Page 9
by @sanazty
SUMAYYA
Wattpad@SaNazdeeyah_
Arewabooks@sanazty
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[tushen mu'amula tagari]
```Page 9```
Kuka sosai take ta riƙe hannun Atika ta ce "Na cuci kaina Atika, iyayenmu duk sun mutu ne sanadina, gashi na jawa kaina yoyon fitsari, meyasa nayi haka? Duniya gabaɗaya ta isheni Atika, na tsani duniya na tsani kaina" Itama Atika hawaye take kafin ta kai hannu fuskar Sumayya tana share mata hawaye, "Ki bar faɗin haka Adda baki da hannu a ciki dama Allah ya yi lokacin su ne" Jamilu ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Kiyi haƙuri insha Allah za ki samu lafiya komai zai so da sauƙi, za ki samu lafiya ki daina faɗar maganganu haka" Atika da Jamilu dai haɗuwa suka yi suna ta bawa Sumayya haƙuri ta daina kukan da take.
Haka Atika ta cigaba da jinyarta sam taƙi zuwa katsina saboda ba zata iya barin Sumayya ita kaɗai ba, sannan kuma basu da number ko mutum ɗaya a 'yan uwan Iya bare su kira, 'yan gidansu ma haka dan basu ga maciji duk da a cikin gidan Sumayya na layin masu haƙuri.
Ɓangaren Jamilu kuwa kusan koda yaushe yana gurinsu dan ma Atika tana yawan matsa masa kan yaje ya yi hayarsa saboda duk sati yana kai balance gun ubangidanshi mamallakin adaidaitan. Abinci kuwa tun daga kan na safe har zuwa na dare daga gidan ake kawo musu. Itama mahaifiyar Jamilu duk bayan kwana biyu ta kan zo ta duba Sumayya. Jamilu kuwa tuni ya fara nunawa Atika soyayya sai dai ita sam taƙi ma bashi fuskar da zai sanar da ita sirrin dake ransa.
**** **** ****
Kallonshi tayi ta ɗanyi murmushi tare da sipping milk shake ɗin dake gabanta "Yanzu kai fa ka zama ango ko?" "Eh na zama angon Hamdiyya" Hannu ta saka ta rufe fuska "Ka saka naji kunya" "To mene na jin kunya ƙiris ya rage fa" Murmushi ta sake yi "Yanzu dai ba wannan ba ya batun dinner?" "Wannan Kamal ke tsara komai, ni ai nawa ɓangaren cocktail ne kuma mun gama shirya komai dasu Nasir" "Ai na san indai da Dr Nasir a tare da kai lallai ba zanji kunya a bikina ba" "Aikam dai ba za ki ji ba, dan Nasir shi ne yake ta shige da fice, Kamal ɗinma mun yi waya ya ce next week zai dawo satin biki" "Gaskiya da alama yana jindaɗin Dubai amma fa in nice ba zan iya bari ka tafi ba, sai dai ka haƙura bayan biki sai muje tare" "Ke ko?" "Eh mana ai gaskiya ne" Murmushi kawai ya yi, suka cigaba da hirarsu cikin farin ciki da annashuwa.
A harabar tanfatsetsen gidan nasu ya parker mota "Babe na dawo dake gida" Ɗan taɓe fuska tayi cikin shagwaɓa ta ce "Yanzu tafiya za kayi ka barni?" "Babe ai zamuyi waya ko?" "Gaskiya ni dai bana so na rabu da kai dai-dai da second ɗaya" "Karki damu ai mun kusa zama a inuwa ɗaya" "Allah ya nuna mana wannan rana" "Amin Babe" Ya furta tare da janyo ledar da ya yi mata shopping ya miƙa mata "Oh wai kana nufin ba zaka taka min ba?" "Sorry, yi zamanki bari ma na buɗe miki ƙofa da kaina, ai ke princess ce" "To gara a lallaɓani" "Fiye da ƙwai kuwa" Ya faɗa yana ɓalle murfin mota. Sai daya rakata har ƙofar part ɗin sannan ya miƙa mata ledar "Take care of your self my dear" "You too" Ta furta tana ƙarɓa. "Baka faɗa ba" Ta yi maganar da shagwaɓa tana ɗan buga ƙafa "Sorry, i love you" "Love you more dear" Ta wuce da sauri, shi kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da ɗan lumshe ido, sai da har ya ga shigarta sannan ya juya ya tafi.
