Page 11
by @sanazty
SUMAYYA
Wattpad@SaNazdeeyah_
Arewabooks@sanazty
```Page 11```
"Ba za ki hanani auren wanda nake so ba, saboda ke an miki auren dole shi ne nima zaki min? Ko kuma baƙin ciki kike min dan kin ga zan auri mai kuɗi" "Atika!" Sumayya ta faɗa cike da mamaki "Ni kike faɗawa wannan maganganu?" "Eh ke nake faɗawa, akan haka zamu samu mugun saɓani dake, shi nake so ko kisan kai yake to ni shi nake so ki rabu dani kiji da kanki kema" Ta furta tana huci.
Jin haka ya saka Sumayya ta fita daga ɗakin sai kuma taji jikinta ya yi sanyi ƙafafunta sun kasa ɗaukarta, da bangon ɗakin ta jingina, lokaci guda ta fashe da kukan data kasa riƙewa. "Lafiya Sumayya?" Umma ta faɗa lokacin data fito daga ɗakinta ta ƙarasa gaban Sumayya. Kuka kawai take bata saurareta ba, ta buɗe labule ta shiga ɗakin ta tarar Atika zaune kan katifa sai ƙara haɗe rai take. "Mene ya haɗaku da 'yar uwarki har take kuka?" "Saboda nace bana son Jamilu shi ne take min baƙin ciki dan taga na samu mai kuɗi" Jin haka ya saka Sumayya shigowa a fusace "Idan kika ƙara cewa ina miki baƙin ciki wallahi sai na miki mugun duka" "To karki fasa, ƙarya aka yi ne, wallahi ko da kina Yayata ba zan taɓa yarda ki tauye ni ba" A fusace Sumayya ta tafi Umma ta riƙota "Haba Sumayya ke babba ce" "Umma kina jin abinda take faɗa fa" Sumayya tayi maganar tana kuka. "Ke da ita ba ɗaya ba, muje ɗakina ba zan bari ku zauna tare ba har sai kin huce" Ta janyeta suka tafi. "Mtsww aikin banza, shi Yaya Kamal ya sanki aka aura miki? Ni kuma mutum ya ganni ya ce yana so har alqawarin makka da mota ya yi min amma a hanani aurensa, taɓ wallahi sai dai a koreni a gidan nan" Ta faɗa tana gyara zama.
Zaunar da ita Umma tayi har lokacin bata bar kuka ba, ta zauna kusa da ita tare da faɗin "Ki daina damuwa Sumayya, ni nayi niyyar riƙeku kuma ba zan taɓa canja muku ba, tun ranar da Jamilu ya faɗa min Atika bata son shi nace masa ya haƙura, kuma daga ni har shi sam ba zamu taɓa canja muku ba, kuma yazo min da maganar yana so ya aure ki nice ma na dakatar dashi akan kar ya muku dole ya samo dai-dai shi ba dole sai ku ba, ke Jamilu ya taimakawa har ya kawoku asibiti sannan ya ga Atika yake so, to mu kuma ba zamu taɓa tilastawa Atika taso Jamilu dan kawai tana zaune a ƙarƙashinmu" "Ni bana son ta auri wanda take so, ance ba mutumin kirki bane, bana son tasha irin wahalar dana sha" "Addu'a kawai za ki bita da ita, tunda dai ba mazinaci bane, ba kuma ɗan giya bane ai da sauƙi" Kai kawai ta dafe tana jin wani irin zugi a ranta.
07:30pm
Yana zama ya sauke numfashi tare da faɗin "Umma barka da dare" "Barkanmu dai Jamilu ya aiki?" "Umma gashi nan muna ta ƙara himma" "To Allah ya taimaka" "Amin ya Allah" Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin ya ce "Umma ya naji gidan shiru sai ke kaɗai a tsakar gida?" "To gidan ne yau da sauƙi gaskiya, Sumayya dai na nan ɗakina, ita kuma Atika naga ta fita ba daɗewa" "Fita kuma a wannan dare, ina taje?" "Gaskiya bata sanar dani ba, ta fita kawai, ina mata magana ma ko kulani bata yi ba" Jin haka ya tabbatar da akwai matsala, dan haka ya miƙe tsam. "Abincinka yana nan na saka maka a flask ka duba madafa" "To Umma" Ya faɗa tare da shigewa ɗakin Umma.
