ƘITSO DA KWARKWATA 009
KITSO DA KWARKWATA 009
Maimuna Bala
Shuukran
Young Talented Writers Association
P9
Washegari alhamis karfe tara da mintina ashirin Hafsah ce tare da Salma zaune cikin kamfanin Youth dream Co-operation Company,can gefinsu kuwa wasu ƴan mata ne da samari da alama duk wa'inda suka samu aikin ne,dukkaninsu jira suke a yi masu capturing kamar yadda aka faɗa masu shiru Hafsah ta yi tana tunanin wani rayuwa za ta yi a gidan da za ta je aiki tana kuma tunanin halin da mahaifiyarta da ƙaninta zasu shiga bayan bata nan saboda duk saba ita ke yin komai na ayyukan gida Hajjo ƙiwa ne da ita sam bata son aikin gida,tana cikin wannan tunanin ne wayarta ta fara ringing cero wayar ta yi daga jaka inda ta duba mai kiran taga Usman ne kwana huɗu kenan yana kiranta bata amsa kiran,shi kuma ya ƙi hakuri kullum sai ya kira sau uku safe rana dare kamar baza ta amsa sai kuma ta ɗaga,cikin sanyi yanayi ta yi masa sallama kamar jira yake ya amsa sallama nan ya fara jero zance inda yake faɗin
''Hafsah kwana biyu kuma shiru ko dai na yi laifi ne? na yi ta kiran layin ki amma ba ƙi ɗaga wayata'' Hafsah ta ce ''ba ka yi komai ba kawai dai bana kusa da wayar ne shi yasa''
"Ayya to ya ki ke ya su Mama?"
''Kowa lafiya'' cewar Hafsah
''na ce in babu damuwa ko zan iya zuwa gobe kin ga mun kwana biyu bamu haɗu ba''
Taɓe baki Hafsah ta yi kafin ta ce ''ka yi hakuri sai wani lokaci gobe bana gida''
Numfasawa Usman ya yi kafin ya ce
''A gaskiya Hafsah ba ki kyauta min duk sanda na ce zan zo zance sai kin kawo min uzuri,me yasa ki ke yi min haka saboda Allah'' murmushi me sauti Hafsah ta yi ta ce
''Ba rashin kyautawa bane da akwai abinda zan yi goben shi yasa''
"To shikenan na ji na kuma yarda gobe ba ki da lokaci amma yaushe ki ke da lokaci?" Shiru Hafsah ta yi ta rasa me za ta ce masa sai kawai ta ce ''mu yi magana zuwa anjima wani abun na ke yanzu'' Usman ya ce
''A'a Hafsah kullum haka ki k''..yana cikin magana ne ya jiyu sautin wani gardi yana faɗin ''next person please'' Hafsah ta yi saurin katse wayar ta ajiye wayar jikin Salma kafin ta tashi ta bi bayan wannan mutumin daman ita ce next ɗin,kashe wayar Salma ta yi gaba daya tare da sa shi cikin jakarta ba karamin haushin Usman take ji ba mutum sai shegin naci kamar maye ita bata san me Hafsah ta ke da shi ba har yanzu da bata rabo da shi ba,da ita ce ayi da wani zancen ake
Bayan shigar Hafsah ɗakin cikakkiyar sunarta aka tambaye ta sai unguwar da ta ke zama da wasu tambayoyi kan kula da gida da kuma yadda zata tsara ayyukan gida,duk ta basu amsa dai-dai yadda ya kamata,daga nan sun ƙarɓi account number ɗinta bayan haka kuma suka miƙa mata appointment tare da ID card me dauki da hotonta da sunanta matar da ta yi mata interview ɗin ta yi mata congratulations ta ce mata gobe misalin sha daya na safe ta zo kamfanin daga kamfanin za'a wuce da ita gidan da zata yi aiki
