Chapter 6
by @reeeyarh
page 6
*~reeeyarh~*
Suna fitoh wa ta kara saka wayar ta a kunnan ta tace hello mamma, mamma ta dade da kashe wayar ta.
Yarima ne yace du’a bakiga baffa bane, tace ni wallahi ban kula ba, kuma da na daga kai saina ga wani abu, shi yasa na tsaya ina kallon shi.
Yanzu dai kinyi laifi dole muje ki nemi afuwa, okay ba komai, amma wai me kika gani, ba komai, shine kika tsaya kina kalle mana baban mu, murmushi tayi tace ai nima baba nane.
Fatiha ce ta fitoh har lokacin yarima bai saki hannun du’a ba, besting kina lafiya, lafiya me kika gani, ba komai.
Adam ne ya fitoh, du’a are you okay, naga kin tsaya a gaban baffa, kunga dalla ku rabu da yar mutane.
Yanzu zamu je ko sai anjima, ina, wurin mai martaba, aa mu bari sai anjima, akabar fatiha da adam suna kallon ikon Allah.
Umar ne ya fitoh tare da maryamu, suka zo har inda su yarima suke, yaya lafiya inji maryam wacce ce wannan, fatiha ce tace kwawa tace, kuma shine zata zo gaban baffa ta tsaya, saiga siyama da sadiq da muhammad.
Suka daura a inda maryamu ta tsaya.
Fatiha ce tace bafa ta sani ba, ke dalla yiwa mutane shiru ita bata gani ne, inji Muhammad da yake sauran suna dardar din magana saboda yarima.
Du’a tuni idon ta ya cika da kwolla, yarima ne yace yar abbah mu tafi ko, hayaniya tayi yawa a wurin, yaja hannun ta, kai malan magana muke da ita inji Muhammad, umar dama tunda yazo baice komai ba dama yazo yasan wacce ita.
Yarima bai tanka wa kowa ba yace fatiha live there, adam kai ma nasan sai nace ka bar wurin zaka tafi ko, dan Allah kuzo mu tafi.
Abinya bawa Muhammad haushi, ai dama dangin ka basa laifi, juyowa yayi wacce dukan su saida suka shiga cikin hankalin su.
Muhammad kayi harkar gaban ka kar abun yafi haka, adam ne yace kaga zomu tafi, suka tafi, umar shima yaja kawar shi suka tafi, aka barsu a wurin.
Suna tafiya du’a tadan tsaya, suma tsayawa sukayi, menene, bazan koma ba, haba yarinya ai sakin koma inji yarima, inaji tsoro, adam ne yazo kusa da ita yace haba du’a tsoron me kuma, ba abinda zai faru, kinji.
Muje ki bawa baffa hakuri saimu jena kaiki gida inji adam, tafiya sukayi suna shiga kowa sai kallon du’a yake, dan rike rigar yarima tayi, ya juyo ya kalle ta, menene, dan Allah ka bari gobe zanje har gida na bashi hakuri kaji, kowa ni yake kallo, zata mishi kuka, okay tam shikenan, kije kiyiwa mami sallama sai kizo nasa a kaiku gida, fatiha raka ta wurin mami. duk baffa na kallon su.
Suna isa inda mami take tace tafiya zakiyi ko, daga kai du’a tayi, okay shikenan yaushe zaki zo, gobe in sha Allah, okay Allah ya kaimu.
safna da tun dazu take son gani du’a dan ta kira driver yazo ya dauke su, tazo inda take tace du’a zomu tafi, mami ce tace safna bari nasa a kaiku, aa mami na kira driver, okay sai gobe.
Yarima da ya koma waje yana jiran fitoh warsu, shida adam suna tsaya, suka fitoh, du’a fatiha safna sultana.
Gurin da motocin yarima suke suka nufa, suna zuwa adam yace muje na kaiku gida nima tafiya zanyi, ka bari nasa a kaisu, du’a ce tace aa safna ta kira driver yazo ya dauke mu.
Amma ba haka nace kije ki kira ta ba, lokacin harta kira shi, okay zo ina son muyi magana, da hannu ta nuna kanta alamar ni, eh ke.