Ɗagowa tayi ta kalleshi tare da saka hannu ta goge hawayen idanunta, duk da babu wuta, kuma fitilar dake ɗakin ba wata mai haske bace can, amma hakan bai hanashi gane fuskarta ta canja sosai. "Sumayya!" Ya ambaci sunanta yana daga tsaye, numfashi kawai ta sauke bata bashi amsa ba, ya samu guri gabanta ya zauna, sai ji tayi kawai ya saka hannu kan fuskarta yana share mata hawaye "Tun ranar dana ji na fara sonki nayi alqawarin share miki duk wata damuwarki, duk da ni talaka ne, amma alqawari na ɗauka zan zame miki mijin marainiya, dan haka bana so ko kaɗan naga hawaye a idanunki" Idanunta ta lumshe kawai duk da tana cikin ɓacin rai amma kuma kalamansa kaɗai sun saka taji ranta ya yi sanyi, ko dan tunda take bata taɓa tsintar kanta a soyayya ba, zata iya cewa wannan shi ne karo na farko. "Na san baki ci abinci ba ko?" "Bana jin yunwa" "Ban yarda ba, bari na ɗauko abinci muci tare" "Umma fa tana nan" "Eh mana watarana bake zaki dafa ki kawo min ba a gidanmu" Jin haka ya saka ta saka hannayenta ta rufe fuskarta. Murmushi ya yi cikin jindaɗi ya ce "Shi kenan yanzu dai kin san mene?" Kai ta girgiza alamar a'a "Sumayya bana son bikinmu ya ɗauki lokaci so nake nan da wata uku ace kina gidana" Ɗan hararar shi tayi tare da faɗin "Umma na jinka fa" "To ban isa auren ba?" "Ni dai na tafi" Ta furta tare da tashi da sauri, ya bita da murmushi, sam baya son Sumayya har cikin ransa Atika yake so, sai dai ba zai iya ƙin karɓar soyayyar Sumayya ba ko dan ya baƙantawa Atika, kuma kar ya watsawa Sumayya ƙasa a ido.
10:30pm
Tana kwance akan katifa sai juyi take, saboda yanzu bata da waya ma, tun suna asibiti ta bawa Atika aka sayar. Jin sallamar Atika a ɗakin ya saka ta tashi zaune, ta fara ƙoƙarin cire kaya Sumayya ta ce "Daga ina kike?" Kallonta tayi kamar za tayi magana sai kuma ta fasa. "Tambayarki nake daga ina kike?" "Adda wai meyasa kike tuhumata ne?" "Saboda ke amanata ce" "Amma kuma ai ni ba yarinya bace" "Oh ni kike faɗawa haka" "To Alhaji ne ya ɗaukeni muka fara siyayyar lefe" "Atika ya kamata ki nutsu ki kuma san me kike, siyayyar lefen ce har kikayi dare?"
"Adda ni fa ba yarinya bace kuma na san ciwon kaina, dan haka dan Allah ki barni bana son irin abinda kike min" Tana jin zafin yadda Atika ta rainata take faɗa mata magana gatse-gatse tamkar wadda ake zugawa. Kaya ta cire ta kwanta tare da juya baya, Sumayya bata ce komai ba kawai ta tsaya tana mata kallon mamaki.
Washe Gari
Ƙarfe bakwai ta gama komai na gida, tana ta ƙoƙarin ɗora ruwan koko ta ga Atika ta fito da akwati, da ido ta bita, da har ba zata tanka mata ba, sai kuma ta ce "Ya na ganki da kaya?"
"Eh zan koma gida ne"
Miƙewa Sumayya tayi, tana kallon Atika kafin ta ce "Wane gida kenan?"
