Page 23
by @sanazty
SUMAYYA
Wattpad@SaNazdeeyah_
Arewabooks@sanazty
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[tushen mu'amula tagari]
Free
Page 23
"Zauna Sadeeq" Kallon Daddy ya yi tare da kallon Jidda sai kuma ya zauna.
Kowa ya kasa cewa komai sai Amma ce ta ce min "Nima ai kun faɗa min magana makamanciyar haka"
"Amma ba gaskiya bane, kawai nayi ƙarya ne saboda in rabu da Kamal ni na tsane shi kawai ya bani takardata" Sai kuma ta saka kanta tsakanin cinyoyinta ta fashe da kuka.
Sadeeq lumshe ido kawai ya yi ya ji kansa yana sara masa.
"Duk abinda zai faru dai ya riga ya faru, Hamdiyya dai an cuceta an ɓata mata suna, ni ban taɓa tunanin abin arziƙi zai zama na tsiya ba, sharrin zina fa, Allah ya isa" Maman Hamdiyyar ta furta rai a ɓace.
"Haba Atine wannan wace irin maganace?"
"Irin wadda ta dace Alhaji, idan kai ba za kayi magana akan cin zarafin da aka yiwa 'yarmu ni zanyi, ai dama saki babu hujja ba yau aka fara shi a gidan nan ba, tashi Hamdiyya mu tafi, in ban da ƙaddara ina ke ina aure a gidan da babu daraja" Ta furta tana miƙewa tsaye. "Kune dai mararsa daraja amma mu babu wannan a zuri'armu" Mommy ta faɗa a fusace.
"Idan da akwai ai da ta nuna kanta, tunda har ƙani zai yiwa wa sharrin ya kama shi da matarsa, wannan wace irin rashin daraja ce, gidan nan ba gidan da za a kawo aure bane ko a nema, muma rashin sani ne ya jefa mu"
Mommy zata sake mayar mata martani Daddy ya hanata. Ita kuwa Maman Hamdiyya da Baban Hamdiyyar ma ya hanata kansa ta koma, ranar dai taron haka ya watse babu daɗi.
Jiri-jiri haka Sadeeq yake ganin komai na masa doubling, dan haka babu shiri ya juya ya nufi ɗakinsa a daddafe, yana shiga ya faɗa kan gado tare da fashewa da kuka a fili, abinda bai taɓa yi ba a rayuwarsa.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shi ne kawai abinda yake ta nanatawa.
"To wai mene ribar Sadeeq idan ya yiwa Kamal ƙazafi?" Cewar Mommy. "Dan Allah for now ina son abar maganar nan ta wuce, tunda dai mai faruwa ta furu a kiyaye gaba kawai"
"Ko da za a kiyaye ya kamata ka kira Sadeeq kayi masa nasiha akan ƙazafi domin ya ɗauki alhaki, kuma idan basu yafe masa ba ba zai taɓa ganin daidai ba, har gara Kamal ma ɗan uwansa ne, amma Handiyya dai zai yi wuya ma ta yafe masa. "Daddy kana tunanin ni kaɗaine ke shaye-shaye? Abinda Sadeeq yake a ɓoye wanda baka sani ba idan an tona ba zaima kowa daɗi ba, amma ni na yafe masa, abar maganar kawai" Cewar Kamal.
"Ka gani ko? Kai ni dai wannan abu bai min daɗi ba" Mommy ta furta tare da wucewa side ɗinta.
Daddy kallon Kamal ya yi cikin nutsuwa da kwantar da murya ya ce "Kamal tunda har abin yazo da haka, duk da dai saki baya da daɗi amma ka sawwaƙe mata a huta, kuma dan Allah komai ya wuce kar hakan ya saka ka samu saɓani da ɗan uwanka ko ka daina magana dashi, in anjima shima Sadeeq ɗin zan yi magana dashi"
"Daddy komai ya wuce a gurina, ni kawai naji daɗin taron nan saboda ko babu komai an wanke ni a gurinku, ba zan taɓa iya cin amanar wani ba bare shi ƙanena da muke uwa ɗaya uba ɗaya."