Barin wurin suka yi kina jina, daga mishi kai tayi alamar eh, dago ki kalle ni, dagowa tayi, yace kar abinda ya faru ya dame ki kinji, kuma karki fadawa abbah. Shiru tayi, kina jina ko, tam bazan fada mishi ba in sha Allah, yawwa saida safe ni bari na koma ciki.
Tafiya yayi yace wa adam kazo mu tafi, suna tafiya bada dadewa ba driver yazo, sukayi musu sallama suka tafi.
***********
Mamma tunda aunty safiya ta tafi, tana daki. abbah ne ya shigo dakin tana zaune bakin gado. Sannu da zuwa, yawwa bakuwar taki harta tafi, eh. Okay ina yarannan, dazu yaya zai fita nace ya kaisu gidan adda, okay kinci abinci ne, aa okay muje muci, tashi tayi suka tafi,
suna cikin cin abinci sai abba yace fatima da wata mastsala ne, aa mai ka gani, okay ba komai kici abincin ki, suka ci gaba da cin abinci, abban dee, na’am!
Ina so zanje gida, dan daga kai yayi ya kalle ta, kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace yaushe, next week indan aunty safiya ta dawo, okay Allah ya kaimu.
Suna kammala cin abincin yace bari yaje gidan hajiya, tam Allah ya kiyaye, dan Allah kace mata ranar alhamis zanzo, tam ya fuce.
********
Washe gari misalin karfe, 11:00 du’a suka shirya ita da safna suka fadawa ammi zasu tafi gidan su fatiha, dan jiya sun fada mata abinda ya faru. bata musa musu ba tace sai sun dawo, driver ne ya kaisu.
Fatiha ce ta turo musu address din gidan, suna isa, lokacin fatiha ta aiki daya daga cikin kuyangu mami tace zatayi baki, a bude musu gate kuma a rako su har shashen mami, shima gidan nasu na nan kamar gidan su na kano yake, kawai dai gidan su na kano yafi girma saboda gidan sarauta ne.
Suna zuwa har shashen mami aka kaisu driver kuma ya tafi.
Fatiha na zaune a palo, tana ganin su ta fara murmushi, Sannun ku da zuwa, yawwa , suka zauna, ya kuke lafiya, yasu ammi, Alhamdulillah, ina mami, mami na sama, okay suna zaune suna hira mami ta sauko.
Gaida ta sukayi bayan ta amsa take ce musu ya ammi, lafiya lau.
Suna zaune suna hira mami take cewa du’a wai jiya me kika gani, hmmm mami wallahi gani nayi baffa na kama da mamma shi yasa na tsaya ina kollan shi na tabbatar ko da gaske ne, mami ce tayi murmushi tace haba dai, wallahi mami sosai yake kamada mamma, lokacin yarima ya shigo.
Kika sani ko dan uwan tane, tab Allah ya kiyaye, me yasa kika ce haka, in sha Allah ma baffa ba dan uwan mamma bane, mami kinsan me.
Nasan kinsan dagin mamma amma ni bana so ki ma fada mini, basu da amfani a wurina, amma du’a ai dangin kine, aa wallahi mami ni ba dangi na bane.
Wallahi mami kamar ace wai baffa dan uwan mamma ne wallahi ba zaku sake ganina ba, harni besting, harke sun jaja miki, shi yasa ma bana son sanin su.
Ni wallahi duk wanda yace baya son abbah na toh bani bashi, kuma ai arziki nufin Allah ne, kudin su na banza, wallahi abbah ya fisu tunda har yau bai taba kirar mamma ba, shida ba shi ya raine ta ba, amma suko.
Shiru tayi ganin yarima yana kallon ta saita yi kasa da kanta, sai a lokacin suka san ya shigo, yar abbah kenan inji yarima.
Mami ya gaida, suma duk suka gaida shi, yar abbah rayuwa ana son yafiya, wallahi a wannan harkar babu yafiya.
Okay ai shikenan Allah ya kauta, mami kuwa tuni jikin ta yayi sanyi.
Kinje wurin baffan, aa banje ba, okay tashi muje, tashi tayi zasu tafi, safna kizo muje mana, aa kuje ku dawo, eh kuje ku dawo nima ba zuwa zanyi ba inji fatiha,
tab wallahi bazan je ni kadai ba, au ni ba mutun bane kenan, huce mu tafi.
