Page 15
by @sanazty
SUMAYYA
```Page 15```
Goro ta gani huhu ɗaya da alawa kwali biyu. "Sumayya kin dawo?"
"Eh Umma, barka da dare" Ta furta cikin sanyin muryarta sannan ta ƙarasa gaban tabarmar ta zauna.
"Gashi inji Atika" Ta miƙa mata ledar da ta zubo musu dubulan dasu alkaki.
"Masha Allah, Allah ya basu zaman lafiya, kece babba sai kin yi haƙuri kar ki yarda wani ya shiga tsakaninki da 'yar uwarki"
"Amin" Shi ne kawai abinda Sumayya ta ce.
Shiru ya ɗan biyo baya har ma ta fara ƙokarin tashi Umma ta dakatar da ita.
"Sumayya wannan goro da alawar da kike gani naki ne, yau bayan kin tafi na saka Jamilu ya sayo, kuma insha Allah gobe lahadi za a ɗaura aurenki da Jamilu"
Ji tayi gabanta ya yanke ya faɗi, ta karanto innalillahi wa inna ilaihi raji'un a cikin zuciyarta lokacin taji Umma ta cigaba da faɗin "Bana son ganin yadda kike a damuwa da kaɗaici shima kuma haka, wannan dalilin ne ya saka na janyo auren naku ya dawo kusa."
Sumayya dai ji tayi kamar tatsuniya Umma ke yi mata.
"Akwai atampopi da leshi gabaɗaya guda goma ne, dan Allah kiyi haƙuri a hankali za a ƙarasa miki, nayi ƙoƙarin ayi miki lefe sai dai baya da ƙarfin yi, na saka gyale biyu da hijab uku da kuma 'yan turaruka da kayan kwalliya."
"Umma wannan ai ya yi yawa, sai kace budurwa"
"Babu macen da za tayi aure ace bata buƙaci wannan ba"
Shiru tayi bata ce komai ba.
Sai gidan da zaku zauna, na samo hayarsa, amma ƙarami ne sosai kuma baya da wani kyau ba sabo bane, nace ya yi fenti gobe, amma ya nuna baya da kuɗi, saboda duk sauran kuɗaɗen ne aka haɗa aka bawa kafinta aka karɓi gado, aka sayi katifa, fulo ma ɗaya aka saya sai zanen gado da aka yanko a wambai. Sumayya duk ban ji daɗi ba daya kasance babu kujeru, kwanuka ma a nawa kawai na ɗiba na baku, tare da katanga guda ɗaya, sai dai na sanar masa daga zarar ya samu kuɗi ya samu ya saya miki mangal da gawayi dan sai ya fi miki daɗi tunda ku biyu ne"
Hannu ta saka ta goge hawaye tare da cewa "Iya wannan kaɗai Umma kin yi min, babu abinda zance sai dai nace Allah ya biyaki da gidan aljanna"
Da sauri Sumayya ta miƙe ta bar gurin tana zubar hawaye. Umma ta sauke ajiyar zuciya dan har ga Allah ba dan Sumayya tayi wannan ƙoƙarin ba, tayi ne dan ɗanta da taga ya shiga damuwa sosai lokacin da aka ce masa Atika tayi aure.
Bayan Watanni Uku
Daga side ɗinsu suka fito, a parlour ta ɗan tsaya, tana ta zuba masa shagwaɓar data saba. "Wai Jidda baki girma ke?"
"Yanzu Habibi har ka fara ce min Jidda saboda ka ganni da ƙaton ciki ko?"
Murmushi ya yi sannan ya kai hannu ya dafa cikin "Baby karka yarda ta haɗamu da kai, domin duniya ma ta shaida bana son kowa sama da kai da ita."
Jin fitowar mutum ya saka suka juya gabaɗaya. Hamdiyya ce ta fito da shirin fita.
