SUMAYYA

Page 16

by @sanazty

SUMAYYA Wattpad@SaNazdeeyah_

Arewabooks@sanazty

```Page 16```

"Yaya Jamilu gaskiya kana da kyakykyawar zuciya, da har ka iya manta komai, ni fa a tsorace nazo gidan nan naku, saboda wata uku da auren ban taɓa zuwa ba, kuma bani da wata 'yar uwa data wuce Adda bana so naƙi zuwa tayi tunanin har yanzu fushi nake"

"Ba za taji komai ba, saboda ai tsakanin bikinki da namu kwana uku ne fa, ta san ke amarya ce ba lallai mijinki ya barki ki fito ba. Ni kuma tani ki daina wannan batun dan sam bana ganin laifinki Atika, har yanzu ina..." Sai kuma ya yi shiru. Murmushi tayi tana faɗin "Karka ce min kana sona har yanzu?"

"Soyayyar gaskiya bata taɓa disashewa"

"Hmmm Yaya Jamilu kenan, yanzu duk irin wulaƙancin da nayi maka har yanzu kana sona?"

"Ko kaɗan banji sonki ya fita a raina ba"

"Allah sarki. Amma ka san mene?"

"Sai kin faɗa"

"Wallahi Adda ta fini komai, tun daga kyaun fuska har kyakykyawar zuciya, tana da kawaici da haƙuri, kayi ƙoƙarin fara sonta da tarairayarta zaka yarda da abinda nake faɗa maka, amma ni dama a yanayin da nazo na sameku naga kamar bata cikin farin ciki"

"Tana cikin farin ciki, kawai dai yau da gobe ne, kin san dai bani da wata sana'a da ta wuce ɗan sahun nan, ga abinci ga kuɗin haya ni kaina idan kika kalleni za ki gane ina tare da damuwar"

Shiyasa naƙi aurenka ai, itama Adda tayi ganganci. Ta furta a rai, kafin a fili ta ce "Yanzu ka san mene zai faru?"

"Sai kin faɗa"

"Zaka iya koya min tuƙin mota? Idan ka iya zan haɗaka da Maigidana kaje a matsayin direba na, na san zaka samu kuɗi"

Washe baki ya yi tare da faɗin "Na iya mota sosai ai har tuƙin mota na taɓa yi, ni in kin yarda ma sai na zama direbanki na dindindin"

"To shi kenan za muje sai na masa bayani, amma karka nuna ka sanni fa yana da kishi"

"To ai zai iya sanina tunda ɗan unguwarmu ne"

"No ba zai sanka ba, karka yarda ka nuna kaine, zan canja sunanka ma"

"To hakan ma ya yi" Ya furta a fili a ransa kuma ya ce Na samu damar da zan riƙa kasancewa dake a koda yaushe.

Tana shiga kai tsaye tafkeken bedroom ɗinta ta shiga, ta cire gyale ta ajje sannan ta ƙarasa gaban mirrow, tana ƙoƙarin cire 'yankunne aka buɗe ƙofar aka shigo, juyawa tayi ta kalleshi. "Kana gida kenan?"

"Eh ai ta sama naga shigowarki ma"

"Eh ban daɗe da dawowa ba"

"Ya kika same su?" Juyowa tayi tana kallonsa kafin ta ce "Eh na sameta lafiya lau, sai dai..." Sai kuma ta zauna gefen gado.

"Sai dai me?"

"Tana ɗauke da ciki kuma yana matuƙar wahalar da ita wallahi"

"To ai yanzu taga tsiyar auren talaka"

Murmushi tayi tare da faɗin "Hakane tayi wauta da yawa, ta kasa gane abinda nake nuna mata"

"Ke da kike ƙarama ai kin fita hankali."

"Gaskiya tana buƙatar taimako"

"Amma dai ba daga gurina ba ko?"

"Alhaji ita ɗin 'yar uwata ce, na san yadda laulayi yake saboda nima nayi kafin cikina ya zube"

Murmushi ya yi tare da janyota jikinsa "Ba yanzu nake so ki haihu ba sai mun gama dirzar amarcinmu"

Itama murmushin tayi tana ƙara shigewa jikinsa "Alhaji na samo wanda zai koya min driving"

"Ai yanzu babu buƙata"

Ɗagowa tayi tana kallonsa "Amma meyasa?"

