5&6
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2/7/2024.....✍️📚🌹
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
*Labarin RAWANIN ZALINCI labari ne a kan sarauta dake tafe da Zalinci, cin amana, tauye hakki, walaƙanci, zanba cikin aminci, ku dama daga jin sunan RAWANIN ZALINCI kun san batu ake a kan sarauta mai tsuma zuciya da gabaɗaya ilahirin gangan jiki, soyayya mai cike da bahagon kuma makauniyar kalubale tattare da kaddarori, fata na dai kada ku yi sauri, ku daure ku bi komai sannu a hankali har mu kai in da kuke da buƙata, duk wanda yake da wata tambaya ko wata magana dangane da littafina RAWANIN ZALINCI, to kai tsaye ya mun magana, *** my contact, ni ce mai littafi, a wajena zaku sami duk wasu amsoshinku da kuke da buƙata. And lastly duk wanda labarin RAWANIN ZALINCI ta taɓo yarensu, al'adarsu, da sauransu, to ya mun afuwa, akasi ne*
E____________5🔥
Ganin lodin magunguna ne a ciki yasa Kamran ɗin ya miƙe tsaye dan ya je ya samowa maman twins ɗin abin da zata ci, saboda ko ba'a gaya mashi ba yasan tana jin yunwa sosai.
Waje ya nufa. Da kallo ta bishi, tana son ta yi mashi magana, amma ba hali, dan bata da bakin iya yin magana, sai kawai ta bishi da idanu har ya kurewa ganinta.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin nan ta dawo da kallonta a kan baby's ɗin nata, har cikin ranta take jin tsananin kaunar yaran nan, tana kuma godewa Allah dayasa ƴaƴa mata ta haifa, da alama ta fi buƙatar mata sosai.
Shi kuwa Kamran, yana fita gida ya koma, ya yi sa'a Mamma tana wanka, a hankali ya lallaɓa ya shiga cikin wajen da take girki, shi kuma Rocky yana tsaye a waje yana jiransa, dan ba zai iya shiga cikin ƙogon ba, kofar ta yi mashi kaɗan, idan baku manta ba dama na gaya maku kofar karama ce sosai, bazaku haɗa jikin mutun da Damusa ba, shi Kamran zai iya shiga, amma Rocky ba zai iya ba.
Kayan cima da mamma ta girma lodi ya ɗebo a cikin kwaninan cin abincin nasu, ya haɗa duk abin da yake ganin ya dace mashi, cikin sauri ya ɗauka ya nufi waje.
Kai tsaye wajen maman twins ya koma. Mamma kuwa, tana fitowa daga wanka ta fahimci ya shigo cikin ƙogon, sahun kafarsa ta gani, kada ku manta gari ne na damina.
Shiru ta yi tana mamakin yadda aka yi yau Kamran ya shigo cikin sanɗa ya kuma sake fita, abin ya bata mamaki, tunani take yi a kan anya kuwa ba zata bi bayansa dan taga me yake yi ba?.
Tunawa da abin da ya faru a tsakaninsu ɗazun na ya ce mata ta taimaki wata mata ta ce ahir ba zata taimaka ba, tuna hakan yasa ta girgiza kai tana mai ciza laɓɓanta, alamar abin bai yi mata daɗi ba. Hakiƙa Mamma tana da wata ɓoyayyiyar baiwa, domin rashin tsoron nan nata da wannan uban jarumtar tata dole akwai ayar tambaya, tabbas ana samun mata marasa tsoro, amma kamar Mamma haka dole a dasa mata ayar tambaya, ita ɗin ba mace bace kamar sauran mata, akwai dai wata a ƙasa, lokaci shi ne alkalin komai.
Cikin ɗakin maman twins ya sake komawa, a kusa da ita ya zauna tare da ajiye mata kayan abincin. Buɗe kwano ɗaya ya yi, wani irin gasasshen nama ne mai matukar kyau a ido, ga kamshi da yake tashi, namar shaniyar daji ce, da alama Mamma bata jima da gama kasawa ba, dan akwai ɗumi a jikinta sosai, ta sha kayan kamshi irinsu curry leaf da sauransu, duk wanda ya ga namar nan sai yawunsa ta tsinke.
Ita kanta maman twins sai da ta ji yawunta ya tsinke da ganin namar, sai dai bata jin kamar zata iya cin wani abin, bakin ta babu ɗanɗano ko kaɗan.
Cikin harshen turanci ya sanar da ita cewa ga abinci ya kawo mata ta ci mana.
Da kallo kawai ta bishi shi da abincin nasa ba tare da ta motsa koda laɓɓan bakinta ba.
Ganin sai kallonsa take yi taki ta yi magana ne yasa ya miƙe tsaye yana gaya mata zai tafi, amma zai dawo anjuma da yamma can.
Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar to ta ji.
Daga haka bai sake yin magana ba yasa kai ya fice abinsa.
Yana fita Rocky ya rufa mashi baya, gida suka nufa, dan ya san in dai Mamma ta fito daga wanka sai ta fahimci ya shigo cikin wannan ƙogon, zata gane sarai, hakan yasa ya yi saurin komawa, saboda kada ta biyo bayansa, ƙarami ne daga cikin aikinta ta biyo shi ta ce bari ta je taga me yake yi, ba yau bane farau wajen biyo bayansa da take yi idan ya fita, in kuma ta zo ta tarar da ga abin da yake yi na taimako, to wlh suna ina samun gagarumin matsala a tsakaninsu, kamar yadda ta tsani ranar mutuwarta, haka ta tsani ta ga Kamran ya raɓi wasu, ko kuma wasu sun raɓesu, shiyasa bata son ya fita, bata kauna ko kaɗan, ita ko maharban da suke wucewa time to time ma sam bata son Kamran ɗin ya ce masu ko sannu. To fah, Mamman akwai matsala babba in kuwa haka ne, da alama dai akwai wani gagarumin al'amari dan gane dake a ƙasa.
Ni kam ina da tambaya sosai a kan Mamma gaskiya, lamarinta akwai ban mamaki, nasan kuma my people kuna da tambayoyi a kanta dayawa, to ku adana tambayoyinku, lokaci zai bamu amsoshinmu.
Yana komawa ya wuce cikin ɗakinsa ya kwanta, zuciyarsa cike fal da tunani iri iri a kan maman twins, yana son sanin wacece ita? Me ya kawota wannan waje?. Da wannan tunani a ran nasa barci ya yi awon gaba da shi.
Mamma ta jima a tsaya tana kare mashi kallo ba tare da ya sani ba, tun shigowarsa cikin ɗakin ta biyo bayansa, sai dai bata shigo ciki sosai ba, ta tsaya ta bakin kofa ne tare da zuba mashi idanu babu ko kyaftawa, da alamar tarin tambayoyi da take son yi mashi sosai a saman fuskarta, amma ko da sunan wasa bata furta ko kalma ɗaya ko ta yi wani motsi da zai sa ya ga tana kallon shi ba, tana gani har ya yi barci.
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙarisowa cikin ɗakin. A gaban ƴar bed ɗin nasa ta tsaya, sosai ta kura mashi idanu babu ko kyaftawa, sai kallon face nasa take yi kamar wadda taga bako daga wani duniya mai wata halitta na daban ba irin na mutane ba, da alama dai akwai wata a ƙasa, wannan kallo bana banza ba, gata da sexy eyes da idan idanun mutun biyu ta tsare shi da kallo to sai ya shiga ruɗu.
Ta ɗauki a kallah good 30 mins tana kallonsa from head to toe kafin ta sa kai ta fice daga cikin ɗakin bayan ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya kenan.
Nata ɗakin ta koma ta zauna a saman bakin bed tare da buga uban tagumi ta afka cikin kogin tunani, sai Allah kaɗai yasan tunanin me take yi.
Shi kuwa Rocky yana kwance a wajen ta bakin ƙogon dutsen abinsa, dama kullum haka suke yi, kamar wani shi ne mai gadinsu, Allah sarki ya yi girman da baya iya shiga cikin ƙogon, hakan tasa sai ya yi zamansa a bakin kofar yana ta kalle kalle, wani lokaci har barci ta ɗauke shi.
To mu dai bari mu kutsa cikin labarin mu duba wani part dan mu ga me ake ciki, wata kila kafin mu dawo wasu abubuwa sun ɗan daidaita ko sun bayyana mana a wannan dajin, dan gaskiya muna da buƙatar bayyanar abubuwa dayawa.
Wasu kyawawan ƴan matasan ƴan'mata ne su biyu suke tafiya, jikinsu na sanye da uniform na islamiyya launin sky blue, wando ce doguwa da riga zuwa gwiwa, sai farar hijabi har ƙasa.
Babbar ba zata wuce 7 years ba, karamar kuma 5 years, kamanninsu kusan ɗaya, sai dai karamar fara ce sosai, babbar kuma ta ɗan yi duhu, ma'ana wankar tarwaɗa, amma da kallo ɗaya zaka yi masu ka fahimci iyayensu guda ne, dan fa ga kamar jinin karara a saman fuskokinsu.
Daga islamiya suke, suna tafiya cikin nutsuwa sosai saɓanin sauran yaran da zaka gansu idan an taso daga islamiya ko makarantar boko suna tafiya a kan hanya suna wasa, wasu ma ka gansu suna guje guje a kan hanya. Su waɗan nan a nutse sosai suke tafiya, bare ma ƴar babban cikin nasu, tana da nutsuwa sosai, da alama sun fito ne daga gidan tarbiya.
