RANA ZAFIFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

RANA ZAFI

  • 1views
  • 13chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

Tunda gari ya waye take jin wata irin faɗuwar gaba mara misaltuwa, ga wani uban zillo da cikinta yake yi tamkar mai shiri fitowa duniya yau, abunka da mai tsohon cikin fari dan haka sam hakan bai ɗaga mata hankali ba.Cigaba tai da sabgoginta na yau da kullum har izuwa lokacin sallar la'asar, yayin da a gefe guda kuma bugun zuciyarta ya sake tsananta, jin abun ba na ƙare bane yasa ta nemi guri ta zauna, zancen zuci ta fara don gaba ɗaya bugun zuciyarta ya hanata sukuni, ga babyn cikinta da yake ƙara takura mata wajan shure shure tamkar zai turo fatar cikinta ya fito."Ikon Allah mu kuma tanan muka fara tamu naƙudar?" ta faɗa lokacin da ta haɗa kai da gwiwa."To amma an ce min ciwo ne zaka ji shi wanda tunda iyayenka suka haifeka baka taɓa jin irinsa ba?, to ai ni kuma ba ciwo nake ji ba, duk da ma iya wannan mutsu mutsun ma ya isa in tabbatar da naƙuda nake yi, don yau lamarin na daban ne" tayi tambayarta ta bawa kanta amsa.Ta jima a zaune kafin ta yunƙura ta tashi tare da ɗaukar buta don yin alwalar sallar la'asar, dakyar take sunkuya wa wajan yin sujjada saboda matsin da cikin yake ta yi mata, gashi gaba ɗaya ya hanata sukuni dan haka tana samu ta idar ta samu guri ta baje ba tare da ta iya samun damar karanta koda ayatul ƙursiyyun da ta kasance tana karantawa a bayan kowacce sallah ba.Barcine mai nauyi ya ɗauke ta, saboda yadda iskar sanyin la'asar yake ta busawa, cikin barcinta taji ƙarar mashin ta karaɗe illahirin cikin layinsu.Har zuciyarta taji ba daɗi saboda yadda ƙarar ta cika mata dodon kunnne, wani guntun tsaki ta ja mara sauti kafin ta fara gyara kwanciyarta don gaba ɗaya wuyanta ya sage. Sai da ta ɗan jingina da jikin gini sannan ta ɗan samu sawabar kwanciyarta ta.A daidai lokacin kuma mai mashin ɗin da ya cika ta da ƙara ya tsaya a daidai ƙofar gidanta, Tsaiwarsa tai dai dai da lokacin da zuciyarta tayi wani irin mumunar bugawar da tunda take bata taɓa yin irinta ba, baki ta buɗe da zummar addu'a amma me kawai taji ana buga ƙofar gidan.Sake jan uban tsaki tayi kafin ta kama jikin banpgon tana ƙoƙarin miƙe wa saboda barci da tayi gaba ɗaya jikinta ya ƙara nauyi.Hijabin dake jikinta ta gyara tare da sanya takalman dake kusa da ita sannan ta nufin ƙofar fita tana faɗin"Waye?" Shiru ba'amsa, dan haka a hasale ta sake faɗin"Wai waye ne haka?""Buɗe ki gani mana!" ya bata amsa cikin kakkausar muryar da sai da ta ɗan firgita saboda yadda muryar tasa take da kaushi.Jitai kamar karta buɗe don sam bata da haɗi da mai makaman ciyar wannan muryar, tanan nan tsaye ƙikam aka sake buga ƙofar tare da faɗin "Ko bazaki buɗe ba ne?, to saƙo aka bamu idan kuma mu mayar to!?" ya faɗa a hasale.Ko amsa bata bashi ba ta kai hannunta da yake rawa tai unlocked ɗin ƙofar.Tana buɗewa tayi arba da waɗansu mutane guda biyu waɗanda yau itace rana ta farko da ta fa...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters13
premium2
11

Chapter 11

Premium
Updated a year agoAvailable now
13

Chapter 13

Premium
Updated a year agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play