"Saboda ni na samo wanda zai koya miki, ba wani bare ba, ina da kishi ai"

"Amma har na masa alƙawari kuma zai fara zuwa gobe"

"Zan baki dubu goma kawai ki bashi ya yi haƙuri"

Ajiyar zuciya kawai ta sauke dan sam ba haka taso ba.

"Maganar zuwa london jibi ce, dan haka sai mun dawo sannan za ayi batun koyon mota ma"

"Jibi kuma Alhaji?" Ta tambaya da mamaki

"Eh har an gama komai ma"

"Amma baka faɗa min ba, ban yi sallama da Adda ba" Jin haka ya saka shi janyeta daga jikinsa tare da kallonta.

"Baby karki manta ƙasar waje gurin zuwana ce, kuma bana iya yin watanni biyar ba tare da naje ba, and dake zamu riƙa tafiya, so ba dole sai kin mata sallama ba, ba wani daɗewa zamuyi ba, wata biyu ne ba yawa"

"Wata biyu ai da yawa, gaskiya zan koma gobe nayi mata sallama."

"Ban amince ba" Ya furta tare da juya mata baya.

"Meyasa?"

"Saboda Yayarki bata ƙaunata Baby, so bana son tana sanin duk wani abu daya shafi rayuwarmu, yanzu ma kin ga zuwan na ganin Dr ne, so no need ta sani zamu je lafiya mu dawo lafiya"

"Na san bata kyauta ba, kuma ita kanta ai tayi nadamar abinda tayi na tabbatar kunya ce take hanata zuwa"

"Yanzu ai ga auren talaka nan ta gani, da yanzu kece a wahalen nan, ina amfanin auren talaka?"

"Hmmm talauci kam babu ta inda zai maka rana, gashi ni yanzu ɗan turancin nan ma ban iya ba"

"Za ki iya ke dai bari muje mu dawo ni na san tanadin da nayi miki"

"Allah Alhajina?"

"Dagaske Baby"

"Amma naji daɗi"

"Kiji daɗinki Baby" Ya faɗa yana hugging ɗinta.

***** ******

Tsaki yake ta jerawa ita kuma bata tanka masa ba, dan idan ya shigo da wannan ɓacin ran muddin ta tanka masa to a kanta yake huce haushinsa.

Tana daga zaune a parlourn tana yankan farce, bayan ta gama kuwa miƙewa tayi da niyyar ta bar ɗakin ya ce "Ke Sumayya me kike nufi?"

Juyowa tayi tana kallonsa kafin ta ce "Kayi haƙuri Yaya Jamilu, na ga ranka a ɓace shiyasa"

"Oh kin mayar dani sakarai kenan, ke a matsayinki na mace baki san idan mijinki yana cikin damuwa ki kwantar masa da hankali, anya ke macece ma kuwa?"

Taji zafin kalamin amma ta danne ta ce "Ai ba a cikin damuwa kake ba, a cikin ɓacin rai kake, kuma indai kana cikin wannan yanayin da zarar na maka magana to ni nake kwana a ciki, domin a kaina kake hucewa"

A fusace ya miƙe tare da faɗin "Mahaukaci kike ɗaukeni?"

"A'a amma ka..." Mari ya wanketa dashi tare da faɗin "Ki iya bakinki, ni anzo an haɗani da bazawara mai farar ƙafa, lokacin da ban aureki ba samuna ya fi haka amma yanzu gabaɗaya kin tsiyata ni" Bangajeta ya yi ya wuce, abin yazo da tsautsayi aikuwa ta faɗi ƙasa wanwar, wani mahaukacin ƙara ta saki, ya juyo a tsorace, ai tuni jini ya fara gangarowa ƙasa ta ƙafafunta.

Bayan Sati Ɗaya

Tana zaune a gadon asibitin ta jingina bayanta, Umma kuma tana zaune akan kujerar roba. Shigowa ya yi hannunsa ɗauke da baƙar leda. "Umma sannu da ƙoƙari"

"Yawwa Jamilu sannu kaima"

"Ya jikin nata?" Ya furta yana kallon Sumayya, ita kuma ta sauke kanta ƙasa.

