RAWANIN ZALINCI (BOOK1)

37&38

by @queenofsurprise1

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥

(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 14/8/2024.....✍️📚🌹

For information *** Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________35🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼

🏞️FOREST🏞️

A zaune suke wajen ƙoramar nan, Kamran yana zaune a saman dutse mai ɗan faɗi ita kuma Pretty tana tsaye a bayansa tana ta famar yamutsa mashi kyakkywar gashin kansa, sai busa mai daɗi yake yi masu da abin busarsa. Sweetie kuma tana cikin raminsu tana barci, bata fito ba yau, ta ce zata kwanta ta huta.

Kayan sakar da ya kawo masu Pretty ta sanya a jikinta, ta yi matuƙar kyau over, sai ta zama kamar wata ƴar tsana a cikin kayan, ta kara zama ƴar karama da ita, kamar dai kullum kyakkywar dark black curly hairnta a ɗaure kashi biyu, ta saki jelar gashin har bayanta, sket ɗin kayan ya tsaya mata a iya gwiwarta.

Sai watsa mashi gashin kansa take yi kamar an aiketa, wai zata ɗaure mashi irin yadda mum ɗinsu take ɗaure masu nasu, haka take ɗaurewa Sweetie ma nata, to shi ne wai shi ma zata ɗaura mashi nasa. Ta yi mamakin ganin yadda gashin nasa yake da yawa bakin kirin da shi, ya yi baki sosai kamar tata.

Sai fama take yi, gashin ya fi karfin ƴan hannayenta, shi kuwa sai busa yake yi masu. Da kyar ta iya samu ta raba gashin nasa gida biyu, kitsa mashi ɗayan ta fara yi, sam bai san me take ta faman yi mashi ba, shi dai har cikin ransa yana jin matuƙar daɗin wasa da gashin nasa da yake yi, dan a tunaninsa wasa da shi take yi, so hakan daɗi yake yi masa.

Ita kuwa kitsa mashi su ta yi kamar yadda mummynta ta koya masu, sannan ta nannaɗe jelar gashin nasa ta cusa mashi a ƙarƙashin kitson kafin ta mayar mashi da hularsa ta rufe mashi kan nasa.

A ta gabansa ta dawo ta zauna tare da kwantowa a jikinsa ta kai hannu ta karɓi abin busar. "Kawo bari na busa mana". Ta faɗa cikin sanyin murya.

Ba musu ya miƙa mata, dan shi ma yana jin daɗin busar tata sosai. Hannayensa dukka biyu ya ɗaura a saman shoulders ɗinta a in da ya zuro da su ta gaba ya kara jawota jikinsa yana faɗin. "Rocky fa yana nan zuwa?".

Kai abin busar ɗan bakinta ta yi tana girgiza kai, kafin ta fara busar ta ce. "Yazo nan sai na mare shi, gara mashi tun wuri yasan in da dare ta yi mashi". Cikin tsiwa ta yi maganar, dan fa ita bata kaunar Rocky, sam jininsu bai haɗu ba, har yau har gobe razana take yi idan ta ganshi.

Ɗan murmushi kaɗan ya ɗan yi wadda ba za'a iya kiranta da murmushi bama, dan sam bata fito ba, sannan ya sauke hannunsa ɗaya daga saman shoulder ɗin tata izuwa saman ɗan shafaffen cikinta. "Rocky fa baya da faɗa, kece nan kike sawa yake baki tsoro".

"Ko baya da faɗa bana sonsa, kuma ba zan taɓa sonsa ba". Tana kai karshen maganar ta fara busarta cikin kwarewa, a yanzu ta iya busar sosai da sosai, ga shi kala daban daban ta iya rera busar, har wani lumshe idanu suke yi daga ita har shi idan tana busa masu. Akwaita da ƙwaƙwalwa, cikin ƙanƙanin lokaci take iya koyan abu ta haddace, akwai su da baiwa twin's ɗin nan sosai.

Yanzu ma tsabar daɗin busar yasa suka lumshe idanu su dukkansu, ta kara lafewa a jikinsa tana mai cigaba da busawa.

Wajen ya yi shiru tsit, sai karar sautin zubar ruwa da kuma kukan tsuntsayen dake shawagi a wajen zaka ji, a hankali hankali sautin busar tata yake tashi a arear wajen, hakan ba ƙaramin daɗi da ƙawa ya yi ba, a yanzu akwai wata busa da suke yi wa junansu, wanda Kamran ɗin shi ne ya koya masu, idan suka cutsa cikin daji yawo, da wannan busar suke kiran juna, wani lokaci idan suka je yawon nasu Kamran da Sweetie suna zama a ƙarƙashin bishiya suna hira, ita kuma Pretty yawo take tafiya abinta, so idan Kamran zai nemota sai ya ciro abin busarsa ya fara busawa, idan tana kusa da shi zata mayar mashi da martanin irin wannan busar da tata abin, shi kuma zai bi sautin karar busar tata har zuwa in da take.

Idan kuma ta ji shiru bata mayar mashi da martani ba to ta ɗan yi nisan zango, sai ya kara gaba har sai ya samota.

Wani kyakkyawan parrot ne ya sauka a kusa da Pretty da ta lumshe idanu tana aikin busa mai kwantar da hankalin mai sauraro.

Cikin dabara Kamran ya shammaceta tare da shammatar parrot ɗin ya damko shi. Tana jin alamar hakan ta yi maza ta waro idanunta waje tare kuma da dakatawa daga busar tata.

Aikuwa tana yin ido biyu da wannan parrot ɗin ta fara yunƙurin miƙewa a guje dan ta bar wajen, dama Kamran yasan za'ayi hakan, shiyasa ya shammaceta ya kama parrot ɗin, yasan idan ta ji saukar shi a kusa da ita haukace mashi zata yi, kaɗan daga aikinta kenan sarkin tsoro.

A hanzarce ya riƙota yana faɗin. "Zauna ki ji".

Bata ankaraba sai ji suka yi parrot ɗin ya maimaita abin da Kamran ɗin ya faɗa na zauna ki ji, sai dai maganar akun bata fita sosai. Hakan na nufin akun mai magana ce, kun san akwai waɗan da basa magana, to shi wannan yana yi, sai dai maganar bata fita.

Wani irin zaro idanu waje Pretty ta yi na jin yadda wannan Parrot ɗin ya maimaita maganar Kamran, waɗan nan olive eyes ɗin nata kamar zasu faɗo kasa saboda zarosu da ta yi, cike tab da mamaki ta ce. "Kamran magana fa na ji ya yi......"

Ai bata kammala rufe ɗan bakin nan nata ba Parrot ɗin ya maimaita abin da ta faɗa na cewa Kamran magana fa na ji ya yi, still dai maganar bata fita sosai, amma ana iya gane me ya ce.

"Na shiga ukuna, Kamran dama tsuntsaye suna magana ne?...."

"Na shiga ukuna, Kamran dama tsuntsaye suna magana ne?......" Parrot ɗin ya maimaita abin da ta faɗa.

Ina ai a dubu ɗari ta yunƙura zata tashi, dan ita bata taɓa ji ko gani ba, ta dai san dabbobi basa magana. Kamran dai sai kallonta yake yi, dama da gangan ya kama parrot ɗin, dan kawai ta sanya shi yin nishaɗi, yana jin matuƙar nishaɗi idan yana kallon wannan kyakkyawar face ɗin tata cikin tsoro, idan ta tsorata ba ƙaramin kyau take karawa ba, sai ma ta zaro idanun nan nata, sai ka ji kamar ka yi ta kallonta kada ka gaji, hakan yasa wani lokaci har Allah Allah yake yi ta tsorata ya kalleta da kyau yana nishaɗi.

Kara janyota jikinsa ya yi tare da matso mata da parrot ɗin kusa da ita, ƙasa ƙasa ya fara yi mata magana bayan ya ɗan sunkuyo da kansa a dab da kyakkyawan razanannen face ɗin tata.

"Tsuntsaye basa magana Pretty, amma shi parrot yana magana sosai ma, kada ki ji tsoro babu abin da zai yi maki". Yana maganar yana kallon face ɗinta.

Ai kuwa yana rufe ɗan bakinsa Parrot ɗin ya maimaita abin da ya faɗa mata shi ma.

Sanya idanunta cikin nasa ta yi da kyau. Calmly ta ce. "Kenan ba aljani bane?". Yadda ta yi maganar a kusa da shi sosai hakan yasa sai da ya ji wani iri, ga shi kuma ta yi maganar tana zaro mashi waɗan nan dara daran idanun nata masu rikitar da shi, sannan tana magana kyakkyawan lips ɗinta yana ɗan kerma, dan already ta rigada ta razana tun farko.

Kafeta da idanu ya yi ya kasa iya bata amsa, shi kaɗan yasan a wani hali yake shiga a duk lokacin da zata yi magana kusa da kusa da shi har haka, bare ace maganar ta haɗu da tana cikin firgici ta yi sa tana zaro idanun nan, ai abin ba'a magana.

