Page 7
by @sanazty
SUMAYYA
Wattpad@SaNazdeeyah_
Arewabooks@sanazdeeyah
Youtube: ***
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[tushen mu'amula tagari]
Mg's skincare
```Page 7```
Gabaɗaya kallonshi suka yi, dan yadda ya miƙe a tsorace "Lafiya?" Sai lokacin Mommy tayi magana, dan ko gaisuwa Nihal da Ayrah ne suka yi amma Mommy da Kamal basu ce uffan ba. "Daddy na manta na bar mota a buɗe" "Karka damu ai akwai mutane a waje kuma sun ga mun fito daga ciki." Ba haka yaso ba amma ba yadda ya iya haka ya zauna a sanyaye ya kalli Sumayya ya ce "Ya haƙuri?" Hannu ta saka ta goge hawaye tare da cewa "Alhamdulillah!" "Allah yajiƙansu da rahama ya sa can tafi musu nan" "Amin ya rabbi" Maryam ma cikin mutunci ta gaishesu Atika kuwa jin sune ya saka ko ɗagowa batayi ba.
"Sumayya ku yi haƙuri ita mutuwa haka take, muma nan duk ita muke jira, lokacinsu yayi dole su tafi, kuma Alhamdulillah iyayenki mutanen kirki ne kowa ya musu kyakykyawar shaida, fatan dai Allah ya musu rahama ku kuma Allah ya baku haƙurin rashi" Cewar Daddy. Ita da Maryam suka amsa da amin duk da da ƙyar take iya amsa gaisuwar. "Ko bata da lafiya ne?" Ya furta yana kallon Atika "Eh masassara take amma da sauƙi ma, tasha magani" "Allah ya bata lafiya, damuwa ce ta rage gudun wani ciwo" Shiru dai suka yi ba wanda ya ce komai. Kallon Sadeeq Daddy ya yi, shi kuma ya fito da kuɗi a aljihu ya miƙawa Maryam "Ga wannan" Karɓa tayi tare da faɗin "Allah ya bada lada."
Suna fita Nihal ta ce "Yaya Sadeeq motar ma a kulle take." "Oh nayi tunanin a buɗe take ai." Mommy kallonshi tayi ta ce "Da ƙuruciyarka ka riƙa ruɗewa" Sai lokacin Kamal ya ce "Mommy wace ƙuruciya, mutumin da zai shiga shekaru 30 babu aure babu shirin aure ba dole yake ruɗewa ba" Shi dai Daddy baice komai ba har suka shiga motar. Sadeeq ke driving, Daddy yana gefensa.
"Sam ban ji daɗi da kuka kasa musu gaisuwa ba, akan me? Ko me tayi muku mutuwa ai ta kore komai" "Alhaji naga nazo, kuma na yiwa iyayenta, to dole sai na mata?" "Ita da ban kishiyoyin uwarta da ban, mahaifa ta rasa a watanni da basu wuce biyu ba, sannan kuma ga ciki haba banji daɗi ba da kuka mata haka"
"Wallahi kaine dai da ɗauƙar zafi amma bama zata gane bamu mata ba, kuma tunda munzo ai ta san ba gaba muke da ita ba, mun ma yi ƙoƙari da muka zo ai."
Ayrah ce ta ce "Ni wallahi sun bani tausayi su kaɗai a ɗakin ba kowa, wallahi da tausayi" "To kunji yarinya ƙarama ta fiku hankali" Ba wanda ya ƙara magana dai har aka je gida.
Maryam ta gyaɗa kai bayan ta gama ƙirga kuɗin "Dubu hamsin ne cif" Sumayya bata ce komai ba, haka Atika ma. "Yanzu ya za ai dasu? kin san me Sumayya? Kawai ki saya maku abubuwan da zaku buƙata ke da Atika" "A'a kawai ki ɗauki wasu ki riƙe sauran kiyi sadaka wallahi ko kuɗinsu ban son gani Maryam, gidansu ne sila ta farko na rugujewar rayuwata." Ta fashe da kuka. Da sauri Maryam ta hau gadon tare da rungumota "Ƙaddararki ce a haka, kiyi haƙuri Sumayya" "Meyasa ƙaddarata ta haɗa da raba iyayena da duniya, inajin tsanar duniya Maryam" "Sumayya dan Allah kiyi haƙuri, idan har kina kuka to waye zai rarrashi Atika?" Kukan dai take dan shi ne abinda tafi buƙata a yanzu. Ita Maryam taji daɗi ma daya kasance basu lura da hali na yoyon fitsari da take ciki dan da sai abin ya fi ma Sumayya zafi.
