Page 2
by @sanazty
SUMAYYA
Wattpad@SaNazdeeyah_
Arewabooks@sanazty
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚
[karamci tushen mu'amula tagari]
```Part 2```
"Sumayya a yanzu kuka ba naki bane, saboda abinda ke cikinki, da kuma samun mafita a kansa, ki bar kuka mu tsaya mu yi dogon tunani."
Ɗago rinannun idanunta tayi ta sauke su akan Amarya tare da faɗin "Iyarmu, na gwammace ace fyaɗe aka min na kuma san anyi, ko kuma ace nice na bada kaina aka lalatani har ciki ya shiga da irin wannan abin. Iyarmu me zan faɗawa ɗan cikina idan yazo duniya? Waye ubansa? Sannan kafin ma na kawo shi duniya me mutane za su faɗa a kaina da abinda ke cikina, na rasa wace irin ƙaddara ce wannan?"
"Ya isa haka kar kiyi saɓo, duk wata ƙaddara daga Allah take wala mai kyau ko marar kyau, Allah baya bacci Sumayya, kuma nayi imani dashi ne zai kawo mana mafita akan wannan."
"Iyarmu ki duba irin gwagwarmayar da aka sha akan Kamal, bana son shi na aure shi Iya, 'yan gidan nan har gani suke Baffa ya fi sona shiyasa ni ya samo min mai kuɗi, aka yi ta zinɗanmu, yanzu gashi auren babu inda yaje, ɓullowar wannan cikin ya saka Kamal sakina bayan ya gama wulaƙantani tare da min gori da kuma kirana da munanan suna, nayi dana sanin auren shi dama ba son shi nake ba, umarnin Baffa kawai na bi."
"Sumayya ki sani shi aure rai ne dashi, duk lokacin daya ƙare dole ya mutu, ki manta komai ki shiga sabuwar rayuwa, kar damuwar nan ta saka miki wani ciwon da za azo ana dana sani"
"Dana sani ai nayi shi ya fi a ƙirga"
"Kuma kin san haramun ne, karɓi kisha fura kafin a gama abinci na san baki ci komai ba."
**** **** ****
Safa da marwa kawai yake a ɗakin ya kasa zama sam. Mommy da ta shigo hannunta riƙe da glass cup ta kalleshi "Dan Allah ka yi haƙuri ka sakawa zuciyarka salama"
Kallonta ya yi tare da sauke ajiyar zuciya kafin ya zauna kan sofa. Itama kusa dashi ta zauna tana miƙa masa abin sha tana faɗin "Zoɓo ne mai sanyi nayi maka, yaji kayan itatuwa, na san za ka ji daɗinsa."
Karɓa ya yi ya kurɓi kaɗan, sannan ya kalleta ya ce "Har yanzu abin nan ɗaure min kai yake"
"Ba fa abin mamaki bane Alhaji, duk abinda aka ce yaran yanzu za suyi to wallahi kar kayi mamakin komai"
"Na yi wa Kamal aure ne dan ya nutsu to itama matar ba nutsatstsiya ba, to wai É—iyar waye nutsatstsua tunda ba a samu a É—iyar Malam ba?"
Shiru ta yi kafin ta ce "Kar fa ka manta kirarin da ake yiwa 'ya'yan Malam ɗin, ɗan malam kaƙi halin Malam, Malam na masallaci kai kana gidan 'yan bori, ai Alhaji ni dama tun ranar dana ga yarinyar naga kamar idanunta a tsaytsaye suke"
"Ban yi tunanin haka daga gurin iyalan Malam Bala ba, mutum ne da ake kwatance dashi wurin ibada da kuma tarbiyya ga ahalinsa, dan hatta almajiransa sun bambanta da sauran almajirai."
"To dama ai dole a cikin 'ya'ya sai an samu zakka, kaima a naka ba ga Kamal É—in ba, amma duk laifin ka ne, domin yarinyar nan sam bata dace dashi ba, da ka bari na aura masa É—iyar Haj Mariya wallahi na tabbatar sai ta saisaita tunaninsa."