"Kuma ba zai cinyeni ba Kamran?". Ta sake jefa mashi tambaya tana mai cigaba da zaro idanun nata alamar mamaki abin ya bata.

Sam bai san lokacin da ya saki parrot ɗin nan ya tashi sama abinsa ba, ya luluƙa duniyar sama jannati na kallon ƴar diramarsa.

Ganin ya saki tsuntsun ne yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da ƙara shigewa jikinsa tana hamdala ga Allah daya sanya Parrot ɗin bai cinyeta ba. Sam bata lura da duniyar tunani da kuma kallonta da Kamran ɗin ya afka ba. Ita dai da ta ga ya saki parrot ɗin ya tashi sama sai ta juya ta cigaba da busar da take yi. Wannan shi ne yana yi bata san yana yi ba, ita dai babu ruwanta da wani abu wai soyayya, yo Allah na tuba dama nawa take? Ga rashin nutsuwa a tattare da ita, ita kanta Sweetie nutsatsiyar ma yaushe ta san menene soyayya bare wata Pretty, ai ita Pretty bata da wata damuwa a rayuwarta da ya wuce ta ci abinci, ta yi wanka ta kuma yi sallah, dan suna yin sallah a kan lokaci kam, kuma da rana suke auna lokaci, wani lokaci kuma da yanayin garin suke auna lokaci kamar yadda mum ɗinsu ta koya masu, bayan sallah kuma shikenan sai Kamran ya kaita yawo, iya abin da ta sani a duniyarta kenan ƴar albarka.

Sweetie ita ce mai zama ta yi tunani a kan gobensu da kuma makomarsu, wani lokaci har tana gayawa Kamran cewa tana ji a jikinta tabbas wannan dajin ba iya shi kaɗai bane a duniya, akwai wani waje, sannan shi ma wajen tana ganin kamar mutane suna rayuwa a ciki. Tun Kamran baya wani ɗaukar maganganunta da mahimmanci har abin ta fara shiga zuciyarsa shi ma, hakan yasa shi ma ya fara tunanin ƙure wannan dajin a wajen tafiya ko zai iya ganin makamancin abin da Sweetien take hangowa na wasu mutane da suke rayuwa a duniya........ Tirƙashi, lallai Sweetie tana son ɓallowa Mamma ruwa, dan kuwa idan ya fita wannan dajin dai kunsan zai haɗu da mutane, idan kuma ya haɗu da mutane ku da kanku readers kun san labarin dole ya canza salo, dan kuwa ba karamar dirama zasu buga shi da Mamma ba, idan ma ya dawo a kan lokaci kenan, akwai fa cakwakiya idan har Kamran ya yarda da wannan hasashe na Sweetie, zai iya cewa ma Mamma munafurtarsa take yi ta ki gaya mashi bayan wannan dajin akwai wata rayuwa ta daban, kuma ina da tabbacin zai ce ba zai cigaba da zama a wannan daji ba, dan kowa dai baya son wahala sai dole, bare shi da yake bai yi kalar ƴan kauye masu duhun kai ba, da wayonsa da kuma iliminsa dai'dai gwargwado, kunga kuwa ai dole zai so canjin rayuwa, akwai cakwakiya, Sweetie ta zo da wata al'amari mai girman gaske wanda zai iya tarwatsa zuciyar Mamma, domin kuwa da ni da ku dukka mun san Mamma bata da kowa a duniya sama da Kamran, tana kaunarsa fiye da yadda take son kanta, kuna dai ganin yadda take kula da shi, ko nan da can bata son taga ya matsa, ace rana tsaka ya fita cikin wannan dajin, sannan ya dawo ya ce mata shi ba zai sake zama a nan ba wajen mutane zai tafi ya yi rayuwa? Kuna tunanin zuciyarta ba zai tarwatse ba? Hmmmm akwai case!.

"Pretty". Ya ambaci sunanta a hankali, ƙasa ƙasa kuma a ta cikin kunnuwanta.

Dakatawa da yin busar ta yi tare da juyowa gare shi. "Kamran lafiya ka kirani?". Ta yi tambayar tana riƙo hannayensa dukka biyu. Abin busar ta sanya mashi a hannunsa ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ta ɗaura shi a saman a shoulder ɗinta ta ɗan kwanto a saman kirjinsa.

"Pretty kin san menene soyayya?".

Tana daga kwance a jikinsa ta ce. "A'a ban sani ba, shima wani kalar abincin na Mammarka ko kuma fruits ne?". Ta yi maganar ba tare da ta ɗago ta kalle shi ba, tana kwance tana ganin zubar ruwar ƙorama abinta.

Ajiyar zuciya ya sauke, jiya wuni zunbur ya yi yana bincike cikin littatafan Mammarsa ba tare da sanin Mammar ba, a nan ne ya ci karo da wata littafi mai suna true love never end, da yake litattafin bata da yawa sosai, short story ne da bata wuci pepar ashirin ba, sai ya nutsu ya karanta, a nan ne ya samu abubuwa da dama har amsarsa na dan gane da aure, kasancewar a littafin ya karanta duk wahalar da jaruma da jarumin suka sha daga karshe sun yi aure sun mallaki juna, kuma sun haifi ƴaƴa, a nan ne ya fara tunanin kenan shi ma dai yana da baba? Ba iya mama bace kawai?. Ya dai samu abubuwa da dama a ciki littafin, ya kuma yi masu kyakkyawar fahimta, ya kuma tarawa kansa uban tarin tambayoyin da ƙwaƙwalwarsa take ƙoƙarin kasa ɗauka, ya kasa iya tambayar Mammarsa ina babansa? Ya kasa iya gaya mata labarin su Pretty, ya kuma rasa ta ina zai iya sanar da ita cewa an bashi auren Pretty, kuma da ya karanta wannan littafin ya fahimci yana son yarinyar nan Pretty, kuma zai aureta ɗin kamar yadda mum ɗinta ta bashi aurenta, duk ya kasa samun kwarin gwiwar iya sanar da mamma komai, ya shiga damuwa na wuce misali, sai saƙa da warwara yake yi na yadda zai ɓullowa da Mamma ta bashi amsoshinsa a kan waɗan nan al'amura.

Lallai akwai cakwakiya, finally ga shi dai Kamran yasan menene aure da ma ita kanta soyayyar, sannan kuma yasan cewa yanzu mace bata haihuwa ita kaɗai, har ya fara tunanin to shi ina nasa uban? Ga wani sabon cakwakiya kuma da Sweetie ta matsa mashi a kan su kurewa dajin nan tafiya ko akwai wasu mutane a wajen dajin, dan ita bata yarda da cewa suma warriors ɗin nan a cikin dajin nan suke ba. To Kamran fans ya kuke tunanin makomar Mamma idan har Kamran ya fita daga cikin wannan dajin yaga akwai mutane a wajen? Anya zai sake yarda ya zauna a dajin kuwa? Anya zai iya yin hakuri ya danne ba tare da ya buƙaci sanin ina mahaifinsa yake ba kuwa? One day one time da wuya idan bai tambayi Mamma da ta fito mashi da babansa ba, duk da yanzu yana tsoron tambayarta, amma dakamar wuya ya iya hakuri da babansa... Tashin hankali kenan, babbar magana!!. Forest ma ya kusa kamawa da wuta da alama!.

"Pretty soyayya ba abinci bane sarkin son cin abinci, kuma soyayya ba kayan fruits bane, wani abin ne na daban". Ya bata amsa ta hanyar raɗa mata a kunne.

Jin cewa ba abinci bane kuma ba kayan fruits bane soyayya yasa ta yi saurin ɗago da kanta daga saman kirjin nasa ta juyo garesa. "To menene kenan?".

Yadda ta ɗago da kan nata sai ya zama suna fuskantar juna. Tsura mata ido ya yi yana kallonta, tun da ya fahimci sonta yake yi sai ya dai'na jin wani irin yanayi tare da fargabar kallon cikin idonta, sai ya zamana ma idan bai kalli cikin idanun nata ba sam baya jin daɗi.

"Ya kake ta kallona haka Kamran? Na ce maka menene soyayyar baka bani amsa ba? Wajen yawo ne to? Ko dai wasu dabbobin ne?".

A hankali ya motsa kyawawan lips ɗinsa ya furta. "Kece soyayyar mana".

Kyafta idanunta sau biyu ta yi tare da sakar mashi wani irin cool murmushi mai kara mata matuƙar kyau, har dimples ɗinta suka lotsa. "Kai kam Kamran wani lokaci ka iya maganar banza, ni ce soyayya kuma? To ni dai sunana Pretty ba soyayya ba".

Tun daga yanayin maganar Pretty zaka fahimci duk wanda zai auri wannan yarinya yana ruwa kusa da kada, sai ya shirya shanye duk wani shirmenta har Allah ya gyara mashi ita, ko da yake yarinta ne sosai a kanta, ƴar shekara goma zuwa shaɗaya nawa take dama? Ai yarinya ce sosai.

