da katse kiran.

"Ya salam...! Wallahi Sa'ad sona yake, ya akai haka ta faru? Meyasa tun farkon haɗuwarmu bai faɗa min yana sona ba, meyasa ya kasa faɗa min yana sona? To da yaushe ya fara sona? Wayyo Allah kada alhaki ya kamani, meyasa na shiga rayuwarsu?"

Hawaye ta goge sannan ta kwanta tayi Lamo.

  Ranar ko abinci dare bata ci ba. Kuma kowa sai daya gane tana da damuwa amma idan aka tambayeta sai tace ba komai.

Ranar haka ta kwana rabi bacci rabi ido biyu.

SaNaz Ce✌️