Page 4
by @sanazty
SUMAYYA
Wattpad@SaNazdeeyah_
Arewabooks@sanazty
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[tushen mu'amula tagari]
```Page 4```
"Kece?" Ya furta da mamaki.
"Ni ce wa?" Hafsat ta furta da mamaki itama a fuskarta, sai da tayi magana kawai ya gane Hafsat ce, amma a farko gabaɗaya gizo tayi masa da Sumayya. Murmushin yaƙe ya yi ya ce "Gabaɗaya kin shammace ni Hafsat wai dama kece kika ce ace min baƙuwa ce"
"Eh mana ai so nake na saka ka a zulumi"
"Zulumin me? Sai kace wani mara gaskiya" Ya ƙarasa maganar yana zama a ɗaya daga cikin kujerun parlourn.
Hafsat cousin sister ɗinsu ce, ɗiyar ƙanin mahaifinsu, ita a gidan kakanninsu ta taso ita da Sadeeq, kuma tun tashinta take ƙaunarsa sai dai bata taɓa nuna masa hakan ba, duba da bai taɓa nuna mata wata alama ta yana sonta ba ita ma sai ta fawwalawa Allah komai.
Kallon Nihal ya yi sannan ya ce "Wato har dake za a haɗa a tsorata ni ko?"
Murmushi tayi tare da faɗin "Am very sorry Yaya, wallahi Aunty Hafsat ce ta ce nace ɓaƙuwa ce"
"Kun kyauta ai"
Dukkamsu dariya suka yi, kafin Nihal ɗin ta miƙe ta bar parlourn.
"Ai fushi nake da kai Sadeeq"
"Na san laifina amma ayi min afuwa"
"Ni ba zanyi ba, wai har ka diro ƙasar amma sai a family group zan ji, wannan wace irin ƙiyayya ce, dan ban faɗawa Goggo ba kaima ka san da sai ranka ya ɓaci yadda take ji dani"
"Na sani, amma kiyi haƙuri ina so nayi suprising ɗinku ne, kuma bana son ku wahalar da kanku wurin haɗa min liyafa na dawowa"
"Ai shiyasa naƙi zuwa tun lokacin daka dawo, amma still baka nemeni ba" Ta furta da muryar shagwaɓa.
"Ai na bada haƙuri"
"Ni hakan bai wadatar dani ba"
"To me ake so nayi wanda zan wanke kaina"
Shiru ta ɗanyi kafin ta ce "Ka bari I'll think about it, dan dole ayi maka hukunci mai tsauri"
"Indai ba na abinci bane it's normal ai"
"Kar fa kasa na haɗa dashi"
Murmushi ya yi yana haɗe hannu alamar roƙo.
Da mamaki ta hau kan gadon ta zauna tare da faɗin "Ayrah kukan mene kike?"
Hannu Ayrah ta saka tana goge hawaye tare da jan majina. "Babu komai"
"Ai ba zai yuwu kice babu komai ba, ki faɗa min kinji" Nihal ta faɗa tana kallonta. Kuka ta fashe dashi a fili, ta rungume Nihal ɗin ta cigaba da rerawa. Tun Nihal ɗin na ganin abin kamar na hankali har tazo ta daina. Janye Ayrah tayi daga jikinta ta ce "Haba da Allah tun ɗazu sai rarrashinki nake kinƙi kiyi shiru, ke matsalata dake kafiya wallahi" Ayrah dai bata ce komai ba sai hawaye da jan majina da ta cigaba da yi.
Sauka Nihal tayi daga gadon ta ce "Idan kin gama kukan daɗin na dawo ɗakin" Ta fita tare da jan ƙofar.
***** *****
Maryam ta kalleta cike da tausayawa ta ce "Kenan sai kin haife cikin?" Tayi maganar ƙasa-ƙasa.