Bayan fitar Hafsah aka kira Salma ita ma dai tambayoyin da aka yiwa Hafsah su aka yi mata,aka karɓi number ɗinta aka kuma bata ID card
A hanyarsu ta komawa gida ne Salma ta kalle Hafsah ta ce ''wai ke kam me yasa har yanzu kin ƙasa rabuwa da wannan mayen saurayin nan na ki wai?ko dai sonsa ki ke ne?" Hafsah ta sake wata dariya ta ce ''Wa Usman wai? tab wlh ba ni sonsa hasali ma tausayinsa na ke ji,shi yasa na ƙasa fitowa fili na faɗa masa bani sonsa''
Baki buɗe Salma ke kallon Hafsah sai kuma ta ce ''ah lallai Hafsah tausayi fa ki ka ce? daga tausayi fa sai soyayya abu mafi sauƙi kawai ki fito ki faɗa masa baki sonsa nake ganin hakan zai fi maki sauƙi'' numfasawa Hafsah ta yi kafin ta ce
''ki barsa da kansa zai gane bani sonsa zai tafi''
''Ah wa ya faɗa maki sarai fa ya sani ba ki sonsa amma bazai rabu da ke ba sai kin fito kin faɗa masa,ni dai na faɗa maki ki yi masa bayani yadda zai fahimta kar ki faɗa masa wata kalma marar daɗi'' numfaswa Hafsah ta yi ta ce
''to shikenan zan jarraba''.
''Ya dai fi maki'' cewar Salma
''Kin ga fa shi yasa duk talakawa nan ba ni sakar masu fuska da naga alamar talaka ne kai wlh wulaƙanci kala kala za ka rinƙa gani da kanka za ka rabu da ni...tabb na tashi a talauci na ƙare a talauci ba zai yiwu ba walh,sai dai in Allah ya ƙaddara min hakan to babu yadda na iya''
Taɓe baki Hafsah ta yi ta ce ''ni dai ba na da zaɓin talaka ko me ƙudi mafi alkhari nake roƙon Allah duk bayan sallar farillah''
Wani irin kallon ranin wayo Salma ta yiwa Hafsah kafin ta ce ''sai ki yi ta yi ni dai me ƙudi nake roƙon Allah,ƙinsan Allah yau kwana zan yi addu'a kan wannan mutumin da zan je gidansa Khalid da matarsa Silefarht'' cike da mamaki Hafsah ta ce ''addu'ar me fa?"
Salma ta ce ''addu'ar ya so ni mana matar kuma Allah ya daura ni kanta''
Hafsah ta ce ''kamar na taɓa jin sunan nan Silefarht'' shiru Hafsah ta yi tana nazarin inda ta taɓa jin sunan can ta ce ''alhamdulillah na tuna matar da Mama ta taɓa yiwa aiki da na baki labari me mugun hali da wulakanta mutane sunar ta kenan Silefarht''
Cike da mugunta Salma ta ce ''Allah ya sa ita ce walh sai na aure mijinta'' duk suka fashi da dariya,kamar yadda Salma ta faɗa hakan kuwa ta yi kwana ta yi tana addu'a in Allah Khalid alkairi ne gareta Allah ya jifa soyayyarta cikin zuciyarsa
Washegari juma'a Hafsah da Salma ne tare da sauran wa'inda suka samu aiki zaune suke cikin wata doguwar mota bus kowanne da jakar kayansa gefinsa, kowace ana kaita har kofar gidan da zata yi aiki bayan an ajiyeta agent dake tare da su ke yi masu rakiya har cikin gidan ya yi introducing ɗinsu ga masu gidan ya kuma basu takarda su sa hannu cewar sun ƙarɓi aiki da aka Turi masu,bayan nan sai ya yi masu sallama