Yana tayar da mota Sumayya ta faɗo masa a rai. Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin "Idan naje me zan ce mata ma, zobenta ne kuma na bayar da kyautarta a gabanta, bani da wani abu da zai kaini gurinta. "Ya furta lokacin daya tayar da motar ya bar gidansu Hamdiyya.
*3 weeks later*
Tana daga kwance kan lafiyayyen gadon dake hotel ɗin data kama ta miƙe zaune, cikin tashin hankali take ƙara karanta I.V ɗin da take gani kamar a mafarki. Ji tayi jikinta ya ɗauki rawa har wata zuffa taji ta karyo mata duk da AC data ƙure a ɗakin. Da sauri ta janyo waya rai a ɓace ta kira mahaifiyarta, tana fara ringing ta ɗaga "Yaushe kika dawo?" Shi ne abinda mahaifiyarta ta furta "Mommy keep that aside wai da gaske ne auren Jidda da Kamal jibi ne?" "Da gaske ne, nima basu faɗa min sai a fulanin talla naji" "Ai ba zasu faɗa miki ba saboda sun shirya cin amana" Ƙitt ta kashe wayar tare da miƙewa tsaya. Yawo ta fara a ɗakin kafin ta kira ƙawarta "Wata sabon gani, ba dai kin dawo ƙasar ba?" "Hmmm Zee ba wannan ba, wai kin san Kamal aure zai yi?" "Ban gane Kamal ba, wane Kamal?" "Wane Kamal kika sani bayan wannan" "To ba tare kuka tafi shaƙatawa Dubai ba, ai na ɗauka ma tare kuka dawo" "Zee zuciyata zafi take, wato Kamal sai daya gama lalata rayuwata sannan zai auri wata bani ba, kuma dan rainin wayo cousin ɗina fa" "Gaskiya Kamal maci amana ne, kuma dole mu ɗau mataki" "Ƙawata faɗi ma ai ɓata baki ne, wato shiyasa ya barni a Dubai ya taho, kamar na sani yana dawowa da kwana uku na dawo banje gida ba na zauna a hotel ashe sai rabon naga baƙin ciki ne na dawo Nigeria" "Kiyi haƙuri Laila" "Hmmm" Kawai ta iya faɗa kafin ta katse.
Dinner Party
The Royal avenue event center dake Nassarawa nan aka kama, aka ƙawatashi sosai ya yi kyau matuƙa. 'yan uwa da abokan arziƙi duk suna zauna suna jiran zuwan angwaye da kuma amare. Tun daga main gate ba a bari a shigo sai in har mutum ya bayar da gatepass wanda zai tabbatar da gayyatarsa aka yi ba wai gayyar soɗi bane.
Ƙarfe 9 angwaye da amare suka shigo hall tare da rakiyar abokansu. Kamal da Jidda sun saka Maroon yayinda Hamdiyya da Sadeeq suka yi shigar blue black. Tunda suka zauna Hamdiyya ke watsawa Jidda kallon banza, ganin sarƙa da ɗankunnen da aka mata ado dasu yafi nata kyau da tsada, sannan makeup ɗinda da yadda aka saka mata head shima yafi, duk da kayansu iri ɗaya ne sai taga na Jidda ya zauna ɗam a jikinta. Ita kuwa dama sai da tayi ɗan ƙaramin yaƙi da telanta saboda bai gama ɗinkin da wuri ba kuma ya yi mata style ɗin da bashi ta bashi ba.