"To ni dai for now bani da abin cewa har sai na huce akan abinda ya faru."
****** ***** ******
"Saki?"
"Of course yes saki, mene na faÉ—a a tashin hankali kamar wata 'yarka"
"No ba haka bane Yaya, kawai ban ji daɗi bane da yaushe aka yi bikin naka muna ta murna, ni baƙin cikina ma ban taɓa ganin matar ba kuma ace wai har anyi saki"
"Ganinta ai ba abu bane da zai maka wahala zan iya kai ka gidansu idan ka dawo sai ka ganta tunda akwai amfanin da hakan zai maka"
"No! Ni fa ba wani abu zai min ba, calm down please don't be offended"
Murmushi ya yi yana faɗin "Lallai da alama kayi hankali, kai da baka bayar da haƙuri yau kaine da ba da haƙuri"
"So nima fa Yaya na girma, dan tuni na samu matar aure"
"Wow am so excited 'yar waye?"
"To ka san dai ba zan yi zaɓen da bai dace ba, to na zaɓo mace mai ilmi da kuma aji"
"Oh abin har da 'yar gori"
"No ba haka ba, kawai dai ni ba zan yarda ayi min irin abinda aka maka ba, auren dole fa, haba ai tuni aka daina yayin nan"
Nihal da ta fito daga kitchen zama tayi tana faÉ—in "Yauwa bro dan Allah ka fitar damu outing"
"Lallai ma yarinyar nan" Ya furta yana kallonta.
"Nihal ce wai na fitar dasu outing, seems like ni bani da aikin yi ko kuma na zama driver É—insu ne, kaga let's talk later, bye!" Ya yi hanging wayar yana kallon Nihal.
"Kin san Allah nima akwai inda zan je, dan haka babu inda zan kaiku kima sani"
Ayrah da ta fito a lokacin turus tayi, dan a shirye ta fito tana tunanin zai kaisu kamar yadda Nihal ta faÉ—a mata.
"Yaya dan Allah har mun shir..."
"Ke ba zan kaiku ko ina ba na faÉ—a muku" Yana gama maganar ya É—auki key É—in motarsa ya fice.
"Tofah! Tunda ya saki matarsa ya zama masifaffe fa" Ayrah ta faÉ—a tana zama.
"Dama haka yake ba wani wanda ya canja sa."
Yana driving ya kira number Laila, ta É—aga tare da faÉ—in "Babe naji ka shiru"
"Sorry ban san ma time ya tafi haka ba"
"Ina fata dai ba tunanin tsohuwar matarka ne ya sa ka manta da alƙawarinmu ba"
"Tunaninta kuma? Macen da tayi cikin shege a gidan aurenta, Haba Laila ki daina wannan maganar ma"
"Anyway ni dai na shirya kai kawai nake jira"
"Am on my way, nima ai na matsu mu haÉ—un"
murmushi kawai tayi ta kashe wayar.
Driving ya cigaba da yi yana sauraren waƙoƙinsa masu daɗi na turanci waƙoƙin Ayra star. A bakin layinsu dake cikin lamiɗo crescent ya tsaya sannan ya kirata "Ina jiranki a bakin layi"
"Na yi tunanin za ka ƙaraso ku gaisa dasu Mom"
"Yanzu ai ba a kamal nazo ba, fita fa zamuyi kuma zamu daɗe bamu dawo ba, so kike su hanani aurenki su ce nine ke ɓata ki"
"Ai babu wanda ya san ina wannan harkar kuma har nayi aure ba wanda zai sani, saboda kai kaÉ—ai nake kulawa"
"Babe ina jiranki" Ya yanke kiran.
Bai ɗauki tsawon mintuna da yawa ba sai gashi ta buɗe motar ta shiga. "Babe ina fatan dai ban ɓata maka lokaci ba"
"Never mind" Ya furta yana mata peck a kumatu"
"Baby sarkin zumuÉ—i ina muka nufa yanzu?"
"Gidana"
"Akwai kayan chaji dai ko?"
"Duk abinda kike buƙata an tanada."