Da yake shi Kamran ya saba da halin kayarsa, sai ya ɗan matso da face nasa dab da tata, ƙasa ƙasa kamar mai tsoron wani kada ya jisu ya ce. "Ai ban ce maki sunanki ne soyayya ba bare ki ce mun sunanki Pretty, duba idonta a wajen kamar na raƙumin dawa".

Da yake ba'a yi mata ta kyale sai da ɓallah mashi harara tare da faɗin. "Ai garani ma idon Raƙumin dawa ce da ni, kai kuma idonka kamar na wannan Rocky ɗin naka". Ta kai karshen maganar tana kara ɓallah mashi harara.

Murmushi kaɗan ya ɗan sakar mata kafin ya ce. "Na ji to, yanzu dai koma menene ki sani dai ina sonki".

Shiru ta ɗan yi, sai yanzu kalmar ina sonki ya fara dawo mata a cikin ƙwaƙwalwata, mum ɗinsu tana yawan gaya masu cewa ina sonku ƴaƴana, kune duniyata kuma kune komai nawa, ina alfarhari daku kuma ina son yin rayuwa da ku, na kasance da ku na kuma kula da ku, na baku tarbiya irin ta addinin Musulunci na kuma baku ilimin addini dana zamani, ina kaunarku fiye da yadda nake son kai'na.

Sosai maganganun mum ɗinta suka rinƙa yi mata zarya a cikin kunnuwanta zuwa ƙwaƙwalwarta, kenan yanzu shi ma Kamran irin son da yake yi mata kenan? Irin son da mum ɗinsu take yi mata?

Ganin ta luluƙa duniyar tunani ne yasa ya kai hannunsa ya ɗan shafi lallausan kumatunta haɗe da dogon kyakkyawar hancinta da ya zauna ɗas a face ɗinta.

"Kema kina sona ko?". Ya faɗa a hankali.

Kara kallon cikin kwayar idanunsa da kyau ta yi kafin ta ce. "Ni ban san menene ma'anar kalmar ina sonki ba, mum ɗinmu tana faɗa mana shi, so ni ban san me take nufi ba".

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fara yi mata bayanin menene soyayya kamar yadda ya karanta a wancan littafin, sai dai ya ɓoye mata menene aure da kuma ganowa da ya yi cewa suna da iyaye maza, dukka ya ɓoye mata wannan, saboda a ƙananun shekarun nan nata ba fahimtar komai zata yi ba, sai dai ta kara tabka mashi shirme, dan haka sai ya yi mata bayanin abin da zata gane kawai cikin sauki.

Ɗan taɓe baki ta yi a lokacin da ya gama yi mata bayanin menene soyayyar. "Dama wannan ce soyayya? To ai ina sonka nima". Ta bashi amsa tana kallon cikin idonsa.

Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗi da sakar mata cool murmushi mai matukar kyau, ya ji daɗi sosai. Tabbas kamar yadda ta faɗa tana son shi haka ne, tana son shi amma ba kamar yadda shi yake sonta ba, kunsan kowace zuciya tana son mai kyautata mata, to hakance, dole zasu so Kamran sosai, dan a yanzu shi ne komai nasu.

Cigaba da hirarsu mai shegen daɗi a tsakaninsu suka yi, yana kara fahimtar da ita yadda soyayya take, ta wani kasa kunne tana ɗaukan bayanai, ita kuwa Sweetie tana can tana barci abinta, ba ruwanta da hayaniya.

Sun jima a haka kafin nan ya ce mata zai koma gida ta tashi ya rakata wajen maɓoyarsu da yamma zai dawo su sha hira da soyayyarsu. Sam bata so tafiyarsa ba, kawai dan ba yadda zata yi ne, tana matuƙar jin daɗin kasancewa da shi, idan ya ce zai koma har ji take yi kamar ta yi kuka ko kuma ta bi bayansa su tafi a tare, amma ba hali. Haka ta miƙe tana turo baki, sai hakuri yake bata, har da goyata a bayansa ya yi izuwa wajen bakin ramin nasu, duk dan baya son ganin fushinta, duk dan ya lallaɓata ta yi farinciki kafin su rabu.

Da kyar ya iya sakata dariya kafin su rabu, sai da ta yi dariya mai sauti ma tukun nan, sannan ya ce ta shiga ciki kuma kada ta yarda ta tashi Sweetie daga barci, sannan kada ta sake fitowa waje sai ya dawo da yamma. Da okey kawai ta amsa mashi kafin ta sa kai ta wuce ciki. Shi kuma bayan ya tabbatar da ya rufesu da kyau sai ya nufi gida.

A bakin kofar shiga ƙogonsu ya ci karo da Rocky dake ta faman barci, da alama ya ci ya ƙoshi ne, wucewa ciki ya yi izuwa cikin ɗakinsa. Ga mamakinsa sai ya isko Mammarsa a cikin ɗakin nasa tana yi mashi bincike.

Bai nuna mata ya yi mamakin hakan ba, ya wuce kawai ya haye saman gadonsa yana faɗin. "Mamma sannu da hutawa ina abincina?".

Zuba mashi idanu sosai ta yi na ƴan sakanni kafin ta ce. "Kamran cire hular kankan nan bari na gani".

Da yake ya manta shap da zancen cewa Pretty ta yi mashi kitso, sai bai wani damu ba, yana kallon face ɗin mammar tasa ya cire hular.

Kun san fa idan mutun ya yi kitso koma ya take sai face ɗinsa ta ɗan canza, shi ne yasa Mamma ta iya ganewa, kuma da yake taga wannan uban tulin gashin nasa da idan ya sanya hula take cika hular duk ta ɓace, hakan yasa ta fahimci an taɓa mashi gashin, shi yasa ta ce ya cire hular ta gani, sam bata kawowa ranta cewa kitso ma aka yi mashi ba, ta dai fi tunanin cewa shi ne ya datse gashin nasa ya zubar.

Zaro idanu waje ta yi sosai tana kallon kitso guda biyun, tun da take da shi ko da sunan wasa bata taɓa yi mashi kitso ba, bata taɓa kwatanta yin kitso bama, dan ita gashin kanta baya kitsuwa saboda tsantsi, to a ina kuma ya samo kitso? Tasan dai ba shi ya yi wa kansa ba, dan bai iya ba.

Shi kuwa ganin yadda ta zaro idanun nan nata tana kallon kan nasa ne yasa ya yi saurin kai hannunsa saman gashin nasa dan ya ji menene ya sanyata zaro idanu haka?.

Ai bai san lokacin da ya miƙe tsaye a dubu ba time da ya ji kumbusa kumbusar kitson da rigimammiyarsa Pretty ta yi mashi. Yau ya shiga uku! Wani amsa zai bawa Mamma kenan? Me zai ce yau kuma? Ya mance da kitson ne da tun a hanya zai warwareta........

(Kamran fans yau ba zata yi maku ta daɗi ba😅 baku da amsar da zaku bawa Mamma, kuna tsaka mai wuya, Pretty ta kai ku ta baroku 😅 ku daɗi soyayya ba? To yau zaku ga soyayya kuwa😅)

Readers me kuke tunanin Mamma zata ce mashi? Wani action zata ɗauka? Shi ma wani action zai ɗauka dan kare kansa kada a raba shi da Pretty? Ga shi ya bayyanawa Pretty ɗin soyayyarsa, ya kenan zata kaya?. To ni dai bari na leƙa KINGDOM OF POWER na dawo, wata kila kafin nan Kamran ya samowa kansa mafita.

𝗞𝗜𝗡𝗚𝗗𝗢𝗠 𝗢𝗙 𝗣𝗢𝗪𝗘𝗥💪🔥

Haɗe gabakiɗaya family suke a saman dining table dake dining room ɗinsu na part ɗin King. Kuyanga Zubaida ta yi serving ɗinsu, cikin nutsuwa suke cin abincin nasu. Kowa yana saman table ɗin amma banda Yah Jawad, Yah Jaish and Gimbiya Chuchu dake cikin part ɗin Akka, taki fitowa, Akka ta fito daning room ta barta kwance a saman gado, wai sai anjuma kaɗan zata sha complex or coffee ko dai wani abin mara nauyi, dan bata jin yunwa a yanzu.

Obaid and Omaid duk suna a saman haɗaɗɗiyar dining table ɗin, abincinsu kawai suke ci cikin natsuwa, sai ka rantse da Allah babu su a cikin room ɗin, auta duk ta damu na rashin ganin gimbiya Chuchu a room ɗin, ita kuma Sarina sai faman hararar Aneesa take yi sarakai waɗan da basa shiri, sai mayar mata da martanin hararar Aneesa ɗin ma take yi.

Obaid and Omaid dai har yanzu suna nan suna shirya kalar azabar da za su yi wa Mama, basu janye wannan kuduri nasu ba.