A lokacin da aka shigo unguwar milliner's qauter's ne jikin Hafsah ya yi sanyi jin abun ta yi wani irin tun tasowarta bata yaɓa yin aikin aikatau ba sai wannan karon dalili kuwa Baaba Zulai na tsaye kan ƴaƴanta ita ke zuwa ko wane irin niman ƙudin dan kare mutuncinta da na ƴaƴanta,a lokacin da take aiki gidan Silefarht daurewa kawai take saboda shekarunta sun fara ja ga kuma ciwace ciwace na wahala ba na tsofa ba don har yanzu da sauranta,a lokacin da aka bada sanarwar buɗe sabon kamfanin ƴan aikatau ne Hafsah ta ce lallai tana son applying saboda tana son mahaifiyarta ta huta,ba'a son ran Baaba Zulai ba Hafsah ta apply aikin
Dai-dai lokacin da motarsu ta yi parking kofar gidan Expecter Sanusi ne agent ya ce ''to Malama Hafsah bismillahi'' kallon juna suka yi ita da Salma tuni idon Salma ya kau ruwa muryarta na rawar kuka ta ce
''Allah ya sada mu da alkairi zan kira ki''
Ita dai Hafsah dariya ma Salma ta bata saboda tun suna yara haka Salma keyi duk sanda Hafsah za ta koma makaranta kasancewar bording school Hafsah ta yi sai ta yi ta kuka haka Allah ya yi ta tana da ƙawazuci ne sosai musamman kan mutumin da take so
Fuskar Hafsah dauke da murmushi ta ce
''to Salma sai mun yi waya'' ta faɗa tare da ɗaukar jakarta tana fita daga motar, nocking agent ɗin ya yi a gate ɗin gidan Expecter Sanusi mai gadinsa ya buɗe kofa musabaha mai gadin ya yi da agent tare da gaisuwa nan ne agent ya yiwa mai gadin bayanin daga inda suke nan take mai gadin ya ce
''Kwarai kuwa Alhaji ya faɗa min ya ce za'a kawo ƴar aiki'' daga haka ya buɗe masu kofa suka shiga Compound ɗin gidan, mai gadin ya yi gaba inda ya tsaya a kofar entrance ɗin gidan yana sallama tare da kwankwasa kofa
Expecter Sanusi dake zaune cikin ɗakinsa yana zoom meeting cikin system ɗinsa ya dauki excuse ya ce ya yi ɓaki cikin sauri ta sauko ƙasa sanyi yake cikin wata gray color jallabiya sosai ta yi masa kyau ya fito shar dashi kamar ba tsoho mai shekaru hamsin da takwas ba fuskar na sayau,farar fatarsa har wani ƙyalle yake tsabar kuɗi da hutu, bakar sumar kansa da ya sha gyara ya yi parking ɗin sumar sannan ya cusa sumar cikin gashinsa yadda baza a ga yawan gashin ba,karamin bakinsa ya buɗe ya ce ''sannu ku da zuwa'' agent ɗin ne ya amsa ya ce ''yauwa yallaɓi daga Youth dream muke wannan ita ce ƴar aikin da ka apply kwanakin baya sunanta Hafsah,ina me tabbatar maka duk wasu ayyukan gida ta iya ta kware sosai'' tun da ya daura idonsa kan Hafsah ya ji wani abu ya dira zuciyarsa kallon ta kawai yake ƙaramar yarinya ce ƴar kimanin shekaru ashirin da biyu zuwa da uku a duniya tana da haske dai-dai gwargwado komai na fuskarta daidai hancinta masha Allah haka ma idanunta basu yi girma sosai ba kuma ba ƙananu ba, ɗan madaidaicin bakinta ya kalla da ta shafawa me kaɗan,mayar da duban sa ya yi kan suturar jikinta duk sun sha ruwa nan take ya ji tausayinta ya ziyarci zuciyarsa