"Wannan ɗabi'a ce msi kyau, kada ka zalunci kowa koda kowa zai zalunce ka, Allah ya muku albarka"
"Amin Daddy"
"Nima fita zanyi, kana gida har magriba?"
"Eh to nima naga gidan da Daddy kamar kowa a damuwa yake, zan fita zuwa gobe zan dawo insha Allah, amma kafin nan zan yi magana da Sadeeq dan ya gane cewa ni ban ji haushinsa ba"
"Okay! Ka faɗawa mahaifiyarku na fita"
"Daddy a dawo lafiya"
"Amin Allah ya sa"
"Amin."
Sai da har ya ji tashin motar Daddy sannan ya nufi side ɗin Sadeeq. Yana tura ƙofar Sadeeq ɗin ya taso a fusace ya nufosa.
"Fita, fitar min a ɗaki bana ƙaunar ganinka Kamal"
Murmushi Kamal ya sannan ya ƙarasa gaban gadon ya zauna "Ba zan fita ba Sadeeq har sai na amaar maka abinda ke cikina"
"Babu wata maganarka da nake so ji sai ƙwaya ɗaya"
"Oh ashe dai akwai abinda kake son ji daga gareni?"
Lumshe ido Sadeeq ya yi yana jin ƙunar rai ya ce "Me ka faɗawa Jidda wanda ya saka taƙi faɗar gaskiya? Ka faɗa min me ka mata?" Murmushi Kamal ya yi mai wuyar fassara kafin ya ce "Ai dama sharri ake min kuma gashi nan yau gaskiya tayi halinta.
"Za dai tsyi halinta a gaba, ranar kuma ba zata taɓa maka daɗi ba, baƙi ciki, ƙunci da raɗaɗi sai ka shiga fiye da wanda na shiga Kamal, na san Amira ba zata taɓa maka ƙazafi ba, kuma da ace ba gaskiya bane da Jidda ba zata taɓa ƙin komawa gidanka ba"
"Amma ai na san kunnenka ƙalau yake, kuma ka ji dalilin Jidda na ƙin komawa gidana"
"Wannan bai isa dalili ba"
"A wurinka ba"
"A wurin kowa ma, saboda duk wanda ke zuwa gidanmu zai tabbatar da Jidda na sonka, ni na san akwai wani dalili mai ƙarfi da ya da tayi ƙarya, amma duk daren daɗewa wallahi ni na san sai Mommy ta gane kaine maci amana." Jin an shigo ya saka Kamal gintse maganar dake bakinsa. "Sadeeq ka shirya zamu fita"
Kallonta ya yi sannan ya ce "Mommy ni bani da ƙarfi zuwa ko ina"
"Ina jiranka a mota" Ta furta tare da wucewa. Murmushi Kamal ya yi tare da faɗin "Ka sake lale" Ya fita tare da ja masa ƙofa.
************
Kuka sosai take tunda suka zauna Amma bayan tsaki babu abinda take ja, Abi kuwa tunda ya sauke su yaja mota ya bar gidan. "Kin bani mamaki Jidda, ashe duk maganganun da kika faɗa ƙarya kike masa? Amma kika zauna ki yi min kukan kama shi kikka yi"
Amira da ta fito daga ɗaki kallonsu tayi "Amma ya naga tana kuka kuma"
"Ke dalla rufa min baki, duk bakinku ba a haɗe yake ba, kuka zauna kuka yiwa bawon Allah sharri dan kawai ya saketa"
"Amma ban gane ba, waye muka yi wa sharri?"
"Ban sani ba, idan kika yi wasa a kanki zan huce" Da sauri Jidda ta miƙe tayi ɗakinsu. Zama Amira tayi sannan ta kalli Amma ta take ta ƙara tsuke fuska.
"Amma dan Allah ki min bayani"
"Yanzu Amira kin kyauta kenan? Kuka biyewa Jidda kuka yiwa mijinta mummunan ƙazafi kawai dan ya saketa?"
"Amma ban gane ba? Ta ya zamu yiwa Yaya Kamal sharri?"
