FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
✍️ Welcome to the World of Nazeefah Sabo Nashe ✍️ If you love emotional stories, family drama, secrets, betrayal, destiny, and unforgettable plot twists, then you’re in the right place. 📚 My Published Novels: 🔥 ƘWARYAR WUTA (Now Available) ❤️ Me Zan Yi Da Ita? 🤔 Ya Abin Yak...
Sample · Chapter 1
A al’adance a kuma kowanne lokaci duk dare baya samun nutsuwa ba tare da ya yi wankan da ya zame masa jiki ba, ya fito tsaf cikin pyjamas hannunsa riƙe da wayarsa ɗayan hannun kuma cup ɗin Chocolate hot tea ne, wanda alamu suka nuna yanzu ya haɗa shi. Zama ya yi gefen bed ɗinsa idonsa still akan waya kamar yarda ya saba duk dare a sannan yake duba duk wasu social media don bashi da lokaci sama da wannan lokaci, cikin followers da suka masa requesting ya tsayar da idanunsa kan suna guda da ganinsa sai da ya saka zuciyarsa ta yi wani irin bugawa, har bai san sanda cup ɗin hannunsa ya zame ba sai da ya ji zafin tea ɗin ya ratsa fatar cinyarsa sannan da sauri ya kalli abinda ya yi ɗin, hakan bai saka ya mayar da hankali kan abinda ya aikata ba. Hannunsa na rawa ya sake scrolling sunayen sai gashi still sunan ZAKIYYA ZAWIYYA, ya sake bayyana a saman screen ɗin nasa. Da sauri ya danna yatsant...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.