RAWANIN ZALINCI (BOOK1)

51&52

by @queenofsurprise1

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥

(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 9/9/2024.....✍️📚🌹

For more information *** Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________47🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

Ana dirama a wannan gida dai'dai gwargwado, domin kuwa Hauwa fa ita ce ta bawa maman Zainab ɗakin da zata zauna, gini ne da baban Zainab ya yi ta gabaɗaya rufi ɗaya, manya manyan bedrooms guda huɗu ne a cikin ginin, kowanne da toilet ɗinsa daga ciki, sai parlor a tsakiyarsu, akwai katafaren kitchen a cikin, kofar kitchen ɗin yana ta wajen dining area. Daga waje ta baya kuma akwai Bq, ginin dai ya tsaru sosai, gini ne na zamani, kasa tiles sama pop, ga manya manyan Ac a parlourn da kowa room na gidan. Kitchen ɗin ma already anyi fixing na komai, drawers ɗin duk an yi fixing ɗinsu, harta gas da komai da komai an sanya.

Hauwa da kanta ta zaɓawa maman Zainab ɗakin da yake ta kusa da dining area, wai shi ne ɗakinta, sannan ta bawa su Zainab ɗakin da yake kusa da na mamar tasu wai shi ne nasu, sura room guda biyun kuma ta ce ɗaya nata ita da baban Zainab, ɗayan kuma a bar mata shi zata yi amfani da shi ba yanzu ba.

Nan fa maman Zainab ta ce bata isa ba, dan bata ga dalilin da zai sa ace Hauwa ce zata zaɓa mata ɗakin da zata zauna ba, kunsan mu fa mata haka halinmu yake, mun tsani muga wata macen tana nuna mana ta fimu iko da abin da muka san mu muka sha wahala a kansa, da farko maman Zainab ta ce zata danne zuciyarta ta hakura kome Hauwar zata yi ba zata kulata ba, zata kawar da kai, amma ina ba zata iya yin hakan ba, domin kuwa mu mata bamu da karfin zuciyar jurar ganin kishiya ta nuna ta fimu iko da komai na gida.........😌🙃🌝

Hakan yasa maman Zainab ta ce ina wlh Hauwa bata isa ta zaɓa mata ɗakin da zata zauna ba, ta gama shan wahalar baban Zainab ɗin, su juri wahala a baya domin su gina kansu rana tsaka kawai wata banza ta zo ta ce zata nuna mata ta fita iko da wannan ribar wahala da suka sha? Wlh wannan ne kuwa ba zai taɓa yiwuwa ba.

Ita kuwa Hauwa ta ce yama yiwu ya gama. Baban Zainab wanda tun da suka shigo gidan ya kama hanya ya wuce room ɗinsa bai ma san me ake ciki ba, ya barosu a parlourn ne suna ta dirama. Cikin gatse Hauwa ta fara gaya mata magana.

"Wannan ɗakin shi na zaɓa maku, kuma a cikinsa zaku zauna, idan ba haka ba sai dai ku kwana a waje, dan ba zaku kwana mun a parlour bama, saboda wani lokaci tsakar dare ina fitowa mu ɗan yi hira da mijina idan barci yaki zuwa, so ba zaki kwana mun a parlour mu fito hira mu sameku ba, dan haka in baki son ɗakin da na baki ki san abin yi, ke bari ki ji ko shi kansa mai gidan idan na ga dama yau a waje zai kwana, kuma haka dole zai kwana babu yadda ya iya da ni, ni fa babu yadda kuka iya da ni, na zame maku ƙashin wuya, na fi karfinku sai gani sai hange daga nesa".

Zainab dake tsaye kusa da mamar tata ce ta ce. "Idan kin fi karfinsu ai baki ki fi karfin Allah bako? To da izinin Allah sai rayuwarki ta walaƙanta tun a duniya kafin ki je lahira ki girbi abinda kika shuka, maciyi amana kawai, In Sha Allah idan baki yi hankali ba ni ce nan zan gyara maki zama!". Ta yi maganar tana wurga mata kallon up and down irin wanda take yi wa Haidar idan ya ɓata mata rai, kun san fa Zee ta kware a iya irin wannan ɗan iskan kallo na rai'nin wayo, kamar dan ita aka yi kallon, ga idanun nata kuma manya farare tas, idan ta fara wannan kallo ba'a magana, kallo ne na ƙasƙanci wanda idan ka yi wa mutun sai ya ji kamar bashi da gata, to ita dai Zainab ta kware a wannan part ɗin.

Sai ƙoƙarin rufe mata baki Khadija take yi a kan ta yi shiru kada ta sake jangwalo masu wani bala'in, amma ina Zainab fa taki rufe bakinta har sai da ta kai aya a maganarta.

"Eyeee lallai Zainab kin girma, wuyarki ya yi kwari ya kai yanka, ke ɗin ce zaki gyara mun zama? To uwarki ma mecece a gaba bare ke? Ubanki ma bai wuce na aikesa ya je ya dawo ba bare ke, lallai yarinya kinzo da abin da dukka familynki ba zasu iya ɗauka ba, wato faɗa da ni!!".

Cigaba da wurga mata wannan matsiyacin kallo ta yi tare da cewa. "Ke ɗin wacece ke? Ke ɗin banza ke ɗin hofi, babanmu dai zaki iya aikansa ya je ya dawo kamar yadda kika faɗa ɗin, dan kin shanyesa, amma ni dai wlh nafi karfinki algunguma kanwar shaiɗan kawai!!".

Cikin fushi tare da jin zafin kalaman nata Hauwar ta yi kanta zata daketa. Da sauri maman Zainab ta shiga tsakaninsu ta mayar da Zainab ɗin bayanta. Cikin ɓacin rai ta fara magana. "Wlh Hauwa idan kika ɗaura hannunki a jikin Zainab sai kin gane baki da wayo, sai na tuno maki da lokacin da muke zuwa Islamiya!".

Khadija dai tana tsaye shiru tana ganin wannan iko na Allah, ita kanta ma ciwo yake yi mata, ta gaji da tsayuwa tana son ta zauna.

Birki Hauwar ta ja, cikin kunan rai ta juya fuuu kamar wata kunfa ta nufi ɗakinta in da baban Zainab ya shiga kenan, da alama tana matuƙar tsoron yin faɗa da maman Zainab ɗin, duk da ta san cewa baban Zainab yana nan kuma zai tare mata faɗar, sai dai tasan kafin ya fito ya tare mata ɗin maman Zainab idan ta yi mata duka ɗaya sai ta yi jinya, hakan yasa bata yarda ta yi faɗa da ita idan baban Zainab ɗin ya matsa ko kaɗan ne.

"Zainab ku shiga wancan ɗakin da ta ce naku ɗin ku zauna ina zuwa, ku fa rufe kofa idan kun shiga, kuma ko an buga kofar kada ku buɗe har sai idan ni ce na dawo". Cewar maman Zainab.

Cikin wani irin kasalalliyar murya mai sanyi Khadija ta ce. "Mama ina zaki je?".

Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce. "Ba zan yi nisa ba, yanzu zan dawo, idan na dawo zan gaya maki in da na je". Tana kai karshen maganar bata jira jin me zasu sake faɗa ba ta nufi waje da sauri.

Su kuma suka nufi cikin ɗakin a hanzarce kamar yadda ta umarcesu, suna shiga kuma suka dannawa kofar key.

Da shigansu ɗakin ba'afi da minti ɗaya ba sai ga Hauwa da baban Zainab sun fito daga nasu room ɗin. Sai cika Hauwa take yi tana batsewa, da alama wani munafurcin ta je ta haɗa, ta kwashi karya da gaskiya ta sanar da shi, bawan Allah shi kuwa da already an rigada an shanye mashi ruwan kansa, sai yazama kamar wani yaronta, duk abin da ta faɗa shikenan ya yarda, haka kuma zata taso shi a gaba zalo zalo yana biye da ita, duk abin da ta faɗa ya hau kai ya zauna da shi yake aiki.

Ganin babu kowa a parlourn ne yasa Hauwar ta fara surfa uwar masifa a kan ita lallai ba zata yarda ba sai baban Zainab ya daki Zainab ɗin dan ta yi mata rashin kunya.

Shi kuwa bawan Allah sai hakuri yake ta bata babu kakkautawa, kafewa ta yi a kan lallai sai ya gurzan mata bakin Zainab har sai ya yi jini. Allah sarki Zee baiwar Allah, babanta bai taɓa ɗaura hannunsa a jikinta da sunan duka ba, baya dukansu sai dai rarrashi da lallama tare da nuna soyayya, amma yau Hauwa tana son lallai sai an dirzan mata bakin Zee, akwai cakwakiya kenan.

Sai hakuri yake bata yana gaya mata ai shi bai ga su Zainab ɗin ba, tun da kuma basa nan ta yi hakuri kawai. Sam bata san sun shiga cikin ɗakin ne sun rufe kofa ba, da ta leƙa ɗakin da ta baiwa mamar tasu taga ba kowa sai ta yi zaton fita suka yi, bata yi yunƙurin leƙa ɗayan ɗakin ba.

Ita kuwa maman Zainab tana fita kai tsaye bakin titi ta nufa, da yake gidan nasu bashi da nisa da bakin babban titin.