Suna rike da wata ƴar ƙaramar jaka na zuba litattafai, jaka ce dai ta ƴaƴan dai'dai mai rufin asiri, uniform ɗin jikinsu ya sha guga sosai, har wani kyalli yake yi, ga karin gugur nan ta zauna sosai a jikin uniform ɗin, da alama mahaifiyarsu jajirtatciya ce wajen iya wanki da guga wa yaran nata, da alama suna samun kulawa sosai, dan daga jikin yara ake gane tsabtar uwa, to gaskiya ita dai wannan uwar ba karya, akwai tsabtar.
Karamar ce ta rike masu jakar, da alama jakar babban ce, karamar ta yi karama da abata Alqur'ani mai girma da sauran litattafan addini, bata da wayo sosai.
Ita kuma babbar hannunta na rike da wata bakar leda, da alama aika ne a ciki. Sai magana ƴan yaran cikin unguwar suke yi wa karamar, amma bata kula kowa ba, ko ɗaga idanu bata yi ta kalli in da suke ba, kasancewar yanzu aka taso daga islamiyar, yaran dayawa ne suke shawagi a sararin unguwar, kowa yana ƙoƙarin nufar gidansu, saboda mangariba ta kawo kai.
Wani ɗan madaidaicin gida waɗan nan matasan ƴan'mata suka shiga, gida ne dai'dai na masu rufin asiri, daga kan kofar gidan har izuwa fentin gidan dukka sun nuna alamun mai gidan mutun ne mai zuciyar yi, kun san ba neman kuɗin ba, zuciyar yi ita ce, akwai masu kuɗin da kuɗinsu bata ciwuwa, akwai kuma wadda zaku gani talaka ne, amma mai zuciyar yi, baya samu sosai kamar sauran mutane, amma da yake akwai zuciyar yi ɗin, sai ku ga ƴaƴansa da gidansa duk kusan dai'dai da na wani mai kuɗin, komai mai kyau zaku ga ya sayawa ƴaƴansa da matarsa gwanin birgewa.
Ko'ina na cikin wannan gida siminti ne, babu kasa, an wanke ko'ina fes babu alamar datti ko kaɗan, kana sako kafarka a cikin gidan ma wani daddaɗar kamshin turaren wuta ne zai daki kofofin hancinka, gwanin burgewa gidan.
Babbar parlour ce a tsakiya mai ɗauke da ɗakuna uku a cikinta, kowace ɗaki da toilet a cikinta, sai wata ɗaki irin ta matasan nan ta wajen tsakar gidan, filin tsakar gidan tana da girma ba laifi, akwai kitchen a tsakar harabar gidan sai toilet ɗaya da ake yi a ta karshen ginin ɗakuna haka.
Wannan mai gida yana da ƙoƙari sosai, har da bohol suke da shi a cikin gidan nasu, suna da ruwa available, ruwa abokin aiki kenan.
Parlourn nasu tamkar sauran kowani parlourn na masu rufin asiri ne, kujeru ne set ɗaya manya manya masu laushi, launin ash da baki, sai ƴar madaidaiciyar TV plasmarsu 32 inches, akwai ƴar karamar freezer a ciki ta kusa da TV, sai wasu kyawawan jeren flowers da aka kawata parlourn da su, fanka ke garesu ba A.c ba, haka zalika ceiling garesu ba P.O.P ba, sai dai kasan parlourn nasu fa tiles ne mai kyau da zanen flowers a jikinsa, launin sky blue, ya sha mopping sosai, sam babu alamar datti, ga karamar welcome carpet a bakin kofa, abin dai gwanin birgewa da ban sha'awa, sai tashin kamshi wannan parlourn yake yi, ko'ina tsab kamar ba'a amfani da abubuwan ciki.
Tsabta akwai daɗi, kai da kanka idan ka tsabtace waje sai kaga ya yi wani irin masifar kyan gani, komai talaucin mutun idan yana da tsabta yana da sha'awar kallo a ido wlh.
Bakinsu ɗauke da cikakkiyar sallama irin ta addinin Musulunci waɗan nan yara suka shigo cikin gidan nasu.
Dayawan mutane ba kowa ne yake yin cikakkiyar sallama ko ya amsa sallamar a cikenta ba, dayawa mutane suna yanketa wanda hakan kuma ba dai'dai bane, domin kamar yadda kuka yanketa haka ma'anarta ta yanke.
Dayawan mutane zaka ji suna cewa Salamu alaikum, masu amsata kuma suna cewa Alaikumussalam, wanda hakan sam ba dai'dai bane, nasan dayawanku baku san kuskure kuke yi ba, to tabbas kuskure ne yanke sallama da kuke yi, kuna yanke ma'anarta.
Masu shigowa zasu ce Assalamu alaikum, Mala'ikun Rahma suna amsata da Amin wa'alailumussalam, idan ku dayawa ne kuka shi go kenan, idan kai ɗaya ne, Amin wa'alaikassalam, shi ne cikakkiyar sallama ta addinin musulunci, Allah ka yafe mana kura kuranmu.
Masu cewa in rinƙa rubuta addu'a ko wata tunatarwa kamar dai sallama dana gyara maku yanzu, masu cewa na rinƙa rubutawa da hausa ba da larabci ba, dan basu iya karantawa ba, zan yi ƙoƙarin yin hakan In Sha Allah, amma wani lokaci dole ne na rubuta da larabcin kun gane ai?.
Daga cikin ɗaki aka amsa masu cikakkiyar sallamar tasu tare da cewa. "Ƴan mata na an dawo?".
Babban cikinsu ne ta amsa da. "E mama mun dawo".
Tana magana tana cire hijabin jikinta, sannan ta ajiye wannan ledar dake a hannun nata a tsakar gidan, kafin ta wuce izuwa cikin parlourn.
Ita kam karamar dama tun shigowarsu ta sanya kai izuwa cikin parlourn da sauri abinta tana faɗin. "Mama baba ya aiko mun da lemun?.......".
Turus ta ja birki a tsakiyar parlourn lokacin da idanuwanta suka sauka a kan maman nata tare da wata bakuwar mata suna zaune a saman sofa suna hira. Mama ta sha kwalliya cikin wani haɗaɗɗen lace mai tsada da ya sha ɗinkin doguwar riga, ta yi kyau sosai, launin black color ne lace ɗin da ratsin milk, hakan ya kara mata kyau sosai kasancewarta farar fata, ta sha ɗaurin ɗan'kwalinta ɗas da shi. Ita kuma wannan bakuwa tana sanye da abaya launin ash color, ta yafa mayafin abayar a kanta.
Nan take yarinyar ta ɗaure fuska sosai kamar ba ita ba, duk da cewa dama can fuskar tata ba wani murmushi ne a samansa ba, daga ita har babban yayar tata babu alamar murmushi a saman fuskarsu, da alama basu da yawan fara'a, shi ne ma yasa da suna dawowa daga islamiya sai magana yara sa'anninsu suke yi masu, amma sun ki kula kowa.
"Zinarun babanta ya kika tsaya haka? Ki ƙariso ciki mana". Cewar matar dake hira da mamar tasu.
Kara ɗaure fuska sosai Zainab ta yi, da alama bata kaunar matar ko kaɗan. Daidai lokacin ita ma babbar ta shigo cikin parlourn tana faɗin.
"Mama ga can kayan miyar nan na kawo maki, amma mama wai fa babu attarugun ɗari biyu, shi ne na saya maki ta ɗari biyar kawai, shi ma baki gansa ba ɗan kaɗan da shi........"
Bata kai karshen maganar ba ita ma idanuwanta suka sauka a kan wannan matar, ɗaure fuska sosai ita ma ta yi tare da wucewa zata nufi ɗaya daga cikin ɗakunan dake a cikin parlourn.
"Khadija baku ga Auntynku bane? Aunty Hauwa ce fa, ba zaku gaisheta bane". Cewar maman tasu.
Wucewa Zainab ma ta yi ta rufawa Khadijah ɗin baya, dan su shiga cikin ɗakinsu.
"Sannunki da zuwa Aunty Hauwa". Cewar Khadijah, ta yi maganar tana wani irin kunbura kumatu, alamar sam bata ji daɗin sakata gaisheta da aka yi ba.
Washe baki Aunty Hauwar ta yi tana faɗin. "Hadiza bage maganin maza, wai ni kam duk masu suna Khadijah haka suke ko? Haka kanwata ma take sam bata son baki".
Wata uwar harara Zainab ta wurga mata ba tare da sun lura ba, cikin ɗaki ta wuce abinta, har ga Allah ta tsani wannan Aunty Hauwa ɗin, ko me dalili?.
Turɓune fuska Khadijah ɗin ma ta yi kamar wadda aka aikowa da sakon mutuwa, yara kanana da su sun san kin abu, kome dalilinsu oho.
Uniform ɗin jikinsu suka cire, suka sanya kayan gida, wasu dogayen riguna bakake, iri ɗaya kayan, sai dai na Khadijah mai kwalliyar flowers ja ne, na Zainab kuma mai kwalliya pink color, shi ne kawai banbancin kayan nasu.
Fitowa suka yi suka sake wuce maman tasu da Aunty Hauwa, waje suka nufa, a lokacin sai kiraye kirayen sallar mangariba ake yi.