Kai tsaye can ya nufa, a farfajiyar gidan ya parker mota ta fito tana ƙara ƙarewa gidan kallo, shi kuma ya ƙarasa ya rufe gate.
"Shiyasa naƙi yarda na ajje maigadi dan bana son sa ido"
"Hakan ma yana da kyau, dan masu gadi a yanzu munafukai ne, amma kuma buÉ—e gate baya maka wuya?"
Saɓarta ya yi, ɗaukar jarirai ya nufi ciki yana faɗin indai ina tare dake Laila ba zai min wuya ba"
"Kamal...!" Ta furta da wata iriyar murya, shi kuma sai daya direta a saman bed sannan ya tsaya yana ƙoƙarin cire kayan jikinshi.
Miƙewa tayi zaune tana kallon ɗakin "Anan ake cin amanata ko?"
Murmushi ya yi lokacin da yake zare belt ɗin trouser ɗinsa yana faɗin "Ai babu wanda ya isa ya sa naci amanarki, tunda na auri Sumayya har muka rabu ban taɓa riƙe ko da yatsarta ba"
"Kai Babe faÉ—i gaskiya"
"Gaskiyar kenan" Ya furta yana hayewa kan gadon.
"Nayi tunanin sai mun fara chaji"
"Nafi so mu fara cikin hayyacinmu, ai yau muna tare har 10 na dare"
Ya faɗa yana ƙoƙarin zage zip ɗin rigarta.
***** ***** *****
"Sumayya! Sumayya!! Sumayya!!!" Amarya ta furta tana jijjigata, sai dai gani take tana ta wani abu kamar mai farfaɗiya. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, mene ke damunki Sumayya?" Da sauri ta miƙe tare da fita tsakar gidan, ganin za tayi hanyar waje ya saka Hadiza faɗin "Lafiya kuwa? Za ki fita babu ko mayafi bayan kin san yamma ce Malam na karatu da almajirai a ƙofar gida"
"Sumayya ce take wani abu kamar bata cikin hayyacinta" Ta furta a kiÉ—ime.
"To kuma shi ne hakan zai saka ki fita a yadda kike, ke ko irin karar nan ta 'ya'yan fari baki yi" Cewar Inna Dije da ta fito daga É—akinta.
"Yo ina za tayi ai babu kunya a É—iyar bahaushe" Hadiza ta amshe da faÉ—in haka.
"A'a Hadiza kar kuma ki zagi Hausawa dan hausawan ma ai kala-kala ne ni dai ina da kunya"
Ita dai Amarya da sauri ta koma ciki, dan yaran gidan duk basu nan suna waje tare da Malam. Kallon Sumayya tayi wanda tana kwance kamar gawa sai dai kuma a yanzu babu wannan jijjigar da take. Da sauri ta zari hijab ta fice.
"Ita kuma wannan ina za taje?"Cewar Iya Zulai da ta fito daga bayi.
"Wa ya sani mata"
Da sauri Zulai ta tare ƙofar tare da faɗin "Babu inda za kije muddin ba karatu aka gama ba"
"Wallahi ke baki isa kin hanani fita ba, dan kun ga ina ƙyaleku to a wannan gaɓar ba zan yarda ba"
"Mene ba za ki yarda ba? Irin tarbiyyar taki ce fa 'yarki ta É—auka, a garin yawan kwalta har da ribar ciki ta samu"
"Kul Hadiza, ina ganin mutuncinki"
"To ki daina gani mana ki ga in abin zai dameni, an faÉ—a yawan dandi take shiyasa ma a baya ta kasa auruwa, yaro yazo aka yi masa rufa-rufa ya gano ya sako 'yar banza"
"Waye banza ni ko ita?"
Jin maganar Malam ya saka suka kalli gurin gabaÉ—aya. Hadiza ta É—an sosa kai, ita kuwa Inna Dije da sauri ta fara tattare kaya kamar mai gyara tsakar gidan.
"Tun daga waje nake jiyo hayaniyarku ina karatu, wai meyasa ba zaku taɓa zaman lafiya ba?"