"Dama muna da gida daya wuce namu? Nan da sati ɗaya za a ɗaura aurena kuma a gidan ubana nake so a ɗaura, nayi magana da Yaya Sani kuma sun ce na koma" Shiru Sumayya tayi, lokacin kuma Umma ta buɗe labule "A'a lafiya? Atika ina za kije da safiyar nan?"
"Zan koma gidanmu dan nan ya fi dacewa a ɗaura aurena, kuma dama Sumayya ce matsalarsu bani ba" Lumshe ido Sumayya tayi cikin jin raɗaɗin furucin Atika. Daga Umma har ita babu wanda ya iya magana har Atika ta tafi, sai kuma ta nufi ɗakin da aka basu da sauri, tana shiga ta fashe da matsanancin kuka, kukan da a yanzu ya zame mata kamar jiki.
Ta ɓangaren Atika kuwa tana fita ta shiga motar Alhaji ya jata zuwa gida, a hanya ne yake ce mata "Ina 'yar baƙin cikin Yayarki wadda bata so ki samu ƙashin arziƙi" "Tana nan na baro ta da ciwon hassada, kuma sai dai ta kasheta" "Ki rabu da ita, kina zaune zata zo ta sameki" "Hmmm anya, wannan tana da taurin kai fa" "Sai dai in matsalar kuɗi bata taso mata ba" "Aikuwa a lokacin zan nuna mata kuskuren data aikata na yi min ƙyashi da hassada." Murmushi kawai ya yi. Har ƙofar gidansu ya sauketa, abinda ya bata mamaki bai wuce yadda taga kowa yana nan-nan ita,sai lokacin ta ƙara tabbatarwa da kanta auren mai kuɗi yana kankaro mutunci. "Mu shiga ɗaki Atika" Basira ƙanwarta ɗiyar Anty Hadiza tayi maganar tana jan hannunta. Suna shiga ta tsaya tana ƙarewa ɗakin kallo, sai take ganin kamar za ta ga Amarya a lokacin, hannu ta saka ta share hawaye tare da zama kan katifa luntsumemiya dake shimfiɗe a tsakar ɗakin. "Ki daina dan Allah, ke da Allah ya miki gyaɗar doguwa ai kukanki ya ƙare." Murmushi kawai tayi, wai yau gashi arziƙi ya saka 'yan uwanta na janta a jiki, sai kuma haushi ya turniƙeta da ta tuna Sumayya na mata baƙin cikin samun da tayi.
**** ****
"Umma gaskiya ni ba sonta nake ba, kawai dama nayi ne ko Atika zata ji haushi ta sauko, sai kuma gashi ƙarshe ta bar gidan nan ma, dan haka ni kawai zan bawa Sumayya haƙuri ta neni wani ta aura, nima Allah ya bani wadda nake so"
"Maganar banza maganar wofi, ai wallahi kai baka isa ka saka naji kunya ba, sai da aka saka biki sannan za kace ka fasa, to bari kaji, Sumayya kamar ta zama matarka ta gama, idan har ka ga an fasa wannan aure to ka tabbatar nice na mutu ko kai ko kuma Sumayya"
Shiru ne ya biyo baya kafin ya ce "Sumayyar nan ta taɓa aure fa, sannan..." "Jamilu ka kiyayeni" Ta furta rai a ɓace kafin ta cigaba da faɗin "Wallahi zan mugun saɓa maka akan wannan, ai duk ka san da haka kace kana so, sai da yarinya ta fara sonka kuma kazo kace baka so"
"Umma ita fa ta fara cewa tana sona"
"Koma mene dai kai kace kaji ka gani dan haka ka fita a idona in rufe Jamilu, karka yarda Sumayya taji wannan maganar ko ta gane wani abu da kake shirin yi ranka zai yi mummunan ɓaci" Tana kai aya kuwa Sumayya ta doka sallama ta shigo. Hannunta ɗauke da ƙaton bokiti, ganinsu cikin ɓacin rai ya saka tayi sanyi, duk da Umma tayi ƙoƙarin fito da murmushi a saman fuskarta.
"Har kin dawo?"