Famfo tsakar gidan suka je suka kunnna, Khadijah ce ta fara gabatar da alwala kafin ta bawa Zainab waje ita ma ta ɗauro nata alwalar, da alama mamansu ta saba masu da yin komai cikin tsari, dan daga yanayin yanda suka shigo suka je suna cire uniform suka fito suka ɗauro alwalar nan, alama ya nuna cewa tabbas an sabar masu da hakan ne.
Ciki suka koma, dai'dai lokacin aka kawo wutar nepa, sallah suka je cikin bedroom nasu da yake tsab tsab suka gabatar, ita kuma mamar tasu tana zaune ta biyewa Aunty Hauwa sai zuba hira suke yi har yaran suka idar da sallarsu.
Abin mamaki cikin nutsuwa suke gabatar da sallar nan tasu tamkar wasu manya.
Bayan sun idar ne suka fito parlourn, a yadda suka bar mamarsu haka suka fito suka sameta.
Khadijah ce ta ce. "Mama yau kin manta baki yi sallah da wuri ba".
"Ban manta ba Khadijah, ai ba'a mantuwa da ibada, yanzu nake son tashi na yi".
Da gudu Zainab ta nufi kofar fita daga parlourn jin an taɓa kofar gida, faɗi take yi oyoyo baba oyoyo Yah Haidar. Da sauri Khadijah ma ta rufa mata baya, tamkar basu ne masu ɗaure fuska yanzun nan ba, a take suka fara zuba murmushi na ganin mahaifin nasu da kuma yayansu, ashe dai suna dariya, amma da alama ƴan gidansu kawai suke yi wa dariyar.
Yah Haidar ɗin nasu yana rike da kaji na hausa guda biyu a hannunsa, zakara da kuma mace, sai kuma wani katuwar bakar leda a ɗayar hannun nasa, shi kuma baban nasu yana rike da wata leda irin mai zane a jikin tan nan, kayan fruit ne a cike a cikin ledar.
Khadijah tana zuwa ta fara kiciniyar karɓawa baban nasu ledar hannun nasa, ita kam Zainab tuni ta yi tsalle ta ɗale jikinsa tana dariya har da kyakyatawa, kamar ba ita ce yanzun nan ta gama hararar Aunty Hauwa tare da turɓune fuska ba, dama fa masu suna Zainab da Khadijah wlh sai a hakankali, kusan kaso tamanin cikin ɗarinsu haka suke, akwai shegen tsare gida, sai dai suna yi wa wanda suka ga dama fara'a, kamar dai yadda kuke ganin waɗan nan yaran baban nasu.
"Zeezeena kun yi sallah?".
Shi ne tambaya ta farko da wannan uban na garin ya fara yi masu, ya yi maganar kuma yana sakewa Khadijah ledar fruit dake a hannunsa, yaran kirki, yana da kyau duk wata uwa ta koyawa ƴarta karɓar abin da mahaifinsu ya shigo da shi, hakan shi ne tarbiya.
Khadijah ce ta bashi amsa da. "Mun yi baba, amma mama bata yi ba, tana can suna hira da wannan Aunty Hauwar ta gidansu Khadijan nan na islamiyyarmu".
Dariya kaɗan Haidar ya yi yana faɗin. "Ke yanzu Khadijah waye ya tambayeki mama ta yi sallah ko bata yi ba? Ba dai ke kin yi ba? To Allah ya karɓa, ni bana hanaku faɗi ba'a tambayekun nan bane wai?".
Ɗaure fuska Khadijah ɗin ta yi tare da wucewa ta nufi cikin parlourn tana turo baki, ita a dole Yah Haidar ya shiga maganarta ba da shi take yi ba, ranta ya ɓaci.
Wucewa wajen ɗan madaidaicin kitchen ɗin nasu Haidar ɗin ya yi, a ciki ya ajiye kajin tare da ledar cefenen da yake a hannunsa, sannan ya fito ya nufi wannan ɗakin samarin da yake a harabar gidan.
Ita kuwa Zainab baba ya ɗagata sama suka nufi cikin parlourn.
Bakinsa ɗauke da cikakkiyar sallama ya shigo cikin parlourn.
A tare Aunty Hauwa da maman nasu suka amsa mashi sallamar. Ƙarisowa ciki ya yi tare da wucewa ya nufi ɗaya daga cikin ɗakunan dake a cikin parlourn, har cikin ransa yake jin daɗin shakar wannan daddaɗar kamshin turaren wutar da yake tashi a cikin parlourn, bai ce da Aunty Hauwa ko sannu ba, da alama irin mazan nan ne da idan bakin matansu sun zo gida ba su kulasu, in dai ba su ne suka ɗaga masu gaisuwa ba, to ko sannu ba zasu ce masu ba, ko kallon in da suke ma ba zasu yi ba, dan haka shi ma dai ko kallon Aunty Hauwa ɗin bai yi ba, ya sa kai zai wuce abinsa, yana ɗauke da Zainab a saman kafaɗarsa.
Cikin sauri Aunty Hauwa ɗin ta ɗaga mashi gaisuwa tana wani kara faɗaɗa murmushin da yake a saman fuskarta.
A takaice ya amsa mata da amsa ɗaya wato lafiya, ya amsa kuma ba tare da ya kalli in da take ba, daga haka kuma yasa kai sai cikin bedroom nasa abinsa.
Ajiye ladar da ta karɓo daga hannun baban nata Khadijah ta yi a tsakiyar parlourn, sannan ta yi sauri ta bi bayansa izuwa cikin ɗakin nasa.
Miƙewa Aunty Hauwa ta yi tana faɗin. "Babansu Zainab ya dawo, bari na je gobe zan dawo mu karisa maganarmu".
Da sauri maman tasu ta ce. "A'a tsaya ki sha fruits mana".
Ba kunya ta ce to a bata, ita kuma maman cike da zumuɗi ta buɗe ledar ta fara haɗo mata komai ɗaɗɗaya kamar ita ta kawo ta ajiye.
Kuskure ne idan mijinki ya sayo abu ki ɗauka ki yi kyauta da shi ba tare da saninsa ba, ansan cewa duk abin da zai sayo ku ya sayowa, amma kuskure ne ki kyautar baki tambaye shi ba, koda ƴan uwanki zaki bawa, yin hakan wlh sam bai dace ba, kina zubar da kima da kuma darajarki ne a gabansa, kuma hakan yanasawa namiji ya ji ya daina sha'awar saya maku abu idan ya fita, dan zai ga kamar baku ɗauki abin da mutunci da daraja ba, tabbas idan kin tambaye shi zaki yi kyauta da shi zai yi wuya ya hanaki, wannan tambayarsa da zaki yi ɗin zai kara maki kima da daraja, zai kuma sa mijin naki ya ji cewa yana da kima a idanunki da har zaki tambaye shi kafin ki yi kyauta da abin da ya saya maku, koda bai nuna maki ya ji daɗin tambayarsa da kika yi ɗin ba, wlh ina mai tabbatar maki ba ƙaramin daɗi suke ji ba, dan haka koma me ya kawo koda kannenki zaki bawa, ki tambaye shi cewa zaki bawa su wane kaza abu kaza, musamman ma idan a lokacin ya kawo abin, yasan adadin yawansa da in kin kyautar zai gane, wasu mazan in kin tambayesu zasu ce maki to ki bayar mana ba ke suka kawowa ba? Kada ki damu wlh suna jin daɗin tambayar, kuma kada amsarsu yasa gobe ki fasa tambayarsu, ki tambaya ɗin zai fi.
Ai kuwa ita dai maman su Zainab duk ta haɗawa Aunty Hauwa fruits ɗin nan komai ɗaɗɗaya, ta ɗauko wani leda daga cikin kitchen ta sanya mata a ciki, sannan ta rakota har kofar gida, sai zuba godiya Aunty Hauwa ake yi kamar me.
Naira dubu ɗaya mamansu Zainab ɗin ta bata a kan ta hau abin hawa zuwa gida. Sai murmushi take yi tasa hannu ta karɓa, tana ta zuba godiya ta tafi.
Ita kuma Maman Zainab ta juya ta dawo cikin gida.
A parlourn ta isko su Zainab suna zaune, bata ce da su ko sannu ba ta yi saurin wucewa cikin ɗakin baban nasu, dan ko ba'a gaya mata ba tasan ya fito daga wanka ne ya ce su Zainab su je parlourn bari ya sanya kaya, dama haka yake yi da su.
A hanzarce ta faɗa cikin ɗakin baki ɗauke da sallama, daidai lokacin yana ƙoƙarin zura jallabiya a jikinsa.
Ƙarisowa kusa da shi ta yi tana faɗin. "Ka yi hakuri baban Zainab, yau Hauwace ta tsayar da ni ban zo na fitar maka da kayan sakawa ba".
Fuskarsa a ɗauke da ƙayatattcen murmushi ya bata amsa da. "Kada ki damu, ai kullum kina fitar mun, dan yau kawai baki yi ba ai ba komai, muje bari maje masallaci lokacin sallar issha ta gabato".
Dayawan maza suna bawa mata irin wannan masa da baban Zainab ya bata a yanzu, wanda kuma magana ta gaskiya wlh ba har cikin zuciyarsu wannan amsa take ba, suna dai faɗa ne kawai, dan haka mata sai ku kiyaye, kada ki bari ya maimaita maki irin wannan amsa sau biyu zuwa uku, daga haka za'a fara samun matsala, wani ma idan ya cigaba da maimaita maki sai ki ji ya bushe idanu wata rana yana ce maki ai bama ki taɓa fitar mashi da kayan sawa ko makamancin hakan ba, duk kuma ke kika fara jawowa kanki, kada ki bari dan kin yi bakuwa tasa ki fasa yi wa mijinki abin da kika saba yi mashi, idan bakuwar ba zata jiraki ki yi attending nasa na ɗan lokaci ba, to gara maki ta tafi zai fi, dan haka sai a kula sosai.