King ne ya ɗan yi gyaran murya tare da fara yin magana kamar haka. "Omar dai uncle Abu Abdussalam ya ce ba zai dawo this week ba, na yi na yi amma ya ce wlh na fita idonsa na bar mashi guyson ɗinsa ya kara mashi hutun koda na one month ne kafin ya dawo ya cigaba da karatu, so mummynsa sai ki yi hakuri da shirya mashi walimar sai next month, ku kuma Obaid and Omaid sai next week zaku koma, dama saboda Omar zai dawo ne yasa na yarda zaku koma, to tunda an sake riƙe mun shi nima bari na sake riƙeku a nan kaɗan tun da ma ku baku koma school ba, ke kuma Sarina ina son ki mayar da hankalinki da kyau, kada na kara ji ko ganin wani bako ya zo wajenki, nasa a saki su Yusuf bayan Zafar ya horasu da kyau". Ya kai karshen maganar yana kallon Mommar Zunaira.

Momma ɗin dai bata ce komai ba, domin yayanta ne Abu Abdussalam ɗin, kuma shi ya hana Omar dawowa, ya zata yi da ya wuce ta yi shiru, bata da ta cewa, ita kuma mummy sai cewa ta yi. "Kai gaskiya uncle Abu Abdussalam ya yi hakuri ya bar nana Guyson ɗin mu ya dawo, muna kewarsa sosai fa".

Mama ce ta wani ɓalle masu kallon banza tare da turɓene fuska kamar wadda taga wani abin kyamar.

"Daddy please ka barni mana na je wajen su Uncle ɗin, ba sai mu dawo a tare da Yah Omar ɗin ba". Cewar auta, ta yi maganar tana turo baki.

"Wani zuwa kuma bayan an buɗe school?" King ya bata amsa.

Turo baki kawai ta yi, ta ji babu daɗi, tun kafin a buɗe makaranta take ta son zuwa, amma aka hanata.

"Bari na dubo Aunty Chuchu". Cewar autar, ta yi maganar tare da miƙewa ta nufi hanyar fita daga room ɗin. Sauri sauri ta yi ta fita dan ma kada daddyn nata ya ce ta zawo sai sun ƙarisa cin abinci, dan Akka ta gaya mashi cewa Chuchu ta ce tana ƙoshe bata jin yunwa da ya tambaya.

Kai tsaye part ɗin Akka ta nufa, dan tasan a can zata sameta, bata jin daɗi ne a duk lokacin da take waje ba tare da Chuchu ba, sun yi matukar shaƙuwa.

Ta zo wucewa ta part ɗin Yah Jaish ne Yah Jawad ya fito daga ciki, bayan ya yi sallolin da suke a kansa ne ya yi wanka ya yi shirin barci sai ya nufi part ɗin Jaish kamar yadda suka saba, a nan suka ci abincin dare suka ɗan yi hira kaɗan, kasancewar yana da aikin da zai yi sosai shi ma kuma Jaish ɗin akwai wani bincike da yake yi a kan wata ma'aikata da suke zargin tana haɗa kwayoyin cuta da kwayoyin magunguna na shan al'umma, suna watsa cutar ta wannan hanyar, a matsayinsa na babban ɗan jarida ya kuma samu information sosai a kan ma'aikatan, shi ne yake ƙoƙarin bincikarsu ya tabbatar da abin da jama'a suke zargin gaskiya ce kafin ya fitar da bayanan, wannan dalilin yasa yau suka yi sallama da juna da wuri, saboda duk suna da tulin aiki a gabansu.

Yana fitowa suka ci karo da auta. "Good evening Yah Jawad". Ta faɗa tana ƙoƙarin wucesa.

"Zunaira ina zaki je kike sauri haka? And then ban hanaku yawo da kayan barci babu hijabi haka a cikin gidan nan ba?".

Dakatawa ta yi daga tafiyar da take yi, ɗan turo baki kaɗan ta yi kafin ta ce. "Kayi hakuri ba zan sake ba, na manta ne".

Shiru ya ɗan yi mata na ƴan sakani kafin ya ce. "To ina zaki je haka?".

"Wajen Aunty Chuchu zan je, bata zo dining room bane, tana part ɗin Akka, shi ne zan je in dubota". Ta bashi amsa.

"Idan kin je ki ce ta zo ina son ganinta, ta same ni a part ɗina". Yana kai karshen maganar yasa kai ya wuce abinsa. Ita ma cikin sauri ta wuce izuwa wajen elevatorn da zai kaita part ɗin Akka.

Kwance ta isko Chuchu a saman bed, tana sanye cikin kayan barci riga da dogon wando masu kyau launin maroon color, kayan barcin yana da hula mai kyan gaske, so ta sanya hular a kanta, sai latsa wayar Akka take yi dan Yah Jawad ya kwace mata nata wayar idan baku manta ba.

Saman bed ɗin auta ta haye tare da cewa. "Aunty Chuchu shi ne baki nemeni ba ko? To Yah Jawad yana kiranki".

Zaro idanu waje Chuchu ta yi tare da miƙewa zaune. "Nashiga ukuna! Me kuma na sake aikatawa Yah Jawad da yake nemana?! Ni wlh Allah sai na kai shi kara wajen daddy in dai ya sake bani punishment, kuma sai na gayawa Akka ma, na gaji da shan wannan bakin azaba, haba wai ni kaɗai ce a gidan?". Cikin tsiwa ta yi maganar.

Kwanciya ita dai auta ta yi tare da jawo pillow ta rungume haɗe da karɓar wayar Akka dake hannun Gimbiya Chuchun, sannan ta ce. "Allah ni ban san meyasa Aunty Chuchu kike ganin laifin Yah Jawad ba, yana da saukin kai fa, kuma yana da kirki".

Duka ta kaiwa autar a baki tana faɗin. "Tun wuri ki yi istigifari, dan Yah Jawad kam sam bai bi hanyar da saukin kai ya bi ba, mugu ne na karshe, kuma wlh sai na gayawa uncle Abbas duk muguntar da ya yi mun, Allah har na fara tsanarsa sosai, amma fa kada ki gayawa kowa na ce na tsanesa fa".

Hannu auta ta kai ta toshe ɗan bakinta da shi tare da zaro idanu waje. "Yah Jawad ɗin kika tsana Aunty Chuchu? Yayan mu ne fa, innalillahi". Tana magana tana zaro idanu!.

"Ke zaki yi mun shiru ne ko dai kina gaya mun yayan mu ne? To ni dai bana son shi, mugu ne, kuma idan kika faɗawa wani ko wata nace hakan daga yau mun bata".

Girgiza kai auta ta fara yi tana faɗin. "Ba zan gayawa kowa ba, amma dan Allah Aunty Chuchu ki dai'na cewa kin tsanesa, please, wlh ni bana son jin wannan kalma".

Ƙoƙarin sauka kasa daga saman bed ɗin ta yi tana faɗin. "Zan daina faɗa, amma dai ba zan cire tsanarsa a rai'na ba, sai ya yi ta azabtar da mutane dan mugunta, Allah bari na je na amsa kiransa, idan ya bani wata punishment ɗin kamar a gaban uncle Abbas aka yi, sai na gaya mashi, kuma in gayawa Akka da daddy dukka". Tana kai karshen maganar ta sauko kasa, sai turo baki take yi ta nufi waje, haushi yasa ta manta da cewa kayan barci ne a jikinta kuma bata ɗauki hijabi ba, haka ta nufi part ɗinsa tana kunkuni a cikin ranta, sai faɗi take in dai ya ci zalinta yau to wlh sai ta kai kararsa wajen uncle Abbas, sai dai ya yi duk abin da zai yi mata mugu kawai.

Bakinta a ɗauke da sallama ta shigo part ɗin nasa. Daga jin yadda ta yi sallamar kasan a ƙule take da bakinciki har wuya.

Babu kowa a parlourn, kuyangu masu yi mashi gyara ma sun kammala aikinsu sun fice. Kai tsaye bedroom ɗinsa ta nufa. Ƙasa ƙasa ta yi sallama tare da tura kofar ta shiga ba tare da jira izininsa ba, dan ita fa haushin da take ji yasa ta manta ma a ina take tukun nan, sai kunkuni take yi tana tsine mashi a cikin ranta.

Yana zaune a saman bed ɗinsa, ya tasa laptop a gaba yana aiki a kan aikin da King ya ba wa Companynsa na gina gidan marayu, aikin yake ta fama da shi. Ta wutsiyar idanunsa ya kalleta. Wani irin bakinciki da kishi ne ya taso mashi, hakan yasa ya ɗaure fuska sosai kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa, yauma da kayan barci ta fito kenan? Ya..................