Yau a karo na biyu Maman Zainab ta sake fita ba da izinin baban Zainab ba, hakan kuma ya faru ne saboda tsananin kunan rai da take ji, idanunta sun rufe bata ji bata gani, shiyasa ake son bawa a kowani lokaci ya rinƙa yawaita addu'ar Allah yasa ya fi karfin zuciyarsa, sannan ku kasance a duk lokacin da ranku ya ɓaci ku yawaita istigfari kuna ambaton sunan Allah, hakan zai sa duk ɓacin ran da zaku shiga ba zaku taɓa yin aikin danasani ba, dan haka ni dai shawarata a gareku ƴan uwana mata har ma da maza, kada ku bari zuciyarku ta fi karfinku, duk wuya duk daɗi kuma kada ku bari ambaton sunan Allah ya kubce daga bakunanku, yawan ambaton Allah ya kan sa ku fi karfin zuƙatanku, kuma yakan kai ku ga nasara tare da cinma burikanku da kuma samun babban rabo duniya da lahira, dan haka kada ku yarda ambaton Allah a kowani irin yanayi ne ya kubce daga gareku!!.

Abin hawa ta hau ba tare da ta gayawa kowa ba ta nufi bayan gari. Zuciyarta tafarfasa yake yi mata tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje, ranta ya yi bakin kirin, idanunta sun rufe sosai, burinta kawai ta isa in da take da buƙata, sai sauke wani irin ajiyar zuciya take yi wanda da gajisa kasan na tsananin ɓacin rai ne, wai ace Hauwa ce ma zata zaɓa mata in da zata zauna ita da gidan mijinta, gidan mijin nata ma wanda ta sha wahala ta juri komai dan su gina gidan? Abin da ciwo kam matuƙa, duk kuma macen da aka yi wa haka ba lallai ta iya ɗauka ba, za'a tara mata ɗari da wuya a samu biyu da zasu iya danne irin hakan su shanye, akwai matuƙar ciwo sosai.

Kai tsaye bayan gari suka nufa, ba tare da ɓata lokaci ba ta yi wa mai mashin ɗin kwatance wajen wannan boka na Hauwar, sai kutsawa cikin dajin yake yi ita kuma tana kara yi mashi kwatance. Da kyar dai suka iya isowa wajen dutsen.

Sauka ta yi ta ce ya jirata bari ta je ta fito, dama sun yi da shi tun kafin ta hau a kan zai kai ta ne ya kuma dawo da ita, hakan yasa ya samu waje ƙarƙashin wata bishiyar kuka mai girma ya yi zamansa bayan ya kashe mashin ɗin nasa kenan. Zuciyarsa cike tab da tunani tare da tarin tambayoyi haɗe da mamaki a kan maman Zainab ɗin.

Bai san wacece ita ba, amma ta bashi mamaki yadda ta ce ya kawota wannan ƙungurmin dajin, tunani ya rinƙa yi tare da tambayar kansa me ta zo yi a nan? Sam bai san da cewa a saman wannan dutse ta baya akwai wani la'anannen Allah ba wai shi boka, wani tsinanne wanda wutar jahannama ke jiran gangar jikinsa idan bai tuba ba, shi dai mamaki yake yi kawai na me zata yi a daji, tunani ya yi ko dai ya salallaɓa ya bi bayanta ya je ya leƙa me zata yi ne domin ya samu abin labartawa a gari.

Hakan kuwa a ka yi, ya miƙe daga zaunen da yake ya fara salallaɓawa ya haye saman dutsen shi ma. Tun bai ƙarisa zuwa wajen ɗan kogon da ya gani a wajen ba ya fara jiyo muryarta tana magana kamar haka.

"Ba ni ce na kawo maka aikin ba dama? Ai kuɗina na biya, dan haka na ce ka warware wannan aiki, idan kuma ba haka ba zan shigar da kai kara ga hukuma, macuci kawai azzalumi, wlh da kai da Hauwa ba zaku ga annabi idan baku tuba ba".

Yana daga zaune saman ɗan buzunsa na tsafin ya amsa mata da. "Ke ɗin ganin annabin zaki yi ne aka ce maki? Nasan kin san da cewa idan mutun ya je wajen boka ba tare da ya yi aiki da abin da bokan ya faɗa ba, zuwa kawai ya yi sallarsa ta kwana arba'in Allah baya karɓa, kin san da haka kuma ai kika zo nan har kika yi amfani da abin da na faɗa na kuma baki, ke muma fa ba wai jahilai bane, bari ki ji in gaya maki gaskiya kafin ka zama cikakken boka sai kana da hadda Alqur'ani mai girma a kanka, sannan sai ka san fassarar ayoyin cikinta, babu wanda Allah ya kafurta a Alqur'ani mai girma har sau biyar sai boka!! Mun san komai kawai take sanin muke yi domin biyan buƙatar kanmu! Kuma hakan ce kaddararmu, Alqur'ani da kike ganin nan tun daga farkon duniya har karshenta akwai magungunar duk wasu cuta da suke a duniya a zamanin da ya shuɗe da kuma yanzu har ma da cutar da zata bayyana nan gaba wadda namu sani ba, Allah bai saukar da cuta ba sai da ya saukar da maganinta, kowacce aya a cikin Alqur'ani da kike ganin nan tana da dalilin sauketa, dan haka ki sani ba wai da ka muke komai ba, duk wani sihiri da zamu haɗa in dai da gaske so muke taci to dole sai da Alqur'ani, dole sai da wasu ayoyin da Ubangiji ya saukarwa mutanen da suka gabata domin kawar da matsalarsu, to mukuma da ita muke amfani domin hassasa matsala cikin al'umma, sihirin da yake jikin mijin kurciya ce, sihiri mai wuyar warwaruwa kenan, ba kamar sauran sihiri da kika sani wadda zata yi kwana arba'in ko makamancinta ta kwance bane, wannan babban aiki ne, dole idan za'a kwanceta sai an dawo da kurciyar, sannan tsakanina da Hauwa akwai amana, dan tana mun abin da ba kowa ba, sai dai idan zaki yi mun abin da take yi mun sai na duba na gani.......".

Zaro ido maman Zainab ta yi tun lokacin da ya fara jawabinsa, kenan dama sun san gaskiya shegu?. Ni kuwa na ce kwarai kuwa babu abin da basu sani ba, shiyasa idan Allah ya tashi kamasu suke cin ubansu! Domin da sanin komai suke aikata duk abin da suke aikatawa, Allah baya kama bawa a cikin aikin rashin sani, amma ka sani ka take sani babban laifine wanda idan Allah ya tashi kamaka baya yi maka ta daɗi, babu wani ɗan iskan boka da ya isa ya yi sihiri ba tare da ayoyin Alkur'ani ba, dan haka ilimi ne da su sarai la'anannun tsinannu, kafirtasu da Ubangiji ya yi har sau biyar a cikin Alqur'ani ma duk sun san da haka shegu, sun karanta kuma sun karanci tafsiri, sun san fassarar ayoyi da dama, wasu ma sun san fasarar kowace aya shegu, amma a haka suke take sani suna cutar da bayin Allah, su yi asiri su ɗaurawa wata cuta, wata su haukatata ta shiga duniya a sake samun wasu la'anannu su yi amfani da ita a haukace dan biyan buƙatarsu suma, kuma duk bokayen ke saka hakan, ga shi nan dai abubuwa kala kala, ga cin zarafin Alqur'ani mai girma da suke yi, wata zasu rubuta mata suratul ali'imran su haɗa da magungunansu su ce ta wanke gabanta da shi, wannan ɓangaren sun fi yiwa karuwai wai dan su kara ɗanɗano, kun ga laifi kan laifi, ga bokanci ka taimakawa zinace zinace ta kara yaɗuwa, wani lokaci su rubuta wata sura daga cikin Alqur'ani mai girma su wanke suce mace ta yi wanka da shi, haka zata je cikin toilet wajen najasa ta yi wannan aiki, wani lokaci da jinin al'ada kazanta zasu rubuta Alqur'ani mai girma su wanke su bawa mace ta baiwa namiji, wani lokaci su rubuta wata sura a paper su ce mace ta sanya a gabanta, aiki dai kala kala na cin zarafin Alqur'ani mai girma duk yinsa suke yi, kuma sarai sun san hukuncin da yake jiransu na yin wannan ɗanyen aikin, amma da yake sheɗan ya yi wa Allah alkawarin sai ya samu parsinjoji na tafiya wutar jahannama, sai ya bi ya yi ta kaɗa masu gangan a kunne yana gaya masu cewa kada su damu su yi ta aikata fin hakan ma, idan sun zo mutuwa sai su tuba, haka sheɗan yake ruɗarsu, su yi ta tsula siyarsu a zuwan zasu tuba kafin mutuwa, sai su fake da cewa ai Allah gafurun rahim ne, sai dai sun manta shi Allah ba'a yi mashi wayo, wane mutun, san da zasu mutu ma basa sani bare har su tuba, time da zai kamasu ma basa sani bare su tuba shegu!!!.

Ganin maman Zainab ta zaro idanu tare da luluƙawa duniyar tunani ne yasa bokan ya sake ce mata. "Kada ki damu mu wannan ita ce kaddararmu da Allah ya kaddaro mana".

Wani irin matsiyacin kallo ta bishi da shi kafin ta ce. "Kuka dai kaddarawa kanku, Allah kam bai ɗaura maku wannan kaddara ba, kowani ɗan iska sai ya gama shirga iskancinsa, ya tsula tsiyarsa son ransa sai ya ce kaddararsa da Allah ya kaddaro masa kenan, to shi dai Allah baka isa ka yi mashi karya kuma ka zauna lafiya ba, azzaluman banza kawai..........."

Dakatar da ita ya yi ta hanyar daka mata tsawa ba tare da ya bari ta gama amayar da zafafan zantukan da suke ƙunshe a cikin cikinta suna cizonta ba.