Murmushi ta yi ita ma tana mai kara bashi hakuri, cigaba da gaya mata babu komai ya yi kafin ya ɗauko perfume nasa mai daɗin kamshi da nufin ya feshe jikinsa da shi.
Hannu ta kai ta karɓi perfume ɗin ta fara fesa mashi tana mai yabawa kyan da ya yi. Ba karya fa babansu Zainab kyakkyawa ne sosai, sai dai chocolate color ne, ya fi mamar tasu kyau sosai, ita kuma ta fishi hasken fata, farace sosai, su Zainab duk shi suka ɗauko a kyau, sai dai ita Zainab ta ɗauko hasken mamanta, kyan babanta, ita kuma Khadija komai na baban ne harta launin fata.
Bayan ta gama fesa mashi perfume ɗin ne ta ɗauko mashi wayarsa babba da karamar da suke a saman shinfiɗaɗiyar bed nasu 6/7, gadon ya sha gyara kam, ba karya maman Zainab akwai ƙoƙari wajen sake jiki ta yi aikin gidanta da kyau da kyau, yanzu haka wannan jallabiya na jikin baban Zainab ita ce nan ta wanke ta zuba mata guga, sai kyalli take yi, ta sha iron, ita fa maman Zainab da alama gugan kaya baya yi mata wahala, dan harta bedsheet dake a shunfuɗe a saman bed ɗin nan ya sha guga sosai, da yake ma sun saba shan guga sai ka gansu da karin gugan ya fito ɓaro ɓaro, ya riga ya kama kayan, to abu ne da ake yi ba jiya ba ba shekaran jiya ba, an jima, dole kunga su kama karin guga.
Parlourn suka fito, a nan ya isko sanyin idaniyarsa wato ƴaƴan nasa, Zainab tana kallon Tv, ita kuma Khadija tana rike da wayar mamanta tana buga game.
"Zeezeena zan je masallaci amin addu'a".
Ya faɗa yana nufar kofar fita daga cikin parlourn. Har suna rige rige ita da Khadijah wajen zuba mashi addu'ar adawo lafiya Allah ya tsare ya kiyaye hanya.
Da amin ya amsa masu kafin ya fice. Har harabar gidan maman nasu ta rako shi kafin ta dawo wajen famfo dake harabar gidan ta ɗauro alwala, a lokacin aka fara kiraye kirayen sallar issha.
Fitowa daga nasa ɗakin Haidar ya yi, cikin sauri ya kariso wajen famfon dan shi ma ya ɗauro alwala. Sannu ya yi wa maman Zainab ɗin tare da tsayawa a gefe guda yana jiranta ta gama.
Amsa mashi sannun nasa ta yi tare da tambayarsa ya kasuwa.
Alhdulillah ya amsa mata da shi, sannan ya ɗaura mata da cewa. "Sadiq dai yaki dawowa yau ɗin ko?".
Ɗagowa ta yi daga wajen fanfom tare da kasheta tana faɗin. "Ba yadda ban yi da shi ba a kan ya dawo, ya ce mun sam shi bai kalli mama sosai ba, wai sai jibi zai dawo".
Ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi hanyar komawa cikin parlourn.
"Gaskiya Sadiq bai kyauta mun ba, sam goben nan ban so fita kasuwa ba, dan ina da wanki da ɗan aikace aikace da zan yi a ɗakinmu, amma shi ne yaki dawowa, next time ba zan barshi ya yi tafiyar nan ba".
Murmushi kaɗan ta yi tana faɗin. "Ai kun fi kusa". Daga haka ta wuce ciki abinta.
A parlourn ta isko su Zainab ɗin a saman dadduma, sallah suke yi, wucewa nata bedroom ɗin ta yi, dan ta biya sallar mangariba kafin ta ɗaura da issha.
Bayan sun idar da sallar, zama suka yi a saman dadduma Khadija tana karawa Zainab karatun malumat da Nahhu, a haka babansu ya dawo daga masallaci ya samesu, a lokacin kuma mamansu ta idar da nata sallar har ta zo ta ɗauki fruit ɗin da ya kawo ta wankesu tsab, ta zuba masu su a cikin plate tare da sanya masu wuƙa a saman plate ɗin wanda zasu yanka fruit ɗin, ta ajiye a tsakiyar parlourn haɗe da abincin darensu, akwaita da ƙoƙarin aiki kam, bata da son jiki, bayan ta yi dukka wannan ma kitchen ta wuce ta hau shirya kayan cefanen da Haidar ya shigar dasu ciki, su curry ne dasu maggi, kayan kamshi da dai sauran kayan girki, su tattasai da attarugu ne kawai babu a ciki, baban Zainab akwai shi da iya sayan kayan kamshin girki, ya iya cefene sosai kamar wata mace, idan ya yi cefenensa ma yafi wata macen.
Bayan ta shiryasu cikin robobin kayan miyarta ne ta dawo ta ɗauki kayan miyar da Khadijah ta ajiye mata a tsakar harabar gidan, tomatoes ne da su attarugu, dama su babansu bai cika sayo irinsu a cikin cefenensa ba, da yake cefenen sati sati yake yi, su kuɗi yake bawa maman nasu ta saya.
Kitchen ta kai kayan miyar ta shiryasu yadda ya dace, dan na miyar gobe da safe ne, dama haka suke yi kullum, tun da yamma a hanyar islamiya Khadijah take yo masu cefanen su tomatoes na miyan washegari, dan su ajiye komai ready, saboda kada su Khadijah su yi lattin zuwa makarantar boko a dalilin jiran girki ya nuna.
A parlourn ta isko baban nasu tare da Haidar sun dawo daga masallaci, a kusa da baban ta zauna tare da fara ƙoƙarin zuba masu abinci, dan duk zaman cin abinci suka yi, da alama da yunwa suka dawo daga kasuwar nan.
Jawo plate na kayan fruits ɗin nan baban nasu ya yi, fuskarsa ɗauke da ƙayatattcen murmushi ya fara faɗin. "Zeezeena zo ki sha lemun da kika yi ta tuna mun a waya na saya, sarkin son lemu".
Khadijah ce ta ce. "Baba ni kuma ina inabi na?".
"Mamana na sayo maki kema ai, ban manta ba, duk kuzo ku sha".
Ya yi maganar yana yankawa Zainab lemun zakin da ya ɗauko. Yana yanka lemun yana kallon cikin plate na fruits ɗin, idanuwansa kamar suna yi mashi gizo ne, dan bai ga inabin Khadijah a ciki ba, kuma itace ɗaya ya sayo inabin dama, wa ita kaɗai, ita kaɗai ya sayawa, dan ita kaɗai take shan inabi a gidan, Zainab lemu take so, ita kuma mamansu Apple, kowa da abin da ya fi so, shiyasa idan ya tashi saya yake sayowa kowa nasa, baya manta na kowa, shi kuma kankana yake sha shi da Haidar, sun fi sonta.
"Maman Zainab kin rage wasu fruits kin saka a cikin fridge ne?". Ya yi maganar yana miƙawa Zainab lemu.
Tana kan zuba masu white rice and beans ɗin a cikin plate ta bashi amsa da.
"A'a ban rage komai ba, dukka fruits ɗin ne kenan".
Dawo da kallonsa a kan Haidar ya yi kafin ya ce. "Haidar malam Sani bai saka mana inabin Khadijah da kuma abarba ba".
"Any kuwa? Kamar fa ya saka a ciki, naga lokacin da ya ɗauko ya saka". Haidar ya bashi amsa.
"To amma ya babu a ciki?". Baban ya sake jefa masu tambaya fuskarsa da alamar damuwa, dan shi mutun ne da baya son ko da sunan wasa ƴaƴansa su ji cewa kamar yana yi masu banbanci a tsakaninsu, da yasan babu inabi da ba zai bawa Zainab lemun nan ba har sai ya sake fita ya sayowa Khadijah nata, sai ya dawo ya basu a tare, dan komai a tare yake yi masu, yana nuna masu cewa dukkansu ɗaya.
Shiru maman Zainab ɗin ta ɗan yi na ƴan sakani kafin ta ce "E akwai inabi fa, dan na ɗauki itace ɗaya ma na haɗawa Hauwa a cikin fruit dana ɗeba mata".
Da sauri ya ɗago kai tare da watsa mata wani irin kallo mai nuni dacewa meyasa zata yi hakan?, domin kuwa inabi guda ɗaya ya sayawa Khadijah ita kaɗai. Amma duba da yaran suna nan sai bai yi magana ba, ya yi shiru, har cikin ransa sam bai ji daɗim hakan ba, sai ma ya ji duk abincin ta fita mashi a ransa, ya ji babu daɗi sosai, ya sayowa ƴaƴansa abu ta wani ɗauka ta kyautar kamar ya aiketa, in da ma kankanarsa ta kyautar ba zai damu ba, amma na Khadija takwarar mamansa guda, gaskiya bata kyauta mashi ba.
"Kiyi hakuri mamana, bari Yah Haidar ya je ya sayo maki wani yanzu nan, jeki ɗaki ki ɗauko kuɗi a wajen drawer ta ki kawo mun". Ya faɗa cikin sanyin murya, daga jin yanayin maganarsa kasan sam bai ji daɗin abin da maman nasu ta yi ba, ita ma kuma ta lura da bai ji daɗin ba, duk sai ta ji babu daɗi ita ɗin ma.