Lokacin shan Maltina ta yi🥱

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥

(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 15/8/2024.....✍️📚🌹

For information *** Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________36🔥

Yana zaune a saman bed ɗinsa, ya tasa laptop a gaba yana aiki a kan aikin da King ya ba wa Companynsa na gina gidan marayu, aikin yake ta fama da shi. Ta wutsiyar idanunsa ya kalleta. Wani irin bakinciki da kishi ne ya taso mashi, hakan yasa ya ɗaure fuska sosai kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa, yauma da kayan barci ta fito kenan? Ya tambayi kansa da kansa a cikin zuciyarsa.

Ita kuwa gabansa ta nufo, sam bata tuna komai ba. A ɗan nesa da shi kaɗan ta tsaya tare da cewa. "Yah Jawad gani nan".

Tamkar bai san da shigowarta room ɗin ba, aikin gabansa kawai ya cigaba da yi, sai dai kuma a zahirin gaskiya ya kasa yin aikin dai'dai saboda ɓacin rai, hankalinsa kuma yana kanta, tunanin kalar hukuncin da zai yi mata kawai yake yi.

Ta jima a tsaye a wajen almost 10 mins bai ko ɗaga idanu ya kalleta ba, aikinsa kawai yake yi na latsa laptop ɗin buge dan kada ta gane hankalinsa baya a kan aikin.

"Yah Jawad in ta fi ne?". Ta yi maganar kamar zata fasa kuka, saboda ta gaji da tsayuwa, ta ga bashi da niyar kulata, kuma yau ta sha alwashin wlh ba zata tsaya a cuceta ba, idan ya ce ta yi kneel down ko makamancin haka to wlh guduwa wajen Akka zata yi, sai dai ya bita can ya kakkaryata idan yana so...... Lallai Chuchu ta fara girma, abin ya fara kureta........😅

Sai da suka kara good 5 mins a haka kafin nan ya ɗan ture laptop ɗin daga gabansa izuwa gefensa, ba tare da ya ɗago ya kalli in da take ba ya ce. "Zo nan ki yi mun kneel down, domin yau sai na koya maki hankali sosai, ke kunnanki baya jin magana ko Jannat? To yau zai fara jin magana dole........"

Bai gama rufe baki ba ta watsa a guje zata nufi waje, dama ta ce wlh ba wani hukuncinsa da zata karɓa yau, yana yin yunkurin hukuntata zata gudu, aikuwa sai ga shi ta ruga a guje zata yi waje.

Wani irin miƙewa ya yi babu shiri, dan yasan idan ya barta ta gudu ya shiga tara da Akka na farko, na biyu kuma bai ga dalilin da zai sanya yana yi mata magana zata gudu ba, a cikin kannen nasu ma fa ita da auta sune kanana, amma tsabar ta rai'na shi ne yana magana zata gudu? Lallai yau dole ta ci duka, ba ma zai yiwu ya barta ta gudu ba ai, dole ya kamota ta karɓi hukuncin dama bai taɓa yi ma kowa daga cikin kannen nasu ba, ko Sarina da take sarkin rashin ji yau hukuncin da zai yi wa Chuchu bai taɓa yi wa Sarina ɗin ba, sannan ya ja mata kunne a kan idan ta gayawa Akka ko uncles Abbas sai ya karairayata........ (Ku ji mun mugunta, a dakeka a hanaka kuka, ya azabtar da ita kuma ya ce kada ta gayawa kowa🤔 Allah Yah Jawad ma mugu ne)

Bata kai ga isa kofar ɗakin ba ya damkota ta baya, duk da tasan cewa ko ta yi ihu babu wanda zai iya jinta a cikin gidan, saboda ainahin kofar shiga part ɗin nasa ma a rufe, tana shiga kofar ta rufe, ga shi izuwa yanzu tasan kowa ya rufe kofofin part ɗinsa, koda bama haka ba yanayin tsarin ginin gidan mawuyacin abu ne tana cikin wani part ta yi ihu a jita a wajen, hakan ba zai yi ba.

Amma duk da haka hakan bai hana ta waje baki zata kurma mashi ihu ba, domin ta tsarorata da kamota da ya yi, bata yi tsammanin zai yi yunƙurin bin bayanta har ma ya kamata ba, ta yi tunanin zata iya tsira ne ma yasa ta fara gudun, tasan ba komai yake kulawa ba, so a tunaninta idan ta gudu ma zai kyaleta ya ce wata kila da safe zai kamata, amma sai ta ji an damkota ta baya, shi ne abin ya razanata da har yasa ta waje baki da karfin gaske zata zunduma ihu, ga tsoron kalar hukuncin da zai yi mata, yanzu ma bata gudu ba ma ya ce ta yi kneel down bare kuma ya ce ta yi ta ki yi zata gudu? Ai ita da kanta tasan hukunci ya karu sosai!.

Ina duk da yasan ba wani jin ihun nata family zasu yi ba, amma bai bari ta yi shi ba, tana waje ɗan bakin yasa hannu ya toshe mata bakin nata, ransa ya sosu matuƙa, duk cikin sisters ɗinsu babu wanda ya taɓa yi mashi makamancin abin da ta yi mashi, bai san cewa idan ka cina takurawa mutun dama ya kansa ya rage tsoronka idan ma yana ji ba, takura mata da yake yi ne yasa ta rage jin tsoronsa da har ma take kiransa da mugu, yanzu da Yah Jaish ne ya kirata ai ko yankata yake yi ba zata tsallake abin da ya ce ba, saboda me? Saboda da ni da ku dukka mun san Yah Jaish dai ba wanda ya ishe shi kallo a cikin kannen nasa, baya kulasu kuma baya bi da kansu, kunga kuwa dole a ji shakkarsa sosai, shi ma dai Yah Jawad ɗin chuchu kawai ya sakawa ido, kuma dani da ku duk mun san dalilinsa na yin hakan.

"Stay quiet, if not a cikin daren nan zan kakkaryaki na zubar da kasusuwanki a dustbin". Ƙasa ƙasa sosai ya yi maganar, ya kuma kai karshen maganar tare da zame hannunsa daga saman ɗan bakin nata.

Wani irin kermar tsoro jikinta ya fara yi, danasanin abin da ta aikata ta fara yi, yau dai ta shiga uku ta lalace, haka take ta faɗi a cikin ranta.

Saketa ya yi tare da juyo da ita suna fuskantar juna, sannan ya kai hannunsa ya damko wannan arab hair ɗin nata, saboda hular kanta ya cire tun lokacin da ta watsa a guje zata yi waje, so sai ya zamana babu ɗankwali a kan nata, hakan ya bashi damar damko mata kyakkyawar gashinta da ta ɗaure shi kashi biyu.

Da karfi ya danki gashin nata tare da jan shi baya sosai, hakan yasa dan dole babu shiri sai da ta ɗago kanta sama, wani irin azaba ne ta ji ya ziyarceta lokaci guda.

"Kin girma ko Jannat? Har inai maki magana zaki gudu ko?".

Kai ta fara girgiza mashi ba bakin yin magana, sai wasu zafafan hawayen azaba da suka cika mata idanu, kan ka ce me sun fara wanke mata fuska, amma fa a cikin ranta faɗi take yi wlh yana sakinta sai ta sake watsawa a guje, kuma yau ba sai gobe ba sai ta gayawa uncle Abbas muguntar da yake yi masu ita da su Sarina, sannan zata gayawa Akka da daddy, wlh ba zata hakura da kudurinta na gaya masu ba, ko dan su samu sassauci a kan irin cin zalinsu da yake yi, duk sai ta ji ta kara tsanarsa sosai.

"Zaki yi mun shiru ne ko sai na ɗauko belt?". Ya yi maganar yana kai kallonsa izuwa saman bed ɗinsa, wayarsa ce take kara alamar shigowar kira.

Kara jan mata gashi baya ya yi da ƙarfi, tare da dawo da kallonsa a kanta. Ba komai ne yake kona mashi rai ba face fitowa da kayan barci da ta yi, kishi ne kawai yake cinsa a zuciya yasa yake azabtar da ita har haka. Izuwa yanzu shi da kansa ya fahimci cewa tabbas uncle Abbas gaskiya yake gaya mashi na cewa yana son Jannat, domin kuwa idan har baya sonta ba zai yi kishinta har haka ba, wannan kishi ya wuce na yaya da kanwa sai dai mata da miji, kuma ba zai rinƙa damuwa da son ya ganta har haka ba, yanzu da yasa auta ta kirata a fili idan ta zo dama wayarta zai bata, a zahirin abin da yake cikin zuciyarsa kuma ba wayar yake son bata ba, ganinta yake son yi, dan yana kewarta, shi ne gaskiya!!.

Amma kuma shi fa wai a haka so yake ya cire son nata a ransa, saboda a cewarsa ita ɗin sistersa ce kawai, kuma ta yi ƙanƙantar da zai iya cewa yana so, bugu da kari ba zai iya jawa kansa rai'ni na cewa zai aureta ba, idan ya yi haka ai yagama da kansa, ya jawa kansa rai'ni, shi ne yasa tun farko yake kaucewa yaki yarda da cewa yana sonta, dan bai son rai'ni, yanzu kuma da ya fahimci hakan yake ƙoƙarin cire son nata a ransa. Akwai cakwakiya ga Mammie ɗinsa ma kun dai ji bata kaunar wannan haɗin, uncle Abbas kuma fatansa kenan, wai ma to meyasa Mammien bata son haɗin Jawad ɗin da Chuchun? Akwai dai wata a ƙasa gaskiya.

