Chapter 5
by @reeeyarh
page 5
*~reeeyarh~*
Da murmushi ya karaso inda take yace yar abbah yau ma gashi mun sake haduwa, amma ai bazaka mini komai ba ko, ba abinda zan miki, hala gurin biki kika zo ko, eh! okay mu shiga nima nan nazo.
Sai a lokaci yayiwa ma’akatan sa nuni da su biyo shi.
Suna shiga idon kowa ya koma kansu, du’a har saida taja baya zata koma, yarima ya rike hannun ta, daga kai tayi ta kalle shi, yace ina zaki.
Zan jira fatiha a waje, saimu shigo tare, aa muje zan kaiki har wurin ta, kamar zatayi kuka tace aa ni gida zan tafi.
Ki nutsu mana ba wanda zai miki wani abu.
Fatiha ce ta karaso wurin, besting menene, ni gidan zan koma, waike meke damun ki zomu shiga ciki, sakin hannun ta yarima yayi, yaya ya nagan ku tare?
Kamar ya, dama wannan ce besting taki, eh yaya, hannun sa yasa yadan daga fuskar ta yace Sannu besting fatiha.
Kasa magana tayi, saiya kara cewa fatiha kidai kula da ita kar abbah yasa a daure mu, sai’a lokaci du’a tayi murmushi.
Fatiha mamaki take ya akayi yarima yasan du’a, sai tace idan sun koma gida zata tambaye shi.
Mutane da yawwa idon su na kan du’a musamman ma islam dake jiran zuwan yarima , sai gashi tagan shi da wata.
Ina safna, gasu can a zaune, suna tafiya fatiha tace ke a ina kika san yaya, a jirgi muka hadu, ok.
Mami tayi mamakin ganin du’a, besting muje ki gaida mami kafin muje wurin su.
Suna zuwa mami ce sai ammi, ummah, sai kuma maman amarya(mah).
Nan ta gaida su, taga kowa sai kallon ta yake, mami ce ta fara amsa wa, suma duk suka amsa.
Du’a kice kema an gayyace ki, mami sultana ce ta gaiyya ce ni, da gaske, eh.
Ai nayi tunanin fatiha ce ta gayyace ki, aa, ranar da naje gidan ku baki nan, eh wallahi nazo gidan aunty nane, masha Allah, mami bari muje gurin su sultana,
Kedai baki son a taba kwawar ki, du’a yaushe zaki zo, zan tambayi ammi idan ta barni zanzo in sha Allah.
Suna isa inda su safna suke, suka ce du’a amma kinyi kyau sosai.
Islam ce ta karaso wurin, fatiha bakuwa muka yi, eh, friend din nace du’a, okay wai dama itace, eh, tab, fatiha ce tace eh itace da wani abune, du’a zauna, ta zama nan aka shiga hidimar biki, lokaci da suka tafi rawa du’a na zaune, islam da meeno ne suka zo inda take.
Yanzu ke dan jaraba har nan saida kika biyo ta, hadda wani yin anko. meeno ce tayi maganar.
Ke wai uban wa ya kawo ki gurin nan, yarinya saika ce mayya kodan, ba sani ba abu’a duhu inji islam,
Meeno ki daina zagina ina ganin mutunci mami banso a samu masala, oww mu iyayen mu yan iska, ko.
Ni kike kira da meeno, ke badda fatiha ta jawo ki ko hanyar wurin nan baki isa kinyi ba.
Du’a ta fara kuluwa, kawai sai ta tashi zata fita, islam tayi saurin tura ta, ta zauna, akan idon yarima .
Du’a ce tace ki barni na tafi, gida zan tafi, ta tashi tana tafiya, ta kusa zuwa kofa yarima ya ruko hannun ta, ina zaki je?
Ka sake ni gida zan tafi, me yasa, kawai kaga ni ka kale ni.
Fita sukayi daga cikin event din, islam da meeno na kallon su, duk sun tsora ta dan sunsan yau babu me hana yarima cin uban su, musaman meeno da zasu kwana a gida daya.
Ke kukan me kike, nace ka rabu dani, toh amma saikin fada mini kukan me kike, daga kanta tayi tace ba komai ni gida nake son tafiya.
Tam shikenan muje na kaiki, aa da kaina zan tafi, okay kafin ki tafi fada mini me ya hada ki da meeno, ni kuma, eh ke.