"A'a ta bar kuɗin da akwai kuɗi a jikina bari na sayo mata da shi". Cewar Haidar.
Taɓe baki maman Zainab ɗin ta yi tana mamaki, yau Haidar da kyauta, sam baya taɓa masu kyautar ko Naira biyar ɗunsa, idan kaga ya bawa su Khadijah kyautar wani abin ci ma ba kuɗi ba to wlh sai idan babansu yana nan, eyes service gare shi, in babansu baya nan ko tsinkensa basu ci. Allah mai iko, kaga dayawa idan kana raye.
Miƙewa ya yi ya fice daga parlourn, sai hakuri baban nasu yake ta bawa Khadijah, ta dai ce mashi to, amma ji take kamar zata fashe dan haushi, sai ta ji ta kara tsanar wannan Aunty Hauwar.
(Masu suna Khadijah idan suka tsaneka ka shiga uku😅 kome zaka musu ba zasu ga farinka ba😅 in sun riga sun saneka fa to sai dai ka yi hakuri ka rungumi sorry ka kyalesu😅 ina ga dalilin cinye masu abubuwa da Aunty Hauwa take yi yasa suka tsaneta😅)
Abincin suka fara ci cikin nutsuwa, maman Zainab ba dai iya girki ba, ta kware sosai, idan kana cin girkinta idan ka yi wasa sai ka fara zuba santi ba tare da ka sani ba, saboda daɗi da iya tsara girkin.
A wannan hali Haidar ya dawo ya samesu, bai samu inabi ba, masu fruits na unguwar tasu duk basu kawo inabi, kun san yana da tsada, ba kowa yake sayansa ba, hakan yasa ba kowani mai sai da fruits yake kawo shi ba, sai manya masu sayarwa.
Jin cewa ba'a sami inabin ba yasa Khadijah ta fashe da kuka tare da miƙewa ta bar abincin nata, fuuu ta nufi cikin ɗaki.
Kallon maman baban nasu ya yi, irin kallon nan na ke kika jamun, ita ma shi take kallo, irin kallon nan na kayi hakuri.
Bai ce da ita ko uppan ba ya miƙe ya bi bayan ƴar tasa dan ya rarrasheta, ga shi kuma dare ne, idan ya ce zai je neman inabi a yanzu sai ya hau mashi ya fita cikin gari ta wajajen kasuwar tasu, zuwa wajen kawai ma 500 naira ne kuɗin mashi, dawowa ma haka, bare kuma daren nan kunsan kara kuɗin mashi suke yi, gaskiya maman Zainab dai bata kyauta mashi ba, kuma idan bai nemo wannan inabi ba Khadijah dai ƙaramin aikinta ne ta yi mafarki, shi ma dai ba zai iya yin barci cikin daɗin rai ba, dan yasan waye Khadijah bagensa, sarkin zuciya da rigima, dole dai anemo inabi, kuma tsautsayi ne tasa yau ya sayi inabin guda ɗaya, sau da dama biyu ko ukku yake saya, zaka gansu a jikin itacensu ba'a cire ba an sako mashi guda uku, to yau sai malam Sani ya saka masu guda ɗaya tak, Mama ta bawa Aunty Hauwa, aiki babba kenan, akwai rigima.
Nikuma dole na dakata da rubutu a nan, Maman Zainab baki kyauta mana ba, shiyasa ake son a rinƙa tambayar mutun abu idan ya kawo, ba wai ayi gaban kai ba.....….😌😒
*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, ***.*
🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 3/7/2024.....✍️📚🌹
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________6🔥
Kwance ya isko Khadijah kadina kadin Allah a saman ƴar madaidaiciyar bed nasu 6 by 6. Gadon a shunfuɗe yake da zanin gado mai kyau lunin pink color da ratsin baki, tsab da shi, sai kamshi ɗakin nasu ma yake yi, ga drawer kayansu mai ɗan girma a gefe guda, sai drawer bed ɗin da suke jera kayan kwalliyarsu da kuma mayukan shafawarsu.
Sai wani irin kuka take yi, irin kukan nan da idan mutun zuciyarsa ta hasala sosai, sai ka ji yana wani irin kuka kamar mai sifirin..........😅
To haka Khadijah take wanan kuka. A bakin bed ɗin ya zauna tare da sanya hannu ya ɗagota yana mai bata hakuri.
Cigaba da kuka ta yi abinta, tana yi tana wani irin jan numfashi alamar fa ta kai kololuwa wajen jin haushi.
"Mamana ta shi ki je ki ɗauko hijabinki mu je bakin kasuwa a tare mu sayo wani inabin kin ji?".
Ya faɗa cikin sigar rarrashi.
Maƙe mashi kafaɗa ta yi, da kyar ta iya cewa. "Ni baba ka bari sai gobe, kada ka fita da daddaren nan, kaga ranar ma da ka fita sayowa Zainab magani masu kwacen waya sun tareka a hanya ko? Tom ka bari sai gobe kawai ka dawo mun da shi daga kasuwa".
Tana magana wasu hawaye suna gangaro mata, kai daga jin maganar tata kasan ba daga cikin zuciyarta ya fito ba, ta faɗa mashi hakan ne kawai dan son da take yi mashi, bata son waɗan nan gurɓatattun mutane masu kwacen wayar su yi mashi illah, dan a wancan karon da suka tare shi har sun buge shi da sanda a hannu, sannan suka kwace mashi waya, haka hannun nasa ta kumbura tsawon sati biyu baya zuwa kasuwa, baya fita ko'ina, da kyar ya samu hannun ta yi sauki, shi ne yasa yanzu da sun yi sallar issha dai sun shiga kenan, zasu rufe gidan abinsu, a lokacin da abin ya faru Khadijah ta sha kuka kamar ba gobe, dan tana tsananin son baban nata, yana kyautata masu over.
"Amma mamana ki bari naje a sayo maki, dan nasan kina so, ga shi ma kin kasa dai'na yin kuka, kawai ki barshi bari na je na saya maki".
Cikin sauri ta kai hannunta a saman face nata ta fara goge hawayen nata tana faɗin.
"Baba ga shi nan ai na dai'na yin kukan, ni dai ka bari sai gobe ka sayo mun".
Ƙaƙalo murmushin dole ya yi tare da sanya nashi hannun ya fara tayata goge hawayen yana faɗin.
"Tom shikenan, gobe idan Allah ya kaimu guda biyu zan sayo maki, yanzu tashi muje mu ci abinci ko?".
"Baba Allah bana son wannan Aunty Hauwar, haushi take bani, kullum idan ta zo gidan nan sai mama ta bata abubuwanmu ta tafi da shi gidanta".
Ƴar murmushi ya yi kafin ya fara bata amsa da cewa.
"Haba mamana, kada ki zama mai rowa mana, menene dan mamanki ta bawa wata kyautar abu? Ai lada zamu samu, kin ga wannan Aunty Hauwar taku? Mamanku bata da kawa biyunta, tare suka taso unguwa guda, a tare suka yi wasan kasa, a tare suka yi karatu, Allah da ikonsa kuma sai ya kawosu aure gari guda, kin dai san mamanki bata da kowa a nan ko? Iya ƴan uwana kawai ke gareta, nata ƴan uwan babu ko mutun ɗaya a nan, to haka ita ma wannan Aunty Hauwar, bata da kowa sai ƴan uwan mijinta sai kuma mamanku, kinga dole zasu kaunaci juna su kuma haɗa kai da juna dan su ɗebewa junansu kewar iyayensu da ƴan uwa, dan haka ki dai'na cewa kin tsaneta kin ji ko? A matsayin ƴar uwar mamanku take, ku ɗauketa tamkar kawu Sadiq naku, ba kuna son Kawu Sadiq ba?".
Da suri ta gyaɗa mashi kai tare da faɗin. "E baba muna son kawu Sadiq sosai, kullum baya taɓa dawowa gidan nan ba tare da ya kawo mana abin kwalama ba, amma shi Yah Haidar sam baya bamu komai, sai shegen masifa ya iya, shiyasa ni nafi son kawu Sadiq nawa".
Shiru baban nata ya yi, har cikin ransa bai ji daɗin maganarta ba, ransa ya sosu, amma ya zai yi? Gaskiya take faɗa, dan Khadijah bata karya, Haidar ɗin shi ya jawa kansa.
Nasan zaku so sanin wanene Haidar a gare su, wanene kuma Sadiq, to Haidar dai ɗane ga babbar ƴar babansu, wanda tun yana ƙarami baban nasu ya rike shi, a tare suke zuwa kasuwa, yana taya shi sayar da kaya, mutun ne shi mai irin halin mata, akwai shi da gulma, ga shegen iya eyes service, idan babansu yana nan zai kulasu, a bayan idanun babansu kuma sai hantararsu ya iya yi da zagi, baya wani kulasu, maman nasu ma ba wani ɗaukarta da daraja ya yi ba, ta rike shi tun yana ɗan shekara 8, yanzu har ya kai 18 years a duniya, amma hakan bata hana idan ta yi mashi ba dai'dai ba ya yi mata rashin mutunci, ga shehen kai gulma cikin dangi, ya ja ayi ta zagin Mamansu Zainab ɗin a kan ta mallake babansu, abu dai babu daɗi, yanzu duk ƴan uwan mijinta basu sonta, kuma duk wannan Haidar ɗin shi ne sila, ya je yana kwasan duk sirrin gidan yana kaiwa dangi, har da karawa da karyarsa son ransa.
