SUMAYYA

Page 12

by @sanazty

SUMAYYA

Wattpad@SaNazdeeyah_

Arewabooks@sanazty

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[tushen mu'amula tagari]

Wannan shafin gabaɗaya na sadaukar ne ga masoyan wannan littafi, haƙiƙa kuna faranta min nagode sosai Allah ya barmu tare🥰🙏

```Page 12```

Jikinta har rawa yake dan bata taɓa ganin Iya ta ɗagawa Baffa murya ba, tun kuma wannan abin da ta faɗa sai kuma ta riƙe baki tare da zama kawai a ƙasa.

"Malam dan Allah ka yiwa Sumayya adalci" Ta furta a sanyaye.

"Sam ban yi haka dan bana son Sumayya ba, hasalima nayi haka ne dan na san yaranki sun fi ko wane yara tarbiyya a cikin gidan nan, na san Sumayya zata iya"

Babu wanda ya iya furta wata kalma, Malam ya ɗan yi 'yan nasihohinsa da basu shiga kunnensu ba ya gama. Sannan ya fita.

Sai lokacin Sumayya taji wasu hawaye masu zafi sun sauka a fuskarta, gashi Amarya sam bata bata damar yin wata magana, ita a dole 'yar fari, ga dare ya yi babu yadda za ai taje gidan Maryam ta faɗa mata ko ranta zai yi sanyi, ranar dai bacci sai ɓarawo daga ita kuwa har Amarya babu wanda ya runtsa. Haka suka cigaba da rayuwa a gidan nan babu wanda ya san wainar da ake toyawa sai su da abin duniya ya damesu, ranar da za a cika sati da maganar a ranar ne Amarya ta yiwa Sumayya magana, tana zaune akan gadon Amarya ta zuba uban tagumi kawai taji an janye hannun. A hankali ta ɗago manyan idanunta da suke cike taf da hawaye tana kallon Amarya. "Ƙaddara ta riga fata Sumayya! Wannan itace ƙaddarar ki, kuma ina da yaƙinin wannan auren shi ne abinda zai kawo canji ga rayuwarki, na san wacece ke na tabbatar ba za ki bawa mahaifinki kunya ba, bana son kowa ya san waye mijin da za ki aura ko kin faɗawa wani?" Sai lokacin hawayen da take ɓoyewa suka samu damar zuba "Iyarmu babu wanda ya sani, ko Maryam da nayi tunanin faɗa mata amma sam na kasa"

"Bana so kowa ya sani, mijinki zai shiryu da addu'arki da kuma jajircewarki kinji" Kai kawai ta gyaɗa. "Yanzu ki tashi ki shirya ki tafi gidansu Maryam ɗin ki zauna, dan yau za a kawo akwatunanki kuma kin san yadda al'ada take"

Kasa daurewa tayi ta ce "Iyarmu yanzu nima irin wannan auren za a min wanda ko mijin da zan aura ban sani ba"

Ɗan kauda kai Amarya tayi sannan ta ce "Ke da zakiyi rayuwa tare dashi ai dole za ki san shi Sumayya"

Wasu sabbin hawayen taji sun samu damar kwanciya saman kuncinta.

Tana zaune a ɗakin su Maryam tana goge hawaye, cike da damuwa Maryam ta ce "Haba Sumayya abinda kike nema ne kika samu fa, daga yanzu shi kenan kin huta da gorin 'yan gidanku, Iya ma za ta huta" Bata iya bata amsa ba, dan ji take wani ɗaci a maƙoshonta, tsoro sosai take, dan in zataje islamiyya su kan wuce wasu 'yan shaye-shaye, ko iya fuskarsu kana gani ka san babu imani, amma kuma sai gashi wai ɗaya daga cikinsu zata aura. Jin an dafa ta ya saka ta ɗago ta kai dubanta ga Maryam "Ba kece macen farko da aka yiwa auren dole a garin nan ba, kuma sun zauna da mazajensu lafiya sun hayayyafa, ga Dije 'yar gidan Malam Hassan gurgu ga kuma Sahura, haba Sumayya kema ki haƙura, kin san damuwar da kike wallahi za ki saka mahaifiyarki da ƙanwarki a ciki, bayan su farin ciki suke kin samu mijin daya fi na ko wace yarinya a garin nan"

Har Maryam ta gama surutanta amma Sumayya bata tanka mata ba.

Bata koma gida ba kuwa sai dare.