Maman Zainab akwai karfin hali, ko tsoron wannan boka bata ji ba, ɓacin rai yasa ta fara zazzaga mashi masifa ba tare da jin tsoron kada ya yi mata wani abin ba, bugu da kari tana zaune a cikin muhallinsa tana kwashe mashi albarka.

"Dakata Hajiya, idan maganganu marasa daɗi kika zo gaya mun to tun wuri ina umartarki da ki fita a cikin wajen nan tun ban sauya maki halittar jikinki ba, sha sha sha kawai, ke har kin isa ki zo har in da nake ki ce zaki gaya mun magana? To idan ba aiki zaki kawo mun ba kada na kara ganinki a nan, idan ba haka ba kuma sai na mayar dake kwaɗo ko kunkuru". Yana maganar yana wani irin muzurai da ido, yadda kuka san kwarton da soja ya kama a gidansa, irin shi zai tsoritatan nan, ga idanun nasa jajir da su kamar mutun ya kwakwalesu ya jefar saboda muninsu, hancin nan nasa ba'a magana, a bage yake a saman fuskarsa kamar kan fanfo, ga shi bakin kirin kamar zunubi, bakinsa kamar waga.

Kasancewar ta zo ne domin a kwance wannan aiki da hauwa ta yi wa baban Zee, sai ta ɗane zuciyarta, ta daure ta sassauta muryarta tare da ƙoƙarin kawar da ɓacin ranta ta fara magana a nutse. "Ni ba dukka wannan ne ya kawoni ba, aikin da ka yi wa mijina kawai nake son ka kwance shi kamar yadda ka yi".

To kun san bokaye basu da sirri, dan haka sai ya ce mata. "Ni da Hauwa akwai amana a tsakaninmu, amma idan zaki bani abin da take bani sai na warware".

Da sauri ta amsa mashi da. "E zan baka menene?".

Ba wani ɓoye ɓoye bare kunya ya baje mata komai a faranti. Kanta zata bashi, dan shi ne abin da Hauwa take bashi yasa ya riƙe mata amana, har da wani ɗaurawa da cewa. "Ke kin ma fi Hauwa sura da kaya, kin ga da kin bani sai na warware aikin, kuma zan riƙe maki amana".

Ni kuwa nace wani amana kuma? Na tabbata ita ma Hauwa hakan ya ce mata idan ta bada kanta zai riƙe mata amana, amma ga shi yanzu saboda yaga maman Zainab ta fi hauwa komai da komai har ya tonawa Hauwar asiri, kuma idan da maman Zainab zata bashi kan nata tsab zai iya kwance aikin nan da ya yi wa Hauwar, kun ga kuwa a nan ina amana fisabilillahi? Ko da yake duk aikin da aka ce maka ya saɓawa Allah da Manzonsa ai babu wani amana da tausayi a cikinsa face danasani da nadama maras amfani!!.

Wani irin mahaukacin razana maman Zainab ta yi da jin maganganunsa, nan take ta ji wani irin jiri yana neman kwasanta, wa'iyyazubillah ta furta kusan sau uku. Wani irin tsinanne kallo ta fara bin bokan da shi, wani ƙazami da shi, ai wannan da ta haɗa shinfiɗa da shi gwara ta mutu, da wasu garmar hakwaransa da baya brush kamar na shanu. Wani irin muguwar tsanan Hauwa haɗe da baban Zainab ɗin ne dukka ya kamata, ji ta yi wlh zata iya hakura da baban Zainab har abada tun da ya haɗa shinfiɗa da Hauwa da ta sallamawa wannan ƙazamin la'anannen Allah kanta, waye ya sani ma ko yana ɗauke da wata cuta tun da ya nemeta hakan yana nufin ba da iya Hauwar kawai yake kwanciya ba, yana keta mutuncin mata da dama, daga gani halinsa ne, da wuya kuma idan bai da wata cutan.

Wani irin ƙululun bakinciki ne ta gangaro mata har wuya, kanta dake sara mata tun ɗazun ne ya fara yi mata barazanar tarwatsewa, sam bata san lokacin da zafafan hawaye suka fara bin ƙuncinta ba, ita kanta bata san hawayen me take yi ba. Cikin kunar rai ta juya da sauri kamar zata kifa ta fice daga cikin wajen ba tare da ta sake ce mashi ko uppan ba.

Unexpect wannan mai mashin ɗin da yake yi masu laɓe ya ganta a gabansa, bai yi tunanin zata juya tafito cikin ƙankanin lokaci haka ba, ya saki baki yana kallonsu kuma ya afka duniyar tunani a kan cewa kenan mata idan suka je wajen bokaye haka suke yi? Dama haka ake abin, bawan Allah bai taɓa gani ba sai yau, ya luluƙa duniyar tunani kwatsam ya ganta a gabansa ta fito.

Cikin hanzari ya ɗaga jikinsa daga jikin dutsen ta bakin kofar kogon in da ya samu damar leƙan nasu. Ƴan kame kame ya fara yi irin na marasa gaskiya.

Bata bi ta kansa ba ta yi saurin wucewa zata sauka kasan dutsen. A hanzarce ya rufa mata baya. Da kyar ta iya jiransa har yazo ya hau mashin ɗin ya tayar, kamar zata faɗi ƙasa zaboda jirin da take gani. Tsana da kyamar Hauwa da baban Zainab ne cike fal a ranta, bata da tabbacin cewa baban Zainab ɗin ya taɓa kwanciya da Hauwar, amma da yake zuciya bata da ƙashi sai ta ɗaurawa har da shi ma karan tsana.

Kunna mashi mai mashin ɗin ya yi suka bar wajen, suka nufi hanyar da suka zo domin komawa, sai sake sake take yi a cikin ranta, tana ta tufka da warwara...........

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

🏞️FOREST🏞️🕊️🌹

Sosai Kamran ya sha wahala wajen yawo a bakin wannan tekun domin neman hanya, sai dai kash bai iya samun hanyar da yake ganin e ya aminta da ita ba, ya samu hanyoyi da dama a wajen, sai dai duk yana ganin kamar zasu yi mashi wahalar bi, sannan yana ganin kamar ba za su ɓille mashi ba, domin kuwa dukka hanyoyin daji ne gaba daji baya, babu kamshi alamar gida ko motsin wata halittar ɗan adam, hakan yasa yake ganin kamar har yanzu bai samu hanyar da ta dace ya bi ba.

Komawa ya yi wajensu Pretty jiki duk ya yi tsami saboda wahalar neman hanya, a kasale yake tafiya, yanayi yana tunanin mafita.

Lokacin da ya koma wajen nasu Pretty tana barci, ita kuma Sweetie tana karatun husnul Muslim da kai ba tare da littafi ba.

Kasancewar Prettynsa ta yi barci sai ya ji babu daɗin zaman wajen nasu, domin kuwa babu abokiyar rigimarsa, babu wanda zai tsokana ta yi mashi rigima ko kuka ya rarrasheta, hakan yasa ya ce da Sweetie bari ya je wajen mammarsa kada ta nemesa.

Sam Sweetie bata so tafiyarsa ba, ta so su yi hira sosai, amma ina ba dama.

Da okey ta amsa mashi kawai, daga jin yadda ta amsa mashi kuma kasan ba har cikin zuciyarta wannan okey ɗin yake ba, ta dai amsa ne kawai rai bai so ba.

Miƙewa ya yi ya nufi hanyar fita. Yana tafiya yana waigo Pretty dake kwance, ji yake yi kamar ya mayar da yarinyar nan cikin cikinsa ko zai huta da irin kaunarta dake azalzalar zuciyarsa. Ita kuma Sweetie ji take yi kamar da sanya hannu ta buɗe idanunta ta fara gani domin ta ga mutumin da take jin tana kauna a duniya sama da komai nata a halin yanzu.

Yana fitowa ya cikaro da Rocky ya dawo daga yawonsa. Bai kula shi ba yasa kai ya yi gaba, baya Rockyn ya rufa mashi suka cigaba da tafiya kamar yadda suka saba, a haka suka nufi gida wajen mamma.

Pretty kuwa tana barci tana mafarkin Kamran ɗin, ita kuma Sweetie idanunta biyu tana tunaninsa, shi kuma yana tunanin Pretty tare da tunanin babansa da kuma yadda za'ayi ya samanwa Sweetie maganin idanun nan nata, yau ya ƙuduri niyar tambayar mamarsa maganin, in ta gaya mashi kuma tabbas ko a ina ne komai wahalar da zai sha wajen nemowa zai nemo mata, a cewarsa ya gaji da ganinta bata gani, so gara ya nemo mata maganin idanunta zu buɗe ko dan su rinƙa zuwa yawo a tare. Wani ɓangare na zuciyarsa kuma yana tunanin meyasa Mamma take ɓata rai sosai a duk lokacin da ya yi maganar addinin su Pretty? Wato a duk lokacin da ya yi mata wata kalma da ta danganci musulunci irin su Alhamdulillah da dai sauran word's da yake tsinta a bakin su Prettyn..........

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

KINGDOM OF POWER 💪🔥💘

"Yah Jawad meyasa zamu ɓuya to?.....".

Bata ƙarisa maganar ba ya yi saurin sanya tafin hannunsa ya rufe mata baki yana mai kallon cikin idonta, har yanzu basu dai'na sauke ajiyar zuciya ba daga shi har ita.

Ƙura mashi ido ta yi tana jiran ta ji me zai ce, tana kuma mamakin meyasa suka ɓuya? Meyasa bai bari ta yi magana ba ya rufe mata baki.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥

(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 10/9/2024.....✍️📚🌹

For more information *** Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________48🔥

KINGDOM OF POWER 💪🔥💘

Ƙura mashi ido ta yi tana jiran ta ji me zai ce, tana kuma mamakin meyasa suka ɓuya? Meyasa bai bari ta yi magana ba ya rufe mata baki.