Shi kuma Sadiq kani ne ga maman nasu, yaron kirki, ko da yake dama dole ya zamana yana kaunarsu Zainab ɗin sosai, saboda ƴar uwarsa, tun da aka aurota tana amarya ta taho da shi, dan bata da kanwa mace, sai shi kaɗai, shi ne ta roki babanta lokacin tun yana da rai, ta roƙe shi ya bata Sadiq ɗin, da kyar aka yarda aka bata shi, a lokacin yana da shekaru 7 a duniya, ta rike shi har yanzu ya kai yana da 17 years, yaron kirki mai yin komai tsakaninsa da Allah, yana kaunar su Khadijah ɗin sosai, ko fita ya yi waje zai sayi abu, to ba zai dawo cikin gidan ba sai da sweet ko biscuits, ya kawo masu, su yi ta murya, yana kyautata masu sosai, duk abu mai kyau idan ya gani zai saya masu ya kawo masu, ko kaya ya gani a kasuwa an kawo sabbi masu kyau, da kuɗinsa yake cirewa ya saya masu, wani lokaci har faɗa yake yi da Haidar ɗin akan hantararsu Khadijah ɗin da yake yi idan babansu baya nan, kullum kuma idan suka yi faɗa sai Haidar ɗin ya yi mashi gorin cewa wai iyayensa basu da karfin rikesa ne yasa suka haɗawa kawunsa wato banansu Zainab ɗin kenan nauyi, wai yazo yana cinye masu arziki shi da ƴarsa, wani lokaci har ikirarin cewa sai ya yi sanadiyar barinsu gidan daga shi har ƴaƴar tasa Haidar ɗin yake yi, shi ala dole ana cinyewa kawunsa kuɗi, saboda jahilci, bai san me ake nufi da mata ba!.
Wani lokaci har kuka Sadiq ɗin yake yi ya ce ba zai zauna a gidan ba zai koma garinsu, dan yana da zuciya, Mamansu Zainab ɗin ce take bashi hakuri ta yi ta lallaɓa shi, ta ce mashi idan ya koma ya barta ita da waye zata zauna? Waye zata gani ta ji daɗin rayuwa? Ya sani ƴan uwan mijinta duk basu sonta, idan ya tafi ya zata yi da rayuwarta?. Da haka take lallaɓa shi ya yi hakuri ya zauna.
Shi Sadiq ya yi karatu, yanzu haka yana Ss3, shi kuwa Haidar tun daga primary 4 ya fasawa malamin English nasu kai dan bai yi class work da aka basu ba malamin ya zane shi, shi ne ya fasa mashi kai da katako ya gudu ya bar makarantar, tun daga lokacin ya ce ya ajiye karatu, ba yadda ba'ayi da shi ba ya koma makaranta, amma fir yaki yarda, har canza mashi makaranta banansu Zainab ya sake yi, amma sam yaron nan yaki, ya ce shi neman kuɗi zai yi, ga jahinci a cike da kai, shiyasa yake gulmace gulmace da tsugudidi tare da kananan maganganu, da ace yana da ilimi ya yi karatu, da sam ba zai yi wannan shirme ba, yanzu yana nan babu boko babu Arabic, shiyasa a haukarsa yake ganin cewa wai Mamansu Zainab tana cinyewa kawunsa kuɗi ne ita da kaninta Sadiq, to bai ma san me ake nufi da mata ba, ba ilimi, matar ma wadda ta haifawa kawun nasa ƴaƴa har guda biyu, ai ta wuce wasa.
Allah ya gani baban Zainab yana iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya kyautata masu, daga Haidar ɗin har sauran ƴan uwansa, shi yake ciyar da Mamansu Haidar ɗin, dan mijinta dai sai a hankali, bashi da ko sisi ba aikin yi, hakan tasa baban Zainab ɗin yake ɗawainiya dasu, amma duk basu gani, sai suce Maman Zainab tana hana shi ya taimaka masu, ta kanainaiye komai ita da ƴan uwanta.
A kasuwa duk wani harkar kuɗi da lissafi da Sadiq baban Zainab yake yi, dan Haidar kam kan fanko ce, bai san komai ba, hakan ne ma yasa ƴan uwan baban Zainab ɗin suka dage a kan lallai maman Zainab asiri ta yi wa ɗan uwansu, wai tun da harta harkar kuɗi a kasuwa da Sadiq kaninta ake yi, Haidar ya zama bare saniyar ware ɗan kallo, ita dai maman Zainab sai dai ta toshe kunne kawai baiwar Allah, shi ma Sadiq ɗin yanzu dan dolensa ya ko yi toshe kunnensa, baya kula kowa, idan maman Haidar ta isko shi a kasuwa, zagi da cin mutuncin kala kala take yi mashi, idan ta gama sai ya ce Allah ya bata hakuri kawai, dan bai san me zai cigaba da ce mata ba kuma.
Wannan shi ne kaɗan daga cikin tarihin Sadiq da Haidar, to mu je dai zuwa.
"Baba ya ka yi shiru?". Cewar Khadijah.
Doguwar numfashi ya ja tare da saukewa a hankali. "Babu komai mamana, muje parlourn ki ci abinci ko?".
Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar to suje. Miƙewa ya yi tare da riƙo hannunta ya sauketa kasa, sannan suka nufi parlourn.
A yadda suka bar Zainab da Maman Zainab haka suka dawo suka samesu, kasancewar baban nasu yana nan ne yasa Haidar ya ce.
"Khadijah uwar rigima, daga cewa ba'a sami inabin ba har kin fara kuka". Cewar Haidar sarkin eyes service.
Wata uwar harara ta wurga mashi ba tare da ta amsa mashi ba, yanzu haushin kowa take ji, har maman nata da ta bawa Aunty Hauwa wannan inabin, ita ma duk haushinta take ji.
A baki baban nasu ya rinƙa bata abinci yana rarrashinta, yau an yi sa'a ƴan mutunci suna gaba goshi, dan haka sai ta hakura ta ci abincin, ba musu.
Bayan sun kammala ne suka zauna yin kallo kaɗan, ita kuma Maman Zainab ta hau tattare kayan abinci. A cikin wannan daren ta yi wanke wankenta, ita bata barin kayan abincin da aka yi anfani da su da daddare su kai wayewan garin gobe, a daren take wanke su tsab, haka kayan wanki, waɗan da aka cire a ranar bata taɓa bari ya kai gobe ma bare har ya taru mata sosai, a ranar take wanke su abinta, so haka ta wanke kayan abincin nan fes tare da dawowa ta sake yin mopping na parlourn sosai, sannan ta kunna buner ta zuba turaren wuta mai daɗin kamshi kafin ta haye saman sofa kusa da baban nasu ta zauna.
Wani American film suke kallah a MBC, sun nutsu tsit kamar babu kowa, ita kuma Khadijah kaf hankalinta baya a kan Tv, sai tunanin islamiya take yi, dan an kara masu karatu yau, kuma da daddare ne kawai take samun damar yin karatun, da safe zasu tafi makarantar boko, ba zasu dawo ba sai karfe uku, idan suka dawo kafin su ci abinci su yi wanka haɗe da shirin islamiyar, karfe huɗu ta yi, dole islamiyar zasu wuce a dai'dai wannan lokacin, so babu time, yanzu haka Khadijah tana primary 2 a makarantar boko, ita kuma Zainab primary one zata shiga yanzu, suna da ƙoƙari sosai, saboda kula da suke samu daga wajen iyayensu, babansu ba wai ɗan kasuwa bane kawai, degree gare shi a fannin electric engr, kuma ya fito ne da first class, kawai yanayin kasar ce tasa ya zama ɗan kasuwa mai sayar da atamfofi, lace, shadda, da dai sauransu, babu aikin yi, ya gama karatu bai sami aiki ba, shi ne ya zaɓi ya fara kasuwancinsa kawai, ya tattara result na makarantar ya ajiye a gefe guda.
Mammansu kuwa ta gama secondary school nata, tana da ilimi dai'dai gwargwado, sannan macece mai ilimin addini, ga saukin kai da tausayi tare da fawwalawa Allah komai nata, so a takaice dukkansu daga maman har baban duk ba jahilai bane ba, suna da ilimi, shi ne yasa suke kula da karatun su Khadijah sosai da sosai.
Sai misalin ƙarfe 9:30 su Khadijah suka miƙe suna yi wa iyayen nasu sai da safe, dama already sun rigada sun sani, karfe 9:30 suke shiga su kwanta, saboda tashi zuwa makaranta, tun suna yara mamansu ta tsara masu tsari mai kyau na rayuwa, wani abin ba sai ance su yi ba, sun riga da sun saba yi.
"Mamana kada ku manta ku yi addu'ar kwanciya, nima zanzo in yi maku nawa idan zamu shiga". Cewar babansu.
Da to suka amsa mashi tare da wucewa cikin ɗakin nasu. Wata riga da wando mai laushi sosai Khadija ta ɗauko masu daga cikin drawer saka kayansu, iri ɗaya ne kayan launin navy blue.
Miƙawa Zainab nata ta yi, karɓa ta yi suka hau canza kayan ba ɓata lokaci, kayan barcinsu ne.