Tun daga zaure take jin hayaniya kamar ana gaɗa, hakan ya saka ta ƙarasa cikin gidan da sauri. "Eyeee ni nawa 'ya'yan meyasa baka haɗa su aure dashi ba, sai 'ya'yan Basira ko? 'ya'yan mowa, ai dama tuntuni na san ni baka ƙaunata da 'ya'yana zaman dole kake yi damu kamar yadda muma shi muke yi da kai" Ji tayi gabanta ya faɗi, haka nan ta daure ta kutsa kai bakinta ɗauke da sallama. Duk sukayi shiru lokacin da ta shigo, har ƙasa ta durƙusa tare da faɗin "Baffa barka da dare" "Barkanmu dai Sumayya daga ina kike?" "Naje gidansu Maryam ne" "Ki daina yin dare a waje kinji ko?" Kai kawai ta gyaɗa tare da miƙewa ko ƙafa bata ɗaga ba taji Inna Dije na faɗin "Munafuka mai ladabin kunama" Bata tanka ba ta wuce kawai.

Suna zaune a ɗakin amma suna jiyo irin sababin da akewa Malam, Atika ta kalleta ta ce "Adda wai fa duk akan an kawo akwatunanki goma sha biyar shi ne suke ta wannan abin, tun yamma ake abu ɗaya a gidan nan"

"Akwati sha biyar?" Ta maimaita da mamaki. "Eh wallahi Baffa ma ya ce a mayar"

Sumayya kallon Iya tayi taga hankalinta na kan littafin tauhid dake hannunta tayi imani ba karatun take ba, dan hayaniyar da ake ma ba zai bata nutsuwar yin karatu ba. "Ni kam Allah yasa ba ɗan fashi za a aura min ba" Ta furta lokacin da hawaye masu zafi suka zubo mata, sai lokacin Amarya ta ce "Wai ke meyasa bakin ki ba zai riƙa faɗar alkhairi akan aurenki ba, haba Sumayya ke fa ba yarinya bace" "Amma Iya akwati sha biyar, ni gaskiya tsoro nake" Sai lokacin ta fashe da kuka a fili dan ta kasa ɓoyewa, gashi an hana ta faɗawa Maryam ɗan shaye-shaye zata aura"

Da sauri Amarya ta miƙe, duk a tunaninsu gurin Sumayya zata zo ta rarrasheta amma da mamakinsu sai suka ga ta fice kawai. "Iya ta daina sona Atika" Sumayya ta furta da muryar kuka. "Dan Allah Adda ki daina, wallahi ita kanta Iyarmu ta damu, ina gani ɗazu tana ta goge hawaye, bana so ta gane na gani shiyasa kawai na share na fita na bar gidan" "Mene abinyi? Ya zanyi" Ta furta tana dafe fuskarta dake jiƙe da hawaye.

***** *****

Cikin ɓacin rai yake kallonsa, kafin ya samu kujera ya zauna "Mahaukaci kawai, dan Allah dubeka, gabaɗaya bakayi kama da mutane masu kamala ba"

"Haba Alhaji Kamal fa ɗanka ne, idan har kana jifansa da kalamai mararsa daɗi to waye zai masa masu daɗi?" "To ba za a faɗa masa gaskiya ba, nawa Kamal yake? Duk shekarunsa dai dole sama nake dashi dan duniyarma nina kawo shi, ace ɗana na cikina yana wannan ɗabi'ar taya kike tunanin zan ji daɗi, abokaina so nawa zasu zo su faɗa min sun gashi a mota yana yawo da 'matan banza, ko kuma a wani joint suna shan kayan maye"

"Wallahi in har zaka daka ta mutane to za suyi ta haɗaka da yaranka, to su mene ma ya kaisu gurin da har suka ganshi?"

Murmushi takaici Daddy ya yi tare da cewa "Na lura kamar ke kike goya masa baya akan abubuwan da yake, office ma Kamal sai ya ga dama yake zuwa, meyasa ban yiwa Sadeeq ko su Ayrah ba"

"Hmm! Ba gashi nan da kace Sadeeq Ayrah ce ta biyo bayan meyasa baka ambaci Nihal ba" Ajiyar zuciya kawai ya sauke kafin ya cigaba da faɗin "Ni dai ga abinda na yanke, na yiwa Kamal aure kuma na san ita kaɗaice hanyar shiriyarsa"

A tsorace Kamal ya ɗago ya kallesa, Mommy kuwa da mamaki ta ce "Aure kuma?"

"Ƙwarai da gaske, dan insha Allah wani satin za a kawo masa matarsa, dan haka gidanka za a gyara shi inda zaka zauna da ita, idan ka ga dama karka shiryu ka cigaba da rashin mutuncin daka saba, ni kuwa zan ɗauki babban mataki a kanka, idan kana da buƙatar ganinta zaka iya yi min magana na kwatanta maka ƙauyensu." Yana gama faɗa ya tashi ya wuce bedroom ɗinsa da sauri.

