RANA ZAFI

Chapter 7

by @khadijagamboali951

"Zainab ki share hawayen ki na miki alƙawari zan tabbatar na tsai da wannan hawayen da ƙuna da zafinsu yake azabtar da rayuwarki, zan sanya ki a inuwar da sam babu rana acikinta,zan mantar dake wani abun wai shi RANA ZAFI,zan tabbatar da Kabiru ya rubuta takarda ya baki"

Hawayen idanunta ne ya sake ninkuwa saboda tuna irin shamakin dake tsakanin su, tana jin dama zata ga wannan ranar da ko iya wannan ranar ta gani ta cika da ko tabbas ruhinta zai samu salama, gashi har yanzu ta gaza sake kallon kyakykyawar fuskarsa wadda a da ta tilastawa kanta da nisanta ta da sake kallonta, murmushi tai mai ciwo kafin tace dashi

"Da soyayyarka na rayu kuma da ita zan mutu a cikin zuciyata ina fatan zamu sake nisantar juna a karo na biyu ya sadeeq, har yanzu ni da kai akwai shamaki" baki ya buɗe zai yi magana ya tsinkayi muryar kilakin fari tana faɗin.

"To baban soyayya hajiya dai najira don naga da alama a wannan karon za'a tsallake maganar uwa ko kuma abiyo hanyar da ta dace, don da kabiyo hanyar da ta dace ai fa da yanzu ba mamaki sai dai muji ku a hotel ɗin Abuja ko kuma a wata ƙasar ma"

"Wa'iyazubillah" sadeeq ya faɗa lokacin da yake fita.

Baki ta taɓe tana faɗin "zama ka dawo hanya ne. oh kinga ina ta surutu ko ya jiki ban miki ba, ya jikin?, to Allah ya sauwaƙe, bara inje in dawo sannan kin ɗan wartsake"

Ko kallonta ba tai ba duk da cewar tana son taga shin ta canja ko ko tana nan yadda ta santa, amma tasan ko bata kalli fuskarta ba hali yana nan, kanta ta ƙarewa kallo kafin tace

"Ya Allah kaine kasan halin da nake ciki kuma kai ka ƙaddara hakan a rayuwata, ya Allah kasa bani da ƙaddarar zama kilaki ko da ko wuyar rashin aikata hakan zata kashe ni...

"Ai ko da alama kwananki ya kusa ƙarewa dan wallahi yadda ake shan gashi a damunarnan, kin kwana da ɗan ɗagwas ɗimma gari ya waye kuna zare ido bare kin aje kadarar ki, to wa zai baki kwabonsa

Kinga ma dai ba wannan ba takardar sallama na ƙarɓo in ya so sai muje gida a gargasaki, tunda kinga ance aminiyar uwa uwace don ko jummai uwar daba na nan dolene in mata kara bare bata nan"

zuciyarta fes don ko bakomai taci naira dubu hamsin ɗin da Alhaji Ashir ya bata cikin abinda bai fi daƙiƙa uku ba, nan da nan ko ta fara shirya 'yan tarkace da ta gani agurin, sai data haɗa tsaf kafin ta kalli zainab tace da ita

"Kiyi haƙuri zainab nasan da ciwo dadiro ma ya gudu ya barka bare miji, duk da haka karki damu dama can Allah ya tsara Kabiru ba'abokin zamanki ba ne na dundundun dan haka ki ma daina ɓata ranki a banza dama inba kaddara ba mai ya kaiki auren Kabiru?, mutumin da yayi ƙoƙarin cillaki a masifa, ki manta dashi kawai kizo ki mori ƙuruciyarki, taso kinji" ta faɗa tare da rungumo ta a jikinta.

"Ina zamu?"

"Daba mana Zainab, ko kina da inda yafi daba ne?"

"A'a"ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa.