Ni bansan ta ba, du’a!!
Na’am, me suka miki, ba komai, okay bari naje na karbo key saina kaiki gida kinji, nifa zan iya zuwa gida da kaina.
Okay bari na kira abbah nace mishi wai da tsohon daran nan zaki tafi gida da kanki, bata ce mishi komai ba.
Number abbah ya lalubo ya nuna mata, data ga da gaske yake, sai tace toh yaje ya karbo.
Aa saida muje tare, ni bazan koma ba, saiki jira ni a kofa, sukaje har bakin kofa.
Fatiha tun dazu take neman du’a, ta duba ko ina a event din amma bata ganta ba, suna kofar tazo ta gansu, besting wai ina kika je sai neman ki nake.
Gida zata tafi inji yarima , gida kuma me yasa, gata nan ki tambaye ta.
Du’a mai yasa zaki tafi, kuma ai safna na nan, eh na sani ki kale ta banson takura mata.
Haba besting dan Allah kizo mu koma, lokaci yarima ya tafi amso key, nan ta fada mata abinda ya faru.
Wai dama saboda su zaki tafi toh wallahi ba inda Zakije, fatiha amma kin san ai, gaskiyya suke fada, kawai ni ki barni na tafi, kinsan halina zan iya jure komai, amma bada zagin abbah.
Kuma idan na koma komai zai iya faruwa.
Du’a mami na kiran ki, daga kai tayi ta kalle shi sannan tace ina key din, gashi amma ki fara zuwa mami na kiran ki,
Ai wallahi saina fada wa mami, kamar ya nidai bance ki fada mata ba, saina fada, nace karki fada tunda bake akayi wa ba.
Suna isa inda mami take tace du’a wai gida zaki tafi, eh mami kayna na mini ciwo shi yasa, ke kuma lafiya, ba komai, du’a ki dan bari a kara jima wa, ni dakai na zan kaiki har gida, kinji.
Shi kuma tunda yaga ta je wurin mami ya koma cikin abokan sa
Suna bari wurin mami, du’a tace fatiha ni banason komawa, ke muje mu zauna bazan kara zuwa ko ina ba.
Du’a ina kika je inji safna , naje wurin mami ne. kinga bari na kira driver yazo mu tafi, fatiha ce tace aa mami tace tare zamu tafi.
Zama sukayi, aka kawo abinci du’a tace bazata ci ba.
Mami ce ta kira fatiha suzo su tafi, tashi sukayi fatiha da du’a, safna, sultana.
Suna zuwa fatiha tace ita ba yanzu zata tafi ba zata toho da su ummah, okay du’a kuzo mu aje ku a gida.
Suna fita lokaci yarima na waje shida abokin shi, suna ganin mami suka je inda take, adam (abokin yarima ) ne yace mami tafiya zakiyi, eh adam tafi zanyi, sultana ce tace yaya ina yini, lafiya lau sultana, sai su du’a suka gaida shi, fatiha ce tayi kasa da kanta tace ina yini, lafiya lau, mami tun yanzu, adam wallahi na gaji kuma zan kai yarannan gidan, okay,
sultana ce tace yaya wannan besting nace, ta nuna du’a, wata harara fatiha ta mata. Mami tayi murmushi tace oh ni Safiyya, fatiha wannan wana irin kallo ne, anya fatiha zan kaiki gidan kishiya.
Adam ne yace haba mami ai fatiha ita kaidai ce babu wata kishiya, Kaga fa yace take dan ance friend dinta ce besting.
Mami tana da gaskiyya, nima duk ranar da tace mini tayi wata friend din akoy matsala, ko besting. Ni wallahi mami kice sultana ta daina mini wannan abu.
Besting karki damu babu wacce zata shiga tsakanin mu, kinga nima fa ina da besting ko safna, murmushi safna tayi tace gaskiyya sultana ki daina tsokanar ta.
Adam ne yace fatiha yanzu zaki tafi ne, aa du’a na rako.
Mami ce tace du’a mu tafi ko, mami kawai yaya ya kaisu tunda area gidan shine fatiha ce tayi maganar, toh ce miki nayi a can zan kwana.
Toh a ina zaka kwana, mami ni yau a gida zan kwana, me yasa, akoy abinda zanyi a gidan shi yasa.