Matsowa kusa da ita sosai ya yi, cikin murya wadda za'a iya kiransa da kamar raɗa, in a low sosai kenan ya fara magana. "Kada ki sake yin magana kin ji ko?". Ya yi maganar tare da zame hannunsa daga saman bakin nata. Sai binta da wani irin kallo yake yi.

Ƙasa sosai ita ma ta yi da murya kamar yadda ya yi. "To Yah Jawad meyasa muka ɓuya?".

Bin ɗan bakin nata da kallo ya yi kafin ya ce. "Because of Akka mana, kin san wannan tsohuwa da bala'i, yanzu sai ta samun hawan jini, so stay quiet har sai ta tafi zamu fita, don't let anyone to know abin da ya faru".

"Har da Auta?". Ta faɗa tana ɗan zaro ido.

Hannu ya kai ya ɗan matse ɗan bakin nan nata har sai da ta ce wash. "If i say don't tell someone anything about me and you doesn't means har da Auta a ciki, i know kece Auta, sannan Auta ce ke, dan haka ki dai'na raba kanki da ita, coz nasan ma ko na ce kada ki gaya mata sai kin faɗa ɗin, so is better na ce ita kam a gaya mata". Yana magana yana ɗan wurga mata hararar wasa.

Zata yi magana suka ji motsin mutun yana tinkaro dressing room ɗin wanda ko basu ga waye bane sun san King ne, dan sun san ya shiga wanka.

Jawad ba zai damu sosai ba idan kin ya gansu, saboda shi da daddyn nasa kun san yadda suke ai, gwara mashi King ya yi ta ganinsu a haka sau dubu a kan Akka, Akka ce matsalarsa shi.

Cikin hanzari ya sanya hannu ya toshe mata baki dan kada ta yi maganar, sannan ya fara matsawa a hankali kusa da ita, ita kuma ta fara ja da baya a hankali har suka matsa daga wajen glass ɗin suka ɓuya a bayan wani shirgegen drawer dake shaƙe tab da haɗaɗɗu kuma tsadaddun King shoes kala kala.

Cikin nutsuwa King ya shigo room ɗin waist ɗinsa na'a ɗaure da wata tsadaddiyar towel sky blue mai haske, yana shigowa cikin kuma yana magana a in da yake ce da Akka ta jira su je a tare, bari ya sanya kaya five minutes yana zuwa.

Mannuwa da jikin bangon wajen Chuchun ta yi, a hankali ya zame hannunsa daga saman bakin nata, sannan ya kara matsowa kusa da ita sosai, ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa a in da suka bawa King baya kenan.

Cikin nutsuwa shi kuma ya fara shirinsa tare da fitar da kayan da zai sa, sai dai yana yi yana ɗan yin sauri saboda ya tsayar da Akka a kan ta jirasa.

Sosai Yah Jawad ya kura mata ido, ita kuma hankalinta na can wajen tunanin daddyn nata dake a cikin room ɗin, dan ma Allah yasa room ɗin yana da matuƙar girma, sannan wajen jera takalmar sakawarsa har drawer kala uku ne, kuma ba'a waje guda suke ba, dukkansu suna da ɓangarori daban daban, haka shi ma glass na jera watch ɗin nasa ma manya manya ne har guda uku, dukkansu kuma a shaƙe suke da tsadaddun agoguna kala kala, mafiya yawancin komai da yake cikin room ɗin guda uku uku ne, da alama wannan tsarin su Momma ne, shi kuma dan ya yi adalci ya biye masu kowacce ta jera nata kalar abubuwan da take buƙata ya rinƙa yi mata kwalliya da shi, ranar da yake wajen Momma sai ta shirya shi da kalar kayanta da ta sanya aka shirya mashi, haka idan yana ɗakin su mama kenan, yana ƙoƙarin kamanta adalci kam, shi ne yasa komai nasa uku uku ne kala daban daban, kowacce da kalarta, kuma kowacce a ranarta duk kalar da ta zaɓa mashi baya reject koda baya son wannan kalar, dan zaman lafiya, yana hakuri ya nuna yana matuƙar so ya kuma yi amfani da shi fuska ba yabo kuma ba fallasa!!.

Shiru ya ɗan dakata daga ƙoƙarin zura ash color arab jallabiyarsa da yake ƙoƙarin yi, kunnuwansa ne suka jiyo mashi kamar alamar motsi a cikin room ɗin. Ƴan waige waige ya fara yi da mamaki fal a saman fuskarsa.

Jin haka yasa Yah Jawad ɗin ya ƙara matsawa kusa da ita sosai ta yadda har suna iya jiyo sautin numfashin juna, dan gudun kada King ya gansu, still idanunsa yana a kan face ɗinta ya kasa kawar da kallonsa, ɗan rage gudun sautin fitar numfashinsa ya yi ta hanyar ɗan rike numfashin da yake yi kafin daga baya ya ɗan saki a hankali, duk gudun King ya gansu ne, yanzu sun ji ya fara waige waige dan yana ɗan jin motsi, so sun san zai iya ganosu, kuma fitar sautin numfashin a wajen da ya kasance babu hayaniya yana bada sauti mai ɗan karfi da har mutun zai iya ji kamar motsin wani abin!.

Ganin bai ga alamar komai bane yasa ya cigaba da yin shirinsa cikin natsuwa.

Daga karshe dai jawota jikinsa mai gabaɗaya ya yi tare da rage tsawonsa kaɗan, sannan ya sunkuyo da kansa izuwa kunenta, cikin raɗa ya ce mata. "Ki rage sautin fitar numfashinki, ki rinƙa sakin numfashin a hankali hankali......".

Still wannan ɗan magana da ya yi yasa King ya sake jin alamar motsi a karo na biyu, a lokacin kuma yana sanya alkyabba a saman jallabiyar jikinsa. Dakatawa ya yi shiru, cus cus ya ji yo kamar ɓera na fasa ledar indomie, mamaki ne ta kara bayyana sosai a saman fuskarsa a in da ya fara waige waige a karo na biyu, sai kuma ya ajiye rawanin da ke hannunsa a saman wani haɗaɗɗen show glass dake shake da hatiman masarautar wadda suke dukka iri guda ne masu kan zaki kenan. Fara ƴan dube dube ya yi ko zai gano ta ina yake jiyo wannan ɗan motsin.

Jin ya zo ta kusa da drawer da suke ɗin ne yasa Jawad ɗin ya kara mannata da jikinsa sosai suka yi wani tsit kamar babu wata halitta mai rai a wajen. Yan dube dubensa King ya gama yi tsab, sannan ya juya ya koma wajen da yake shirinsa.

A hanzarce ya ƙarisa shirin dan Akka na jiransa kuma ya ɓata lokaci wajen tsayawa da ya yi ta yi dan jin motsin da ya yi, dan haka sai ya ƙarisa shirin a hanzarce ya fice daga room ɗin.

Yana fita a tare suka sauke wani irin nauyayyar ajiyar zuciya, kara ƙanƙameta ya yi yana fitar da numfashi da sauri da sauri saboda rike numfashin nasa da ya yi ta yi dan kada King ya gansu.

Ita ma da sauri sauri take sakin numfashin tata. Hannunsa ɗaya ya ɗaura a saman bayanta dai'dai tsakiya. "My Jannat mun tsalleke rijiya da baya, da Akka ko daddy sun ganmu am in trouble wlh". Ya faɗa da wata kasalalliyar murya kamar mai jin barci.

"To Yah Jawad meyasa kake gudun su ganmu? Ai naga sun saba ganinmu a tare, bare ma shi daddy da a can baya kai da Yah Jaish kuke zuwa cin abincin a dining room ai kullum suna ganinmu a dining room ɗin a tare ko?....."

Ɗaga kansa sama ya yi tare da jinginta da jikin drawer, a wahalce ya ce. "Banda irin wannan kallon kam, ai idan suka ganmmu a irin wannan yanayi akwai matsala, musamman Akka sai ta saka mun hawan jini...."

"To meyasa?". Ta tambaya da mamaki sosai a saman face ɗinta, ta kuma yi maganar tana ɗan ɗago kanta daga saman chest ɗin nasa.

Slowly ya sauƙo da kansa daga ɗagata da ya yi, ya zamana suna fuskantar juna sosai saboda ta ɗan ɗago kanta ita ma. Kura mata idanu ya yi kamar wani ya ce zai kwace mashi ita. A hankali ya motsa lips ɗinsa wajen furta. "Kina son sanin dalili?".

Da sauri ta gyaɗa mashi kai haɗi da cewa e. Rankwafo da face nasa dab da tata ya yi, ɓangare ɗaya na zuciyarsa tana azalzalarsa da ya faɗa mata kawai, ya furta mata saboda yana sonta ne, ɗayan ɓangaren kuma yana ƙoƙarin hana shi yin hakan ne ta hanyar bijiro mashi da tunanin cewa zata rai'na shi, zakuma ya samu matsala da Jaish da dai sauran tunani marassa kan gado.

"Yah Jawad ka faɗamun mana". Ta katse mashi tunanin da yake yi.

Ji yake yi kamar ya yi kissing ɗinta idan tana magana a kusa da shi, kuma ji yake yi kawai ya daure ya gaya mata yana sonta. Amma ina ko kusa ko alama ba zai iya yin hakan ba.

Nisawa ya yi tare da sumbatar goshinta, sannan ya ɗan ja baya kaɗan tare da raba jikinsu.