"Wai ba, ni wallahi ban san ya zanyi ba Maryam, wallahi na tsani cikin jikina, tsana mafi muni"
"To yanzu ya za kiyi? Dole sai haƙuri, in kuma za ki iya gwada na gargajiya to ki gwada"
"Ya yake shi?"
"Ruwan gishiri tsurarsa za ki sha, shima fa sha yanzu magani yanzu ne"
"Aikam bari nayi"
"A'a ki bari sai na tafi dai"
Har Sumayya za tayi magana Amarya ta shigo, dan haka taja baki tayi shiru. Dukkansu sauke kai ƙasa suka yi. Ita kuma Amarya ta kai dubanta kan gado inda Atika ke kwance tana sharar bacci. "Wannan bacci na Atika har dana rashin son zuwa makaranta." Murmushin yaƙe Sumayya ta yi tare da faɗin "Karatun fa har yana son fin ƙwalwarta"
"Waya faɗa miki karatu yana fin ƙwalwa?"
"Iyarmu ita Atika da ban ce fa, Allah tana ƙoƙari sosai da take gane abubuwan"
"To karta gane ma mana, ai ta san halin Malam sarai"
Sai lokacin Maryam ta motsa tare da faɗin "Iyarmu ni bari na tafi gida, Sumayya insha Allah zan shigo gobe tunda jibin da wuri za ki tafi."
"To Maryam har za ki wuce?"
"Eh Iyarmu"
"To ki gaishe min da yaran na gode sosai zuwanki yake saka Sumayya itama ta ɗan samu ta saki rai"
Murmushi Maryam tayi, ita kuma Sumayya ta tashi dan ta taka mata.
"Taƙi zaman aure ku haɗata da karuwai 'yan zamani" Bilki dake shara dai-dai saitin ɗakinsu take wannan waƙar ganin fitowar Sumayya da Maryam.
"Wannan ba ɗiyar Anti Hadiza bace?"
"Itace" Sumayya ta faɗa a sanyaye.
"Ki ga waƙar habaici fa da take, idan nice ke wallahi sai na kwakwkwaɗa mata mari, kin bata wajen shekaru biyar fa"
"Ki rabu dasu iyayensu ke yi a gurinsu suka gani" Jin haka ya saka Bilki tasowa a fusace "Ka da ki yarda, karki soma zagin uwata dan ba ƙyaleki zan yi"
"Wallahi ki dirji bakin duk wacce ta zagi Umma" Ƙarama dake wanke 'yan kayanta a gefe ta faɗa.
"Ke ashe dama baki da kunya?" Maryam ta furta tana kallon Bilki.
"Idan ana sayar da ita a gidanku ki bani bashi ko alakoro"
"Ke ni ba Sumayya bace, wallahi ki bar gani gidanku nazo, zan ladabtar dake ne idan baki san yanda ake girmama na gaba ba, to ni zan koya miki"
"Oh Allah? To bismillah" Ta furta tana murguɗa baki. Jin haka ya saka Maryam fusata, tana ƙoƙarin damƙo Bilki, Sumayya tayi saurin riƙeta "Haba ba girmanki bane ki tsaya faɗa da yarinyar nan"
"Da kin bari na koya mata hankali ai."
"Mene ke faruwa anan?" Inna Dije ta furta tana fitowa daga ɗakinta.
"Wai kawai dan ina waƙata shi ne ta saka ƙawarta ta bugeni." Bilki ta furta a fusace. Daga Maryam har Sumayya sakin baki kawai suka yi.
"Su buge ki kuma akan me?"
"Akan tayi mana rashin kunya" Maryam ma ta faɗa a fusace.
"To gata nan bugarta in gani" Inna Dije ta faɗa a fusace. Ita kuwa Maryam jin haka ya saka ta damƙo Bilki ta kai ƙasa ta fara duka, ganin haka ya saka Sumayya ƙoƙarin ƙwaceta, a haka dai har wasu almajiran Malam da suka jiyo ihun Bilkin suka shigo suka ƙwaceta da ƙyar a hannun Maryam.