Ita ko Hafsah tun fitcowarsa ta shagala da kallonsa a zuciyarta cewa take dama ana ganin mazan novel a zahiri sosai ya yi mata kyau gashi ya ɗan manyanta amma ƙuɗi da hutu sun ɓoye tsofarsa dogo ne amma ba can can ba fatar nan smoth kamar baya shiga rana,ido hudu suka yi wani abu ya ziyarci dukkansu biyu Hafsah ce ta yi saurin kawar da idonta kafin Expecter ya cire idonsa daga gare ta inda ya mayar da dubansa ga agent ya ce ''ok na gode sosai''paper agent ya miƙowa expecter ya ce muna bukatar da hannunka a nan,sai da Expecter ya karanta rubutun dake cikin paper kafin ya yi singing,bayan ya gama singing ne ya miƙawa agent ɗin paper,daga nan suka yi sallama ya cewa Hafsah ''bismillah'' ya faɗa tare yi mata jagora zuwa cikin gidan yadda mai gaɗi ya dauki jakar Hafsah Expecter na gaba Hafsah da mai gadi na biye da shi
Bayan shigarsu ciki ne mai gadi ya dire jakar Hafsah nan parlour,fita ya yi daga parlour,bayan fitar mai gadin ne Expecter ya mayar da dubansa ga Hafsah da ta ƙasa sakin jikinta ya ce
''Yaya sunan malamar?" Hafsah ta amsa masa cike da ladabi kanta ƙasa ta ce
''Sunana Hafsah'' jinjina kai Expecter ya yi ya ce ''masha Allah..to Malama Hafsah ni kaɗai ke zama cikin gidan nan, Allah ya yiwa matata rasuwa tun shekarun and bana da yaro ko ɗaya though matata ta taɓa haihuwa''.. Expecter ya ɗan yi shiru tunawa da wani abu da ya yi kawai ya ce ''aikin ki a gidan nan shine sharar da wanke-wanke da kuma girki,na ga kin zo da jakar kayanki bana ganin za ki riƙa kwana a nan saboda kin ga dai ni kaɗai ke zama so l think za ki riƙa zuwa daga gida kawai,and kar ki damu da maganar transport zan riƙa ba ki ƙudi mota kullum'' wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Hafsah nan ta shiga yi masa godiya ya ce ba sai ta gode masa ba,daga nan ya nuna mata ko ina na gidan ɗakinsa ne kawai bata shiga yadda ya ce banda gyaran ɗakinsa cikin aikinta bayan sun gama zagaye ko ina na gidan ne Expecter ya cewa Hafsah ta koma gida sai jibi zata fara aiki kuɗi ya dauko daga ɗakinsa kusan dubu biyar ya miƙa mata da farko Hafsah bata so ƙarɓar kuɗin ba saida Expecter ya takurata kafin ta ƙarɓi kuɗin
Khalid ne zaune cikin ɗakin Silefarht inda yake zaune bakin bed ɗinta kallon Silefarht dake shirin zuwa office ya yi ya ce ''magana na ke maki amma kin yi shiru''mayar da dubanta ta yi garesa ta ce ''me ka ke son na faɗa l all ready told you bani da lokaci ka taimaka ka gyara min ɗakin saboda yanzu haka jirana ake a office'' ta karasa magana tare da ɗaukar hand bag ɗinta cikin yanayi rashin jin daɗin abinda Silefarht ta faɗa Khalid ya ce ''minti nawa za ki gyara ɗakin? I know you think you don have time kamar yadda kika faɗa, yanzu saboda Allah kina jin daɗin zama cikin wannan ɗakin?kamar mahaukaciya Silefarht bata ji daɗin sunana mahaukaciya da Khalid ya faɗa ba hakan yasa cikin yana na ɓacin rai ta ce
''thanks nagode da kirana mahaukaciya nagode sosai'' tana gama faɗin haka ta sa kai zata fita daga ɗakin Khalid ya yi saurin bin bayanta inda yake faɗi
''ba ni son wata ƴar aiki ta zo ta raina ki ne Silefarht dube inda ki ke kwanciya saboda Allah,ko ma wa ce ta zo ta ga wannan ɗakin wallahi raina ki za ta yi, That's all I'm just trying to let you understand shine kawai'' ya karasa magana yana riƙe hannunta