A gefe napep ya sauketa ta durfafi gate kai tsaye, ɗaya daga cikin securities ɗin ya taso yana faɗin "Hajiya muna son ki bamu gatepass ɗinki kafin ki wuce" Kallon wulaƙanci masa tare da faɗin "Bikin matsiyatan har sai an nuna gatepass?" Ɗayan dake zaune ya buɗe ido cike da mamaki. "Eh duk da haka dokarmu ce sai an bayar da pass ake wucewa" "To ai ni dama ba nazo nan bane dan inbi doka" Kawai ta bangaje shi ta shiga da gudu. Har zai bi ta ɗayan ya dakatar dashi "Tunda ta wuce a barta, irin matan nan ne masu nacin sai sun zo biki ko sun dace da mijin aure" Kujera ya samu shima ya zauna.
Cikin hall kuwa amare da angwaye na zaune yayinda wasu daga cikin ƙawaye ke rawa, ana ta kuma serving abinci a ko wane table. Tana shiga kuwa kai tsaye ta nufi stage ɗin MC na mata magana bata ko kulashi ba. Kamal kuwa sai daya ji gabansa ya yi mummunar faɗuwa ganin Laila daya bari a Dubai gata a Nigeria. Bai ƙarasa tunanin ba kawai yaga ta saka hannu biyu ta ture ƙaton cake mai hawa biyar da aka yi, ko yanka cake ba a yi ba ta lalatashi. "Wannan tana da hankali kuwa" MC ya furta da mamaki. Hannu ta saka ta fito da wuƙa daga jaka ta nuna masa "Ka ƙara cewa bani da hankali wallahi sai na caka maka. "Laila meye hakan? Me kike ƙoƙarin yi?" Jin muryar ƙanwar babanta ya saka ta juya "Kisa! Kuma ai duk munafukai ne, kun san ina tare dashi saboda kun tsani uwata shi ne kuka zagaye a munafurci kuka aura masa Jidda" "Laila kin kuwa san dawa kike magana?" "Na sani kuma wallahi kika matso sai na caka miki" Ta juya tana kallo Kamal, Jidda, Sadeeq da Hamdiyya da duk suka miƙe tsaye "Wallahi Kamal baka isa kaci amanata ka zauna lafiya ba, sai na kashe ka, na kuma kashe kaina" Juyawa tayi a fusace mutane duk aka ja baya, ta fara fasa verses ɗin gurin duk wani abu na docaration sai data wancakalar ana mata magana sam taƙi saurarar kowa ga kuma wuƙa a hannunta. Wani security ne ya samu ya lallaɓo ta bayanta ya cafki hannun aikuwa ta fara ƙoƙarin ƙwacewa securities biyu suka mata cali-cali zuwa ƙofar waje, dai-dai lokacin Mommynta ta fito daga mota. "Subhanallahi!" Ta furta tana ƙarasawa da sauri gurin. "Ku sauketa" Ta furta a fusace. Suna sauketa Mommy ta ɗauketa da marin da har sai data ga giccin walƙiya ta wuce ta gefen idanunta, shiru tayi lokacin da take jin wani dummm a kunnenta kafin daga bisani taji komai ya fara dawo mata, mutane ta duba taga sai fitowa ake daga hall wasu na shiga motocinsu, dariya ta kwashe kafin ta mayar da kallonta ga Mommy "Ko kasheni za kiyi Mommy na ɗan huce takaicin wani sashe na zuciyata, yadda ya ɓata raina nima na ɓata bikinsa." Bata tankata ba ta fuzgi hannunta ta saka a mota ta figi motar da gudu.
"Haba Jidda mene na kuka, zaki ɓata kwalliyarki fa" "Taya ba zan yi kuka ba Faty, wannan wane irin muzanci ne a gaban jama'a me nayiwa Laila?" "Dan Allah ki daina kuka, ki share hawayenki" "Burinta dama ta ɓata bikina kuma ta ɓata taji daɗi" Tissue ta saka tana ɗan goge hawayen daya zubo. Wasu daga cikin family ɗin suka zo ana ta bawa Jidda haƙuri. Ƙarshe dai bata ma jira ango ba ta saka kawai aka ɗauketa aka kaita gida.