Sultana ce tace besting na du’a sai gobe, dadai kinyi wa besting ki ta gaskiyya sai gobe dan du’a ba zuwa zatayi ba.
Mami ce tace fatiha banson iskanci akan me zaki hanata zuwa, bani na hanata ba ita tace bazata zuba. Me yasa, ba komai.
Mami mu mun tafi du’a sai munyi waya, okay bye.
Mami mu tafi inji du’a, adam ne yace mami kije kawai zan kaisu.
Bafa hanyar gidan ku bane malan inji yarima , aa muda mami zamu tafi, toh yar abbah ku tafi yarima ne yayi maganar.
Saida mami tasa aka fara kaisu har gida sannan itama aka kaita.
Lokaci da ta dawo yarima har ya dawo.
A palo ta tarar dashi, har ka dawo, eh mami! Zama tayi tace yawwa dama dazu nayi shiru ne saboda mutane, me yasa bazaka kwana a gidan ka ba, mami wallahi inada abin yi shi yasa, okay ai shikenan tashi tayi ta tafi daki domin ta canza kaya. Shima tashi yayi ya tafi dakin shi.
Lokacin dasu du’a suka dawo ammi na zaune a palo, har kun dawo, eh ammi sannu da hutawa. Yawwa, ya bikin, du’a dan turo baki tayi, ammi tace beyi dadi bane. Aa ammi.
Mami ce ma ta dawo damu, wace mami, maman fatiha, okay, zaku ci abinci ne, safna ce tace nidai na koshi, saidai ko du’a, eh ammi zanci.
Okay kije kici abinci, tam.
Yarima na tafiya adam ya turowa fatiha massage, teema na kizo ina jiran ki ina son tafiya, yaya ya tafi, eh mana,fatiha futowa tayi sun dade ita da shi sannan tace bari ta koma saboda kar su ummah su tafi, teema muje na kaiki gida, aa, me yasa, ni banson yaya ya ganni.
Toh sai me idan ya ganki karki manta wata rana aure zamuyi, amma fah, ni zan mishi magana ma, aa dan ALLAH karka fada mishi, me yasa kike da tsoro nifa gaskiyya bana son matsoraciya, ok tam shikenan, kaje ka auri wacce bata da tsoro, zata bude mota yace, ayimin afuwa da wasa nake, amma ni gaskiyya karka fada mishi, okay bebee, tazo fita tace good night, badai good night ba sai munyi waya, okay bye.Ya tafi.
Tana gama cin abinci lokacin 10:00 yayi, daki suka tafi. Fatiha ce ta kira ta sukayi hira, du’a ce tace fatiha wai wannan mutumin ba shine boyfriend din naki ba, kedai bari shine, kinsan fa har yau yaya baisan yaya adam surayi nane ba.
Amma gaskiyya kuna cin amanar yaya,hmmm kedai bari ni wallahi banson ya sani, ayko dole wata rana ya sani, nidai ba’a baki na ba, waike ya akayi na ganki tare da yaya, fatiha, na’am na boye miki wani abu.
Nan du’a ta fadawa fatiha abinda ya hada ta da yarima har haduwar su ta yau.
Fatiha tayi dariya sosai, amma haduwar ku tayi kyau, besting ba na fada miki dan ki tsokane ni ba, wallahi yanzu zan kashe waya ta.
Yi hakuri du’a yaya, amma gaskiyya kuma dai, kuma ai ina kamada yaya, toh ni kallon shi nake ne.
Ai shikenan tunda yanzu kowa ya fahimci kowa, wallahi kuwa, amma wallahi marin nan ya shige ni musamman ma na biyun, amma wallahi yaya sai ya gane ya taba besting na.
Aa ba ruwa na karma ki nuna mishi na fada miki, okay ai shikenan, waike ya taba marin ki, ni mezan mishi ya mare ni, meeno ce tasha marin shi saboda bata ji.
Kuma wallahi abinda tayi miki yau shi zan fadawa, fatiha please don’t tell him, I most, toh meye na fada ai ya huce kinji besting na, okay bye, saida safe. duk abinda suke safna na dakin amma bata san me suke cewa ba, saboda ta tsunduma kogin soyayya.
Yarima ne zaune a palo, meeno ta shigo, yaya sannu da hutawa, yawwa sai yanzu kika dawo ko, saboda bikin kawar uwar ki ake, yaya, huce ki bani wurin, mami na jinsu, dan ta saba da halin yarima amma yana da gaskiyya saboda meeno idan ba’a taka mata burki sai a hankali.