"Eh Umma" Ta furta tana dire bokitin.
"An samo kenan"
"Eh" Ta furta a sanyaye.
"To Allah yi albarka, na san kin sha wahala ko?"
"Ba wahala sosai ma" Ta faɗa tare da miƙewa ta wuce ɗaki.
Zama tayi kan katifa, ta rafka uban tagumi, kawai Iyarsu ta faɗo mata, da kuma Baffa, sai kuma lokacin da mahaifin Kamal ya fara ganinta, abubuwan suka dawo mata tamkar a lokacin aka yi
Waiwaye
Maryam ce ta fara fitowa daga Napep sannan Sumayya, ta kalleta ta ce "Ke ki ga wata dalleliyar mota a ƙofar gidanku" Kallon motar tayi sannan ta kalli Maryam wadda duk ta ruɗe saboda mota. "Ke dalla wai mene haka, sai wani abu kike kamar yau kika fara ganin mota"
"Ba yau na fara ganin mota ba, amma dai kin san irin wannan manyan motocin sai dai mu ga sun wuce ta babban titi amma ba cikin wannan ƙauyen namu ba"
"To naji wuce muji" Dariya Maryam tayi tare da cewa "Ke fa kina nuna kamar mota bata dameki ba"
"Hmmm Maryam kenan, ai ni a duniya babu abinda yafi damuna sama da nayi aure"
"Aure Sumayya?"
Kai ta gyaɗa sannan ta cigaba da faɗin "Maryam ina muradin yin aure, kina ganin yadda ake min gori a gidanmu tun Iyarmu bata damuwa har tazo ta fara, Baffa har sadaka ta ya bayar amma babu wanda ya karɓa ni ban san wane baƙin jini ne dani ba"
"Ki daina faɗar haka, kawai lokaci ne bai yi ba, nima ai na ɗan juma ban yi aure ba a cikin sa'o'inmu."
"To ai ke kin ga Baba bai matsa miki ba, amma ni dai kin ga ai yadda ake aure a gidanmu sai gashi na zarta hakan, ga Atika ma ta kai lokacin tayi auren itama shiru babu wani tsayayye"
"Karki damu Sumayya za kiyi aure ki kuma hayayyafa, lokaci na zuwa, ƙila wani hamshaƙin mai kuɗi za ki aura yadda kike da kyau da diri ai ke matar manya ce"
"Kin ga ki bari bana so" Tayi ƙwafa tana kallonta, dariya tayi dan ta san Sumayya bata so a riƙa kiranta mai kyau, duk da kuwa ita ɗin kyakykyawar gaske ce, amma ta ce ai mace mai kyau dama bata auruwa tsoronta maza suke"
Suna shiga soro suka tarar da shimfiɗar tabarma da kuma sabuwar dadduma akai, lallai da ka ga haka ka san baƙo ne na musamman. Babban mutum ne da a ƙalla zai iya dosar shekaru 60, har ƙasa suka durƙusa suka gaisheshi shi da Baffa, sannan suka miƙe za su wuce, Baffa ya yi saurin cewa "Yawwa dakata Sumayya" Hakan ya saka Sumayya tsayawa ita kuma Maryam ta wuce ciki. "Wannan ita ce Sumayya, tana daga cikin yarana da nake ji dasu saboda kamun kai da kuma tarbiyya irin tata, haƙiƙa sun samu horo ne daga uwa tagari" Har cikin ranta taji daɗin wannan yabo da Baffa ya yi mata"
"Masha Allah, daga yanayinta na lura da hakan, lallai Kamal ya yi mata" Ya furta yana kallonta, ita kuma kanta a ƙasa, taji ƙirjinta ya bada wani dumm. "Sumayya tashi ki shiga ciki" Miƙewa tayi a nutse ta shiga.