Kaga malan wannan bafa su fatiha bane da zaka na mata tsawa, du’a kuje kinji, mami ce tayi magana.
Mami idan na dawo zanci abinci, banyi girki da kaiba, haba mami, idan ma zaka je kayi aure kayi dan wallahi na kusa fara hana ka abinci, fita yayi bai tanka mata ba dan yasan yana magana sai ranshi ya baci.
Suna fita yace yar abbah kin dade da zuwa, eh tun wajan 11:00 nazo kai nake ta jira saboda ina son tafiya.
Haba dai yau sai dare zaki bar gidan nan, tab wallahi gida zan koma, suna tafiya duk inda suka huce sai an gaida su, kollon shi tayi tace wai su basa gajiya da tsugunna wa, jeki tambaye su. dan turo baki tayi lokacn ya juyo yana kallon ta, iyee ni kike turowa baki, nifa tambayar ka nayi amma, amma me, ba komai.
Sunzo daidai shashen ammi saiga Muhammad ya fitoh, da sauri du’a ta matsa kusa da yarima , ke meye, kallon inda take kallo yayi, ganin Muhammad ne yasa yayi tsaki ya rike hannun ta yace huce mu tafi.
Har kofar shashen baffa suka je sannan ya saki hannun ta, ya tura wani a cikin hadiman kofar yace ayi musu iso, suna tsaye mutumin ya fitoh yace su shiga.
Baffa na zaune suna shiga yace kowa ya fita su jira a waje, gaida yarima yayi bayan ya amsa tace baffa ina yini, ke ba haka ake gaida sarki ba, kaga babu ruwan ka, lafiya lau, ku zauna, zama sukayi.
Baffa munzo neman afuwa ne, murmushi yayi, du’a tace baffa kayi hakuri wallahi ban sani ba, yarima ne yadan taba ta da kafa, ta daga kai ta kalle shi.
Baffa na kallon su, yace ya sunan ki, du’a. sunan ki na gaskiyya, da sauri yarima yace sunan hajja ne da ita.
Okay an yafe muku, babana a ina ka Santa, baffa friend din fatiha ce, okay haka ne kece wacce aka mana hotoh ranar sauka ko, eh nice.
Amma yan mata mai yasa kika tsaya kina kallo na, murmushi tayi tace kana kamada mamma ta shi yasa, a gaskiyya ya kamata wata rana a kaini wurin mamma ki naga mai kamada ni, murmushi tayi tace, idan ka koma kano, in zanzo tare zamu zo, sosai kuna kama.
Yarima har mamaki yake yace baffa yake ta hira da du’a itama sai biye shi take, dama haka take da surutu.
Madan mu tafi, haba babana ka barta mu dan kara hira mana, toh ni baffa tafiya zanyi yunwa nake ji, ga abinci can kaje ka ci, yawwa dama mami tace bata dafa dani ba. dalili wai naje nayi aure mata ta tana dafa mini, ai nima farko da nagan ka da du’a nazata matar aure ka kawo mini, murmushi du’a tayi tace haba baffa, ai ni saida yayi daughter dani, yayi mini girma da yawa.
Ko tanka musu baiba, murmushi baffa yayi yace daughter kije kuci abinci, aa Alhamdulillah na koshi.
Saida yarima ya gama cin abinci suka tafi.
Suna tafiya yace ashe kin iya magana haka, kodan dama ai masu sunan ku haka suke.
Kuma kike cewa baffa nayi miki girma, ai nima kin mini kankanta, naji ba komai, wata yar fucila dake a wurin.
Suna isa shashen mami, suna zaune har sunyi sallah sun dawo, dama lokacin da yarima ya shigo anyi sallar azahar.
Yanzu nake cewa azo aje gidan radio ayi cikiyar ku, ko kunyi batan hanya, mami tun dazu nake san tahowa amma an hana ni, har cewa nayi zanzo naci abinci akace mini gashi can naje naci.
Hala tayi halin nata inji fatiha, ai dama tunda naga kun dade nace nasan du’a nacan suna hira da baffa, au da kinsan halin ta shine baki fada mini ba.
Ai da, da musa(hadimin yarima )zan hada ta suje.