"A'a kece yau kika samu fitowa, jikin da sauƙi kenan" Hamdiyya ta faɗa tana kallon Jidda.
"Eh da sauƙi, Habibi ne zai fita sai nace bari na ɗan taka masa"
"Aikam dai kin kyauta, amma naga har yanzu ƙafufunki a ɗan kumbure."
"Eh wallahi shiyasa ma aka ce in ɗan riƙa tattakawa"
"Allah ya raba lafiya, amma wannan Baby da ba dan ɗana bane da sai na ranƙwasheshi in yazo duniya dan ya wahalar mana ke"
Murmushi kawai tayi tare da faɗin "Kamar fita za kiyi ko?"
"Wallahi kuwa zanje duba wata friend ɗina bata da lafiya"
"Tare da Yaya Sadeeq zaku je?"
"Wannan tambayoyin fa kamar wata 'yar jarida" Cewar Kamal.
Ɗan turo baki tayi tare da faɗin "Ni fa kawai tambaya nayi in ba tare zasu fita ba sai ka sauke ta tunda fita za kayi"
"Sorry Madam dan naga yanzu a kusa kike"
Murmushi kawai tayi, Hamdiyya kuma ta ce "Ke da kika san Yayan naki sai 5 yake dawowa, ai ba a samun kanshi in ba da weekend ba"
"Habibi ka sauketa ko?"
"Angama ranki shi daɗe" Ya furta yana mata peck a kumatu.
Yana saka mota a titi ya kalleta "Hotel zamuje ko guest house?"
Harara ta watsa masa tare da faɗin "Oho!"
"Me nayi ne?"
"Oho!"
"Haba my watermelon ni ɗin zakiyi fushi dani?"
"A gabana kayi pecking ɗinta ka san ai zanji kishi ko"
Riƙo hannunta ya yi, ta fuzge.
"To wai hakan da nayi ba gashi mun samu mun fito hankali kwance ba sai kinje wani wuri na ɗaukeki acan ba"
"Ni dai bana so, karka kuma yin haka a gabana, dan zuciyata zata iya fashewa, ko in nuna naji haushin haka a gabanta"
"Bazan sake ba dear, ita fa peck ne, ke kuma yanzu mai gabaɗayan ne, sai yanda kika yi dani, muna nan fa yau har dare."
Murmushi tayi ta kwanta a kafaɗarsa tare da lumshe ido.
Kai tsaye ɗaya daga cikin gidajensa da yake sheƙe ayarsa ya kaita, dan ko maigadi babu, haka suka yi badaƙalarsu suka gama, basu ko kunyar juna, shi wan mijinta ita kuma matar ƙaninsa, amma haka suke a sati in basu haɗu sosai ba to su haɗu sau biyu, sun mayar da kansu kamar mata da miji, sun maida Jidda da Sadiq shashashu dan basu gane komai ba, duk da ita Jidda at times ta kan so ta gane amma kuma basu bata wata ƙofar da zata ankare ba.
Suna kwance kan gado yana rungume da ita yaji ta sauke ajiyar zuciya, da kanshi ya ɗago da kanta suna fuskantar juna "Ya dai? Kamar kina da damuwa? Ko mu tashi muyi wanka ne?"
Kai ta girgiza alamar a'a. "Mene damuwar?"
"Baby ina son na haihu!" Jin haka ya saka ya janyeta daga jikinsa, ya janyo jallabiya ya saka yana ƙoƙarin tashi tayi saurin rungomoshi "To ina kuma zaka je?"
"Zan yi wanka, kema in ba zaki iya jira na fito ki shiga ba sai kije wani toilet ɗin, gara nayi dropping ɗinki akwai inda zanje "Babu inda zakaje sweet kawai magana ta ne ta ɓata maka rai, ni banyi dan kaji ba daɗi ba"
Shiru ya yi baice komai ba.
"Baby please ka fahimceni ina so na haihu koda cikinka ne ba dole sai Sadeeq ba"
"Ni kuma bana son ki haihu yanzu ki haƙura kawai."