**** *****
Kallon agogon dake ajiye a side drawer ya yi, 2:15am amma babu alamun bacci a idanunsa, tunda ya ga Sumayya hankalinsa ya kasa kwanciya, maganganun da ta faɗawa Dr Nasir ne suke ƙara masa yawo aka. "Zan sake komawa ko dan zoben gold ɗinta" Ya furta gami ta kwanciya kan gadon. Da ƙyar dai ya samu ya yi bacci sai dai asuba nayi ya farka tare da nufar toilet ya ɗora alwallah. Ko bayan da suka je masallaci suka dawo shi a parlor ya yi branching nan ya kwanta kan three seater.
07:30am
Turus ta tsaya tana kallonsa lokacin da ta fito daga bedroom ɗinsu. "Yaya" Ta furta tare da ƙarasawa gabansa, ta zauna kusa da kujerar da yake kwance. "Ya dai?" Ya furta yana kallonta "Yaya kana lafiya kuwa?" "Eh lafiya lau, me kika gani?" "Naga idanunka sun kumbura kamar baka samu bacci ba?" Murmushin ƙarfin hali ya yi tare da faɗin "Nayi bacci kuwa me zai hanani bacci" "Sumayya mana" Zaro ido ya yi yana kallonta kafin ya ce "Kin san kuwa abinda kike faɗa Ayrah?" Murmushi tayi ta gyara zama ta ce "Tun jiya na lura ganinta ba ƙaramin ɗaga maka hankali ya yi ba" "Ke ki kiyayeni yaushe kika ga nayi hakan, tsohuwar matar Kamal ce karki manta da wannan" "Ai kaima tsohuwar matarsa kace Yaya, ni wallahi tausayi ma take bani" "To ke take ba tausayi bani ba, kin ga ki wuce school time kar ya ƙure miki" "Nihal nake jira, kuma ma sai mun yi breakfast ai" "To nan ne dining da zaki zo kiyi min zaune" Miƙewa ya yi ya wuce, ita kuma da kallo kawai ta bi shi.
Yana shiga bedroom ya janyo waya tare da kiran number Nasir, har tayi ringing ta katse bai ɗaga ba, har ya haƙura sai kuma yaji ya kasa dan haka ya sake kira a karo na biyu, shima sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. "Sadeeq yane? Lafiya kuwa kake kira da sanyin safiyar nan?" "Nasir akwai matsala ina son na haɗu da kai" "To ai ni yanzu ma na tashi daga bacci, impact kiranka ne ma ya tasheni" "Nasir dan Allah ka shirya nima zan shirya ka fito mu haɗu" "To shi kenan mu haɗu a asibiti ko" "Anya maganar za ta yuwu anan, gaskiya mu samu wani joint" "Okay bari na shirya sai naga ina ya dace mu haɗu"
08:00am
"Dama ina taso mu haɗu da kai, to kuma kai baka kwana a gida" "Ai an sallameni shiyasa" Murmushi Sadeeq ya yi tare da faɗin "Haba dai ai kuma yanzu kaima baka da kowa" "To ya na iya Mommy ma ka ga ko abincin ba kullum take bani ba." "Hmmm! Dama ina so nayi maka wata tambaya Kamal" "Wace tambaya fa?" "Akan matarka ne" "Ok. Ina jinka" "Mene ya saka har ka saki matarka, ƙaramar yariny..." "Dan Allah Sadeeq ka dakata min, wai taya zan zauna da matar da tayi zina har ta samu ciki da aurenta" Ajiyar zuciya Sadeeq ya sauke, sannam ya ce "Idan kuma ƙaddararta ce a haka fa? Ta bani tausayi Kamal, ba uwa ba uba sannan babu miji"
"Sadeeq ka daina yi min maganar wannan fasiƙar" Bai san meyasa yaji zafin furucin Kamal ɗin ba, bai kuma ƙara cewa komai ba. "Bari na tashi na san nayi" "Ina zuwa? Ko office?" "Eh har na so na makara ma" "Okay sai ka dawo" "Allah yasa"
*******
Shiru Nasir ya yi na wani lokacin kafin ya ce "Ko dai sonta kake Sadeeq?" "So kuma?" "Eh ai indai kana kishin mace to so ne ke jawo hakan" "Gaskiya ban yarda cewa so bane, tsohuwar matar Yayana ce fa" "Duk da haka, indai ba so bane to mene ne?" "Tausayi mana" Murmushi Nasir ya yi tare da faɗin "Sannu sarkin masu tausayi" Shima murmushin ya yi tare da faɗin "Yanzu meye abin yi?" "Abinyi ya wuce ka kai mata gold ɗinta, amma dai ka bari sai an ɗan kwana biyu"
"Okay to shi kenan, ya kuma batun zuwa gidansu Hamdiyya?" "Ai yanzu ba shi ne ya haɗamu anan ba ka bari sai lokacin da ka daina son matar yayanka" "Wai wace irin magana ce haka Nasir?" "Tuni nake maka Sadeeq saboda karka zurfafa domin ka san ko giyar wake kake sha ba za a aura maka ita ba bayan ba daɗi ne ya fitar da ita daga gidan Yaya Kamal ba" "To yaushe ka ji nace ina sonta bare har akai ga maganar aure, so dai kake so ka lalata farin cikina ko?" "Sorry abokina, am just kidding you" "Stop it dan Allah i don't like" "An daina, yanzu dai bari na wuce hospital kar na makara, kaima ya kamata ka wuce office" "Eh dama ai na fito ne gabaɗaya."