"Mommy kin ji abinda Daddy ya yi, Mommy har sai an zaɓa min matar aure"

"Ka san halin mahaifinka ai mutum ne mai kafiya, Kamal kaima ya kamata ace ka nutsu, yanzu kana ji kana gani zaka auri wata banza daga ji ma baƙauyiya ce"

"Mommy yanzu mene abinyi?"

"Haƙuri mana, ai babu abinda ya wuce wannan"

Miƙewa ya yi ransa a ɓace ya bar ɗakinsa.

A week Later

Guɗa kawai kake ji ta ko ina, an ja mata hijab ɗinta ya rufe mata fuska, tana zaune gefen gadon, Maryam na kusa da ita a lokacin da Iya Zulai ta shigo tana faɗin "To sai ki fito ai, anzo ɗaukarki, mene na kuka ke da babanki ya zaɓa a cikin dubban 'ya'yansa ya yi miki auren gata" Babu wanda ya tanka ta tayi ta yada maganganu har aka fita da Sumayya. Motoci kuwa reras haka aka jera, duk wanda zai je kai amarya to ba zai taɓa rasa mota ba. Gidanta babban gidane daya amsa sunansa gida, tun daga gate gidan abin kallo ne bare a shiga farfajiyar gidan da take zagaye da kyawawan flowers, sai kuma rumfar ajiye motoci tare da kuma ta shaƙatawa a gefe. Makeken mansion ne da yake ɗauke da parlour biyu a ƙasa da kuma ɗaya a sama, sai bedrooms guda biyar, uku a ƙasa biyu a sama, kitchen ɗin babba ne sosai kuma a parlour na biyu yake tare da dinning area.

"Taɓɗijam wannan shi ake kira da aljanar duniya" Cewar Harisa ɗaya daga cikin yayyen Sumayya, Zuwaira kuwa taɓe baki tayi tana ƙarewa bedroom ɗin kallo a ranta take faɗin Malam baya ƙaunarsu daya haɗasu da talaka ita kuma Sumayya ya zaɓa mata mai kuɗi. Ansha cece kuce sosai kafin su tafi, sai dai har suka bar gidan babu ɗaya daga cikin dangin miji da suka gani. Direbobin da suka kawo su sune dai suka mayar dasu, Sumayya da Atika da Maryam kuwa sun sha kukan rabuwa, dan da ƙyar aka ɓamɓare Atika daga jikinta. Gidan ya yi shiru babu abinda kake ji sai ɗan ƙaran fridge ɗin dake bedroom ɗin, a hankali ta zame hijab ɗin jikinta, ta dafe ƙirji tare da dira daga kan gadon. Kallon ɗakin kawai take tana ƙara jin furgici, sai kuma ta fashe da kuka tare da lafewa jikin bango "Baffa gidan 'yan yankan kai ka kawo ni" can ƙarshen gadon ta takure ko motsin kirki batayi, ranar bata yi bacci ba, yadda taga rana haka taga dare, tana takure guri ɗaya, ga sai ta riƙa jin kamar ana ƙoƙarin shigowa, gabaɗaya ta tsorata sosai. Kiran sallar asuba ne ya saka ta sauko tana tafiya cikin sanɗa kamar wata ɓarauniya, ƙofar dake cikin bedroom ɗin ta murɗa a hankali, tana buɗewa taga toilet ne, dan da farko ma bata gane ba, bata san yadda za tayi amfani da komai ba, dan Jacuzzi ne a ciki, ta dai samu ta murɗa da ƙyar har tayi alwallah. Tana fitowa ta ƙarasa jikin drawer ta buɗe, kayanta na gida da kuma lefenta an jeresu a ciki, hijab ɗinta na islamiyya ta janyo tare da abin sallah, bata ma san ina ne gabas ba kawai ta kintata inda ya mata ta shimfiɗa abin sallah. Tana idarwa kuwa ta fashe da kukanta a fili, sai da tayi mai isarta sannan bacci ya ɗauketa anan kan abin sallah.

***** *****

Gyara kwanciya ya yi tare da faɗin "Sadeeq wannan fa ba abin dariya bane"

"Bro ai dole nayi, wai auren dole abin ma babu daɗin ji"

"Ka bari kawai, ni ban san wane laifin nayi wa Daddy ba"

"Ya gaji da ganinka a haka ba aure"

"Amma sai a kasa bani zaɓina, meyasa za a aura min 'yar ƙauye kuma talaka, wallahi ba zan taɓa ƙaunarta ba, jiya aka kaita ko gidan banje ba saboda bana ƙaunar ganinta ma"

"Wai ya take ne?"

"Ina zan sani bayan ban ma taɓa ganinta ba"