Hucewa tayi dakin ta, tana tafiya ya bita, mami na ganin haka tasan meeno tayi laifi, kenan dama saboda haka yace a gidan zai kwana,.
Tana shiga daki taji an kuma bude dakin, juyowa tayi suka hada ido, da sauri ta suke kanta, tsayawa yayi yana kallon ta, fatiha ce ta shigo tace au kin dawo kenan, dama ke nake jira ki dawo, wallahi meeno ki fita harkar du’a idan ba haka ba wallahi baffa zan fada wa, kuma,
shiru tayi ganin yarima a dakin. Ke futa kafin na dauke ki da mari, ba shiri ta fuce daga dakin , a zuciyar ta tana cewa yau kuma ko me tayi.
Tana fita yaje inda take, yaya dan Allah kayi hakuri, kunnan ta ya murde,amma ta kasa magana saboda tasan halin shi tana magana abin saiya fi haka, wallahi duk ranar da aka ce kin kuma yiwa yarinyar nan wani abu saikin raina kanki, kuma idan wani ya tambaye ki saboda me na miki hukunci ki fada.
Yana dawowa palon fatiha na zaune kusa da mami, mami ce tace yau kuma me tayi, ba komai, saida safe.
Mami ce tasa fatiha taje ta kira ta, nan ta tambaye ta me tayi, ba komai dan ban dawo da wuri bane, Allah ya shirye ki.
Mami, na’am auta wallahi ki shiga tsakanin meeno da du’a, me kuma ta mata, nan fatiha ta fadawa mami abinda ya faru, tayi mata fada sosai.
meeno wai yaushe zakiyi hankali, kefa ba karamar yarinya bace, wai da talaka da me kudu duk ba Allah ne ya halice su ba, kuma karki manta kema kanki a gidan naku gori ake miki, akan uwar ki ba dangin saruta bace.
Ni duk yarana babu wanda yake irin wannan abun, wallahi nasiha nake miki meeno, kinga rayuwa ba tabbas, ba fata nake ba, meeno idan bana gidan nan zaki sha wahala. Fadan ya shige ta sosai, kuma tace in sha Allah bazata sake ba.
Washe gari, sai kusan 10:00 suka tashi koda suka tashi an gama breakfast, bayan sun ci abinci suka koma palo, sai kusan 5:00 sultana ta zo suka tafi da safna saboda zasu je makeup, du’a dan Allah kizo muje, bazan jeba karki bata musu lokaci, tafiya su kayi.
Du’a na zaune a daki bayan sallar magriba, ammi tasa aka kira ta, tana fitoh wa tayi tozali da fatiha dake zaune a kan kujera, ammi ce tace kinyi bakuwa, tana tashi.
Zama tayi kusa da fatiha tace ya dai, baki tafi wurin bikin ba, eh ke nazo dauka,
Haba fatiha anyi ta maimaita magana daya kenan, bazan jeba.
Dan Allah besting kizo muje inma dan meeno ne jiya mami tayi mata fada, kuma tace zata baki hakuri, yanzu saida kika fadawa mami, eh, wayar tace tayi kara, teema bafa kayan wanki bane, sorry du’a ce taki shirya wa, bata wayar, mika wa du’a wayar tayi.
Dan Allah du’a ki taimaka kije idan ba haka ba, mata ta bazata ji dadi ba, nan ya dinga lallaba du’a har saida tace zataje sannan ya kashe wayar, dalla dama bake kaidai kika zo ba, eh nida yaya adam ne.
Shine kika barshi a waje, dan Allah kije ki shirya dama na tambayi ammi yanzu, toh sannu, yawwa, tashi tayi taje dakin ammi,
Ammi bari na shirya naje, saimu dawo da safna, okay ai dama haka nace mata ta goda sa’ar ta, murmushi tayi ta tafi ta shirya.
lokaci da ta gama shirya wa, dakin ammi ta fara zuwa, sai taga ba kowa, tana sokkowa kasa ta ganta, harkin shirya, eh ammi, okay saikun dawo, amma karku dade, 11:00 ta muku a gida, okay in sha Allah.