"Jiki da sauƙi sosai ma"

"Allah ya ƙara sauƙi"

"Amin"

Zama ya yi gefen gadon tare da kallonta "Babu abinda kike buƙata?"

Kai ta gyaɗa alamar eh.

"To sannu"

"Yawwa" Ta furta a sanyaye. Ya mayar da kallonsa ga Umma. "Anyi sallama amma bayan sati uku zamu dawo za a ƙara dubata"

"To Allah ya kaimu ya kuma bata lafiya, sannan ya mayar mata da mafi alkhairi"

"Amin"

Har ƙofar gida suka sauke Umma, ya shigar mata da kaya, sannan ta kalleshi "Ko zata ɗan zauna nan zuwa kwana biyu?"

"A'a Umma ai ta samu sauƙi"

"To shi kenan kai dai girki ne baka so kuma baka so kazo ka karɓa anan wai kai ka girma ko?"

Murmushi kawai ya yi yana ɗan sosa kai.

"Sumayya Allah ya sawwaƙe amma idan kinji ba za ki iya ba, ki saka ya dawo dake nan kinji"

Bata ce komai ba sai ma ƙara sauke kai da tayi ƙasa.

Yana fara driving wayarta ta fara ringing, ganin number waje kuwa abin ya matuƙar bata mamaki, a hankali ta kara a kunne tare da sallama.

"Adda ya kike?"

"Atika!" Sumayya ta furta tana ƙara kallon wayar.

"Kin yi mamaki ko?"

"Eh sosai ma, naga ba number Nigeria ba"

"Eh wallahi munje london da maigidana, zamu ɗan yi wata biyu mu ɗan huta"

"Amma ba zaki faɗa min ba sai yanzu Atika"

"Kiyi haƙuri Adda tafiyar ce tazo babu shiri"

"To shi kenan Allah ya kiyaye hanya, ya dawo daku lafiya"

"Amin, ya jikin naki?"

"Da sauƙi sosai"

"To Allah ya ƙara sauƙi"

"Amin"

"Kamar naji kina magana da Atika" Jamilu ya tambaya yana tuƙa ɗan sahu.

"Eh itace"

"Dama waje ta tafi?"

"Nima yanzu naji"

"Shiyasa taƙi kirana kenan"

Bata ce masa komai ba dan bata ma da abin faɗa.

**** **** ****

"Amma Dr kana ganin babu matsala"

Tun kafin Dr ya yi magana Hamdiyya tayi saurin cewa "Babu wata matsala ma, shi ya ce zai iya fa, ni ina ganin babu komai"

Gyaran murya Dr ya yi tare da cewa "Hakane shi ya ce zai iya, kuma tunda sun amince ai baka da matsala."

Kai Hamdiyya take gyaɗawa tana kallon Sadeeq kafin ya ce "To shi kenan."

Driving yake ita kuma tana daga gefe ta ce "Nima dai zan fara tutiya da Baby na"

"Dear dan dai kawai kin dage, amma kin ga ko Nasir da muka fara tuntuɓa ƙin amincewa ya yi"

"Ni dai zan ɗauki wannan kasadar Baby saboda ina son naga jinina"

"Allah ya kawo mana masu albarka"

"Amin ya rabbi"

"Zan sauke ki a gida ni kuma ina son wucewa gurin Mommy"

"Zuwa yaushe zaka dawo?"

"Gaskiya zan iya kaiwa dare"

"Haba Babe dare kuma"

"Sorry kin san na kwana biyu banje ba"

"To shi kenan amma ka dawo da wuri please"

"Insha Allah"

Yana sauketa yaja motarsa, ita kuma kai tsaye ta nufi gidan, tana shiga main parlour ta tarar da Kamal a kwance kan three seater hannunsa ɗauke da remote.

"Welcome my sweet melody" Jin haka ya saka tayi saurin kallon bayanta, shi kuma da sauri ya tashi zaune. "Ba dai tare da Sadeeq kuke ba?" Kai ta girgiza tare da faɗin "Jidda fa?"

"Bata nan, come give me a hug" Murmushi tayi sannan ta ƙarasa, ya rungumeta tare da zaunar da ita kan cinyarsa. "Me kike ci naji kinyi nauyi haka?"