Few Minutes Later
Dukkansu suna zaune a tsakar gidan, sun taru guri ɗaya, matan da 'ya'yan gabaɗaya. Malam na zaune bisa kujera, ya ciza sannan ya furzar, ya kallesu ɗaya bayan ɗaya kafin ya fara magana "A kullum godiya nake ga ubangiji daya bani ikon hayayyafa, kuma a cikin 'ya'yana babu wani wanda ya taɓa abin kunya"
"Ada kenan" Inna Dije ta furta ƙasa-ƙasa.
"Waye ya ce ada kenan?" Shiru kowa ya yi.
"Tambaya nake waye ya yi maganar nan, ku faɗa ko kuma na hukuntaku gabaɗaya"
"Malam Dije ce" Hadiza ta faɗa tana taɓe baki.
Kai ya gyaɗa sannan ya cigaba da faɗin "Duk abinda ko wanne yake a cikinku ina kallo kawai nayi shiru nake dan gudun kar na ɓata muku, amma sai na fahimci ku sam hakan bai muku ba, kullum kune faɗa kamar kaji, yanda ka san a gidan nan ne kaɗai aka haɗa mata sama da biyu, wannan wace irin rayuwace? Ko Sumayya dana ce zan kai legas ba fa dan kun fi ƙarfina bane, kawai bana son shiga sabgar mata shiyasa a lokuta da dama nake ɗaga ƙafa, to amma yanzu dole zan kafa sharuɗɗa kuma ya zama wajibi ko wanne a cikinku ya bi. Na farko bana son sake jin wani faɗa ko tashin hankali, idan kun haɗa kai ni nafi ƙaunar haka idan kuwa kuka ƙi haɗa kai to kowa ya yi sabgarsa amma ban son jin hayagaga idan kuwa tayi yawa zan ɗau hukunci, sannan ku kuma ƙanana dole ku girmama yayunku suma manyan su kama girmansu, masu aure ku sanar musu dan a cikinsu ma akwai wanda sam basu son zaman lafiya, kuna ganin ina taraku bana ɗaukar mataki kullum shiyasa kuke abinda kuke so kuna ganin kun hayayyafa ba zan iya rabuwa daku ba ko? To yau zan tabbatar muku ku kuma tabbatar ba wasa nake ba." Ya kalli Inna Dije ya ce "Dije, kije na sakeki saki ɗaya."
Gabaɗaya kowa ya girgiza da jin hukuncin Malam, ita kuma a kiɗime ta miƙe tsaye "Yanzu Malam akan na faɗi gaskiya shi ne zaka sakeni saboda na taɓa 'yar so ko?"
"Na daɗe da sanin irin fitintinun da kike jawo min cikin gidan nan, koma me za ki faɗa ki faɗa amma ki tattara ki bar min gida, idan kin gyara halinki na dawo dake"
"Ba zan dawo ba, me zan dawo inyi a gidan nan,wace tsiyar ake bayarwa ban da wahala da mutum ke kwasa, daɗinta ma 'ya'yana nada arziƙi ba zan rasa matsugunni ba. Kuma wallahi indai zaka riƙa fifiko to yanzu ka fara ganin ɓarna"
"Ɓarna ta ƙare a kanki, tunda ke kullum bakinki baya faɗar alkhairi"
"Ai ko ya faɗa ba gani za kayi ba, tunda ba daga matar so da 'ya'yan so ya fito ba, kuma gaskiya ce dole mu faɗa, babu ɗan iska babu ɗan shaye-shaye a gidan nan amma a yanzu gashi an kwaso cikin shege an kawo za a haife maka, gaskiyar da baka so dole a faɗa, abin kunya dai an gama zabgashi"
Bai ƙara tankata ba, haka gidan babu wanda ya kulata tayi ta sababinta.