"To idan ba sharri bane meyasa Jidda ta musa a gaban mahaifan Kamal, ta ce ita bama ta faɗa ba"
"Haka ta ce?"
"Ban sani ba" Amma ta faɗa cikin ɓacin rai.
"Amma na rantse da girman zatin Allah ƙarya take, ranar da muka je gidan akan gadonta na sunnah ta kamasu, ihunta na jiyo naje, kuma ina zuwa na tarar da wannan ƙazantar wallahi Amma sai dana shiga ma ya fara laluben rigarsa, Amma me Yaya Kamal ya yi min da zan masa ƙazafi?"
"To meyasa ta ƙaryata Sadeeq?"
"Gaskiya sai dai in wani dalili, amma wallahi ba sharri aka masa ba"
"Tashin hankali"
"Amma bari naje na sameta" Amira ta furta tana miƙewa da sauri. Tana shiga ɗakin ta tarar da Amira tana zaune ƙasan gado tana kuka. "To mene abin kuka, ai Yaya Sadeeq ya kamata ya yi kuka bake ba" Bata tanka mata ba, ta cigaba da faɗin "Gaskiya baki kyauta ba, kuma ban taɓa tunanin za ki faɗa ba, yanzu wane kallo kike tunanin za ayi masa da kika kasa faɗar gaskiya"
"Amira ki ƙyaleni dan Allah"
"Ba zan ƙyaleki ta ya ya kin san gaskiya amma zaki ɓoye"
"Babu ruwanki"
"Da ruwana, kuma wallahi sai naje na faɗa cewa ƙarya kike kuma nima ai ganau ce ba jiyau ba"
"Hmmm! Amira kenan kar ma ki fara wannan ganganci"
"To so kikeYaya Kamal ya ci bulus shi kuma Yaya Sadeeq ya shiga matsala?"
"Gara Sadeeq ya shiga matsala da ya rasa rayuwarsa"
"Me kike nufi?"
"Ni dai na faɗa miki, nima ceton Sadeeq nayi daga halaka saboda ya rayu ya kuma ɗauki mataki anan gaba, amma da na dage dai na faɗi gaskiya wataƙila da yanzu Sadeeq baya raye"
"Kamarya kenan? Kina nufin Yaya Kamal cewa ya yi zai kashe Yaya Sadeeq"
"Kamal zai iya komai dan ganin ya rufe sirrinsa"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Amira ta furta tana zaman dirshen a ƙasa.
"Amira na cece rayuwar Sadeeq ne" Jidda ta faɗa tana goge hawaye.
"Dama Yaya Kamal baya da imani?"
"Wallahi Allah text ya yi min a waya saboda ya kira naƙi ɗauka, ya ce min muddin na faɗi gaskiya sai ya kashe Sadeeq"
"Barazana fa yake miki wallahi ba zai iya ba"
"Zai iya, ya tabbatar min zai halaka Sadeeq tunda har ya tona asiro, maimakon ayi taron tonom asiri sai dai ayi zaman makokinsa, sai ni kuma na roƙesa akan dan Allah kar ya yi haka, ni zan ƙaryata abin"
"Taɓɗijam!" Amira ta faɗa tana dafe goshi.
"Nayi dana sanin auren Kamal"
"Shege mugu, in Allah ya yarda sai ya tagayyara a duniya matsiyacin banza"
Ita dai Jidda kasa cewa komai tayi.
***** *****
Sai daya gama rubuce-rubuce sannan ya ɗago ya kalleta "Hajiya a gaskiya mun duba mun ga babu wata matsala da yake da ita"
"Dr ka tabbata?"
"Ba zamu taɓa faɗa miki abinda ba dai-dai ba"
"Okay! Yanzu ba za a iya bashi magani ko wani abu da zai yi ba?"
"Ai baya da wata matsalar da za a bashi magani, gaskiya ƙwalwarshi daidai take sai dai ko yana da wata damuwa amma dai ba ta taɓin hankali ba"
Kallon Sadeeq tayi ta ce "Tashi muje"
Mamakin Mommy kawai yake haka ya tashi ya bita suka tafi.