"Soyayya mana"

Dariya sukayi gabaɗaya, ya bata peck a kumatu tare da faɗin "Muje ciki ko?"

"Sadeeq ba yanzu zai dawo ba, amma Jidda fa?"

"Itama haka, na turata gida, kuma na tabbatar ba yanzu za ta dawo ba"

Bedroom ɗinsa ya kaita, ya ɗorata a bisa gado suka fara sheke ayarsu.

"Mommy ni ina ganin Ayrah ba za tayi haka ba"

"Aikuwa gashi nan tayi, sai anyi abu ta ce an tsaneta, bayan itace sam bata jin magana, ga kuma daƙiƙanci"

Hannu Ayrah ta saka tana goge hawaye "Wallahi na tsani halin yarinyar nan, kuma ubanta ne yake ɗaure mata"

"Mommy stop saying that insha Allah ba zata ƙara ba"

"Ta cigaba wallahi idan har ta ɗebo min abun kunya sai na ɗauki mummunan mataki a kanta, ai taga yadda aka wa matar yayanka"

Jin haka ya saka gabanshi ya faɗi, dan har ya manta da Sumayya sai yanzu ma ta faɗo masa.

"Insha Allah zan mata magana"

Miƙewa Mommy tayi ta bar gurin rai a ɓace.

Nihal da Ayrah kuwa babu wanda ya iya motsawa daga inda yake. "Meyasa kike haka Ayrah?"

"Bata ƙaunata ne kawai, wallahi guduwa zan yi na bar mata gidan"

"Baki da hankali kike irin wannan maganar kuma a gabana"

Ajiyar zuciya Nihal ta sauke tare da faɗin "Yaya maganar gaskiya Ayrah bata kyautawa"

"Hmmm" Shi ne abinda Ayrah ta ce sannan ta miƙe ta bar gurin da sauri.

Tayi ruf-da-ciki a kan gado haka ya sameta tana kuka tana shashsheƙa. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yaje bakin gadon ya zauna "Tashi Ayrah muyi magana"

Jin haka ya saka ta miƙe zaune, ta saka hannu ta goge hawayen daya mata shaɓe-shaɓe a fuska "Yaya wallahi ba 'yar iska bace ni, ban taɓa riƙe ko hannun namiji ba, Mommy bata sona kawai saboda bani da ƙoƙari, kuma a hakan ma ina dagewa nayi karatu"

"Meyasa in driver yaje ɗaukarku ake nemanki a rasa?"

"Bana son dawowa gida da wuri saboda yadda ake muzguna min, shiyasa nake bin ƙawata gidansu."

"Ita Mommy ai ba zata fahimta ba"

"Amma Yaya zargina fa take, har asibiti ta kaini aka dubani, ni na gaji da zaman gidan nan, ban san laifin da na yi wa Mommy ba"

"Ya isa haka kiyi haƙuri zan yi magana da ita, zata daina insha Allah"

Za tayi magana wayarsa ta fara ringing. Ɗagota ya ya yi kalla, number ce dan haka bai san waye ba.

"Ina zuwa bari na ɗaga waya" Ya furta yana kallon Ayrah. Kai kawai ta gyaɗa masa, shi kuma ya ɗaga wayar.

"Malam Sadeeq barka da yamma"

"Barkanmu dai"

"Fatan kana lafiya kuma kana keɓaɓɓen guri"

"Ban gane dawa nake magana ba?"

Daga cikin wayar yana jiyo dariyarta kafin ta ce "Ba sanina ne abin daya fi muhimmanci ba, kawai ina son ka saurare ni"

"Duka biyun suna da amfani amma dai ina jinki"

"Nayi mamaki da har aka kai wannan lokacin amma baka taɓa sanin ko gane matarka tana cin amanarka ba"

"Ban gane ba?"

"Idan kana son sanin komai ka sameni yanzu a Calido, zan maka bayanin."

"Amma..." Ƙit ya ji an kashe ya kalli wayar, ya sake kira sai dai ba a amsa ba.

"Yaya lafiya?"

"Ayrah ina zuwa!"

Ya furta cikin tashin hankali sannan ya fita, ko Mommy bai yiwa sallama ba sai jin tashin motarsa tayi.

SaNaz_deeyah🌸