Kasa iya yi mashi shirun ta yi, sai ma kara karfin gudu hawayen nata suka yi, sakamakon ya kara ja mata gashi kanta baya, zafi ya karu, dan haka ita ma sai ta kara kukan nata. Har cikin ransa yake jin zafin wannan kuka da take yi kamar yadda ita kuma take jin zafin jan mata gashin da yake yi. Ya yi iya kar yinsa, ya yi mata iya barazanar da zai yi mata akan ta yi shiru amma taki, bashi da zaɓin da ya wuce ya sakin mata gashi idan har yana son ta yi shiru, zuciyarsa ba zata iya jurar ganin kukan nata ba, dan haka sai ya zame hannunsa daga kan nata tare da gyara tsayuwarsa da nufin ya fara magana, ya gaya mata kalar hukuncin da zai yi mata a yau, dan ba zai barta ba.

Ai kuwa yana saketa ta sake watsawa a guje ta nufi waje. Ba shiri ya sake rufa mata baya a karo na biyu. Tana fitowa parlourn ya damkota, da hannu ɗaya ya ɗagata sama, ɗayan hannunsa kuma yasa ya toshe mata baki saboda waje bakin da ta yi zata zunduma mashi ihu.

Kai tsaye sai saman carpet dake a gaban bed ɗinsa ya sauketa, wani irin ɗaure fuska sosai ya yi kamar hadari, tamkar bai taɓa sanin me ake kira da murmushi ba. Tsawa ya daka mata a kan ta zube gwiwowinta a kasa ko kuka ya karairayata a cikin daren nan, ashe abin nata har ya kai haka? Dole ya yi mata hukunci mai zafi tun da rai'ni ya fara shiga tsakaninsu, irin wannan rai'nin yake gudu yasa yaki yarda da yana sonta yake kuma ƙoƙarin yin patali da soyayyar tata daga cikin zuciyarsa, sai ga shi tun ma bai bayyana mata yana son nata ba, tun bai bayyana wa kowa bama rainin ta fara shiga tsakaninsu, dole ya ɗauki mataki!.

Jikinta na kerma ta zube gwiwowinta a ƙasa tana mai cigaba da yin kukanta. Remote na door room ɗinsa ya ɗauka ya rufe kofar mai gabaɗaya, yau ba ita babu fita kenan, sannan ya wuce dressing room ɗinsa ya ɗauko ɗaya daga cikin belt ɗinsa mai mugun zafi yadda kuka san da gaske zai iya zaneta ɗin, ya wani ɗaure fuska irin babu wasan nan, bai san shi so ba'a kawo mashi wargi ba, ba ruwansa da shekaru ko girma, in dai ya shiga zuciya to sai ya yi pata pata da duk wasu dokoki ko matakan da mutun yasawa kansa, so ai bashi da adalci wani lokaci, sai ya kaika ga son wadda kai da kanka kasan ka kusa haifarta, dan bala'i ya barka ka yi ta fama kana ɗawainiya, to wannan irin shi ne a tsakanin Yah Jawad dan Aunty Chuchunmu fashion babynmu ƴar wanka.

Yo ko dan shegen iya ɗaukar wankarki da iya gayu, ki yi gayu ya zauna a jikinki kamar dan ke aka yi ba dole ma Yah Jawad ya sarara maki ba, dole ba zai iya jure wuni bai sanyaki a idanunsa ba, irin wannan haɗuwa da kike yi, ga zuba kamshi kamar me, duk wasu perfume na Momma ke da auta sai kun bi kun karar mata, ai dole ki sanya zuciyar bawan Allah cikin tunaninki kullum da ko yaushe, dole ya rinƙa fakewa da kwace maki waya dan ya rinƙa sami damar ganinki, shiyasa yake zuwa part na Akka wai ya je duba Akkar da ba shiri suke yi ba, ba wani nan mun san komai ke yake zuwa gani, me zai yi da ganin fuskar Akka da daddare fisabilillahi? Salon ya yi mafarkin wannan masifaffitar tsohuwar? Gimbiyarsa yake zuwa gani ya fake da Akka, to yanzu dai mu kam mu gano komai ato, sai dai ya ɓoyewa su daddy, Momma, mummy, Mammiensa, da kuma su Jaish, amma ba dai ya ɓoyewa PRINCESS TEEMA da tawagarta ba ko my people's? Ba zai ɓoye mana komai ba!.

A bakin bed ɗin ya dawo ya zauna ta yadda suna fuskantar juna. Ganin shi da belt a hannu yasa ta ƙara ruɗewa sosai, nan take jikinta ya kara tsananta kerman da yake yi. A hanzarce ta kai hannu ta riƙo kyawawan fararen tafukansa ta wajen gwiwowinsa, kuka mai sauti ta fashe mashi da shi tana faɗin.

"Dan girman Allah Yah Jawad kada ka dakeni, ba zan sake ba, wlh na duba, bana son duka, last week ma da uncle a school ya mun bulala ɗaya a hannu Allah sai da hannuna ya kumbura, wlh tsoron duka nake ji, ba zan sake ba, ka bani wani punishment ɗin amma banda duka, wayyo Allah Momma na na shiga uku, uncle Abbas kazo ka ceceni". Tana yin magana tare da ƙara ƙanƙame kafafun nasa sosai, tana kuma tsananta kukan da take yi.

Zafi sosai zuciyarsa take yi mashi na jin kukan nata, amma a maimakon ya rarrasheta ta yi shiru, sai ya jefa mata tambaya kamar haka. "Me kika yi wa uncle ɗin naku ya dakeki? Kuma wani uncle ɗin naku ne?".

Tana kuka sosai kamar ranta zai fita, dan ita harga Allah bata son zancen duka, tun da take ma a makaranta ne kawai aka taɓa dukanta, muguwar tsoron duka take ji,

"Babu abin da na yi mashi, ƴan class ne suna ta surutu shi ne ya zo ya haɗe mu gabaɗaya ya yi mana bulala ɗai ɗai". Ta bashi amsa tana ɗan kwantar da kanta a saman kafafun nasa, domin zafi wuyarta yake yi mata, ta ci kuka sosai, sannan ga jan mata gashi da ya yi yasa ta ɗage wuyarsa sama da har ya kusa sagewa a haka, so zafi yake yi mata da ba zata iya jurar cigaba da ɗaga shi ba.

Wani irin yanayi ya tsinci kansa a ciki, abubuwan sun haɗe mashi, ga kukanta da yake taɓa mashi zuciya, ga kishin ta fito da kayan barci a gefe, sannan ga ɓacin ran uncle nasu ya dakar mashi ita, ta wani bangaren kuma ba haushin abin da ta yi mashi na yana magana ta watsa a guje, yanzu kuma ta kwantar mashi da kanta a jikinsa, duk sai ya ji wasu damuwar sun ragun mashi ma.......🙄

Muryarta ne ya dagi dodan kunnuwarsa cikin kuka take faɗin. "Yah Jawad na tuba ba zan sake ba, dan Allah kada ka dakeni, na yi alkawarin ba zan sake ɗin ba".

Bai san lokacin da ya sassauta muryarsa a gareta ƙasa ƙasa ya ce. "Sau nawa kike ce mun ba zaki sake ba kuma ki sake kara yin abin da na hanaki ɗin Jannat?".

Kara kwantar da kanta da kyau a saman kafafun nasa ta yi, tana shessheƙar kuka hawaye na zuba ta fara magana da kyar da kyar. "Yanzu da gaske nake yi ba zan sake ba, wlh na tuba......"

"Kenan da can baya duk ba da gaske kike yi ba ko?". Ya katseta ta hanyar jefa mata wannan tambayar.

Girgiza mashi kai ta shiga yi tare da kara ƙanƙame kafafun nasa ta shiga bashi hakuri. "A'a dukka da gaske nake yi, amma wannan shi ne babban da gaske, ba zan sake ba........". (Oho Allah Chuchu kenan, wai shi me babban da gaske 😅 to my people's kun dai ji babbar da gaske 😅)

"Kina saka mun ciwon kai sosai Jannat". Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya, zuciyar tasa ta ɗan yi sanyi a yanzu.

"In Sha Allah ba zan sake saka maka ciwon kai ba, na tuba".

"Promise?". Ya faɗa kamar mai yi mata raɗa.

Da sauri ta gyara mashi kai alamar e ta yi alkawari.

(Ni dai na ce Allah yasa wannan alkawari ta ɗaure, dan Chuchu da ɗaukar hoto sai Allah, ga shegen mantuwa)

Hannu ya kai saman dark black arab hairnta, a hankali yake shafa kan nata ya furta. "My God bless you my lovely sister".