Bayan sun canza Zainab ta haye saman gado, ita kuma Khadijah ta ɗauko takardun islamiyarsu tare da ɗauko littafinta na Nahhu ta buɗe shafin filul mahdi dan ta kara duba karin karatun da aka yi masu.
Ta ɗauki a kallah minti goma tana ta karanta wannan filul mahdi'n kafin ta rufe takardar ta mayar cikin jaka, sannan ta mayar da jakar mazauninta, a lokacin har Zainab ta fara zuba barcinta abinta.
Zama ta yi a tsakiyar gadon ta fara karanta kulhuwallahu kafa uku, falaki da nasi suma kafa uku uku, sai ayatul kursiyu kafa ɗaya, sannan amanar rasulu shi ma kafa ɗaya, ta tofa a hannunta kafin ta shafa a jikinta gabaɗaya, ta juya ta shafawa Zainab ma, kamar wata babban mace, bayan ta shafa mata ne ta jawo masu bargo, dan garin akwai sanyi sosai, gari ne na damina, Khadijah tana tsananin son Zainab over to over wlh, ita kaɗai ce ke gareta.
Su kuma iyayen nasu, sai da suka kai har karfe 11 suna kallo, sai da suka ƙarisa kallon wannan film ɗin, shi ma Haidar saboda tsabar gulma yaki wucewa ɗakinsu, yana nan a tare suka ƙarisa kallon, sannan ya miƙe ya nufi ɗakin nasu yana yi masu sai da safe.
Mamance kawai ta amsa, baba bai amsa ba, dan shi har ga Allah baya son wannan hali na Haidar, kawai ba yadda zai yi ne, ya yi iyaka bakin ƙoƙarinsa a kan yaron nan ya canza hali, ya koma makaranta lokaci bata kure mashi ba, amma sam yaki yarda, ya zauna sai shirmen banza da wofi yake yi, yana mayar da kansa irin local matan nan masu shegen tsugudidi. Ga shi babu halin baban Zainab ɗin ya kore shi daga gidan, dama yaya lafiyar kura bare ace ta yi zawo? Yanzu ma ana cewa maman Zainab ta yi mashi asiri ta mallake shi, to ina ga kuma idan ya kori Haidar? Ai shikenan abu ya sake kwaɓewa, sai aje ayi ɓatattciya da dangi, zaman lafiyarsa kawai ya cigaba da bin Haidar ɗin da idanu har lokacin da zai girma hankalin manyantaka ta shigesa, wata kila a lokacin zai iya gane dai'dai da ba dai'dai ba.
Miƙewa baban Zainab ya yi ya je ya rufo masu kofar parlourn bayan tafiyar Haidar ɗin kenan, dama already ya rufe masu kofar gida kam tun tuni, suna dawowa daga sallar issha suke garƙame kofar gidansu, saboda tsaro, akwai gurɓatattun matasa ɓata gari a unguwar tasu sosai, shi ne yasa basu wasa da rufe kofar gida.
Kowannensu ɗakinsa daban, baban nasa daban, ita ma Maman nata daban, amma dayawa lokuta a ɗaki ɗaya suke kwana, inma na maman or na baban, a dai ɗaki ɗaya suke kwana, yau ma ɗakin baban suka wuce a tare bayan sun kashe kayan kallon nasu tare da wutar parlourn haɗe da tattare komai nasu, suka shiga wajensu Zainab suka yi masu addu'a, sannan ne suka nufi ɗakin barcinsu. A suba ta gari............
♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥♥︎♥︎♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥
🏞️Forest🏞️
Tun da Kamran ya yi wannn barci bai farka ba har washegari da safe, abin abin ban mamaki mai rikitarwa, ko da ya farka kuma ya jima sosai idanuwansa biyu ya kasa motsawa, jikinsa duk wani irin azabbabben ciwo yake yi mashi, duk ya ji wani irin tamkar ba shi ba, kamar wanda ya sha kayan maye overdose suka sanya shi barci, jin jikinsa yake yi tamkar ba shi ba, kamar an canza shi, da kyar ya iya samun dama ma ya waro idanuwansa waje, wani irin nauyi idanun nasa suka yi mashi, da farko ma ji ya yi tamkar an manne mashi su da super glue, sai da ya yi da gaske ne ya iya buɗesu.
A hankali hankali ya fara kallon wani irin jiri jiri tana ɗebarsa daga kwance, saman ɗakin nasa ne ya fara juya mashi kamar fanka.
To me ya sami Kamran ɗin mu?.
Dishi dishi idanuwansa suka fara ganin masa, like idan mutun yana ƙoƙarin sumewa, haka zai fara gani dishi dishi, yunƙurin miƙewa ya fara yi domin ya lura abin tana so ta fi karfinsa, sai dai ina, bai iya ko motsin kirki ba, tamkar an sanya igiya ne aka ɗaure shi ɗaurin goro, ƙoƙarin buɗe bakinsa ya yi domin ya kira Mamma, nan ma ina ya kasa, dan kuwa ji ya yi tamkar an ɗaure harshen nasa ne kam, ya kasa.
Sanya dukka ilahirin karfinsa ya yi da nufin ya miƙe da karfin gaske, duk da haka a banza man kare, ko motsawa bai iya yi ba, ya juyar da idanuwansa ya kalli gefe guda ma ya kasa, iya saman ɗakin nasa kawai yake iya kallah, duk wata jijiya a jikinsa sai da ta tsaya sak da aiki! Jinin jikinsa duk ya dai'na gudu, nan take idanuwansa suka kara firfitowa waje sosai tamkar zasu faɗi ƙasa, tamkar wadda aka matse sosai, sai ƙoƙarin ya yi magana yake yi, yana son ya kira Mamma ta kawo mashi agaji, amma ina ya kasa, harshensa ma a ɗaure take gam.
Dai'dai lokacin Mammar ta faɗo cikin ɗakin tana faɗin.
"Tun jiya barci yaki karewa kamar ba lafiya ba, maza ka tashi lokacin motsa jiki ya yi, ka kama ka tafi yawonka ba dole ka gaji ka yi ta barci ba, kafa baya zama waje ɗaya, baka bawa jikinka hakkinsa na hutawa!".
Jin motsin shigowar Mamma tana waɗan nan surutan ne yasa gabaɗaya ya ji jikin nasa ta sake, nan take ya ji ya koma normal kamar ba shi ba, abin da ɗaure kai da kuma mamaki.
Waro idanuwnsa da suke jajir saboda barci ya yi a kan Maman tasa dake tsaye a kusa da bed ɗin nasa tana faɗin ya tashi su tafi, ya zo sai wani zuba barci yake yi tun jiya da yamma, da daddare ta tashe shi har ta godewa Allah yaki ya tashi, har ruwa ta shafa mashi a fuska, amma yaki tashi, sai dai ya ɗan motsa kaɗan ya sake cigaba da barcin abinsa, da farko abin har ya fara bata tsoro, sai daga baya kuma ta kyale shi kawai ta je ta ci abincinta ta kwanta, to shi ne fa bai iya farkawa ba sai yanzu, e gaskiya kam abin da abin mamaki sosai Wlh, akwai kuma ɗaure kai!.
Kada ku manta daga cikin littafin RAWANIN ZALINCI wanda alkalamina ni PRINCESS TEEMA ya rubuta maku kuke karanta wannan daddaɗar labari mai cike da ruɗu da ɗaure kai, to yanzu muka fara, bamu ma fara kutsawa cikin labarin ba tukun nan, bamu ma yi komai ba, ku dai ku kasance dani, na tabbata In Sha Allah ba zaku taɓa yin danasanin karatan wannan littafin ba!.
Har yanzu lokacin harshensa ta yi mashi nauyi wajen magana, da kyar ya iya furta.
"Mamma ya naji kina cewa tun jiya nake barci sai yau na tashi? Kina nufin kwana ɗaya ta wuce kenan?".
"E mana Kamran, kwana ɗaya ta wuce, wai me kasha jiya ne? Ka je ka sha ƴaƴan wata itaciyar mai bugar da mutun ko? Ina ta tashinka daga barci kaki ka tashi" .
Zaro idanuwansa ya yi tare da furta what?! Da ɗan karfin, kwana ɗaya ta wuce kuma? Ya sake tambayar kansa.
Ganin haka yasa Maman ta ce. "Kamran anya are you okey kuwa? Menene kuma ya faru?".
Ɗago dara daran idanuwan nan nasa ya yi a in da ya sauke su a saman fuskarta, shiru ya ɗan yi kafin ya ce.
"Mamma yau ba zan motsa jiki ba, ina zuwa, bari na je nan baya yanzun nan na dawo, sai na zo na yi wanka......."
Wani irin kallo da ta wurga mashi da waɗan nan sexy eyes ɗin nata ne yasa bai san lokacin da ya haɗiye sauran maganar tasa bai ƙarisar ba.
"Wuce muje ka fara aikin motsa jiki, idan ka gama ka yi wanka ka ci abinci sai ka tafi in da zaka je, dama zaka je kawo mana nama ai, babu abin da zai hanaka yin training, wai shin ni ina ma ka je jiya da ka dawo mun kamar a buge ne?".
Da kyar ya iya miƙewa zaune yana turɓune fuska tare da ɓata rai. "Mamma ni ina kuma zanje da ya wuce in da muka saba ni da Rocky, wai Mamma please yau ki kyaleni da zancen motsa jikin nan mana".
Shiru ta yi mashi bata sake ce mashi ko uppan ba. Yasan fassarar shirunta, hakan yana nufin dole sai ya motsa jikin nan ko yana so ko baya so, ga kuma ciwo a yatsarsa.