"Malam zaman lafiya fa baka so ayi shi ba, dan babu yadda za ai ka fifita 'ya'yan Amarya kayi tunanin zaman lafiya, ko dan ai ga ƙarshen sangarta mun gani" Cewar Iya Zulai.
"Ke Zulai ki kiyayeni, kibar ganin muna da tarin 'ya'ya da jikoki dake kiyi tunanin ba zan iya hukuntaki ba, ba zan lamunci cin kashi ba"
"Tunda an taɓo matar so ai zaka ce haka, a kaf tarihin gidan nan duk yawan 'ya'yanka ba a taɓa samun wanda ya ɗauko abin kunya ba sai a tsatson Amarya, ta ja maka zagi har mu kishiyoyinta bamu tsira ba" Tana gama faɗa ta wuce rai a ɓace.
"Amarya lafiya?"
"Malam Sumayya ce ke wani irin abu"
"Tana ina?"
"Tana ɗaki" Da sauri suka nufi ɗakin, ya taɓata yaga tana numfashi amma kuma ba bacci take ba. Addu'o'i ya yi sosai a ruwa ya bayar aka bata sannan ya ce Amarya ta shafa mata a jiki. Sai da ta gama sannan suka ga kuma ta buɗe ido, sai kuma kuka.
"Sumayya kiyi haƙuri babu wanda yafi karfin ƙaddara, na gamsu da bayanan da kika mana akan cikin nan, kuma muna ta addu'a koma waye uban yaron zai bayyana da iznin Allah, kiyi haƙuri kin ji"
Shiru amarya tayi kafin ta ce "Malam ina da shawara idan ba zaka damu ba"
"To ina jin ki"
"Malam nace me zai hana na kai Sumayya can Katsina gidan ƙanwata ta haihu acan, ina ganin kamar hakan zai fi mata samun sauƙin abin, tunda ka ga acan babu wanda ma zai mata sababi bare har taji ciwon abin"
"To shawarar ki akan Sumayya abu ne mai kyau, amma kuma gaskiya bana so taje gurin danginki, dan abu idan aka ce dangi zai zama magana, amma dai zan yi magana da Yayanta taje can legas har zuwa ta haihu"
"Legas kuma Malam"
"Eh nan dai nake ganin sai yafi ai"
"Sai naga kamar in Legas ne ta mana nisa"
"To inda aure ne ya kai ta nan ace me? Hakan dai za ayi dan shi ne kawai mafita a garemu da ita baki É—aya, in ta haihu sai ta dawo"
Shiru Amarya tayi duk da bata so amma kuma babu yadda za ai tayi masa musu tunda ita ta fara kawo shawarar, kuma tana so Sumayya ta É—an manta wasu abubuwan, ta san muddin tana wannan gidan ba zata manta ba.
Bayan Kwana Biyu
Tana kwance akan gadon Amarya, hannunta riƙe da carbi tana ja, sai hawaye da ya yi mata dafifi, dan in dai idanunta biyu sai tayi hawaye, shiyasa kullum idanunta ja suke, kasancewarta fara sol, yanzu kuma kullum cikin kuka take ya saka fuskarta ta ɗan yi ja.
Ji tayi an dafa ta, ta É—ago kai a hankali.
"Sumayya wai sai yaushe hawayen ki zai bar zuba? Ko so kike sai kin saka wa kanki wani ciwo?"
"Iyarmu..." Sai kuma ta kasa ƙarasa faɗar saboda yadda kuka ke ƙoƙarin kubce mata. "Mu rungume ƙaddararmu Sumayya" Ta faɗa tana goge mata hawaye.
"Ki kwantar da hankalinki dan Allah"
"Iyarmu dana fita gori suke min"
"Ki bar su ai Allah baya bacci, ki manta komai kin kusa bar musu gidan ma gabaÉ—aya."
"Ina zan je?" Ta tambaya da dasashshiyar murya.
"Babanku ya ce zai yi magana da Saminu za ki je can gidansa ki ƙarasa idda sannan kuma ki haihu acan"
"A'a Iyarmu ba zan iya tafiya mai nisa na barku ba" Ta furta tana hawaye.
