BABBAN GIDA

Chapter 1

by @nazeefanashe

A al’adance a kuma kowanne lokaci duk dare baya samun nutsuwa ba tare da ya yi wankan da ya zame masa jiki ba, ya fito tsaf cikin pyjamas hannunsa riƙe da wayarsa ɗayan hannun kuma cup ɗin Chocolate hot tea ne, wanda alamu suka nuna yanzu ya haɗa shi. Zama ya yi gefen bed ɗinsa idonsa still akan waya kamar yarda ya saba duk dare a sannan yake duba duk wasu social media don bashi da lokaci sama da wannan lokaci, cikin followers da suka masa requesting ya tsayar da idanunsa kan suna guda da ganinsa sai da ya saka zuciyarsa ta yi wani irin bugawa, har bai san sanda cup ɗin hannunsa ya zame ba sai da ya ji zafin tea ɗin ya ratsa fatar cinyarsa sannan da sauri ya kalli abinda ya yi ɗin, hakan bai saka ya mayar da hankali kan abinda ya aikata ba. Hannunsa na rawa ya sake scrolling sunayen sai gashi still sunan ZAKIYYA ZAWIYYA, ya sake bayyana a saman screen ɗin nasa. Da sauri ya danna yatsantsa wajen sunan don ya kai shi direct page ɗin nata hannunsa sai rawa yake kamar yarda zuciyarsa take daka tsalle a cikin ƙirjinsa ya fara tunanin ko mafarkan da ya saba ne? A kullum a koyaushe da suke masa jiki na ɗabi'a? Ko kuma imagination ɗin da ya zame masa abokin tafiya ne?

Ba komai a shafin nata na Instagram blank yake haka nan ba wani hoto a profile nata illa sunanta da ya bayyana sosai ZAKIYYA ZAWIYYA, ya runtse idonsa yana kallon yarda har date of birth ɗin ma irin na Kiyya ne, Kiyyansa Kiyyan Anna Kiyyan JADDA, how comes? Ya tambayi kansa da kansa don bai taɓa ji ko ganin irin haka ta faru ba shin wanda ya mutu aka binneshi dama yana dawowa duniya? Kanshi ya kulle ya rasa mai bashi wannan amsar nan da nan ya fara jin ciwon da ya kwanta masa yana shirin dawo masa. Da sauri ya ɗau wayarsa ya fara kiran gida sai dai duk wanda ya kira bata shiga. Kasa nutsuwa ya yi bai san sanda ya shiga internet ya fara booking flight da zai isa Nigeria a washegari ba ko in the next two days, duk da wata zuciyar na son ƙaryata shi da nuna masa tabbas ba Kiyya ba ce may be wani ne a cikin ZAWIYYA Family ke son amfani da sunan, KIYYA TA MUTU. Sun kuma binneta da hannunsu al’amarin da har yau ya kasa barin zuciyarsa, al’amarin da yake girgiza duniyarsa lamarin da har yau kuncinsa da ɗacinsa bai bar zuciyarsa ba, ranaku ɗaiɗaiya ne baya kwana da kukan zuciya na tunanin Kiyya a ransa. Kiyyan da ta hana shi kallon kowacce mace a matsayinta na Mace, tuni ya saka kansa a layin waɗanda suka zo duniya ba don su yi aure ba, tun bayan rasa Kiyyarsa, wannan tunanin yana yin sa ne ba tare da ya san mai ZAWIYYA Family suke

ciki ba.

Ya zubawa Frame ɗin da yake side bed ɗinsa ido. Kiyyan ce a cikin hoto sanye cikin uniform ɗinta na primary school ranar da ta shiga grade 2 ba abinda take sai zabga murmushi an mata ƙananan Kalba a kanta, bai manta sanda aka yi hoton ba ya zauna daram a zuciyarsa a lokacin ta gama kukan kitso har ya zaneta saboda rigimar banzan data zauna tana musu, Jadda ce ta saka aka mata hoton bayan ta gama lallashinta

Ya saki ajiyar zuciya har yau idan ya tuna a sanda Kiyya ta mutu ba mutumin da ta tsana take kuma masifar jin tsoro sama da shi, sai yaga kamar ba zai iya yafewa kansa ba, ya ji haushin kansa ya ji tsanar kansa, nadamar abubuwan da ya aikata mata sun sabbaba masa wani ciwo da har yau yake jinsa a ƙasan zuciyarsa.

Ya janye idonsa daga kan hoto yana danne leɓensa na ƙasa da ɗan ƙarfin gaske ya furta “YA ALLAH KASA ZAKIYYA TANA CIKIN NIIMARKA”