"Wani lokaci zan gaya maki, but now come let us go". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta cikin nasa da nufin su fice daga room ɗin.

Ba musu ta bi bayansa, hankalinta yanzu gabaɗaya ya karkata izuwa room ɗinta, tana son ta koma can ta je ta cigaba da yin waya da Yah Rizwan wanda yanzu shi ne tauraronsa yake haskawa a idanunta tun daren jiya, ya tsarata ne da wasu shegun love word's, shi da yake cewa Jawad a yanzu ba shi da lokacin mace, amma kuma ashe ya iya zafafan kalamai masu tsayawa a rai, ko daga ina ya koyo? Allah masani sai kuma shiɗin haɗi da alkhalamina........💘

A cikin room na King suka tsaya, hannun nata ya saki tare da juyowa gareta da kyau. Zuba mata idanun ya yi na ƴan mintocin da basu wuci biyu ba, kafin ya nisa tare da cewa. "Jeki room naki".

Da sauri ta juya zata ta fi, har ta kai tsakiyar room ɗin kamar a mafarki ta tsinkayo muryar can ƙasa ƙasa ya furta sunanta. Da sauri ta juyo tare da dakatawa daga tafiyar da take yi.

Siririn murmushi ya sakar mata mai matuƙar ƙayatarwa wadda idan aka yi maka shi dole ka mayar da martani ko kana so ko baka so, dan time ɗin da martanin zai bayyana a saman fuskarka ma ba zaka sani ba sai dai kawai ka ji ka yi. Ita ma kuwa hakance ta faru da ita, sam bata san lokacin da ta dawo mashi da martanin nata siririn murmushin wadda ya kara jefa shi cikin yanayi ba.

"Ki kula sosai my sister, bana son dai mu rabu, amma ki je ni zan je wajen Jaish tun jiya yake nemana ban samu mun haɗu ba". Ya faɗa yana kallon cikin idonta.

"Tom Yah Jawad zan kula sosai". Ta yi maganar tare da juyawa, yanzu tana jin Yah Jawad ɗin nan nata a matsayi na musamman a cikin zuciyarta, haka kawai take jin daɗin ganin fuskarsa musamman idan yana ɗan murmushi. Zuciyarta cike tab da tunanin Yah Rizwan ɗinta ta nufi kofar fita.

Tsareta da kallo Jawad ya yi babu ko kyaftawa, ita kuma tana tafiya tana tunanin zafafan kalamai Rizwan bare ma yadda ya rinƙa yabon kyanta tare da nuna mata ya mace a kanta, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, tana son taga ana nuna mata so ana kuma yabon duk abin da ta yi, ta wannan hanya Rizwan ya yi nasarar sace zuciyarta, kuma a nan ne suka sha banban da Jawad, shi Jawad koda yaushe sai faɗa ya iya yi mata a kan kada ta yi kaza ko idan ta yi kaza sai ya bata punishment, amma shi Rizwan jiya da ta ce mashi zata je wajen Momma da daddare, cikin nutsuwa ya tambayeta da kayan barcin zata fita? Da e ta amsa mashi, ƙasa ya kara yi da murya tare da kara nutsu kafin ya ce mata a'a shi bai yarda ba yana da kishi sosai, ta sanya hijabi har ƙasa, kuma me zata je yi a wajen Momma da daddaren nan?

Gaya mashi ta yi zata je ɗebo turaruka. A sanyayye ya ce mata ta bari sai da safe mana, shi yanzu gaskiya ba zai iya hakura da hiran nan nasu ko na minti ɗaya ba, bai shirya dai'na jin zazzaƙar voice ɗinta ba, ta yi hakuri ko dan soyayyarsu ta bari sai zuwa da safe. Cikin rarrashi da nuna soyayya ya yi mata magana ba kamar yadda Jawad ya ce idan ta sake fitowa da kayan barci sai sun ɓata kuma ya bata punishment ba, wannan shi ne banbancin da yake a tsakaninsu, Rizwan da daɗaɗan kalamai yake amfani wajen hanata yin abu.

Sai da ta kurewa kallonsa da kamar minti biyu sannan ya rufa mata baya, kai tsaye part ɗin Jaish ya nufa.

Ga mamakinsa sai ya ga ɗan uwan nasa sai shirga aikin shiri yake yi alamar zai yi tafiya.

"Travel without telling me, why? And where are you going?". Ya yi maganar tare da zama a gefen gado idanunsa na'a kan ɗan uwan nasa babu ko kyaftawa.

Sai da ya kammala zuba kayayyakin da yake zubawa a cikin haɗaɗɗiyar echolac ɗinsa mai bala'in tsada kafin ya juyo da kallonsa izuwa kan ɗan uwan nasa.

"How do you expect me to tell you that I want to go to somewhere bayan gabaɗaya you're totally useless now, wai ma ni this two day's what's wrong with you? Where are you going that very important better than my issues?......"

Katse shi ya yi da cewa. "Woooo zaka fara halin naka ko Jaish? To wai ni mema na yi ne? Am with you bro, i didn't give anyone my attention or my time, kawai dai lokacin haɗuwarmu mu tattauna a kan issues ɗin naka ne bai yi ba........".

Hararar da Jaish ɗin ya wurga mashi ne yasa ya dakata da yin maganar yana son fahimtar wani abu, shin da gaske ran ɗan uwan nasa ya ɓaci ne? Ko dai wasan da suka saba yi ne?.

"Since day before yesterday nake binka a kan kazo mu yi magana, amma you're always try to show me you're busy, you don't have my time, you're doing something or you go to somewhere, you're not around and some miscellaneous excuse".

Cikin zolaya ya ce da Jaish ɗin. "Meyasa ba zaka tambayi uzurin nawa ba? Do you know maybe I fall in love with someone ne yasa am going up and down since that time you said?".

Cigaba da kwaso wasu abubuwan buƙatarsa da zai buƙata ya yi yana zubawa a cikin echolac ɗin nasa ba tare da ya sake bi ta kan Jawad ɗin ba.

Ganin hakan yasa shi Jawad ɗin ya ce bari ya janyo attention ɗinsa ko baya so, dan haka sai ya ce. "I think fa auren gida ma zan yi, dole na dawo cikin kannena na sami mata, bari mu gani wacece zata ɗan dace dani...."

Still dai Jaish bai kula shi ba, sai harkar gabansa yake yi cikin zafi zafi.

Shiru ya ɗan ɗaga kansa sama irin mai tunanin nan, yana tunanin abin da zai cewa Jaish ɗin.

Can kuma sai ya sauko da kan nasa haɗe da kallonsa a kan ɗan uwan nasa. "I think Jannat zata dace dani ko my blood bro?".

A wani irin hanzarce Jaish ɗin ya ɗago da idanunsa izuwa kan shi. Dariya ce ta so kubce mashi saboda yadda Jaish ɗin ya zaro ido, amma sai ya danne ya ɗagawa Jaish ɗin gera guda alamar ya ne Jannat ɗin ta yi ko?.

"A'a ba Jannat ba, cewa zaka yi dai ka gaji da kallona da mutunci ne kawai a cikin gidan nan, ai gara ka ja mutuncin nawa a kan titi sai ka fi jin daɗi, please get out from my side ma, am very very angry wlh, I don't want to talk to much, idan ka matsa mun kuma Allah you know the rest, i will make you regret". Yana magana yana banka mashi harara da waɗan nan idanun nasa na gado wadda da ka gansu kasan yes yaran Momma ne ba tambaya, dan ita idanun yaranta sun sha banban da na kowa a gidan, sun fi na kowa dara dara a gidan, saboda ita da King ban san waye za'a ce ya fi wani manyan manyan kyawawan ido ba, da yake dai shi da ita duk tushe ɗaya ne sai suka gaji idon daga wajensu King Badeen.

Harararsa Jawad ɗin ma ya fara yi kafin ya ɗaura da cewa. "I can't go anywhere, wai da kake ce mun baka son yin magana sosai ni zaka yi wa iskanci? Kaga malam ni ka bar dukka wannan zance let's talk serious, bar wasa, what's going on? What's wrong with you? I know ban kyauta maka ba, amma ka sani jiya wlh naso zuwa mu yi magana, amma sai na sha'afa gabaɗaya da zancen kace nazo mu yi magana, am sorry about that..."

Wani irin kallo Jaish ɗin ya wurga mashi kafin ya janyo zip ɗin echolac ɗin ya rufeta tare da cewa. "Bani da mahimmanci a gabanka ne yasa ma zaka sha'afa da zancena".

"Kai bro, ni ban san kalarka ba, gaka da saurin fushi, gaka kuma da balai'n kunya, sannan idan ka yi fushi baka sauƙowa da wuri, ayi ta yin magiya amma duk a banza sai time da ka ga dama kake saukowa, ga zuciyar bala'i, kuma a haka wai baka son haɗa ido da mutane saboda kunya, yanzu na gano ba kunya bane ne yake damunka tsantsar rashin kunya ne yake damunka, ni mu bar wasa please, a ƙage nake da na ji me yake damun ɗan uwana, if not zuciyata zata buga". Ya kai maganarsa ta karshen nan cikin serious babu wasa.

Bayan harara babu abin da Jaish ɗin ya bisa da shi, sannan ya zauna a gefensa. In short ya bashi labarin abin da yake faruwa da kuma tafiyar da zai yi, daga karshe ya rufe mashi da cewa kada ya gayawa kowa ya yi wannan tafiya har da Momma, dan ba zai wuce kwana ɗaya ba, gobe zai dawo.