Malam ya mayar da kanshi ga Alhaji ya ce "Ina ganin Sumayya za ta dace dashi, dan tana da haƙuri da nutsuwa, kuma tana da addini, ba zata gajiya ba dan ganin ta ceto sa"
"Amma kana ganin babu matsala ka ɗauki 'ya ka bamu duk da ka san halin Kamal"
"Haba Alhaji, ai tarenmu tafi ƙarfin haka, shekara da shekaru nan kake zuwa karɓar addu'o'i da abubuwan da suka dace, to kuma kazo da buƙata indai ina da halin taimakawa ai zan taimaka"
"Na gode sosai, lallai haɗuwata da kai alkhairi ne."
"Ke wai ya naga kin shigo a sanyaye"
"Ji nayi fa wancan mutumin yana faɗin wai lallai Kamal ya yi mata"
"Kece matar?" Maryam ta tambaya.
"Nima na kasa ganewa" Ta mayar da kallonta ga Amarya dake zaune da littafin addu'o'i a hannunta "Iyarmu...." "Kin ga karki saka ni a shirmenki" Ta furta tare da miƙewa ta fita. Sumayya zama tayi jagwaf "Ni fa ban gane ba?"
"To kuma dan baki da kunya Iya zaki tambaya" Ɗan dafe goshi tayi tare da lumshe ido. "Rikicewa nayi"
"To ki daidaita, ai koma dai mene za kiji a gurin Baffa.
Maryam sai bayan magariba ta bar gidan, bata kuma daɗe da tafiya ba Baffa ya shigo, Sumayya na kwance da littafin azkar a hannunta, Atika kuma tana cin tuwo tare da Amarya. Shigowar Baffa ya saka Sumayya tashi zaune. "Baffa barka da shigowa" Sumayya da Atika suka haɗa baki wurin faɗar haka.
"Barka dai" Ya furta tare da zama.
Har za su miƙe su fita ya ce "Ku zauna, ai zuwan naku ne baki ɗaya"
Shiru ba wanda ya yi magana, ya saka hannu a aljihu ya ciro kuɗi masu yawa ya miƙawa Amarya.
"Malam wannan uban kuɗi haka na mene kuma?"
"Ke dai ki riƙe mana ai zan miki bayani"
Karɓa tayi tare da faɗin "Ina jinka Malam"
"Naira dubu ɗari ne, sadakin Sumayya, kuma nan da sati mai zuwa za a ɗaura aure insha Allah"
"Alhamdulillah Allah na gode maka, Sumayya ma lokaci ya yi"
Sumayya har cikin ranta tayi farin ciki duk da bata san waye mijin ba, amma dai ta san Baffa ba zai zaɓa mata mutumin banza ba, sannan kuma ita ko dan gorin da akewa mahaifiyarta tana so ta ga tayi aure, sai dai jin Malam ya ce su dakata sai taji gabaɗaya tayi sanyi.
"Akwai abu ɗaya da nake son faɗa muku, wanda ina so ya zama sirri, shiyasa ma nace gabaɗayanku nake son mu yi magana"
Babu wanda ya iya cewa ƙala a cikinsu, ya cigaba da cewa "Sumayya na san ke macece mai ibada, da haƙuri da kamala, na san za ki iya" Ya ɗan yi shiru kafin ya cigaba da magana "Wannan mutumin daya zo gurina mun daɗe tare, a ƙalla za ayi shekaru biyar, mutum ne da yake girmamani duk da cewar shi ɗin yana da abin hannu, mutum ne da yake taimaka min dan hakanan ya kan ɗebo kayan abinci ya kawo min tare da kuɗin cefane duk kun san wannan"
"Wannan Alhajin na birni?" Cewar Amarya.
"Ƙwarai shi kuwa. To yau ya sameni da wata buƙata wadda naga ina da yadda zan taimaka masa shiyasa na taimakeshi"
"Malam kana ta magana a duƙunƙune dan Allah ka fito ka faɗa mana ko ma mene"
"Yaron shi baya ji kuma ɗan giya ne, sai yake so a masa aure ko ya samu ya shiryu"
Amarya miƙewa tayi tsaye, tare da faɗin "Wallahi ba dai Sumayya ba."
Sumayya kuwa ji tayi gabanta ya yi mummunan faɗuwa.
*** chat me up for your business advert
_SaNaz deeyah✍️