"Amma meyasa baka son na haihu bayan ga Jidda nan da tsohon ciki kuma tana ƙara samun kulawa daga gareka"
"Idan wannan ke ɓata miki rai to na daina, amma ki sani da kin haihu kyaunki zai fara disashewa sannan idan kina da ciki ba zamu samu mu riƙa sheƙe ayarmu ba, ni kam kawai ki haƙura ba yanzu ba, kuma karki yarda kije asibiti dashi kamar yadda na faɗa miki saboda zai gane ke da kanki kike shan maganin hana ɗaukar ciki, amma idan Sadeeq ya matsa sai kunje to ni na san ta inda zan ɓullo masa karki damu akwai Dr da zan yi magana dashi duk ranar da Sadeeq ya matsa miki kice aje gurin Likitanki daga nan ni na san abinda za a ce masa wanda dole zai haƙura"
"Duk da nima ina son haihuwar amma Sadeeq ya fini gaggawa domin da auren namu dududu shekara ɗaya ne fa da wata biyu amma duk ya bi ya wani damu kansa kamar ba wayayye ba"
"Rabu da sakarai in banda ƙaddara ma ace mace mai diri kamarki gaki nan full option amma ace Sadeeq ne mijinki wannan lusarin wanda bai iya kula da mace ba"
"Ya cika babban lusari kam, tunda a cikin gidanma muna kashe ƙirshirwarmu amma har wannan lusarar Jiddar bata ganewa ai gara Sadeeq ma ba wani zama yake ba"
"Ya za ki cewa Jidda lusara?"
Baki ta saki ta ce "Oh ni babu daɗi ka cewa Sadeeq? Shi da yake ɗan uwanka na jini ma"
"Jidda ma jinina ce tunda aurenta nake"
Da sauri ta sake shi ta zauna a gadon "Ya naga kamar ka ji haushi? Oh kenan dai kishi kake baka son na faɗa? Ka faɗa min idan Jidda ta fini muhimmanci?"
Murmushi ya yi tare da faɗin "Dama so nake naga wannan haɗe ran naki, amma ai kinsan Jidda ba komai bace indai kina nan, ai itace babbar lusara ma" Murmushi Hamdiyyar tayi tana faɗin "Dan ka ga ina kishi shi ne kake son tsokanata ko?"
Murmushi ya yi tare da faɗin "Babe yamma tayi muje muyi wanka"
Yaja hannunta suka shige toilet.
***** ***** *****
Tana zaune a gaban murhu tana ta faman iza wuta, sallamar da taji ya saka ta ɗago ido ta kalli ƙofa, dan jin abin tayi kamar a mafarki.
"Wai dama ke ɗin ce ba mafarki nake ba?"
Atika tayi murmushi tana ƙarewa gidan kallo "Wallahi nice Adda"
Miƙewa tayi ta saka hannu tana goge hawayen da take na dole "Wallahi itace na samu ɗanye, shigo mana"
"Ince dai ke kaɗai ce?"
"Yana nan yana ciki, amma shi ɗin ai ba baƙonki bane"
"Kar inje ya koreni fa" Ta furta a hankali.
"Ah haba taya zai yi haka, shigo mana bacci ma yake"
"To shi kenan" Ta furta tana kutsa kai ciki ita kuma Sumayya ta mara mata baya.
Ledar tsakar ɗaki ce kawai a ciki, sai dustbin na roba dake gefe. "Bari na ɗauko miki abin sallah ki zauna"
"A'a nan ma ya yi Adda ai naga babu datti" Ta faɗa tana zama. Itama Sumayya zama tayi, a dai-dai lokacin Jamilu ya fito daga ɗaki, yana ganin Atika ya washe baki "A'a Hajiya Atika manyan ƙasa, kune a garin"
"Wallahi kuwa Yaya Jamilu ina wuni" Ta furta tana sauke kai ƙasa.