Sosai Jawad ɗin ya yi mashi fatan alkhari tare da addu'oi masu karfi. Cike da son ɗan uwan nasa ya amsa da amin. Daga haka suka shiga hirar duniya har zuwa lokacin da jirgin Jaish ɗin zai tashi. Kafin ya tafi zuwa airport sai da ya je cikin dabara ya ga Momma, sannan ya je wajen King, daga haka ya nufi in da Auta take, dan ba zai iya tafiya ba tare da ya sanyata a cikin idanunsa ba.

Sosai ya tsareta da idanu kamar wadda yake yi mata kallon bankwana, har sai da ta tambaye shi lafiya? A lokacin kuma Gimbiya Chuchu tana kwance ta shige cikin bargo tana waya da Yah Rizwan, Autar tana kwance tana fuskantar kofar shigowa tana latsa wayar Yah Jawad da ya bari a wajensu.

Lafiya lou ya amsa mata da shi kafin ya buɗe mata hannu a kan ta zo. Da sauri ta diro ƙasa daga saman gadon ta tafi ta faɗa jikinsa tana murmushi, duk wannan bidiri da ake yi Chuchun bata da labari, hira ya yi daɗi ga shi tana ƙule a cikin bargo ne yasa sam bata jiyo komai sai kalman yayan nata da yake zazzaga mata tana kara macewa haɗe da narke mashi.

Sosai ya rungumi Autar a jikinsa yana jin tsantsar kaunar ƴar uwar nan tasa, ita kaɗai suke da shi mace a ɗakinsu, suna ji da ita kamar me, da kyar ya iya raba jikinsa da nata sannan ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba. Ta ɗan yi mamakin ganin hakan da ya yi, amma bata kawo komai a ranta ba ta koma cikin ɗakin tare da hayewa gado ta kwanta.

A wannan rana dai Jaish ya bar kasar ba tare da sanin kowa ba sai Jawad ɗin da yake tamkar jinin jikinsa, kun san shakuwar da take a tsakaninsu tun suna yara. Ko airport ma Jawad ɗin ne ya kaisa a sirrance, sun jima sosai a lokacin da suka yi hugged na juna kafin jirgin ya ɗaga, ba yau bane farau na su yi tafiya ba tare da sanin kowa ba, su je su dawo, amma su kansu yau ji suke yi kamar waɗan da zasu yi rabuwa ta har abada.

Jiki ba kwari Jawad ya juya ya dawo gida, duk sai ya ji wani iri, yana tukin mota yana tunanin Jaish ɗin kamar yau suka saba rabuwa.

Yana dawowa gida room ɗinsa ya shige ya yi kwanciyarsa dan ya ɗan huta.

Da misalin karfe 8 na dare gabaɗayansu sun haɗu a saman table a dining room domin cin abinci, Mama dai tana can room nata ta sha allurar barci, saboda azaban da take ji a jikinta na raɗaɗɗin cizon kwarin nan da kuma tsakanin kaikayi da wajen yake yi mata, ga shi babu halin sosawa, hakan yasa da kanta ta buƙaci ayi mata alluran barci ko zata huta da azaban!.

Kasancewar yau Jaish baya nan sai Jawad ya halarci dining room ɗin, ba zai iya cin abinci shi kaɗai ba, dama kun san a tare da Jaish ake kai masu nasu part ɗin ɗaya daga cikinsu, so yau baya nan sai ya ji gara mashi ya fito su haɗu a dining room ɗin ko ya rage kewar ɗan uwan nasa.

Sosai King ya yi mamakin ganinsa a room ɗin, bai yi nauyin bakin tambayarsa yau kuma a nan ya ga damar cin abincin ne? Da e kawai ya amsa mashi. Sosai King ya lura da yadda jikinsa yake a mace, ya yi wani sukuku da shi, nan ma bai yi nauyin bakin tambayarsa ko bashi da lafiya bane yake yi kamar wani mai jin barci?. Sam basu kawo a ransu cewa Jaish baya gidan ba, dan kowa yana da ra'ayin zuwa in da yake so ya ci abinci, sun yi zaton Jaish ɗin yana ɗakinsa.

A'a lafiyarsa lou ya amsa da shi. Shiru King ya kyalesa da nufin idan sun gama cin abinci sai ya tasashi gaba ya gaya mashi me yake damunsa? Dan dai ga damuwa kam nan karara a saman fuskarsa.

Kowa ya hallara a room ɗin ban da Gimbiya Chuchu dake cikin room ɗinta tana ta aikin zuba soyayya da Yah Rizwan, waya suke ta yi ba kakkautawa, ya gaya mata gobe zai biyo su Ramish domin kawai ya zo ya ganta, sai daɗi take ji. Da alama Rizwan ya iya soyayya sosai, sai zuba uban murmushi take yi fuska cike fal da annuri. Allah sarki shi kuma Yah Jawad yana can daning room yana tura abinci kamar dole yana fama da kewarta da kuma tunanin Jaish. Da dai ya gaji sai ya ce da Auta.

"Auta ina Jannat ne?". Ya tambayi in da take ne kuma domin yana da buƙatar ta zo nan ko zai rage kewa da tsananin tunanin ɗan uwan nasa da ya tsaya mashi a rai sosai, bai san meyasa ya damu har haka ba.

"Aunty Chuchu tana ɗakinta". Auta ta bashi amsa.

King ne ya ce. "Meyasa bata fito cin abinci ba?".

Still dai Autar ce ta bashi amsa, domin babu wanda zai iya ce maka yasan halin da Chuchu take ciki a gidan biyun Autar. "Daddy nima ban sani ba, ina ganin kamar bata jin yunwa ne ko kila sai ta yi shirin kwanciya zata sha wani abin mara nauyi kamar shekaran jiya da jiya".

Jawad ne ya ce. "Go and call her for me". Ya yi maganar ba zato ba tsammani yana kawar da kallonsa daga kan Autar suka haɗa ido da King.

Wani irin kallo King ɗin ya jefa mashi wanda ya ɗan sanya shi sakin siririn murmushi. Hannunsa ɗaya ya kai ya ɗan shafa sumar kansa yana cigaba da ɗan murmushi. Hararar wasa King ya wurga mashi yana mai cigaba da kai abinci bakinsa.

Sai kallonsu a sace momma take yi, ta fahimci akwai wani abin dai da King bai gaya mata ba dan gane da Jawad, dan yadda yake binsa da irin wannan kallo akwai wata a ƙasa.

Shi kuma Yah Jawad sai ya kawar da kallonsa daga kan King ɗin ya cigaba da cusa abincinsa cikin baki wanda yake jinsa kamar magani saboda rashin daɗi.

Miƙewa Auta ta yi ta nufi fita daga room ɗin. Ko da ta je manne da waya ta isko Chuchu, sai zuba hira suke yi, tana ta kashe Yah Rizwan da shagwaɓa, soyayya ta yi daɗi tama mance da abinci. Kiranta Autar ta yi sannan ta juya bata tsaya ta jirata ba, dan yunwa take ji Allah ya gani.

"Yah Rizwan daddy na kirana in je in ci abinci, ka bari sai na dawo ko?".

Daga other side ɗin ya amsa mata da. "Bari na zo to na baki a baki ko? Dan bana son ki sha wahala, da akwai yadda zan yi in tauna maki ma sai na tauna maki".

Wani irin sihirtatcen murmushi ta saki kafin ta bashi amsa da. "Kai Yah Rizwan, ai zan ji kunyar su daddy idan ka ce zaka bani abinci a baki, ba zan iya ci ba, har da Akka fa da su Mummy dukka a wajen, kuma sai ka iya bani a baki ba zaka ji kunyarsu ba?".

Nisawa ya ɗan yi. "Wacece kuma Akka? Ina ruwana da ita? Zan dai ɗan ji kunyar Mummy, amma banda daddy".

(Da alama Akka fa dukka jikokinta ne basu kaunarta 😅 kun ji Rizwan da walaƙanci wai wacece kuma Akka😅 ko da yake wannan tsohuwa zama da ita sai irinsu Guyson ne za su iya, wato masu mugu mugun hakuri sosai kenan 😅 babu ruwana dai ni kam kada ace na ce, to ban ce ba.🌝)

Ɗan zaro idanu ta yi na jin ya ce wacece kuma Akka da kuma ba zai ji kunyar daddy ba sai Mummynta.

"Yah Rizwan ni kuma na fi jin kunyar daddy a kan Mummy fa". Ta faɗa tana sauƙowa ƙasa daga saman gadon.

"To bana son gimbiyata ta zauna da yunwa, jeki ki ci abinci ki ƙoshi sosai, hirarmu ba zata kare ba, idan kin dawo zan baki wani labari kin ji ko?".

Da okey ta amsa mashi tana ƙoƙarin katse kirar ta tsinkayo muryar can ƙasa ƙasa yana faɗin. "I love u my sister, ki kula mun da kanki, i will going to miss this your sweet voice wadda idan kina magana yana sanya na rinƙa jin mamar barci zai ɗaukeni, bana........" Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon shigowar Ramish da Bilal cikin room ɗin nasa.

Ita kuwa jin ya dagata yasa ta mayar mashi da kalmar i love u too tare da katse kiran ta nufi waje.

Kai tsaye dining room ta nufa. A saman kujera kusa da Auta ta zauna, ya zama suna fuskantar juna ita da Yah Jawad ɗin, shi kuma daddy da kujerarsa take a gaba yana iya ganin fuskar kowa, a side ɗin kujerarsa ce kawai a wajen.

"Meya hanaki fitowa ki ci abinci?". Jawad ya tareta da wannan tambayar.