Dafe goshi tayi gami da sauke ajiyar zuciya "Iyarmu sam ban so wannan abin ya faru ba, meyasa Baffa zai ɗauki zafi da yawa haka, shi kenan yanzu za a ƙara tsanarmu a gidan nan."
"Yo dama waye yake ƙaunarmu? Wallahi duk munafukai ne"
"Kul Atika, kar na ƙara jin wannan furucin daga bakinki."
Turo baki tayi sannan ta haye gado tana faɗin "Iyarmu wai mutum ba zai faɗi gaskiya ba"
"To sarkin fushi maida wuƙar" Sumayya ta furta da sigar rarrashi duk da a cikin damuwa take.
****** ****** *******
"Babu mai sona a gidan nan" Ta furta tana goge hawayen idanunta wanda basu bar zuba ba. Sadeeq ya sauke numfashi yana kallonta "Tun ɗazu fa aka ce min kina wannan kukan awa nawa kenan, ya isa please wai ma mene aka miki?" Bata faɗa ba illa hawaye kawai da take ta faman gogewa.
"Ayrah ko dai kukan daɗi kike kamar yadda Nihal ta faɗa?"
"Yaya Sadeeq!" Ta ambaci sunan a hankali
"Ina jinki Ayrah"
"Yaya Sadeeq kowa baya sona a gidan nan, anfi ƙaunar Nihal saboda tana da ƙoƙari, Yaya ni brain ɗina ne a haka kuma ina dagewa inci bana faɗuwa exams sai dai bana samun marks ɗin da suka kai nata shiyasa"
"Meyasa za ki kawo haka a ranki? Duk muna sonki Ayrah kuma dake da Nihal baku da wani bambanci ki daina doubting kin ji, we all loves you babu wani fifiko"
Kai ta gyaɗa, ya saka hannu yana share mata hawaye tare da faɗin "Ki shirya anjima mu fita ki rakani unguwa hakan zai sa ki ɗan samu relief ko"
"Okay, thanks a lot Yaya"
"It's alright."
***** *****
Jin cikinta tayi ya hargitse tamkar ana niƙe hanjinta, ta miƙe tana ƙoƙarin shiga bayi amma sam ta kasa, a gurin ta zube tana murƙususu, gabaɗaya jikinta ya ɗauki rawa, taji wani abu na bin ƙafarta wanda ta tabbatar jini ne. "Wayyo Allah na shiga uku" Shi ne abinda ta furta tana riƙe cikinta a dai-dai lokacin Amarya ta shigo ɗakin. "Sumayya, subhanallahi me nake gani haka?"
"Iyarmu zan mutu dan Allah ki riƙeni cikina zai fashe Iya...." Bata ma iya ƙarasawa ba saboda yadda murɗawa ta tsayar da furucinta. "Wai mene ke faruwa haka, ba dai ɓari bane, innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
Daga tsakar gida Zulai ta miƙe, Hadiza ta kalleta tare da faɗin "Ba dai shiga ɗakin za kiyi ba?"
"Shiga zan yi mana, ni ce babba a gidan nan yanzu wani abu na faruwa za a ce laifina ne, kuma wannan salatin da ƙaran ai bana lafiya bane"
"To ni dai ba zani ba, dan ina gudun sharrin kishiya, akansu aka saki Dije fa, ai su ɗin abin tsoro ne" Bata ƙara tankata ba kawai ta wuce.
"Mene ke faruwa a gidan nan?"
"Sumayya ce take ta zubda ruwa na rasa me ke faruwa" "Gashi kuma Malam baya nan"
Ajiyar zuciya Amarya ta sauke tana kallon Sumayyar da take ta murƙususu. "To ina Atika a kirata a kirawo Habi Unguwar Zoma" "Atika ban san ina tayi ba" Amarya tayi maganar tana goge hawaye.
"Kin ga irin abin, ya za ki bar ƙaramar yarinya kamar Atika tana fita ba tare da kin san inda take ba" "Hadiza ta aiki Rabi shi ne ta ce Atika ta rakata."