Yana ƙoƙarin fita Mommy ta fito daga side ɗinta "Wa nake gani kamar Kamal?" Juyowa ya yi, ya gaisheta "Yaushe ka zo?" "Babu daɗewa so dana ga baku fito ba zan wuce gurin aiki" "Yaran sun tafi school amma bana jin Sadeeq ya fita, baku haɗu ba?" "Mun haɗu dashi ya fita" "Taɓ yau wace rana Sadeeq ya tafi gurin aiki da wuri." "Ni kaina nayi mamaki" "Dama ina son magana da kai Kamal" "Okay" Ya furta yana gyara zama. "Mun yi magana da mahaifinka, naga bai kamata ace an ɗauki tsawon lokaci kana zaune haka kai kaɗai ba, shi ne ya ce nayi maka magana idan kun daidaita da Laila ka ga sai a tura gidansu ko?" Shiru ya yi na ɗan lokaci kafin ya ce "Mommy ai ni ba Laila bace zaɓina, akwai yarinyar dana gani kuma ina so naje mu fahimci juna da ita" "Wace ce? Kuma ni dai a iya sanina Kamal baka da wata da kake so kamar Laila, tun kafin ayi maka auren nan na dole, amma kuma yaushe ka canja, ko dai ka koma shaye-shayen?" Dama ban daina ba Ya furta a ransa, a fili kuma murmushi ya yi ya ce "Mommy karki ɗaga hankalinki fa, mun ɗan samu saɓani da Laila amma kuma yanzu mun shirya sai dai ni da ita a yanzu friends ne kawai" "Friends" "Eh Mommy" "Okay to ita waccan yaushe zaku daidaita?" "Soon Mommy" "Ya kamata dai, tunda ka ga Sadeeq ya fitar da mata, so ina so a saka rana tare ayi komai tare, dan gidaɗaya ma zaku zauna har an kusa gama ginin" "Ok Mom, insha Allah zan san abinyi" "Ya dai kamata."
Yana shiga mota ya kirata a waya "Morning babe" "Morning darling yanzu nake tunaninka" "Wow that's nice me kika tuna a kaina?" "Soyayyarka da kuma kasancewa tare da kai" Murmushi ya yi cikin jindaɗi ya ce "Ai mun kusa kasancewa tare dake Jidda ke dai ki shirya saura kaɗan" "Hmmm! Ni dai ba zan daina fargabar rasaka ba har sai na mallakeka" "Ki bani dama kawai na turo iyayena" "Idan har wannan damar kake so an baka" "Jidda ba fa wasa nake ba" "Nima ba wasan nake ba, dagaske nake" "Shi kenan, ina mai tabbatar miki a cikin satin nan za a tura kuma bikinmu ba zai wuce wata uku ba" "Allah ya mana tsawon ran gani Babe" "Abin ya rabbi."
2 weeks later
Tana kwance ita kaɗai a ɗakin tana ta saƙawa tana kuncewa kawai taga an bankaɗo labule "To sai ki taso ana kiranki a waje, ke kullum a kwance kamar ruwa" Anti Hadiza ce tayi maganar, ita Sumayya mamaki ma tayi waye zai kirata a waje. Miƙewa tayi ta zura hijabi dama bata daɗe da dawowa daga toilet zubar da fitsari ba, ledar ma har ta fara fita hayyacinta. Takalmi ta zura ta buɗe labule ta fita. Kallon ɗai-ɗai taga suna mata 'yan gidan, ita dai ta sauke kai ta fice.