Fari da ido Silefarht ta yi kafin ta ce
''ok me zai hana ka gyara min ɗakin kaga dai na makara i don't have much time to west Beb'' ta yi magana tana langwaɓar da kai, numfasawa Khalid ya yi ya ce
''Ok then zan gyara ɗakin amma banda banɗaki in ta zo sai ya wanke..ya faɗa tare da sakar mata murmushi rungumarsa Silefarht ta yi tare da manna masa kiss a kunci shi kuwa sai ƙoƙarin haɗa lips ɗinsu yake Silefarht ta yi saurin zare jikinta daga garesa tana dariya ƙasa-ƙasa murya can ƙasa ta ce
''Stop it please kar na makara'' sake riƙeta ya yi a karo na biyu ya matseta sosai da jikansa da ƙyar take fitar da numfashi cikin salonsa ya kai bakinsa dai-dai kunneta ya ce
''Can we have one? a good morning to make your day nice'' wata iriyar murmushi Silefarht ta yi kafin ta ɗan ɗaga murya ta ce
''No we can't l'm sorry''
''Hmmm'' kawai ya faɗa cikin zuciyarsa ya ce na sani ba lallai ki yarda ba Silefarht na ta kokarin raba jikinta daga garesa amma Khalid bai bata daman yin hakan ba sai wani gyara tsayuwarsa da kyau ya yi yana ƙare mata kallo ita dai ta ƙi yarda ta haɗa ido da shi bata anƙara ba sai jin lips ɗinsa ta yi kan nata ya mata wani kiss mai kashi jiki,nan Silefarht ta shiga kokarin raba jikinta daga garesa,yanayin riƙon da Khalid ya yi mata ne yasa ta ƙasa kwatar kanta daga hannunsa,ta yi iya yinta amma ta ƙasa daga karshe dai ta hakura
Bayan mintina arba'in Khalid ne ya fito daga bathroom ɗinsa daga shi sai towel da ya daura a ƙugunsa,cikin sauri ya shirya kansa cikin wata farar yaɗi da aka yiwa ɗinkin jamfa,ya fesa jikinsa da turarukansa masu khamsin gaske,wani irin kyau na musamman ya yi,ya fito tsaf da shi kamar wani ango
Ɗakin Silefarht ya koma ya tarar da ita kwance kan bed tana barcin wahala murmushi ya yi kafin ya tako har inda take kwance,hawa bed ɗin ya yi ya janyota jikinsa a hankali ta buɗe ido, Khalid ya ce
''Oya tashi ki je ki yi wanka kafin su ƙaraso'' rufe ido Silefarht ta yi tare da gyara kwanciyarta a jikinsa murya can ƙasa ta ce
''Sai anjuma zan yi'' dafe kai Khalid ya yi ya ce ''come on Beb daurewa kawai za ki yi ki tashi ki je ki yi wankan'' ya ƙare magana tare da manna mata kiss a goshinta a hankali Silefarht ta tashi zaune har sannan idonta rufe,bargon da ta rufe jikinta da shi ta ja tana ƙara gyara rufa jikinta da kyau wani irin kallo Khalid ke yi mata ji yake kamar ya ƙara kwantar da ita yanzu,gaba daya baya gajiya da Silefarht
A hankali ta sauko daga bed ɗin tana ƙara rufa jikinta da bargon, a haka je ɗakin Khalid sauran bargon na ja ƙasa saura kuma ta rufa jikinta,bayan fitarta ne Khalid ya shiga gyaran ɗakin,kayan Silefarht masu datti ya fara haɗe su wuri ɗaya,ya zuba su cikin wata jaka da Silefarht ke zuba kayan wanki,sharar ƙasan ɗakin ya yi kafin ya fito zuwa nasa ɗakin kayan wankinsa ya kwaso ya haɗa su wuri ɗaya da na Silefarht ya sauko downstairs hannunsa riƙe da jakar kayan wankin
