FreeArewaPen original
RAWANIN ZALINCI (BOOK1)
- 1views
- 28chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
THE WRITER OF DUK KARFIN IZZATA💪 TRIPLETS👊🔥 RAWANIN ZALINCI 🔥(CROWN OF INJUSTICE 🔥) THEN NOW ZAKUNA BIYAR (FIVE LIONS)
Sample · 1&2
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥🔥💔𝑨 𝒕𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝒉𝒆𝒂𝒓𝒕𝒔 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒔𝒕𝒐𝒓𝒚, 𝒅𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚 𝒐𝒃𝒔𝒕𝒂𝒄𝒍𝒆, 𝒂𝒏𝒅 𝒓𝒐𝒎𝒂𝒏𝒄𝒆💔🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥 (❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻*Gargaɗi! Gargaɗi!! Gargaɗi!!! Ban yardaba! ban Amince ba! ban lamunceba! A juya mun labarin LITTAFINA tako wacce sigar, bana so, ban bada damaba, idan kana buƙata akwai numberta a jiki ki\ka nemi izinina, ban yarda a karanta mun shi a youTube ba, ko a haɗa mun Document, a kiyaye domin zama lafiya yafi zama ɗan sarki! In kunne yaji gaggan jiki ya tsira. Wannan littafin RAWANIN ZALINCI haƙin mallakarsa nawane FATEEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA)!.**Ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani ikon fara wannan littafi lafiya, Allah ya bani ikon kamala shi lafiya.**BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM. mun fara da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai, da shi muka dogara kuma a gare shi kawai muke neman taimako.🥰 Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Rahma ɗan gata a wajen Allah, kuma fiyayyen halitta wato Annabi MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA🤍* ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 28/6/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥❤️𝑬𝑷𝑰𝑺𝑶𝑫𝑬__________1🔥Iska mai matukar ƙarfin gaske ne yake kaɗa dogayen bishiyoyin dake a kewaye da wannan ƙungurmin dajin! Tamkar za'ayi ruwan sama, garin ya haɗe ya yi duhu bakin kirin da hadari, sararin samaniya ya bada wasu launuka, ja, sky blue, navy blue, da kuma dark ash masu matuƙar ɗaukar hankalin, saboda hadirin!. Daga gabas ta tsakiya wani tapkeken bakar gizo ne wato Rainbow ya fito a sararin samaniyar.Sannu a hankali walkiya ya fara wanzuwa a sararin samaniyar, haka zalika tsawa ta fara bayyana, alama ce ta ruwan saman ya gabato.Iskar kara tsananta take yi sosai, while shima hadarin kara baki yake yi sosai, yana mamaye ko'ina a faɗin garin, gabaɗaya korayen ganyayyaki da dogayen ciyayin dake cike a wajen, sai wani irin kaɗawa suke yi har suna kwanciya, tamkar za su tsigo daga jikin tushensu, da alama dai wannan ruwa ne mai karfin gaske yake zuwa, da iska da tsawa!. Daji ne mai cike da yalwar itatuwa, dogaye, manya manya masu kauri, akwai yalwar ƴaƴan itatuwa kala kala sosai a cike a cikinta, akwai ƴelwar abubuwa masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, irinsu koramai dake zubar da ruwa mai ban sha'awa, duwatsu manya manya masu ɗaukar hankali, koguna wato kogon dutse manya da kanana, tsaunika masu tsawo, rafuna masu cike tab da ruwa mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, a saman mafiya yawan tsaunikan dake a cikin wannan dajin da akwai jiga jigan kogunan duwatsu a wajen, ga kuma bishiyoyi masu ɗaukar hankali, da dai sauransu.Sai dai da alama akwai haɗari matuƙa a cikin wannan daji, do...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.