Kunga ina ruwan ku, kuma kuyi mana, du’a zo kije kiyi sallah, kizo kuci abinci,
Hucewa tayi fatiha da safna suka bita, suna tafiya galadima ya zauna, mami kinga yace baffa ya saki jiki da du’a sai hira suke, murmushi tayi tace jini ba wasa ba, mami ban gane ba, hmmm a gidan nan waye zaice ya manta da fatima, saidai kawai a ki gaskiyya, dama wasu haka suke so.
***************
WACECE AISHA AHMAD YUSUF MUDDIBO ,(du’a)
Alhaji Yusuf Muhammad muddibo kakan du’a, haifafen dan kasar niger, kaddara ce ta kawo shi Nigeria, yana zaune a jahar jigawa babura local government, lokacin da yazo garin bashi da komai, bashi da kowa, a garin akoi wani mutun mai kirki, shiya dauke shi ya bashi gurin zama, yana sana’a har Allah ya rufa mishi asiri.
A kwana a tashi, lokaci yana ja har yayi shekara hudu a garin, nan mutumin da yake ruke dashi yace tunda yanzu Allah ya rufa maka asiri, kayi aure ka.
Ko ina yaje sai ace baza’a bashi aure ba bashi da asali, dama wannan mutumin yana da yara su biyu mata, nan yace ya zabi daya daga cikin yaran shi zai aura mishi ita, shi kuma yace duk wace ya aura mishi zai zauna da ita.
Abu yayi ta yawo a gari wai ya asirce shi, abinka da buzaye, Yusuf fari ne tas, ga gashi. kuma shiba aske gashin shi yake ba.
Koda mutumin ya koma gida ya sanar wa matarshi, bata ce komai ba, sai Allah ya sanya alkairi, wa kuma zaka aura mishi Aisha ko saudat, gara dai Aisha saudat ba wani hakuri ne da ita ba.
Bayan anyi aure suna rayuwar su hankali kwance.
Ananan ananan Aisha ta samu ciki, ta haifi yarta ta farko mai suna ummulsalma(adda) bayan wani lokaci ta haifi da na miki mai suna Ahmad (abbah) , bayan wasu shekaru Yusuf ya kara aure.
Lokaci Ahmad yana jss3.
Matar shi mai suna Khadija ( mama) suna rayuwar su hankali kwance.
Anan anan Khadija ta hafi yarta mace mai suna hafsat (ammi), Aisha tunda ta haifi Ahmad bata sake haihuwa ba,
Khadija har ta sake haifar yarta ta biyi maisuna asma’u.
Lokacin abbah ya kamala secondary school dinshi, Aisha ta haifi yarta aka sa mata suna fatima.
Rayuwa tana musu dadi a tsawon shekarun nan baban Aisha Allah yayi mishi rasuwa, yar uwar ta kuma tayi auren ta hadda yara biyu.
Bayan abbah ya kamala secondary school dinshi baban shi ya saka shi a jami’a a jahar kano bayaro university kano (buk) lokacin adda ta fara zuwa jami’a a kazaure.
Adda tayi aure a jahar kano wani malamin makarantar su, shi kuma Ahmad aka mishi aure a dangin mahaifiyar shi, yana level 2 lokaci.
Ahmad yana da kokari sosai yana karatun business management, lokacin yana level 3 suka hadu da fatima, ita kuma lokacin tana level 1.
Soyayya ce mai karfi tsakanin Ahmad da fatima.
Ahmad yana sana’a bayan karatun da yake, suna soyayya da fatima. Ya fara gini a jahar kano, ita kuma matar shi Khadija tana garin su.
A kwana a tashi Ahmad ya kamala kartun sa, business dinsa yana samu sosai.
Bayan ya kamala karatu fatima tace ya kamata ayi maganar aure su, yace toh zai fada wa iyayen sa sai a turo, hakan yasa fatima farin ciki.
WACECE FATIMA MUHAMMAD AHMAD MAZAN FAMA,( mamma).
Fatima haifafi yar garin kano ce, yarinya yar gata,mahaifinta mai martaba Muhammad Ahmad mazan fama (papa) shine sarkin kano Muhammad Ahmad na biyu.
Muhammad Ahmad an hayfe shi a cikin gidan sarauta yayi makarnta, har zuwa lokacin da yayi auren shi na farko yar sarkin yobe Aisha(hajja) bayan wani lokaci ya aure waya matar tashi mai suna zainab shine baba a gurin mahaifinsa. Yana da yan uwa biyar duka mata ne,
Ananan ananan Allah yayi wa mahaifin shi Allah yayi mishi rayuwa, bayan wani lokaci aka nada shi sarki.