Ɗan ɗago kanta ta yi a hankali dan ta saci kallonsa, ta ji yadda ya yi maganar ne alamar ya huce, har wani sanyi ita ma ga ji a ranta na jin abin da ya faɗa na Allah ya yi mata albarka, yanzu kenan ba zai bugeta ba? Amma abin ya yi mata matuƙar daɗi sosai.

Shiru suka ɗan yi kowannensu da abin da yake tunani, sai shafa kyakkyawar arab hairnta yake yi. Kasancewar ta ci kuka sosai hakan yasa barci ya fara ƙoƙarin ɗaukarta a wajen, saboda sun yi shiru suna tunani, ita tana jiran ta ji me zai sake ce mata, shi kuma ya luluƙa wata duniya ta daban.

A haka har barci ya ɗauketa, bai ankara ba sai ji ya yi tana ƙoƙarin salalewa ƙasa saboda barci. Cikin hanzari yasa hannunsa dake saman gashin kanta ya tallabota tare da ɗan kura mata ido yana mamakin yadda barci ya ɗauketa cikin ƙanƙanin lokaci haka.

Ganin yadda face ɗinta ya yi jajir da shi, abin ku da farar fata, ta sha kuka fuska ya yi jaga jaga da hawaye ya kuma yi jajir da shi, duk sai ya ji babu daɗi, sai ya ji sam bai kyauta mata ba. Ƙasa ƙasa ya furta "Am so so sorry my sister". Ya yi maganar ta yadda koda idanunta biyu ma ba zata ji me ya faɗa ba, dan ƙasa ƙasa sosai ya yi ta.

Hannunsa ya kai saman ƙuncin nata ya ɗan shafo ruwan hawayen nata kaɗan a yatsunsa, nisawa ya yi tare da miƙewa tsaye, cak ya ɗauketa ya saɓa a shoulder ɗinsa.

Remote ya ɗauko ya buɗe kofar room ɗin. Mutsu mutsu ta fara yi mashi alamar tana son farkawa, amma da yake barci ya sha kanta sosai ga kuma kukan da ta sha hakan yasa ta saƙalo wuyarsa da hannunta ɗaya tare da kara kwantar da kanta a saman shoulders ɗin nasa.

Yana jinta a haka ya nufi room ɗinta da ita. Babu kowa a room ɗin, kuyangu sun gyare ko'ina tsab, da yake ita ƴar son kamshi ce over, sai ya zamana kamshin room ɗinta ma ya fita daban da nasu Sarina, ita a wajen Mommar Zunaira take ɗauko perfume na jiki da na ɗaki, momma kuma kunsan daga Dubai ake kawo mata komai nata, so yana da daɗin kamshi sosai, shi kansa Jawad ɗin da ya shaki kamshin sai da ya ji hankalinsa ta kara kwanciya ta wani fannin, ta wani fannin kuma hankalinsa a tashe yake, fannin kamshin room ɗin dai lafiya lou ne, kamshin ta yi mashi daɗi over, sai dai sauran fannin kuma sai a hankali.

Ita fa Chuchu kullum kuyangun nan sai sun gyara mata room ɗinta, su zuba turaruka kala kala, amma yarinyar nan sai ta fi kwana uku bata kwana a cikin room ɗin, tana can wajen Akka, ko Momman Zunaira, ko kuma dai ɗakin Zunairan, bata cika zuwa wajen mummynta bama sai jefi jefi, na gaya maku sun fi sabawa da Momman Zunaira dama, idan baka sani bama sai ka ce ai Momma ita ce ta haifeta ba mummy ba.

Saman haɗaɗɗen bed ɗinta dake shinfiɗe da shinfiɗa ta alfarma ya shinfiɗeta, sai sauke ajiyar zuciya take yi, ƴar kaniya ta ci kuka har ta ƙoshi. Zuba mata idanu sosai ya yi yana kare mata kallo from head to toe. A nan ne ya kalli ta yi mashi girma da yake renata kullum, kawar da kallonsa daga jikinta ya yi izuwa saman kyakkyawar face ɗinta. Shi kaɗai kome ya tuna sai ya ɗan yi wani guntun murmushi tare da kai hannu ya janyo duv ya lulluɓeta da shi, sannan ya ɗan duƙo da jikinsa izuwa dai'dai saitin face ɗinta.

Can kasan maƙoshinsa ya furta. "You're so cute, very very beautiful my sister and my wife to be In Sha Allah".

(Wato shi Yah Jawad ya mance da cewa Mammiensa ta daka mashi warning a kan babu shi babu Chuchu ko?🤔 Har da wani cewa my wife to be In Sha Allah, zaka ga wife kuwa, dan Mammie dai ta fika bala'i ato, ga shi ita ma Chuchun ba sonka take yi ba, hasalima duk cikin brothers ɗinta kai ta tsana bata so sosai, mu dai ana yi muna shan Maltina mai sanyi.)

Ya kai karshen maganar tasa tare da kai hannu ya goge mata hawayen da yake a saman face ɗinta, ji yake yi mamar ya sumbaci lallausan kumatun nan nata, amma kuma ba zai iya yin hakan ba, yana cikin yanayi haka ya miƙe tsaye tare da ɗaukar remote ya rage mata gudun Ac sosai, sannan ya zauna a saman bedside drawer ya hau kwaranyo mata karatun addu'oin barci da bata samu damar yi ba barci ya yi mata shigar sauri.

Tsab ya kammala addu'ar ya tofa a hannunsa, lokacin da ya zo zai shafa mata addu'ar a jikinta sai hannunsa ta fara kerma, kamar mai tsoron taɓata, kamar kuma wadda yake tsoron wani abin a jikinta. Haka dai ya kai hannu ya shafa mata addu'ar from head to toe, amma fa ya ji a jikinsa kam.

Miƙewa ya yi da sauri ya nufi wajen switch, kashe wutar room ɗin ya yi tare da nufar waje ya janyo mata ƙofa.

Yana ɗan matsawa daga saitin kofar tata da nufin ya tafi part ɗinsa sai ga King sun ci karo, yana sanye da farar jallabiya mai bala'in kyau sosai, ga arab hairn nan nasa ba'a magana, tana kwance har gaban goshinsa, sai sheki wannan kyakkyawar gemu da sajen nasa suke yi.

Dama idan baku manta ba King fa kafin ya kwanta ya yi barci sai ya bi ƴan'matan nan nasa dukka ya duba ya suka kwanta? Ya tabbatar da suna cikin aminci, sannan ya yi masu addu'a ya koma part ɗinsa.

Zubawa Yah Jawad waɗan nan idanuwan nasa King ɗin ya yi, bai ce da shi ko uppan ba, shi kuwa Yah Jawad sai ya wani sunkuyar da kai yana ƴan kame kame kamar wani mara gaskiya.

A hankali ya ɗago ido dan ya saci kallon King ɗin, sai ya kalli still dai kallonsa King yake yi, da suka haɗa ido ma sai King ya ɗaga mashi gera guda alama ya aka yi ne, abin gwanin ban dariya.

"Kai daddy to me kuma na yi?". Ya faɗa yana ɗan murmushi.

"Ashe kenan ka yi laifin tun da har kake tambayar me ka yi, me ka zo yi a room ɗin ƴata cikin daren nan?". Ya yi maganar yana ɗaga mashi gera guda.

"Kai daddy wai ba sisters ta bace ba? Ni fa kun saka mun ido a gidan nan". Yana kai karshen maganar yasa kai yana son zullewa King ɗin. Yasan halin daddyn nasu sarai, yanzu zai saka shi faɗar abin da bai yi niya ba, King ya iya basaja sosai, ya fi uncle Abbas kaifin ƙwaƙwalwa, yanzu zai yi maka dabara ka faɗi magana ba tare da kasan ka faɗeta ba, yanzu dai kunga da ido kawai ya tsare Yah Jawad amma har ya ruɗe ta yadda ya ce shi bai yi laifin komai ba, kunga kuwa babu rami me ya kawo maganar rami? Ya yi laifin kenan, shiyasa dukkansu basu cika son yin doguwar hira da King ɗin ba sam sam, cikin ruwan sanyi yake kamasu a hannu, bare ma Jaish da yake shiru shiru, duk shiru shirunsa King yana iya buga cikinsa yasa shi yin magana ba tare da yasan ya yi ba.

"Zonan, ai ban sallameka ba". King ya faɗa.

"Kai daddy barci fa nake ji, Allah kafara ko? To ni yanzu ma wai me na yi?".

"Sai ka gaya mun me ya kawoka room ɗin ƴata, and kuma ka gaya mun wai ma a naira nawa ne kullum kake kalle mun yarinya? Ka biya Abbas sadakinta ne? Ko dai kawai a free kake kalle mun ita?".