"Sumayya dole ce ta saka, wannan ita kaÉ—ai ce hanyar da za a bi wajen ganin an magance damuwarki, bamu so wani ciwo ya riske ki"
Hannu ta saka tana goge mata sabbin hawayen da suka fara zubo mata.
Sallamar Maryam ce ta dakatar da Amarya, ta amsa mata sannan ta shigo.
"Iya ina wuni"
"Lafiya lau Maryam ya maigidan naki da yara"
"Duk lafiya"
Zama tayi kusa da Sumayya tana faÉ—in "Jiya fa sai dana miki nasiha wato ba za ki bar kukan nan ba ko"
"Wataƙila taji naki maganar amma ni taƙi jin tawa" Amarya ta faɗa tana miƙewa "Tunda kin shigo bari in fita in ƙarasa aiki"
"Laaa Iya bari nazo na kama miki"
"Haba kisha zamanki Maryam, gata nan ki rarrasheta"
"Atika bata nan?"
"Suna can islamiyya hadda ake yanzu"
"Masha Allah, Allah ya taimaka"
"Amin."
Amarya na fita Maryam ta kalli Sumayya "Ya kamata ki daina kukan nan, dan ba shi ne mafita ba"
"Maryam ba za ki gane, har yanzu ina tunani akan wanda ya yi min ciki, cikin jikina ya zubar da martabar gidan nan, duk sauran da suke da tarbiyya yanzu duk zaginmu ake, Maryam wai ba ayi min fyaɗe ba sai da nayi aure, auren dama ɗan ɗosane nake saboda Kamal sam baya ƙaunata to kuma ga wannan abin daya faru"
"Gaskiya akwai É—aure kai abin, taya haka ta faru? Amma ko a musulunci fa É—a na mijinki ne"
"Taya? Bamu taɓa haɗa shimfiɗa ba tunda muka yi aure"
"To waye zai shigo ya miki fyaÉ—e? Cikin aljani dai ba zai bayyana a jikinki ba"
"Shiyasa mutane da dama gani suke ƙarya na faɗa, ni nayi iskanci na samu ciki, Maryam wallahi ko ƙarfe ɗaya na dare Kamal zai kai bai dawo ba bana taɓa kwanciya idan bai dawo ba, saboda ni tsoro ma nake duk da ana barin wuta, tunda aka kaini ban taɓa ganin an ɗauke wuta ba. Akwai ranar da sai asuba ya dawo wallahi haka na kwana zaune. Kuma ko ya dawo sai na rufe ɗakina da mukulli nake bacci"
"Cab, dama mai fitar dake sai Allah, tunda yana fita yawonsa haka zai ce in ya fita kema fita kike"
Hannu ta saka ta goge hawaye.
"Gaskiya dole akwai ranar da aka samu wani ya shigo baki sani ba ya gusar miki da hankali tare da amfani dake."
Kai ta girgiza tare da faɗin "Ni dai na san haka bata taɓa faruwa dani ba, dan yawanci ma baccin rana ne ban rufe ɗaki kuma shima sai na tabbatar yana nan nake baccin saboda tsoro, sannan ba shigowa ɗakina yake ba kuma kin san dai bani da nauyin bacci."
"Yanzu dai mene mafita?"
"Maryam na fi so cikin nan ya zube ko na samu salama, amma bana so kowa ya sani dan na san ba za a barni ba"
"Kin san ana cin kuÉ—i wajen zubar da ciki"
"Ina tunanin akwai dubu ashirin a gurina"
"To yanzu ki shirya gobe muje asibiti"
"Gaskiya ba gobe ba, kin san kafin na fita wani aiki ne, amma ranar juma'a Baffa da wuri yake fita sai muje"
"To shi kenan Allah ya kaimu"
"Amin ya rabbi"
Sumayya ta ɗan samu sauƙi sosai ganin sun samowa kansu mafita.
#Share fi sabilillah
SaNaz_deeyah🌸