Dariya Sadeeq ya yi tare da faɗin "Ai ya kamata kaje ka ga amaryarka muma sai munzo cin abincin amarya"

"Ranka zai ɓaci Sadeeq"

"Tuba nake bro"

"Ya yi, bari na tashi na shirya, zamuyi waya anjima"

"Okay bro"

Yana katse wayar Laila ta sauke ajiyar zuciya, kanta ya shafa, wanda ke kan cinyarsa. "Babe ya dai?" "Am jealous wallahi, ai nice kaɗai ya dace na kasance matarka ba waccan sakaran 'yar ƙauyen"

"Mene na kishi da macen da ko kamanninta ban sani ba, na tsaneta tun ma kafin na ganta, ni fa sam bani da wacce ta fiki a rayuwata"

Murmushi tayi, tare da faɗin "Ya kamata muje mu ga amarya ko?"

Kai ya gyaɗa tare da faɗin "Ya kamata kam."

Kamar daga sama taji ana bugun gidan, a hankali ta buɗe idanunta da suka mata nauyi, ga bacci ga kuma kukan da tasha, daga kan abin sallah ta miƙe tsaye, jin an ƙara bugawa ya saka ta matsa baya, sai dai kuma ganin mai bugawar ba zai haƙura ba ya saka ta nufi hanyar ƙofa, tana buɗewa ta tarar da ƙaton parlour yasha kujeru ash and red tare da wata ƙatuwar plazma da sauran kayan alatu, tsayawa tayi tana ƙarewa ɗakin kallo, ƙirjinta na ƙara dukan uku-uku, bata ma san ina zata nufa ba saboda ƙofofi biyu ta gani, sai dai tana kai dubanta gefen dama taga slicing door a buɗe ma take, a hankali ta fara sauke takunta cikin sanɗa, sai dai tana ƙarasawa taga wani dogon corridor du kda da fitulu masu haske amma hakan bai hana ta dawo wannan parlourn da sauri kuma a matuƙar furgice, a binka ga mace mai zama a gidan yawa kuma tana rayuwa a ɗaki falle ɗaya rak tare da mahaifiyarta da kuma ƙanwarta.

Tunda ya shigo layin ya hango motar gidansu a ƙofar gidan, driver'n Mommy tsaye yana ta faman knocking. "Baby karki fito idan mun ƙarasa"

"Okay" Ta furta tana cigaba da latsa waya, a ƙofar gate ɗin shima ya parker ya fito tare da ƙarasawa gaban driver. "Musa ya dai?"

Juyowa ya yi ya kallesa, suka gaisa sannan ya ce "Ashe ma baka nan ina ta bugawa naji shiru"

"Eh na ɗan fita ne"

"Dama Hajiya ce ta ce na kawo abinci" Ya faɗa yana ɗago basket"

"Allah sarki Mommy kace mungode zan shigo anjima"

"To Yallaɓai Allah ya kaimu."

"Amin ya rabbi."

Yana yin parking ta buɗe murfin ta fito tana ƙarewa gidan kallo. "Duk girman gidan nan ace wata banza 'yar ƙauye ce a cikinsa"

Murmushi ya yi tare da faɗin "Baby sarkin kishi"

"Kishi ko gaskiya"

"Ban santa ba fa, ban kuma taɓa ganinta ba, tare zamu fara ganinta yau"

Ɗan taɓe baki kawai tayi suka wuce.

Tana tsaye a wannan parlour da shi kaɗai ta gani a cikin parlours uku dake gidan, gabaɗaya a tsorace take tana ta kalle-kalle tana sauke ajiyar zuciya da ƙarfi, jin shigowar mutane ya saka tayi saurin juyawa, idanu ta ƙurawa Kamal wanda bata san waye shi ba. Fari ne sol yana da kwantaccen saje da baya gajiya da gyaransa, sai kuma sumarsa ɗan cike take da alamu kan yana jin mayuka amma kuma ba a masa aski ko kaɗan, yana da manyan idanu sai dai kana ganinsa ka san yana cakewa, sai dogon hancinsa wanda ya ɗan baje kaɗan daga ƙasa amma ba irin sosai ɗin nan ba, ya yi dai-dai da fuskarshi, yana da ƙaramin baki mai ɗauke da lips pink tamkar ya saka janbaki, a taƙaice shi ɗin mai kyau ne.

"Wacece ke?" Ya furta lokacin daya ƙarasa gabanta, bata ɗauke idanunta daga kanshi ba, ba kuma ta bashi amsar tambayar da ya yi ba. "Ko ke kurma ce?" Kai ta girgiza alamar a'a.

"Wace ce ke?" Ya furta a fusace.

"Babe wai sai ka tsaya kana bin ta da laluma, bari ka gani" Laila ta furta tare da tafiya gurinta a fusace.

*** for your business advert

SaNaz deeyah🌸✌️