Tana driving ta kalleshi ta ce "Amma gaskiya Sadeeq nayi mamaki sosai da aka ce min lafiyar ka lau, a iya sanina baka shan komai, sai da matsalar ta faru ka fara, ko kuma dama kana sha bamu sani ba?"
"Mommy ni a yanzu babu abinda zan iya cewa amma dai na san koma mene a gaba zaku gane gaskiyar abinda nake faɗa, kuma ko bana raye dole gaskiya za tayi halinta"
"Wace gaskiya? Kawai dai a bar maganar nan, Allah ya sawwaƙe, amma na tabbatar sunan gidanmu ya gama ɓaci"
"Mommy ki saukeni a gidan Goggo"
"Meyasa?"
"Saboda can nake so na koma da zama"
"Can kuma? Saboda ka san acan babu mai tsawatar maka?"
Bai ce komai ba, kawai ya juyar da kai gefe.
Gida ya ga ta wuce, bai tanka mata ba, saboda baya son yawan magana ma. Tana yin parking ya sauka tare da saurin shigewa cikin gidan.
Ayrah da Hafsat suna hira ya shigo. "Yaya sannu da zuwa" Ayrah ta faɗa, bai tanka ta ba ya wuce kawai, Hafsat ta bi bayanshi da kallo. "Ayrah mene ke faruwa?"
"Ɗazu anyi meeting a gidan nan"
"Amma kuma baki faɗa min ba"
Tana shirin magana Mommy ta shigo. Kallonta suka yi, itama dai da ganin fuskarta akwai damuwa a cikinta.
"Mommy sannu da zuwa"
"Yawwa Ayrah" Ta kalli Hafsat ta ce "Ita kuma wannan mene ya kawo ta?"
"Mommy Aunty Hafsat ce fa?"
"Ai na fiki sanin wacece, mene tazo yi mana bayan ta gama lalata komai"
"Ni kuma Mommy?"
"Ke mana!" Ta faɗa cikin faɗa. Hafsat sakin baki kawai tayi, ganin laifin wani yana neman shafarta. "Me nayi?"
"Gidanku" Mommy ta furta rai a ɓace. "Dalilin waye Sadeeq ya fara shaye-shaye? Ke ba dan darajar mahaifiyarki ba ai wallahi sai na saka an ɗaure min ke"
"Mommy ni ban saka Sadeeq ya yi shaye-shaye ba, iya abinda na sani kawai na san ya kirani ya sanar dani yana gidan friend ɗinsa."
"Ke dalla gafara can, tun a lokacin da kin faɗa mana ai da anyiwa tufƙar hanci"
"Ni bani da laifi akan haka" Ta faɗa tare da fashewa da kuka, jakarta dake kan center table ta fuzga sannan ta juya ta fita da sauri. "Idan kin ga dama karki sake dawo mana gida" Ayrah kallon Mommy kawai tayi ranta a ɓace, tana mamakin hali irin na Mommy.
Sadeeq daya fito da trolley Ayrah ta mayar da kallonta gareshi "Yaya...! Yaya dan Allah karka tafi" Ta faɗa tare da fashewa da kuka. Kallonta kawai ya yi cikin ƙunci ya ce "Ayrah ba zan iya zama a gidan nan ba, saboda wanda ake so ne kaɗai ake bashi gaskiya"
"Me kake nufi?" Mommy ta tambaya tana kallonsa. Bai bata amsa ba kawai ya wuce.
"Karka sake ka je ko ina, dan baka da gidan daya fi wannan?"
"To ai ni wannan gidan a baƙin gida nake kallonsa, gara ma daji da gidan nan, wallahi Mommy ko tsine min za kiyi ba zan kwana a gidan nan ba." Yana gama faɗa ya wuce.
Har yanzu akwai ragowar kwanaki uku kafin promo ya ƙare, wanda basu biya ba su hanzarta su biya ₦300 ta account ko kuma katin waya. Idan promo ya ƙare za a saya ne a farashin ₦500 kafin a saka ko group, dama ce gareku yanzu
Adamu Halima Salahu
7035111671
Opay
Sai shaidar biya ta wannan number ***
SaNazdeeyah_🌸