"Kai daddy kai daddy kai ko, zaka fara kenan ko?, to ni yanzu yaushe ma na kalleta? Ni ina ga zuwa zan yi na koma Dubai, kawai kun saka mun ido a gidan nan". Yana magana kuma yana ɓoye fuska, dan baya son su haɗa ido da King ɗin, yasan idan suka haɗa ido sai ya yi dariya.

Shi kuwa King ya tsaresa da kallo sosai yana faɗin. "A'a ba abin da ya haɗaka da ita, ai kasan yanzu ma ba kai na kama a room ɗinta ba, kai Jawad Allah ku kuyayeni".

"To shikenan daddy na yarda ni aka kama a room ɗinta, amma to ni da sister ta? Dan nazo wajenta kawai sai ace mun wani abu, addu'ar barci to na zo yi mata ba shikenan ba?". Yana kai karshen maganar ya ɗago ido tare da sauke kallonsa a kan King ɗin.

Wani irin kallo da King ke wurga mashi ne yasa bai san lokacin da murmushi ta kubce mashi ba, dama yasan sai dai idan ba su haɗa ido ba, sai ya saka shi dariya, irin kallon da King ɗin yake yi mashi irin kallo ne na e ba shakka addu'a kam ka yi mata naga zahiriyya.

"Kai daddy wai kallon fa?". Yana magana yana murmushi. "Kai daddy haka kake yi, sai ka tsare mutun da kallo har kasa ya yi karya".

Ko sannu dai King bai sake cewa ba bayan ido da ya tsare shi da shi tare da ɗaga mashi gera guda sama.

"To ni yanzu daddy in tafi tun da na gaya maka gaskiyar abin da ya kawoni, addu'a nazo na yi mata, kuma yanzu ma room ɗin auta zan je na yi mata nata addu'ar kafin na wuce nawa room ɗin na kwanta".

Shi da kansa fa yasan maganar da ya faɗa ɗin nan ba yarda da shi King ya yi ba, amma ya zage sai ƙoƙarin yiwa maganar tasa kwaskwarima yake yi.

"Ba shakka Jawad da kai da Jaish na kusa aurar da ku a gidan nan, dan na gaji da ganin abubuwa kala kala". King ya faɗa yana karewa Jawad ɗin kallo from head to toe, dama da kallo ɗaya zaka yi mashi idan kana da hankali zaka faminci yana cikin yanayi, bare kuma shi King da dama already dole ya gane cewa Yah Jawad fa to sai dai shiru.

"To wai daddy fisabilillahi me muka yi kuma? Shi Jaish ma yana da budurwa ce da zaka yi mashi aure? Allah daddy mu fa......" Sai kuma ya yi shiru.

"Idan Jaish bashi da budurwa kai kam ba kana da ita ba? Shi ma kuma kwanan nan zan je Dubai na samo mashi mata, na gaji da ganinku tsakar dare kuna yi mun yawo kun kasa barci".

"Wai daddy ko su Yah Rizwan fa basu yi aure ba sai mu? Gaskiya a'a ka bari dai idan suka yi aure sai mu duba mu gani idan zamu iya, kuma ma wai daddy mu munce maka rashin samun barci ne yake fito damu tsakar dare? Kawai fa shan iska muke fitowa yi, sai mu ɗan lelleƙa mu gani ko akwai wanda bai yi barci ba a gidan, kaga tsaron kannanmu muke yi".

"E haka ne babu shakka, to zo ka wuce na ji bayananka, ka jira nawa kuma, yanzu zaku yi tsaro da tushe". King ya faɗa tare da wucewa zai shiga room ɗin Chuchu.

"Daddy to wani mataki zaka ɗauka ne wai?". Ya tambayesa a ƙage, dan yasan halin King ƙaramin aikinsa ne da safe suji wata zancen da basu yi tsammani ba.

"Good night son ka yi addu'a kafin ka kwanta, babu ruwan ka da matakin da zan ɗauka". Yana kai karshen maganar ya shige cikin room ɗin.

"Kai daddy Allah ka iya jefa mutun cikin tunani, to yanzu wai wani mataki zaka ɗauka a kan mu kuma?". Ya tambayi kansa tare da sa kai ya wuce izuwa nasa part ɗin. Yana shiga ya haye saman bed ɗinsa tare da jawo bargo mai laushi ya shige ciki, sannan ya kashe wutar ɗakin ta hanyar amfani da remote, ya ɗaura hannayensa ɗaya a saman cikinsa, ɗayan kuma a saman fuskarsa, nan take tunanin Gimbiya Chuchu ya faɗo mashi cikin ransa, yadda take kwance take sharara barcin nan kawai yake hangowa, da alama dai yanzu ma sai ya yi mafarkinta, dama yaya lafiyar kura bare ace ta yi zawo?.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

Idan kuma koma ɓangaren su Kamran kuwa wato Forest.

🏞️FOREST🏞️

"Kamran me nake ganin a kan nan naka haka?". Mamma ta faɗa tana ɗaure fuska sosai, domin bata taɓa zaton ganin kitso a kansa ba.

Shiru ya ɗan yi yana tunanin me zai ce mata ya tsira? Yau dai bashi da mafita gaskiya.

"Kamran am i not talking to you? What's this I said?".

Kame kame ya fara yi, tsabar ruɗewa ma har in'ina ya fara yi a magana. "Mamma i don't know, kuma ni ban san ta ya aka yi ya zo kai'na ba, and Mamma please don't ash me any questions again now, am feeling to much of hungry, and my Head is penning me". Yadda yake maganar rashin gaskiya ce ƙarara ta bayyana a tattare da shi, ya yi wani tsuru tsuru da shi.

"Kamran am i your mate?".

Girgiza mata kai ya yi alamar a'a yana faɗin. "Sorry Mamma".

"Na yi maka kalar wadda zaka yi wasa da hankalinta?".

Nan ma girgiza mata kai ya yi alamar a'a.

"Okey now tell me who did this thing to you? Dan nasan dai kai kam baka iya ba".

Wani irin tsoro ne ya kamashi, yasan da cewa tabbas idan tasan da su Pretty sai ta rabasu babu makawa, shi kuma har ga Allah ba zai iya rabuwa da su ba, gara ta kashe shi kawai ta huta da ta rabasu, sun zamar mashi wani ɓari na rayuwarsa.

Har wani zufar tsoro ce take tsastsafo mashi, duk ya ruɗe ya rasa abin faɗa. Voice ɗinta ne ya katse shi da cewa. "I'm waiting for your amsa ne fa Kamran".

Ɗago da idanuwansa izuwa kanta ya yi, sannan ya koma bakin bed ɗin ya zauna, ko zai mutu ba zai gaya mata ga wadda ta yi mashi wannan kitso ba, sai dai yau duk abin da zai faru ya faru. Dan haka shiru ya yi mata bai iya sake cewa ko uppan ba, yana jinta sai tambayarsa take yi, da yaga zata matsa mashi sosai ma sai ya miƙe da sauri ya nufi waje da nufin ya barmata kogon ma mai gabaɗaya.

"Where are you going?". Ta jefa mashi tambaya.

Ina ai bai tsaya ba, da sauri ya nufi waje irin shi ya yi fushin nan. Da sauri ita ma ta rufa mashi baya. Kusan a tare suka fito wajen kogon.

Damko gashin kan nasa da karfi ta yi har sai da ya furta wash. Ai kuwa yana furta wash ɗin nan Rocky da yake kwance ya yi tsalle da nufin ya haye kanta. A hanzarce ta kauce mashi, kamar dama tasan zai aikata hakan, ko da yake tasan cewa ko ita ta taɓa Kamran Rocky baya barinta, dan yafi sabawa da Kamran ɗin sama da ita, so in dai zata taɓa shi sai ya yakusheta da waɗan nan shegun faratunan hannun nasa dake fasa fatar mutun.

Ko da ta kauce mashi kuma bata saki gashin Kamran ɗin ba, kaucewar da ta yi kuma yasa ta ja mashi gashin da karfi ta yadda ya sake furta wash da karfi, hakan yasa Rockyn ya sake daka tsalle ya yi kanta da karfi a karo na biyu.

A wannan karon kam dan dole ta saki Kamran ɗin tare da yin baya baya. Tana sakinsa kuma bai bi ta kanta ita da Rocky ɗin ba yasa kai ya sauka ƙasa daga saman dutsen.

Sunansa ta fara kira da karfi karfi, amma ina Kamran yaki ko juyowa ya kalleta, yasan idan ba haka ya yi mata ba ba zai rabu da ita lafiya a kan su Pretty ba, yasan yanzu idan ya nuna mata ya yi fushi ya tafi wuni zunbur bai dawo ba, to da kanta zata fita nemansa, idan kuma ta nemosa lallaɓasa zata fara yi tana rarrashinsa, daga haka zata mance da zancen kitso......... (Ashe dai Kamran ma ya iya tsiya😅)

To bari dai mu leƙa gidansu Khadija mu je mu dawo.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

Lokacin shan Maltina ta yi🥱

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