Bayan fitar Silefarht daga wanka shirya kanta ta yi cikin wata doguwar riga Egyptian abaya ɓaka mai sauƙin ado, down stairs ta sauko inda ta tarar da Khalid zaune yana danna wayarsa kallonsa ta yi ta ce
''Har yanzu basu ƙaraso ba?" ajiye wayar Khalid ya yi ya mayarda dubansa gare ta kafin ya ce ''eh basu ƙaraso so nake na kai kaya wajen wanki'' ya karasa magana tare da tashi tsaye
Silefarht ta ce ''oky then sai ka dawo,l have some work to do inside tun da ka hana ni zuwa office yau,i will work from home'' ta karasa magana tana barin wajen murmushi kawai Khalid yana bin Silefarht da kallo har ta haura upstairs
Bayan fitar Khalid da mintina ashirin motar kamfanin Youth dream Co-operation Company ne ya yi parking dai-dai kofar gidan Silefarht da Khalid numfaswa Salma ta yi kafin ta dauko jakarta agent na gaba tana biye da shi har kofar gidan,nocking agent ɗin ya yi a gate ɗin gidan,ba tare da ɓata lokaci ba mai gadin ya buɗe masu kofar nan agent ya yi masa bayanin daga inda suke mai gadin ya ce ya san da zuwansu saboda Khalid ya faɗa masa cewar za'a kawo ƴar aiki,hakan yasa ya yi masu jagora zuwa kofar entrance ɗin shiga gidan,sallama mai gadin ya shiga yi tare da kwankwasa kofa
Silefarht dake zaune cikin ɗaki tana aiki cikin laptop ta ji kamar ana sallama hakan yasa ta dakatar da abinda take ta nitsu dan tabbatar da abinda take ji,can ta ji an sake yi sallama tare da nocking kofar hakan yasa ta ajiye laptop ɗin kan bed gyalen doguwar riga dake jikinta ta dauko ta yi rolling ɗinsa a kanta kafin ta fito daga ɗakin,buɗe kofar ta yi mai gadi ya gaishi ta agent da Salma duk suka gaishi,gaisuwar mai gadin dana agent ya amsa bata amsa gausuwar Salma ba agent na shirin yi mata bayanin daga inda suke mai gadin ya shiga gero mata kirari,ba tare da ɓata lokaci ba Silefarht ta dakatar da mai gadi ta hanyar ɗaga masa hannu tare da fadin ''na faɗa maka ba na''cikin yanayi na jin kunyar yarfa shi da Silefarht ta yi mai gadi ya ce ''Allah ya huci zuciyar Hajiya'' daga haka ya ja bakinsa ya yi shiru,banza ta yi masa ta mayar da dubanta ga agent dake tsaye tare Salma ta ce
''is she the maid?" ta faɗa tare da nuna Salma da ɗan yatsa a hankali mai gadi ya bar wajen ya yi shigiwarsa ɗakinsa dake kusa da gate
Amsa agent ya bata da ''yes Madam she is the one'' Silefarht ta ce ''oky then thanks alot za ka iya tafiya'' agent ya ce ''amma Madam kafin na tafi ina buƙatar sa hannu ki a nan''ya faɗa tare da nuna mata inda zata da hannu karɓar takardar ta yi ta yi singing kafin ta mayar masa da takarda daga haka ya yi mata sallama ya wuce
Kallon Salma ta yi cike da tsana ta ce ''me ki ke jira? dauki jakarki ki shigo'' tana gama faɗin haka ta koma ciki ta bar Salma tsaye, murmushi Salma ta yi tare da tafa hannayenta cikin zuciyarta ta ce ''ikon Allah'' jinjina kai Salma ta yi kafin ta dauke jakarta zuwa cikin parlour,bakinta dauke da sallama ta shigo parlourn ganin Silefarht ta yi zaune kan kujera one siter ta daura ƙafa daya kan ɗaya Salma ta shiga bin parlourn da kallo sosai parlour ya tsaru, cikin sanyi jiki ta karasa shiga parlour