Tana gama saka kayan bacci ta dawo ta zauna tare da faɗin "Ke ina wannan ice cream ɗin ɗauko mana" Kallonta Mansura tayi ta ce "Hamdiyya sai naga kamar ke baki damu da abinda ya faru yau a bikinku ba, har fa a social media" Taɓe baki tayi tare da faɗin "To ai dama 'yan media ƙiris suke jira ni kam ko a jikina ba mijina aka muzanta ba ba kuma ni ba wallahi sun daɗe basu yaɗa ba" "Amma ai Yayan mijinki ne" "And so what? Wallahi ko a jikina, ni dai na san mijina bai yi abin kunya ba, kawai baƙin cikina ɗaya yau da a gidan mijina zan kwana amma wannan abin ya saka an ɗaga" "Kefa baki da kunya" "Wallahi ba wani rashin kunya gaskiya ce ai. Kin ga da Allah ki miƙo mana ice cream kafin ya yi melting" "To jarababbiya" "Naji" Ta furta tana dariya ita kuma Mastura ta miƙe ta fita. Text daya shigo mata ta buɗe a waya ta karanta wanda hakan ba ƙaramin gigita ta ya yi ba Kura nannaɗe da fatar akuya, ki bi a sannu dan akwai ranar ƙin dillanci. Wannan saƙon ba ƙaramin mamaki ya bata ba, kuma lambar da ta turo saƙon an rufeta ta yadda ba zata taɓa gane waye ba. "Me hakan ke nufi? Waye ke neman yi min sharri?" Ta furta a fili tana mai sauke numfashi.
Washe Gari
Kuka sosai take lokacin da za a fita da ita, a haka dai 'yan ɗaukar amarya suka sakata a mota har zuwa Rijiyar Zaki inda katafaren gidan Kamal da Sadeeq yake. Babban parlour ne a ƙasa da dining area a gefe tare da kitchen sai wasu curve guda biyu dake facing juna, anan ne ɗakunan baccinsu yake, na daga gabas shi ne na Kamal da Jidda na kuma daga yamma shi ne na Sadeeq da Hamdiyya, ko wanne dogon corridor ne sai kuma ɗakuna guda uku. Sai upstairs wanda shi kuma babban parlour ne sai ɗakuna guda biyu suna kallon juna suma a cika su da kayan alatu na more rayuwa. Gidan ya haɗu ya kuma ƙawatu abin dai sai wanda ya gani.
"Jidda kukan ya isa haka, muma fa duk da haka muka saba, idan kuma dan abinda ya faru jiya ne to ki fawwalawa Allah, kin san shi bawa baya tsallake ƙaddararshi kuma ta yuwu dama ta shirya haka ne dan ta haɗaku faɗa ta tarwatsa miki farin ciki, kin dai san wacece Laila wacece uwarta ba sai an faɗa miki ba" Kai kawai ta gyaɗa "To kiyi haƙuri kinji" Bayan tafiyarsu ba jimawa ango ya shigo tare da rakiyar abokai, ƙawayenta da suka zauna aka yi siyan baki abokan ango suka kwashesu dan su mayar dasu gidajensu.
"Jiddanah" Ya furta yana hawa gadon, ta cikin mayafi ita kuma kuka kawai take. Hannu ya saka ya buɗe mayafin, idanunta a ƙasa fatun idon gabaɗaya sun cika da hawaye. "Yau ranar farin cikinmu ce, bai kamata naga hawaye a idonki ba" Bata ce komai ba, ya saka hannu zai goge mata tayi saurin matsawa tare da miƙewa kamar an tsikareta ta sauka daga kan gadon. "Lafiya?" "Ba zaka taɓa samun kaina ba har sai ka auri Laila ka kuma dawo da Sumayya" "What...?" Ya furta a kiɗime yana kallonta.
Na rage ganin comments ɗinku why?
SaNazdeeyah_✍️