Wani irin bacci ya yi a cikin daren, mai cike da tarin mafarkai game da Kiyyan. Don haka ko bayan tashin sa daga bacci ya yi sallahr nafila ya zauna yana karatun kur’ani kafin gabatowar sallahr asuba. Fatansa da burinsa Allah yasa Kiyyan na cikin Ni’ima. Sai ya ji zuciyarsa ta yi nauyi da ya tuna tabbas wancan şuna da yaga yana yawo a media ba mamaki wani ne yake amfani da sunan, amma saboda me to? Me yasa za’a yi amfani da sunan yarinyar da ta daɗe da mutuwa, yana buƙatar sanin amsa, idan ya tabbatar kuma ɗaya daga cikin Zawiyya’s ne ya aikata hakan tabbas mai raba shi da shi sai mutuwa. Ya samu zuciyarsa da ɗugunzuma da ɓacin rai, har yana Jin yarda yake fitar da huci a saman laɓɓansa. Da ƙyar ya miƙe daga saman sallayar bayan kammala Azkar ɗinsa. Yana zaune kawai ya samu kansa da sake Jan wayarsa da laptop a karo na biyu ya hau Twitter kamar abin al’amara idanunsa suka sauka akan sunan ZAKIYYA ZAWIYYA ta yi liking wani shirmen posting da aka turo, da sauri ya sake shiga page ɗinta still page ɗin ba komai blank ne zuciyarsa na wani irin tafasa ya hau binciken sunan a Google sak ya yi bayan da Google ya watso masa bayanan ZAKIYYA ZAWIYYA, jim ya yi yana mamakin yarda aka rubuta Biography ɗin sunanta da komai date of birth ɗinta da sunan Mamy da Aby ɗinta unguwar da take a Kano da kuma inda ta girma ENGLAND. A can ta yi karatu from primary har secondary da University, wannan karan zuciyarsa ta tsananta bugun da take bayan ganin ta nuna ta dawo Nigeria 2Weeks ago ya dinga scrolling yana mamaki da al’ajabin wannan abin. Tabbas ba abinda jakan yake nuna masa sai Kiyyansa is still alive! da gaske tana raye? Ya akai hakan ta kasance?

Tambaya da rashin amsa daga zuciya ɗaya, zuciyarsa, me hakan ke nufi?

Bai san sanda ya fara booking flight ticket ba da zai kawo shi Nigeria a next few hours, ba zai wa kowa maganar ba har sai ya je Nigeria zai tabbatar musu ZAKIYYA tana nan da rai.

*

Sanyi ake sosai a cikin garin Bauchin sanyin da ke ratsa jiki ya saka wata irin kakkarwa a gaɓoɓi. Duk da wannan sanyi da ake yinsa sam ZAKIYYA bata Jin sa don tana tsaye a balcony ɗin da yake cikin ɗakinta. Idonta zube a harabar masarautar kamar mai nazari ko ƙididdige tsuntsayen da suke shawagi a filin Masarautar. Sai dai sam ba haka bane wani irin zafi take ji a zuciyarta zafin da ya haddasa mata rashin nutsuwa ya kuma sabbaba mata ciwon kai. Hannu ta cusa cikin şumar kanta tana yamutsa gashin da şaurin gaske tamkar hakan da take shi zai saka mata nutsuwa, tamkar hakan shi zai saka ta ji sauƙin abinda take ji a zuciyarta. Madadin hakan ɓacin ranta ne yake sake hauhawa har tana Jin yarda idanunta suka tara ƙwalla. Shin me yasa Granny ba zata gane adadın yarda zuciyarta take buri da zumuɗin komawa cikin ZAWIYYA Family ba ne? Me yasa ba zata gane akwai waɗanda take son gani waɗanda basu mata komai ba ƙaunarsu still tana nan cikin zuciyarta, me yasa aka zaɓi ta yi nesa da ahalinta zuri’arta har ma aka maishe ta matacciya a wajensu? Tana ganin Mammy kamar yarda Aby ma baya daɗewa bai kawo mata ziyara ba har can inda take an England amma Jadda fa? Kakarta da take Jin wata irin kewarta? Ta saka yatsa ta share ƙwallar da ta gangaro ƙasan idonta kafin ta lumshe idonta a hankali leɓenta ya ɗaga kaɗan cikin natsuwa wajen furta

“I missed them, i missed all of them…..,”

Cak leɓenta ya tsaya kafin a hankali zuciyarta ta yi wani irin masifaffen bugu da rawa da ta tuna abinda ta ce “ZAYYAD!” shima tana missing ɗinsa? "Nop!" ta furta da ƙarfi idanunta yana sake runtsewa ta fara tunano mummunar ranar da ta yi sanadiyyar zamanta matacciya, kamar yanzu abin ya faru ta dinga kallon majigin yanayin cikin idanunta, zuciyarta na sake bugu, tsanarsa na sake hauhawa a sokar zuciyarta muryar.

Mammynta da Jadda raɗau a kunnenta cikin wani irin kuka Mammy take furta “Me ye wannan? Jini Jadda jini ne yake zubowa dubi ki ga, ZAYYAD sakamakon alherin da ke tsakanina da kai kenan?”

Ta ji Jadda ma ta şaka şalati tana furta “Ka yi asara Zayyad… me zaka ce da Uban yarinyar nan da ya sadaukar da duka lokacinsa wajen son yaga ka yi farin ciki? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!” da sauri ta dinga yamutsa gashin kanta tana girgiza kanta sai kuma ta ja jikinta cikin azama ta koma ɗakinta a guje, ganin tuna maganganun da suka shuɗe na ƙoƙarin sake azabtar da zuciyarta, ta zube a saman gado tana sakin wani sabon kuka da ƙarfin gaske wanda ya yi sanadiyyar da Anna ta ji ta fito da sauri zuwa bedroom ɗinta tana furta “Zakiyya menene?”

JIKAR NASHE✍🏽