ƙafarta ta fara ajewa a ƙasa kafin ta fara ƙoƙarin miƙewa, tashi guda wani abu mai kama da ruwa ya fara bin ƙafafunta ba tare ɓata lokacin ba gurin gaba ɗaya ya ɓaci.

tsaye tai tana kallon ikon Allah saboda ganin yadda abubuwa ke fitowa daga jikin Zainab,ranta babu daɗi ta kali Zainab tace

"Yanzu saboda Allah Zainab fitsarin ma bazaki riƙe ba ga wannan uban jini to ya kike so inyi, kin dai san ba aikin jini zan miki ba?" ta faɗa ran nan a ɓace kamar ta daki Zainab.

Cikin ruɗani da tashin hankali take kallon malalen ruwan da ya fito daga jikinta tare da uban jinin da ba tai tsammanin akwai kamarsa a jikinta ba,jin abinda kilakin fari ta faɗa yasa ta sake kiɗimewa, tashi guda kuma ta koma kan katifar dabas

"Innallillahi wa'inna ilaihirraju'un, Amina kinga wannan baiwar Allahr ma yoyon fitsarin ne?" Wata mata wacca gadonta ke facing ɗin gadonsu Zainab ta faɗa cikin damuwa da ganin Zainab acikin mawuyacin halin da 'yarta take ciki.

"Yo me!!!?" Kilakin fari ta faɗa tana zare idanu

"Yoyon fitsari mana baiwar Allah, kinga tawa 'yarma a haihuwar da tayi jiya ta haɗu dashi yadda kika ga haka muma haka tamu tayi likita na zuwa tace mana yoyon fitsari ne, kema ki kira likitan kiji"

"Dan ƙari!!!, yoyon fitsari kuma!!!? Kice da ganganma Alhaji ya janyensu hajiya suka fece suka barni dake?, aiko wallahi baza ta saɓu ba wai bindiga a ruwa!, eh yehhh ai waallahi ba dubu hamsinba ko million ɗaya za'a bani bazan yi jinyar yoyon fitsari ba, iyy......

"Haba kuwa? Anya kinsan kaddara kuwa?, aiko baki santa ba bai cancanta ki dunga waɗannan maganganun a gabantaba, ai ba ita ta ɗorawa kanta ba,to idan ace ke...." Matashiyar budurwar da aka kira Amina ta faɗa cikin jin haushin abinda kilakin fari take faɗe.

"Dakata!!! uwar 'yan jan bala'i, bakinki ya sari ɗanyan kashi, ni zaki jawa bala'i, shegiyar yarinya mai zubin aljanu, to wallahi kiga akan ki, kinga tsohowa sai tai aikin fitsarin mutum biyu dan itace 'yar wahala, ni kilakin fari zaki kirawa mala'ikan bala'i da magaribar fari haka?"

Zuciyarta cike da ƙuna ta kalli kilakin fari tace "Ai nima ban wuce ƙaddara ba, idan ta faɗomin zan rugume ta hannu bibiyu haka kuma umma nasan wahala ko rintsi baza tasa ta gujemin ba, ke kuwa fa? iyakaci kema kiyi karshe irin nata, to inda umma tasan ku ɗin karuwai ne Ko kula ku tayi?, kunje kunyo yawon barikinku ta samo cikinta acan Allah ya taimaka kun barshi baku kashe shi tun aciki ba shi kuma da bai da rabon ganin karuwa amatsayin uwa Allah ya karbe, to ai wannan ciwonma kamar dan kankare mata zunubi ya jarabce ta Ke ki jira kiga ƙarshen ki, Aragi kawai"

Tunda fitsari da jini suka fara bin jikinta ta sake ruɗewa hakan yasa ta koma kan gadon ta dabas, nan ta sake shiga kogin tunanin, batai nisa ba ta tsinkayi muryar umman Amina lokacin da take ambaton yoyon fitsari. Nan danan jikinta ya Hau rawa idanunta suka fara ƙakƙafewa, ƙirjinta ya dunga duka tamkar ganga da ake kaɗawa, tana son ta kurma ihu ko zataji sauƙin tokarewar da tantanin maƙollatonta da ya yi, jin gaba daya ma kafar sadar da maganarma bata, bata dama ba yasa ta fara zancen zuci.