Gaisuwa ta fara ɗagawa daddyn nasu, bayan ya amsa ta gaishe Akka sannan su Momma haɗe da Akka, sannan ta bawa Jawad ɗin amsa da tana waya ne, da yake bata iya karya ba, amma bata gaya mashi da waye take yin wayar ba. Bayan ta bashi amsarsa ne ta ɗagawa su Sarina gaisuwa a matsayinsu na sister ɗinta.

Cikin nutsuwa suke cin abinci. Kuyanga Zubaida ta zubawa Chuchun abin da take buƙata. Room ɗin ya yi tsit kamar ba mutane, sai sautin spoon ɗai ɗai zaka ji yana tashi.

A hankali Chuchun ta ɗauki cup mai shake da pina colada zata kai ɗan bakinta, tana jin ra'ayin shansa kaɗan ba dayawa ba.

Bata ƙarisa kai shi bakin nata ba ta ɗan yi ƴar ƙara tare da sakin kofin ya faɗi a saman table ɗin.

A hanzarce gabaɗaya kowa dake saman dining ɗin ya ɗago da kansa tare da kai kallonsa kanta. Auta ta riga kowa tambayarta lafiya me ya sameta?.

Autar bata rufe baki ba King ya jefo nashi tambayar. Nan take kowa ya fara jefo nasa tambayar, sun tsura mata idanu suna jiran amsa.

A hankali ta ɗan ɗago idanunta ta saci kallon Jawad da suke fuskantar juna, ya yi wani yin ƙasa da kai kamar babu shi a room ɗin. Bin in da take kallo da kallo King ya yi, ganin Jawad take kallo yasa ya cigaba da cin abincinsa ya fita shirginsu, dan yasan in ya biye masu ma shi zai ji kunya a banza.

Su Momma sai tambayarta suke yi ta ƙasa yin magana, kowa ya ruɗe yana ta cewa lafiya kuwa? Amma ina ta ƙasa magana.

King ne ya ce. "Wai ku ku rabu da ita mana, Zubaida ki sake zuba mata wani pina colada domin ta sha dan naga shi take ra'ayi".

A hanzarce kuyanga Zubaida ta zo ta fara kwashe wanda ya zube ta gyara wajen, sannan ta zuba mata wani ta turo mata shi gabanta.

Ɗauka ta yi tana ta kallon fuskar yayan nata. Shi kuwa kamar babu shi a wajen.

Tana ƙoƙarin kai cup ɗin bakinta a karo na biyu ya sake yi mata abin da ya yi mata ɗazun yasa ta zubar da wancan pina ɗin, ba tare da ya ɗago ya kalleta ba. Ba komai yake yi mata ba face babbar yatsar kafarsa yake zurowa ta ƙasar table ɗin yana ɗan yi mata kamar tafiyar tsutsa a kafafunta, da yake doguwar riga ce a jikinta, ta ƙasar rigar yake zura kafar tasa yana taɓa mata tata. To da ya yi mata na farko tsoratata ya yi, dan bata yi expect na jin hakan ba, ta tsorata.

Yanzu ma a hankali ya sake zuro kafar tasa ya fara yi mata kamar ɗazun. Still yanzu ma ta tsorita, sai dai bai kai tsoron da ta ji ɗazun ba, ɗan lumshe idanunta ta yi tare da kai cup ɗin ɗan bakinta.

Bata cire cup ɗin daga bakin nata ba ta waro idanun nata a saman fuskarsa, a lokacin shi ma ya zuba mata idanu yana kallonta, wani irin kyau ta yi mashi lokacin da ta lumshe idanun nata, sai ya ji ta gama tafiya da shi mai gabaɗaya, da babu kowa a room ɗin ba abin da zai hana shi rungumota.

Cigaba da yi mata tafiyar tsutsa a kafar tata ya yi yana mai cigaba da kallonta, ita ma tana shan pina ɗinta tana kallonsa tana ɗan murmushi. A hankali ya gangaro da kafar tasa izuwa dai'dai sai tin tata, sannan ya sanya ƴatsun kafafun nasa ya riƙo nata babbar yatsar kafar yana wasa da shi.

Duk abin da suke yi King yana kallonsu, amma ya cigaba da cin abincinsa tamkar bai ga komai ba, tunanin abin da zai yi kawai yake yi a ransa, tunanin kalar hukuncin da zai yanke masu yake yi.

Matse mata babbar yatsar kafar tata ya yi a cikin tsakiyar nashi yatsun. Har sai da ta ɗan yamutse fuska alamar zafi, ɗan turo mashi baki ta yi tare da ajiye cup ɗin pinan nata, kamar zata sanya mashi kukan shagwaɓa.

Ganin hakan yasa ya ɗan sakar mata ƴatsun nata, yana saki ita ma tasa nata wai zata kamo nashin ta matse ya ji idan da daɗi. Amma ina ƴan yatsunta ba za su iya kama na shi ba, ya yi mata girma. Kamar zata yi kuka take binsa da kallo tare da turo baki.

Wani siririn cool murmushi ya sakar mata wanda ya sanyata sauke ajiyar zuciya, sannan ya kashe mata ido ɗaya. Plate ɗin abinci da kuyanga Zubaida ta zuba mata ta jawo ta fara ci tana sakin murmushi, tana jin daɗin kasancewa da Yah Jawad a yanzu, saboda yana sakar mata fuska kuma yana mata wasa sosai, so tana jin daɗin kasancewa a tare da shi sosai da sosai.

Bayan sun kammala cin abincin ne ya janye kafarsa daga kusa da tata, a hankali ya miƙe tsaye. "Jannat ki kawo mun wayata da na baki room ɗina". Yana maganar unexpect again kallonsa ta sauka a kan King, tun ma daddyn nasu bai yi wani yunƙurin ba ya sakar mashi murmushi tare da sa kai da sauri ya wuce.

Sai dai kafin ya fita muryar King ɗin ta daki dodon kunnuwansa da cewa. "Ka sameni a room ɗina yanzu Jawad".

Da okey kawai ya amsa sannan ya fice. Da ɗaiɗai da ɗaiɗai kowa ya watse a room ɗin.

Akka tana shigowa cikin room ɗinta wayarta dake saman bed ya fara ruri. A hanzarce ta ƙarisa ta kai mashi agaji.

Picking ta yi tare da hayewa saman gadon mai gabaɗaya.

Daga can ɓangaren Rizwan ya fara tsantsara mata sallama tare da ɗaga mata gaisuwa.

Sai da ta zage shi kafin ta amsa, wai yau kuma wani munafurcin yasa ya kirata? Dan rabon shi da kiranta tun last year sallah da ya kirata ya yi mata happy sallah, to yanzu kuma gulmar me yasa ya kirata?.

Hakurin ya fara bata tare da rarrashi yana gaya mata aiki ne ya yi mashi yawa. Tatas ta zage shi daga shi har su Ramish ɗin gabaɗaya kafin ta saurare shi, Akka akwai dirama tsohuwar nan.

Cikin zumuɗi ya sanar da ita dalilin kirata, ya kira ne ya sanar da ita ya samu mata kuma ba kowa bace face Chuchu, dan haka ta taya shi kafin ya zo.

Wani irin matuƙa fari tas ɗin farinciki ne ya mamaye mata cikin zuciya. Haƙiƙa ta ji daɗi kuma ta yi murna, amma sai ta ɓoye murnar tata, ta fara zazzaga mashi masifa a kan ai dama tasan yanzu ma buƙatar kansa ne yasa ya kirata, to dan haka ya sani ba zata bashi Chuchu ba, kuma dai yasan ita ce mai zartar da hukuncin a kan komai.

Lallaɓata ya fara yi yana magiya tare da marairace murya, yasan Akka ita ce nan take da iko da su da iyayensu, yasan idan ta bashi Chuchun to fa babu uban da ya isa ya hana, haka zalika idan ta hana shi, wannan dalilin ma yasa ya biyo ta wajenta kai tsaye bai je wajen daddy ba, dan ko ya je ga daddyn ma zai ce mashi sai abin da Akka ta zartar ne, so shiyasa ya fara bi ta wajenta, kuma Mammaiensu ce ta bashi wannan shawara, ta ce kai tsaye ya tunkari Akka, kuma kada ya wani ɓata lokaci wajen jira, ya yi saurin tunkararta ya gaya mata, hakan yasa ya gaya mata ɗin.........

Lallai da gaske Mammie ta shirya raba Jawad da soyayyar Chuchu karfi da ya ji, domin kuwa hanyar da ta biyo mai karfi ne wanda ya fi na Jawad karfi, tun da Rizwan ya gayawa Akka shikenan kuma, Akkar zata tambayi Chuchun tana son yayan nata ne ko bata sonsa, idan har ta amsa da tana son shi fa shikenan babu wanda ya isa ya sa a fasa wannan aure sai mutuwa sai kuma wani ikon na Allah. Ku ma dai kun san Chuchu dai tana son yayan nata, dan haka da e tana son shi zata amsa. Akwai cakwakiya ba kaɗan ba, akwai tashin hankali.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼

ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥

Nutsuwa sosai Leesharh ta yi tana sauraron abin da yake faɗa. Daga yadda yake fitar da word's ɗinsa kai kasan nutsatsen mutun ne mai ji da izza haɗe da class, ba karya jinin King Zuhair yana gudana a jikinsa.