Dole tasa ya miƙe jiki duk ciwo take mashi, gaɓɓansa duk suna yi mashi zafi, haka ya wuce gaba yana kara turɓu ne fuska.
Rufa mashi baya ta yi, a saman tsaunin ta bayan kogon nasu suka tsaya, ga wasu manya da kananan duwatsu a wajen, a nan suka tsaya ya fara aikin training da waɗan nan duwatsu, ita kuma Mamma ta wani tsaya kamar jarumar sadaukiyar yaki, yacce kuka san wata commender masu bawa mayaka horo, haka ta wani tsaya tana aikin kirga sau nawa ya ɗaga wata katuwar dutse.
Sai da ya ɗaga sau hamsin cif tana kirgawa, sannan ta ce ya fara press up, haka ya fara yi kamar zai yi kuka, yau duk jikinsa ciwo take yi mashi, ga shi Mamma ta zo tana kara mashi azaba a kan azaba, haka dai ba yadda ya iya, dole ne ya yi idan yana son zaman lafiya.
Da Mamma ta lura fa baya yi da sauri zai ɓata mata lokaci, sai ta koma cikin ƙogon nasu.
Tana tafiya ya yi zamansa yana tunanin maman twins, sai wani mai da numfashi yake yi da sauri da sauri, irin ya sha aiki ya ƙoshin nan.
A hanzarce ya tashi ya cigaba da yi jin alamar takun dawowar Mamma wajen, ba shiri ya ɗaura daga in da ya tsaya.
Kusa da shi ta zo ta tsugunna hannunta na rike da wata iriyar doguwar takobi na mayaƙa, sai dai takobin tana a cikin gidanta, bata fito da ita ba, da ƙotar gabaɗaya ta ɗauko. Ɗaga takobin ta yi ta fara kai mashi wajajen hannunsa, hakan yasa ya fara yi da sauri, dan idan ya bari takobin ta taɓa hannunsa zata ji mashi ciwo, dama ga ciwo a yatsar hannunsa tana yi mashi zogi, dan ma dai da diddigen tafin hannu ya dafa ƙasan ne, bai isa ya tsunsa sun taɓa kasa ba, saboda ciwon yatsar nan.
Mamma ta wata fuska idan ka gani sai kaga kamar bata son ɗan nata, amma kuma ita ce ainahin mai sonsa da gaske, yanzu duk in da ya shiga zai iya kare kansa ba sai ya jira wani ya zo ya kare shi ba, sai dai ni PRINCESS TEEMA ina ganin akwai wani dalilin da yasa Mamma ta zaɓi Kamran ya zama jarumi sosai har take bashi irin horo haka mai haɗari, hannunsa yana ciwo ma ba zata kyale shi ba, sai ta sanya shi yin wannan abin, haba mana Mamma..........💔😭
Yau sai da ya kusa saka mata kuka, sannan ne ta rabu da shi tare da kama ƴatsar tasa dan ta cire wannan bandejin nasa ta kara yi mashi dressing na wajen.
Shi dai burinsa ɗaya kawai, shi ne ta barshi ya je ya ga maman twins, ko yunwa ma baya ji, yana son ya koma ya sake ganin yaran ne, amma bai isa ya tirjewa Mamma ba, dole ya bita a yadda take so dan kada ta yi zargin yana aikata wani abin a ɓoye, dan haka sai ya hakura ta sake yi mashi dressing na wajen ciwon nasa, ta gasa wajen sosai da ruwan ɗumi, sannan ta ce ya je ya yi wanka ya zo su yi breakfast.
Ba musu ya je ya aiwatar da duk abin da ta ce cikin zafin nama, dan ya yi sauri ya gama ya laƙa mum twins.
Zama suka yi suka ci abincinsu kamar yadda suka saba, sannan Mamma ta ce mashi ya je gonarsu ya kawo masu masara ɗanya, ya duba ƙosassu ya ciro, sai ya haɗo masu da nama, daga karshe ta yi mashi kashedi a kan ya kula da yatsar nan tasa sosai, dan yatsar kamar tana son samun matsala.
Okey kawai ya amsa mata da shi kafin ya miƙe ya koma cikin ɗakinsa, kwari da bakarsa masu lafiya ya ɗauko domin farautar nama, sai wata ƴar wuka mai kaifin gaske da ya ɗauka dan tsaro, a kugunsa ya sanya ƴar wukar, ita kuma kwari da bakar ya ratayota a bayansa, sannan ya sanya takalmarsa mai kama da waterproof shoe, a hanzarce yake yin komai, duk dan ya yi sauri ya fita.
A wajen madafa ya isko Mamma, kwandon da suke ciro tomatoes a ciki ya ɗauka dan zubo mata masarar da ta ce ya ciro masu a gonarsu, sannan ya ɗauki wata karamar kwando ma wanda zai zubo masu fruits, dukka kwandunar da itace aka saƙasu, sai dai sun saƙu da kyau.
Sallama ya yi wa Mamma tare da nufo kofar fita. Sosai ta sake yi mashi kashedi a kan kada ya yi wasa da hannun nan nasa fa, ya kula sosai.
Okey ya amsa mata da shi tare da ficewa, yau ya fito sak maharbi. Wajen wata bishiyar lemu ya tsaya ya fara ciro lemun da suka nuna, yana cirowa cikin nutsuwa. Ɗan dai'dai ya ciro kafin ya je wajen bishiyar gwaiva, ita ma ba dayawa ya cire ba, sai mangoro da ita ma bata fi biyar ya tsinko ba, dukka nunannu yake bi yana cirowa, haka ya tara fruits ɗin dayawa, sannan ya nufi hanyar wajen mum twins dan ya je ya kai mata fruits ɗin, ita ya cirowa wannan, na Mammansa sai yana dawowa zai ciro mata, yaron kirki...........😅
Tafiya yake yi cike da jarumta, yana wani bubbuɗe kirji kamar wani mayunwacin zaki, ko alamar tsoron wannan daji babu a idanunsa, tsuntsaye sai shawagi suke yi abinsu, shi ma sai tafiya yake yi abinsa.
Wani irin mahaukacin birki ya ja lokacin da ya isa wajen da mum twins ɗin take, sam bai san lokacin da ya saki kwandon fruits na hannunsa ta faɗi ƙasa ta tarwatse ba, fruits ɗin duk suka watse a wajen.
Wani irin kara zaro idanuwansa waje ya yi, nan take fuskarsa ta bayyanar da alamar zallar madarar mamaki, cikin hanzari da zafin nama ya kara matsowa wajen dan ya tabbatar da gaske ne abin da yake gani.
Tabbas gaskiya ce, babu mum twins kuma babu twins, ɗakin bukkar da aka yi masu ma duk an kakkarya shi, an karya itatuwar gabaɗaya, tamkar waɗan da suka yi faɗa da Damusa ko kuma Damusa ya faraucesu, duk komai a kakkarye, ga kwaryar magangunanta a wajen duk a farfashe, an fasasu, ga kuma towel ɗin da aka rufe baby's ɗin duk suna nan, babu abin da aka ɗauka a wajen face baby's ɗin da Mamansu.
Tamkar a mafarki haka Kamran yake ganin wannan al'amari, tambayar kansa yake yi to ko Damusa ce ta shigo wannan yankin ta cinyesu? Kasancewar shi bai san da cewa biyo maman nasu aka yi daga masarauta za'a kwacewa mata baby's ba, sai bai yi tunanin ko mutanen masarautar tasu ne suka zo suka ɗauketa ba, shi dai tunaninsa wata dabbace a cikin wannan daji ta hallakasu ta kuma ɗaukesu suka tafi cikin dabbobi ƴan uwanta suka cinyesu.
To waye ya ɗauki mum twins? Shin da gaske wata dabbace ta cinyesu ko kuma dai waɗan nan warriors na masarautar tasu ne suka dawo suka ɗauketa? Allah mai iko, Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana❤️
Wani irin bakin ɓacin rai ne ya bayyana a saman fuskar Kamran, tamkar ya saba da su, tamkar ƴan uwansa haka yake jin mum twins ɗin nan, kawai daga jiya da la'asar zuwa yau ace bata nan? Ina take?. Idanuwansa ne suka kaɗa suka yi ja sosai saboda tsananin ɓacin rai, har wani huci ya fara fitarwa. Cikin matsananciyar damuwa ya fara kewaye wajen yana nemansu, a cewarsa idan ma damusa ce ta faraucesu zai ga ragowar kasusuwansu, shi ne ya bazama ya fara nema, duk wasu lunguna da saƙuna, bayan bishiyoyi da bayan duwatsun, ƙoguna da ramukan itace dake arear wajen, ko'ina shiga yake yi yana leƙawa, nemansu a haukace kawai yake yi, duk yana kiɗi me, baya damuwa da in da yake shiga, ba ya damuwa ko akwai maciji ko wata muguwar dabba da zata cutar da shi, shi dai kutsa kai a ko'ina kawai yake yi yana nemansu, har cikin ramuƙan dake arear wajen irin ramin da ta faɗa ciki ta haifi twins ɗin, har ciki duk sai da ya bi ya rinƙa leƙawa, amma ko alamarsu babu a wannan arear, tamkar ma ba'a taɓa yin wasu halittu irinsu a wajen ba.
To fa babbar magana, tashin hankali da ba'a saka mashi rana, my people ina mum twins?.
*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, ***.*
🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