Yana rayuwa Aisha ta haifi danta na fari Muhammad Ahmad mazan fama (baffa) bata sake haihuwa ba.
Zainab kuma ta haifi yaran ta guda shida, Ibrahim, Abubakar, Khadija, sa’ada, umar, sai autar ta Aisha( maman salma amarya). Bayan zainab ta haifi Aisha bada dade wa ba Allah ya mata rasuwa.
Aisha ce taci gaba da kula da yaran, lokaci da Aisha ta haifi yar ta karshe Muhammad ya kamala secondary school dinshi dan shi ya fidda rai da samin kanwa, yarta mace mai suna fatima(mamma).
Fatima lokaci da ta kamala secondary school dinta, mai martaba yace zai kaita kasar waje karatu amma tace ita a Nigeria zatayi karatu, dama idan ka ganta baza ka taba cewa yar sarki bace, tare da yan aikin gidan take zama taci abinci.
Lokaci da ta fara zuwa university yayan ta yayi aure matar shi ta farko mai suna safiya(mami), safiya ba dangin sarauta bace amma baban ta babban mutun ne ana ji dashi a kano.
Danta na farko Allah ya mishi rasuwa sai ta sake haifar danta mai suna Ahmad Muhammad Ahmad mazan fana(yarima) (junaid). Matar shi ta biyu kuma mai suna Khadija (ummah) sai kuma ya auri ta uku mai suna halima(ammi). Dukan su gidan su daban, lokaci Khadija nada danta mai suna umar ita kuma halima nada danta mai suna Muhammad.
Fatima tana zaman ta a gidan har lokaci data sanar wa da yayan ta, zatayi aure.
Koda ya tambaye ta waye saurayin nata bata boye mishi komai ba, nan yace bazata aure shi ba, kuma karta sake maganar.
Fatima bata hakura ba taje ta fadawa mahaifin ta, shima yace bazai yuwu ba.
Haka akai ta gaggormaya har saida baban ta yace indai akayi aure bashi ba ita dan bazata ja musu abin kunya ba, mutumin da bashi da asali.
Su Ahmad kuwa sunsha zagi kala kala.
Haka akayi auren fatima da Ahmad suna zaune a gidan haya kafin ya kamala gidan shi, fatima bata taba nuna wa Ahmad wani abuba.
Lokaci da Khadija ta samu ciki ta haifi danta mai suna Yusuf(yaya). A lokaci Allah ya dau ranta tana haifar shi.
Fatima taje gaisuwa har ta roki da a bar mata shi zata kula dashi, nan suka bata shi saboda babu wanda yake kinta duk sun saba da ita.
Ahmad ya kamala gidan shi nan yace kanwar shi fatima ta dawo gidan lokaci tana ss2, su Hafsa kuwa sun kama karatun suna secondary, fatima mamma tace ya dawo dasu suma suci gaba da karatun su, har suka gama karatun su,
Adda nada yara shida Ibrahim ( yaya Ibrahim), zainab(aunty) sadiya( aunty diyah)sai Yusuf (abbi), Aisha(munnira) Khadija(siyah).
Hafsat (ammi) tayi aure bayan ta gama karatu tana da yara uku safna, Yusuf (samir), sai Khadija (mama). Kusan tare akayi auren su ita da amina da fatima.
Fatima( ammu ) nada yara biyu, Aisha ( mufida) sai abdullahi( abdallah).
Ita kuma amina( ummi) nada yara uku Aisha (Hidaya), Yusuf(daddy) , Khadija (noor).
Lokaci da fatima ta haifi yarta mai suna Aisha (du’a ) kusan lokacin Allah yayi wa alhaji Yusuf midibbo rasuwa, lokacin yaya yana shekara 6. Bayan shekara biyu ta haifi fatima(teema) sai Muhammad( baffa) sai Khadija (dee).
Mu hadu a kashi na gaba.😊❤️❤️
Domin neman ci gaban wannan litafin zaku iya following Instagram page dina Reeeyarh ko kumin dm ta WhatsApp ***.
Nagode
*~Book by Reeeyarh~*