"Ya Allah idan nace an haifeni ta hanyar da ta dace, nayi ƙarya. domin 'ya'yan sunna suna gidan sunna haka idan nace zan rayu cikin salama shima nayi ƙarya saboda bansan ƙazantar da aka haɗa wajan samar dani ba, ta yiwu hakan yasa ka kaddaramin kaddarori kala kala a rayuwata ciki har da irin kaddarorin da waɗanda na rayu a cikinsu suke fuskanta, ya Allah kasani na nisanci zina kodan illarta, sai gashi yau na faɗa halin ciwo irin na Anty july"

Dakyar taji dogon numfashi kafinta faɗa kogin tunani akan rayuwar Anty july, ɗib numfashi ta ya tsaya saboda jin kalaman Amina lokacin da take faɗin

"ke kuwa fa? iyakaci kema kiyi karshe irin nata, to inda umma tasan ku ɗin karuwai ne ko kula ku tayi?, kunje kunyo yawon barikinku ta samo cikinta acan Allah ya taimaka kun barshi baku kashe shi tun aciki ba shi kuma da bai da rabon ganin karuwa amatsayin uwa Allah ya karbe shi kizo kina wani ɗagawa mutane murya, to ai wannan ciwonma kamar dan kankare mata zunubi Allah ya jarabce ta ke ki jira kiga ƙarshen ki, Aragi kawai"

Wata irin kyarma ta fara bakinta ya kama tsuna zuciyarta ta fara kyarma tanajin tamkar ana zare mata duk wata laka ta jikinta lokaci guda kuma ta rasa ji dagani ta, yayin da ganganr jikinma ta gaza ɗaukarta, abunka da wacce take a jogane a kan gadon nan da nan ta faɗo ƙasa tim.

Cike da bala'i kilakin fari ta yo kan Amina zata doke ta, itama cike da kwarin gwiwa ta shirya faɗa da ita, tana ɗaga hannun Zainab na faɗowa daga gadon sumammiya.

A razane kilakin fari ta juyo jin faɗowar Zainab daga gado, dasauri ta ƙariso gare ta tana faɗin

"Na shiga uku Zainab!! Zainab!!!, Zainab ki tashi, ki tashi kar ki mutu kijamin bala'i don nasan masifar dake kanki kaina za ta dawo ni da banji ba ban gani ba, shegen son kuɗi na ya jamin ɗaurin rai da rai, dan Allah kimin rai wallahi da sauran ƙuruciyata bana so in ƙare shi a gidan ɗan kande, dan wallahi kina mutuwa ca za'ai ni na kashe!? don kada asirina ya tonu!, ni wallahi ma son kuɗi na ya kawo ni nan" tana faɗa ta kukan ganin wannan tashin hankali.

"Yawwa likita duba ta ki gani nasam ma bata mutu ba, bata mutu ba ko likita?" Sai da ta duba ta sosai kafin tace

"Innallillahi wa'inna ilaihirraju'un, bawar Allah sai dai fa in baki haƙuri don ita kam Allah ya yi mata cikawa?"

"La'ilaha illallahu!!!!! Innallillahi!!!!!, likita!!! likita duba ta, duba ta dai dan Allah likita!!!!" abunka da karuwa mai murya gaba ɗaya ihu da kururuwarta ya cika asibity yayin da hankulan jama'ar dake cikin asibityn gaba ɗaya ya dawo ɗakin hutun da suke.

Mu haɗu next page don Jin cikakken littafin Rana zafi....

Taku oum fu'ad

*** masu buƙatar Daga farko su neme ni ta wannan number