Suna fita suka shiga mota, gaskiyya an bani wahala, ayi mana afuwa inji fatiha, ita kuma du’a tace ina yini, lafiya lau besting mu, murmushi tayi, ya kalli fatiha yace ko taki ce ke kadai, aa ni dakai ai abu daya ne.
Suna tafiya suna hira, yarima ne ya kira shi, wai kana ina, gani nan na kusa zuwa, okay ina jiran ka, toh.
Wai yaya ne, eh shine, kace ya shiga zaka shigo. Jiya baki san drama da akayi ba ne, da karya shiga event din, ni kuma lokaci ina gida, tab ai tare da du’a suka shiga, da gaske, eh.
Suna isa, yarima ya bude motar shi alamar zai fitoh, ganin wada ta sauko daga motar ne yasa shi tsayawa. a zuciyar shi yake cewa meya hada adam da du’a, saiga fatiha ta sauko.
Fatiha ce tace wa du’a su shiga cikin event din, aa ki tsaya muje ta gaisa da junaid , zuwa sukayi har inda yake.
A hankali du’a ta furta ina yini, kamar bazai amsa ba yace lafiya lau, gani nazo, ai na ganka.
Sai kace mini kanada wainda zaku shiga tare ai, yaya mu tafiya zamuyi ba tare zamu shiga ba, toh ku huce ku tafi.
Suna tafiya yace yanzu zamu shiga ko saika kara ja mini aji, ayi min afuwa naje dauko du’a ne, na tambaye kane, murmushi adam yayi yace muje.
Su du’a na shiga suka je suka gaida mami, du’a kinzo kenan, wallahi nazo, amma wannan shirin naki daga gani yanzu akaje aka saka ki a gaba kika shirya.
Murmushi du’a tayi tace wallahi kuwa mami kamar kin sani, ai tunda naga tace mu tafi zata taho nasan akoi abinda zatayi.
Yarima na shigowa indan sa ya sauka akan du’a dake kusa da mami, dauke kai yayi yaje ya samu wurin ya zauna.
Fatiha nifa inaga yau a wurin mami zan zauna, eh saiki zauna tunda wurin mami kika zo, ba wurin na tazo ba du’a tashi ku shiga cikin mutane.
Suna zuwa inda su safna suke safna tace yana ganki, hmmm har gida akaje aka sako ni a gaba. tayi daidai ace mutun bayson shiga mutane.
Ai ba dade wa zamuyi ba, ammi tace 11:00 ta mana a gida, okay.
Du’a sai buyu suna hada ido da yarima daga ta daga kanta sai taga yana kallon ta, meeno ce ta karaso wurin, ita da islam, du’a sannun ki, meeno ya kike, lafiya lau, kinzo kenan, eh har gida naje na dauko ta, islam batayi mamaki ba dan meeno ta fada mata abinda yarima ya mata. bata ce komai ba amma a ranta bata son yarinyar.
Meeno ce taje daidai kusa da du’a tace du’a dan Allah kiyi hakuri abinda ya faru jiya, murmushi kawai tayi tace meeno ki bar maganar. Meeno shekara biyu ta bawa fatiha, shi yasa bata ce mata yaya ko aunty, amma sauran da aunty take kiran su.
Tafiya sukayi, su du’a kuma suka ci gaba da harkokin su.
Wayar du’a ce tayi kara alamar kiran ta ake, daidai lokacin aka sanar da shigowar mai martaba, da yake yau dinner mutane da yawa sunzo wurin, bikin manyan mutane ne.
Du’a tashi tayi zata fita waje dan ita hankalin ta baya wurin, bata ji lokacin da akace mai martaba zai shigo ba.
Kanta a kasa ta kara wayar a kunnan ta, nan sukayi karo da mai martaba, tana dago wa ta kasa magana, kuma taki matsawa sai kallon mai martaba take, mutane sai kallon ta suke, wace wannan ta shiga gaban mai martaba.
Shima kanshi tsayawa yayi yana kallon ta, maganar da mamma keyi ce ta dawo da ita daga tunanin da take, yarima ne yayi saurin zuwa gurin ya janye ta yace tuba muke mai martaba, janta yayi suka fita waje.
Mu hadu a kashi na gaba.😊❤️❤️
Domin neman ci gaban wannan litafin zaku iya following Instagram page dina Reeeyarh ko kumin dm ta WhatsApp ***.
Nagode
*~Book by Reeeyarh~*