"To yanzu ya za ayi?"
"Ko za ki zauna min da Sumayya dan Allah sai inje in dubo Habi?"
"Gaskiya ba zan iya ba, abu ya faru ko ta mace ace ni ce" Tana gama faɗa ta fita.
Ganin babu sarki sai Allah ya saka Amarya miƙewa da sauri ta ɗauki hijab ta zira sannan ta fita kiran Habi da kanta.
*Few Minutes Later*
Habi ta ɗago ta kalleta ta ce "Gaskiya na kasa gane wane ruwa ne yake fita haka a jikinta, kuma ba ɓari bane, akwai buƙatar a kaita asibiti fa, mu unguwar zoma haihuwa ce kawai muke iya karɓa amma akwai abinda dole sai an dangana da asibiti."
"Kin san gidan nan ba a bari akai asibiti, idan nace zan ɗauki Sumayya na kaita asibiti wallahi ba zamu kwashe ta daɗi da Malam"
"To Basira haka za ki barta kina kallonta, da ta mutu ai gara ki karya dokar gidan ko?"
"Ina ga dai gara a bari ya dawo ko rubutun ne ya mata"
"Ina ya tafi?"
"Yaje gona"
"Kin ga dawowarsa sai yamma kenan, ni dai shawara na baki, kalli yadda yarinyar nan ta fara galabaita, haba Amarya zaki bi doka ne ki kashe 'yarki"
Shiru Amarya tayi, ta kalli Sumayya da taga tana ta kakkafa tana wani irin abu da gani bata cikin hayyacinta ma.
"Shi kenan, bari na ɗauki kuɗin da nake tarin bikin Atika sai a kaita asibitin"
"Ya dai fi, sai na taimaka miki kuje ko"
"Na gode"
"Yawwa saka mata hijabi bari na taro adaidaita" Ta furta sannan ta fita da sauri.
"Amarya ina zakije ne da ita haka?"
Kallon Hadiza tayi kamar za ta mata magana sai kuma ta fasa. "Wallahi karki kuskura kice za ki ɗauki Sumayya zuwa asibiti dan naga abinda kike ƙoƙarin yi kenan"
Habi kallonta tayi sannan ta ce "Ke kiji tsoron Allah, yanzu idan 'yarki ce za ki bari ta mutu kina kallo?"
"Ni ai ba za a samu wanda zai kwaso min abin kunya ba, sannan ni ban ma yarda cewa asibiti za su iya yi min wani abu ba, ina fatan kin gane"
Murmushi tayi sannan ta ce "Wannan matsalarki ce" Tana gama faɗa suka wuce da Sumayya suka saka ta a mota.
Hospital
Amarya na tsaye a ƙofar emergency, ita kuma Habi na zaune a ɗaya daga cikin kujerun dake gefe. Amarya kallon asibitin kawai take yadda mutane ke shige da fice, tunda take bata taɓa zuwa ba, karo na farko a rayuwarta shiyasa ya zame mata sabon abu. Fitowar Likita ce ta saka ta mayar da kallonta gareshi. "Likita mene yake faruwa?"
"Ko zaku iya biyoni office?"
"Mene hakan?"
Habi ce tayi saurin tashi ta ce "To Likita" Sannan ta kalli Amarya ta ce "Basira muje, Office wani gurine da aka keɓancewa Likitocin don ganawa da mararsa lafiya"
"To ina Sumayya tana can ne?"
"A'a zai mana bayani ne akan abinda ke damunta"
"To" Ta furta sannan suka bi bayan Likita.
Suna zaune shiru a office, ita kuma Amarya sai kalle-kalle take.
"Gaskiya sai dai kuyi haƙuri amma yarinyarku ta samu matsala sosai"
"Wace matsala kenan?" Amarya ta faɗa cikin tashin hankali.
*** for your business advert✍️
SaNazdeeyah🌸_