"Lafiya lau, ai kam bari aje a samo miki ruwa mai sanyi"
"A'a ka barshi ma kar in sa ka wahala"
"Haba ai dole a samo, bari mintuna biyu yanzu zan dawo"
Sumayya mamaki kawai take yanda yake washe baki yana magana da Atika, ita kuwa yanzu akan gishiri ya balbaleta da bala'i baya da kuɗi sannan ya shige ɗaki ya barta a tsakar gida.
"Adda amma nayi mamaki, wallahi na ɗauka ko kallon mutunci ba zan samu daga Jamilu ba"
"Haba ai ba zai yi haka ba, komai ai ya riga da ya wuce"
"Hakane amma kuma Adda in tambayeki?"
"Ina jinki"
"kina jindaɗin auren Yaya Jamilu?"
"Meyasa kika min wannan tambayar?"
"Na ga kin rame Adda, kuma kin yi duhu"
Murmushi kawai tayi kafin ta ce "Ina fama da laulayi ne shiyasa"
"Laulayi kuma, ba dai ciki ba"
"Eh ciki"
"To kunje asibiti?"
"Muna dai shirin zuwa"
"Adda kamar kina ɓoye min wani abu?"
"Babu komai Atika idan da akwai ai zan faɗa miki."
"To shi kenan tunda dai baki son faɗa, ya gida ya zafi?"
"Alhamdulillah"
"Amma Adda kin fi son ki zauna a haka? Ki auri talaka shi a wahale ke a wahale, ki duba ki gani fa falonki ko kayan ɗaki babu."
"Atika kenan har yanzu kin kasa fahimtar shi aure albarkarsa kawai ake so."
"To ai ni ban ganta ba sai talaucin da kike ciki kawai nake gani. Adda ki kalleni fa wallahi babu abinda na nema na rasa a gidan mijina, ko da akwai matsaltsalu na aure ni daular da nake ciki ta wanke min komai, yau kwananmu biyu a garin nan kuma sati biyu kacal zamuyi mu koma, ni fa yanzu zaman Abuja da Lagos kawai nake na zama 'yar lele a gurin Alhaji saboda nice mai ƙananun shekaru a matansa yafi ji dani."
"Hmmm! Amma..." Jin sallamar Jamilu ne ya saka Sumayya gintse maganar da take ƙoƙarin yi. "Sumayya yi sauri ki tashi ki ɗauko plate da cup" Ya furta yana ajiye ledar, sai wani rawar kai yake kamar yau ne karo na farko daya taɓa ganin Atika.
"Ah haba itace a samana fa. taya zata tashi"
"To ai ke baƙuwarmu ce"
"Ni ba baƙuwarku bace gidan nan gidan Adda ne ka ga kuwa ba baƙona bane duk da yau na fara zuwa"
"Tunda kin hanata ni bari na ɗauko miki da kaina"
Ajiyar zuciya kawai Sumayya ta sauke.
Ranar dai Jamilu bai fita ba, koma sun yi niyyar yin wata magana ta sirri bai basu dama ba, ya kafa ya tsare. Sai yamma liss sannan ta shirya tafiya. "Ko nazo na miƙa ki gida?"
"Ah haba dai ai ba nisa sai na hau napep, direba ne ma baya da lafiya da shi ne zai zo ɗaukata"
"Sai na miƙa ki ai dama daga nan ina son zuwa gurin Umma"
"Kar in takuraka"
"Haba karki damu ba wani takura"
"To na gode"
Sumayya kuwa har ƙofar gida ta rakasu sai da taga tafiyarsu sannan ta koma ciki, sai kuma ta fashe da kuka. Auren mai kuɗi bai mata daɗi ba ta ɗauka haka auren duk wani mai kuɗi yake gashi kuma auren talaka ma baya mata daɗi sam.
*** for your business advert.
SaNaz deeyah