Magana yake yi a kan lallai a cikin daren nan dole zasu yi wannan meeting ɗin, domin gobe da safe za su wuce ƙasar Tunisia, so ya zama dole a daren nan su haɗu, umarni ya baiwa wanda suke yin wayar da shi a kan lallai karfe takwas ya samesu a wani katafaren luxurious guests house ɗinsa. Ba taro ne da zasu yi a ma'aikatarsu, taro ne na team guda ba na gabaɗaya special weapons and tactics ba, manya manyan zakarun gurayen mazan dake cikin Team na Ramish ɗin su sha biyu ne dai'dai, kowanne daga cikinsu kuma yana da yaran aikinsa a karkashinsa, hakan yasa waɗan da suke a ƙarƙashin Ramish ɗin sun fi mutun 200, waɗan nan maza sha biyun sune jiga jigai masu kula da kannar dake cikin team ɗin, su suke karɓar umarni daga wajen Ramish ɗin su zartar wa da na kasa da su ɗin, so haka suke, team, team, suke, sai dai team na Ramish ya fi na kowa shahara a cikin special weapons and tactics, saboda bashi da wasa, duk kuma wanda za su kasance a cikin team ɗinsa to ba karamar horar wa yake sakawa a basu ba, domin kuwa shi baya ɗaukar faɗuwa, burinsa a kullum cin ma nasara, baya wasa da aikinsa, waɗan nan gurayen maza guda sha biyu na cikin team ɗin nasa ba karamar horar da su ya yi ba kafin su kai matsayin da suke kai a yanzu, ba shi da aboki daga waje sai cikin gida, su ne kuma Bilal, Rizwan and Dr Raj, haka zalika bashi da wani kusanci da wani a wajen aiki, duk da ya kasance cewa ƴan team ɗin nasa horonsa ne, amma baya yarda da kowa, dan yasan farautar rayuwarsa ake yi kamar yadda ake farautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana, yasan komai hakan yasa bashi da wani makusanci biyun Bilal, Rizwan and Dr Raj, a waje baya yarda da kowa, kallo da ido kawai ta raba shi da kai.

A ko da yaushe yana yawan zaman meeting da waɗan nan gurayen mazan ƴan cikin team ɗin nan nasa domin kara karfafa team ɗin nasu ya cigaba da kasancewa shi ne na ɗaya a cikin hukumar special weapons and tactics, yana son ya kasance a sahun gaba kullum....... Yo dama jinin King Zuhair jinin Akka ai dole ya zama haka, su fa basu ɗaukar wasa a lamuransu, wai kun manta me Akka ta ce ne a kan jarumta?..........😅

Sosai Leesharh ta tsumaya da sauraron zazzaƙar muryarsa, tana naɗar duk abin da yake faɗa tana kuma jin daɗin yadda yake yin maganar one by one.

Bata bar wajen ba har sai da ta dai'na jin maganarsa alamar ya bar wajen kenan.

Cikin hanzari ta fito daga in da ta laɓe ɗin ta nufi room nata, jikinta sai kerma yake yi kamar wadda ta aikata wani abin rashin gaskiya....... Ko da yake rashin gaskiyar ai ta aikata tun da ta yi wa wani laɓe ta ji abin da yake faɗa.

Tana shiga ta haye saman gadonta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, kirjinta sai bugawa da sauri sauri yake yi. Zuciyarta sai harbawa pat, pat, pat, yake.

Wani irin razana ta yi jin vibrate na wayar dake ƙarƙashin pillownta, dama can a razane take tsabar rashin gaskiya, da wayar ta fara vuuu kuma sai ta kusa rugawa a guje.

Dafe kirjinta ya yi tana furta Hasbunallahu wani'imal wakil cikin rawar murya. A hankali ta kai kallonta kan pillown, jiki a sanyayye ta janyo pillows tare da ɗauko wayar. Da farko kamar ma ba zata ɗauki wayar ba, amma tuna cewa number ɗaya ce take kirarta a wayar kuma wannan number babban barazanace ga rayuwar mahaifinta yasa ta hakura ta janyo wayar.

Wani irin wahalallen yawu ta haɗiye lokacin da idanunta suka sauka a kan wannan number, ji take yi kamar ta maka wayar da ƙasa ko ta haɗiyi zuciya da mutu kawai huta, ta fara gajiya da fargaba da faɗuwar gabar da suke jefata a ciki, idan ta cigaba a haka wlh faduwar gaba ne zai zama sanadiyar rayuwarta.

Picking ta yi tare da kara wayar a kunnanta jiki kamar wadda aka zarewa laka.

Daga other side ɗin aka fara magana cikin sanyin murya. "A'isha na manta ne ban sanar dake wani abin ba, idan kin je wajen walimar nan ki mayar da hankalinki sosai a kan mutane, babu ruwanki da yin magana da kowa, sannan kada ki manta wajen a cike yake tab da camera's sosai".

A tunanin matar yanzu ne Leesharh zata tafi wajen walimar, bata san ita kam har ta je ta dawo ba abinta, zama ya gagareta a wajen walimar saboda rashin gaskiya.

Da kyar ta ɗan iya saita nutsuwarta tare da fara gayawa matar duk abin da ya faru tun daga zuwan ta wajen walimar har izuwa yanzu da take zaune a bakin bed dinta.

One thing about Leesharh yarinyar nan bata karya, kome zaka yi mata in dai zata buɗi baki ta yi magana to gaskiya zata faɗa, sai dai idan tasan gaskiyar bashi da amfani a wajen ko kuma tana tsoron faɗarsa kada ya zame mata illa to a nan kuma shiru zata yi sai dai a kashe ta, amma ba zata taɓa yin karya ba!!.

Wani irin sautin dariya ne ya fito daga ta cikin wayar, a hankali sautin yake tashi, da alama sun ji matuƙar daɗin news da Leesharh ɗin ta basu.

Shiru baiwar Allah ta yi tana sauraron dariyar matar har na tsawon minti ɗaya. Ɗan taɓe baki ta yi tana mamakin ko me ya sanya matar yin dariya? Ta tambayi kanta.

Ta shagala da tunane tunane ta tsinkayo muryar matar tana faɗin. "A'isha Allah ya yi maki albarka, ashe da rabon kin kusa komawa wajen babanki, yau kin gaya mun labari mai daɗi, amma kin tabbatar a guests house ɗinsa ya ce zasu yi zaman?".

Gyaɗa mata kai Leesharh ta yi tamkar tana a gabanta kafin ta ce e ta tabbatar.

"Good! Kenan Ramish zai fita gida kafin karfe takwas na dare, dan shi baya wasa da lokaci, hakan ma dai'dai ne, yanzu dai abin da nake so da ke shi ne, akwai wata magani da zan sanya a kawo maki, ko in ce ki fita ki je ki nemo wacece zata kai wa Ramish abincin dare? Idan kin dawo zan kiraki karfe 6 dai'dai dan na gaya maki a in da zaki ga wannan maganin, abin da nake so da ke lallai lallai ki shammaci mai kai mashi abincin nan ki zuba mashi wannan maganin a cikin cappuccinonsa, dan na san ko bai ci abinci ba tabbas ba zai fita daga gida ba tare da ya sha cappuccino ba, dan haka zai sha maganin kafin ya halarci wannan taron, idan kika yi komai cikin nuna taka tsantsan da kulawa tabbas gobe zan haɗaki da babanki a waya ku gaisa, idan komai ya tafi yadda muka tsara kam ma a cikin daren nan zaki bar gidan, kina barin gidan kuma sai ƙasarku zaki koma....."

Zubur ta miƙe tsaye tare da zaro idanu tana faɗin. "Aunty da gaske zaki haɗani da babana a waya? Kuma da gaske zan koma ƙasarmu?".

Tabbatar mata da hakan matar ta yi kafin ta katse kiran kit. Wani irin farinciki Leesharh ta ji ya rufeta, nan take ta ji kwarin gwiwa, tabbas in dai zata gaisa da mahaifinta a waya to ba shakka yanzu ba sai anjuma ba zata nemo waye zai kai wa Ramish abincin dare.

Lallai ba shakka matan nan sun san lagon Leesharh, sun san da cewa idan suka ce zasu haɗata da babanta to fa zata yi masu abin da suke so cikin sauri, basu zaɓota a kan wannan aiki haka kawai ba sai da suka tabbatar da lallai tana da jajircewa akan abu idan ta sanya kanta, in dai ta ce zata yi abu fa to wlh sai ta yi shi, haka take, sun san zata iya ne yasa suka fara, da sun san ba zata iya ba ba zasu fara wannan aikin da ita ba.

(Ni kuwa na ce tom Leesharh kada dai ki manta Our twin's Obaid and Omaid na Maman Sultan suna nan😌 ki bi dai a sannu.)

Miƙewa ta yi cikin kwarin gwiwa da azamarta har ta ji karfi ya zo mata ta nufi waje, sai murna take yi zata yi magana da babanta, sam bata san illar da abin da zata aikata zai haifar ba. Kasa ta sauko domin neman wacece zata kai mashi abincin dare kuma da wani lokaci zata kai mashi.

Tsabar rashin tsoron irin na yarinyar nan da muradin cin ma burinta karara a saman fuskarta, ba tare da shakkar komai ba ta tinkari kitchen ɗin dake ƙasa kai tsaye abinta, cikin jajircewa take yin komai tare da burin cinma nasara.......... Akwai kura kuwa ba kaɗan ba, kura mai tashi har sararin samaniya ma kuwa. Leesharh fa tana ganin kamar samun gane mai kaiwa Ramish abinci abu ne mai sauki a gareta! Sannan tana gani aiki mai sauki ne ta iya zuba mashi wani abin a cikin abinci ba tare da an gane ba! Ta manta da cewa a Abu Abdussalam empire take. To wai ma me zata zuba mashi? Me amfanin hakan? Kuma da alama so suke ya ci maganin kafin ya fita! Me suke nufi?.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