Silefarht dake zaune sai bin Salma take da kallo taga jikin Salma duk talauci amma babu laifi yarinyar tana da kyau tana kuma da diri masha Allah babu abinda Silefarht za ta nuna mata wajen diri,amma ɓaka ce sosai ta fi Silefarht tsawo kaɗan amma ba can can ba,
Saida ta ƙare mata kallo kafin ta ce ''zauna'' Salma kamar jira take ta samu waje ta zauna kan kujera,Silefarht da har sannan idonta a kanta ta ce ''yaya sunan ki'' cike da ladabi Salma ta ce ''sunana Ummu Salma amma ana kirana da Salma'' ta kare magana fuskarta dauke da murmushi wani mugun kallo Silefarht ta yiwa Salma kafin ta ce ''murmushin me ki ke? akwai wani abinda ki ka gani ne da yasa ki dariya?" ta yi magana tana kafe Salma da ido nan take Salma ta gyara fuskantar ta daina murmushin Silefarht ta daura da ''ni da mijina ke zama a cikin gidan nan bana da yaro ko ɗaya so bana tunanin aiki zai yi maki yawa'' karaf Salma ta ce ''wow gaskiya gidan ki ya yi kyau masha Allah ga ki mai kyau ga gidan ki ma mai kyau'' Silefarht bata ji daɗin abinda Salma ta faɗa ba amma sai ta daure ta ce ''nagode'' tana shirin magana ne Khalid ya shigo bakinsa dauke da sallama Silefarht ce ta amsa masa sallamar har inda Silefarht ke zaune ya tako yadda ya manna mata kiss a goshinta daidai lokacin da ya ɗago ne yaga Salma da ke zaune daya kujerar,a hankali ya cire glasses da ke idonsa yana ƙarewa Salma kallo can ya ce ''wa ce wannan?" karaf Salma ta ce
''Sunana Salm''... bata kai ga ida zancen ta ba Silefarht ta ce ''shout up'' shiru Salma ta yi murya can ƙasa ta ce ''yi hakuri Hajiya'' kallon Khalid Silefarht ta yi da har sannan idonsa kan Salma ta ce
''Sunan ta Salma ita ce sabuwar ƴar aiki'' wayancewa Khalid ya yi ya ce ''oh ok ƴar aiki?..kina gani zata iya aikin kuwa Beb?" Salma ta bashi amsa kamar ita ya tambaya ta ce ''kwarai kuwa yallaɓi zan iya'' Khalid ya ce ''ok then'' mayar da dubansa ya yi kan Silefarht ya ce ''in kun gama ina upstairs'' daga haka ya yi wucewar sa sama
Salma ce ta matso kusa da Silefarht murya can ƙasa ta ce ''kai Hajiya mijinki kyakkyawa ne gaskiya kin iya zaɓe'' shiru Salma ta yi tana gingina kyawun Khalid cikin zuciyarta yayinda haushi ya cika Silefarh tana shirin yiwa Salma magana kenan Salma ta ce
''Kin san Allah Hajiya zai yi wuya mijinki baya da budurwa a waje irin wannan kyauwun nasa ke kadai baza ki iya riƙe shi ba'' daurewa kawai Silefarht ta yi bata wankawa Salma mari ba kokarin saita kanta ta yi kafin ta ce ''ina son wannan na zama karo na farko kuma na karshe da za ki sake yin magana kan mijina,kuma ba na son kina yi masa magana in ba shi ya yi maki magana ba duk ranar da na ganki kina magana da mijina ki sani zaman ki yaƙare a gidan nan'' nan Salma ta shiga bada hakuri
Shuukran