Tana fita taga GLK a ƙofar gidan nasu, fara sol sai sheƙi take, dube-dube ta fara dan sam bata kawo cewa wanda ke cikin motar shi ne yazo nemanta, fitowa ya yi daga motar "Sumayya!" Jin an ambaci sunan nata ta kai duba gareshi. "Kaine ka saka a kirani?" Ta furta a sanyaye" "Eh nine" Ya faɗa yana ƙare mata kallo, ta rame sosai, a sanin da ya yi mata fara ce sol amma yanzu tayi duhu, ga idanunta duk sun faɗa. "Ina wuni" Kawai yaji ta gaidashi, sai yaji daɗi har cikin ransa. "Lafiya lau ya ƙarin haƙuri?" "Da godiya" "Allah ya jaddada rahama a garesu" "Amin ya rabbi" Shiru ne ya biyo baya, ya kalleta ya ce "Sumayya na san baki ganeni ba ko?" "Eh gaskiya ban gane ka ba" Ɗan murmushi kaɗan ya yi tare da faɗin "Ni ƙanin Kamal ne, tsohon mijinki" Gani ya yi ta haɗe rai tamkar ba ita bace wadda ta ɗanyi murmushi suna magana.
Ji ya yi jikinsa ya yi sanyi, ya kalleta ya ga ta ƙura masa manyan idanunta. "Am...kuma ni ne wanda ina nan kuka je gurin Nasir" Bata ce komai ba nan ma "Kin gane Nasir ɗin?" "Ban san waye Nasir ba, amma na san waye Kamal mutumin daya ruguza rayuwata, ya lalata ƙuruciyata, na samu cikin da ban san waye ubansa ba, ni ba 'yar iska ba, ban taɓa fasiƙanci ba, ban san taya na samu ciki ba, amma kuma ya kirani fasiƙa yafi a ƙirga, aka kira mahaifina mutumin da bai iya tarbiyya ba. Kamal har abada ba zan manta sunanshi da kamaninsa ba, kuma ba zan taɓa kallon ahalinsa da daraja ba, saboda sun kasa tsayawa na masu bayani sun kasa fahimtar raɗaɗi da ƙunci da nake ciki, kaima dan Allah ka bar ƙofar gidanmu, kuma ina fatan ko waye ya yi min abin nan Allah ya saka min" Ɗan lumshe ido ya yi, jin zafin kalaman nata yake. Buɗe ido ya yi ya kalleta "Dama zobenki da kika manta a office ɗin Nasir itace na kawo miki" Ya faɗa yana nuna mata zoben da hannu. "To ai ina sane na bari, me zanyi da ita, dama amfanin da nake so nayi da ita ne bata min ba, tunda ta ɗan uwanka ce sai ka mayar masa, na tsani duk wani abu daya fito daga ahalinku" "Keee.....!" Ya daka mata tsawa. "Ya isheki haka kuma, kada ki nemi kici mutuncin ahalina, dan a kansu zan iya faɗa da kowa" "To idan baka so ka bar ƙofar gidan mu mana" "To ki karɓi kayarki sai ki mayar masa da kanki" Kallon zoben tayi sannan a fusace ta warta tare da kwaɗata jikin motarsa. Kallon motar ya yi da zoben a ƙasa, sannan ya juyo a fusace ya kwaɗa mata mari.
Ɗagowa tayi ta kalleshi tuni idanunta sun canja kala, mutanen dake can gefe suka taso da sauri "Haba bawon Allah bai kamata ba, ita fa macece" "Dan tana mace, ni baku ga abinda tayi min ba?" "Kayi haƙuri dai, sha'ani na mata sai a hankali" Tana tsaye tana kallon yadda 'yan unguwarsu ke bawa Sadeeq haƙuri saboda kawai an ganshi da babbar mota, abinda suke so kuwa shi ne ya faru, yana zuwa ya ɗauki zoben ya miƙawa ɗaya daga cikinsu ya ce "Ku sayar ku raba kuɗin" Godiya suka yi tayi har yaja motarsa, suka wuce suka bar Sumayya anan tsaye riƙe da kumatu.
Ta daɗe a tsaye kafin ta shiga gida, sai dai tun a tsakar gida Iya Zulai ta tare ta "Waye kika wa rashin kunya har ya mareki?" "Nima ban san shi ba, hasalima yau na fara ganin shi" "Hmmm! Allah yasa ba ɗaya daga cikin samarin da suke hure miki kunne bane suka fara biyoki gida dan sun ga yanzu Malam baya raye, sai kuma ta fara kukan munafurci hakan ne ya saka Sumayya fashewa da kuka, tayi ɗakinsu da saurinta. Tasha kuka sosai a ranar har kuma tayi ta gama Atika bata dawo ba.
Ɓangaren Sadeeq kuwa kai tsaye gida ya yi, tunanin abinda ya yi gabaɗaya ya mamaye masa rai, ji yake kamar ya koma ya bata haƙuri, sai kuma yake ganin in ya yi haka ajinsa zai zube musamman a gurin 'yan unguwar, dole zai haƙura zuwa wani lokaci.
*** For ur business advert.
#Share