Chapter 11
by @reeeyarh
Page 11
*~reeeyarh~*
Washe gari aka daura aure ranar friday, yaran sarki su uku hauwa Muhammad Ahmad mazan fama, siyama Muhammad Ahmad mazan fama, maryam Muhammad Ahmad mazan fama.
da daddare sukayi dinner, yayi ta baza ido ko zaiga du’a, amma bata zoba.
QBa yacce fatiha bata yida ita ba amma tace bazata je ba saboda dare, amma zataje yini.
Ranar asabar akayi yini du’a sai kusan bayan sallar zuhur sannan ta tafi, harda kukan ta, saboda tace wa mamma tazo suje tace bazata je ba.
Tana zuwa gidan ya cika da mutane, bata fitoh daga motar ba ta kira fatiha, fatiha tace mata bata nan amma yanzu zata dawo, sauka tayi ta huce shashen baffa, baffa na zaune shida yan uwan sa, tace a mata iso, hadiman da suka ga tana kama da baffa shi yasa suka shiga, suka sanar mishi, wani a cikin hadiman ne yaje dan ya duba, yana dawowa yace Yallabai wacce suka zo da yarima wancan ranar ne, kace ta shigo.
Du’a na shiga taga mutane, dan tsayawa tayi, daughter karaso mana. A hankali ta kara sa, ya nuna mata kusa dashi yace zoki zauna, zama tayi ta gaida su, ta lura duk ita suke kallo, baffa bansan kanada baki ba, bari naje na dawo wani lokacin, aa daughter ba baki bane yan uwa nane, nan ya fada mata kowa da sunan su, murmushi tayi tace baffa dama kanada kanne, eh du’a ina fatihar nagan ki anan.
Ta tafi wurin makeup, kuma idan naje wurin mami tana da baki da yawa, amma yanzu zata dawo.
Dukan su tsayawa sukayi suna kallon yace baffa yake hira da du’a kamar yar shi, yarima ne ya shigo shida adam.
Yarima tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, waya kawo du’a nan, babana ku karaso mana, zama sukayi suka gaida kowa na wurin, daughter kun gaisa da yayan naki, aa baffa yaya adam ina yini ku, lafiya lau du’a. Me kike anan nazo wurin baffa ne, okay.
Yarima ne yace adam mu tafi, ku tafi da ita ku kaita wurin hajja su gaisa, du’a tashi kuje kunji, tashi tayi suka tafi.
Nan yan uwan baffa suke tambayar shi wacece du’a, kawar fatiha ce.
Suna fita adam yace kaje ka raka ta, zan jira ka a palo, yaya adam mai yasa bazaka jeba, du’a banson ana mini kidekide a kai, yarima ne ya juyo ya harare shi, sai kun dawo, ya huce ya bar wurin.
Saida sukaje har shashen hajja ganin mutane da yawa yasa tace wallahi baza ta shiga ba, dan haka suka koma .
Yanzu ina zaki, juyowa tayi tana mishi wani irin kallo, anan zan jira ta, kizo mije part dina saiki jira ta acan, no need thanks.
Du’a adam nacan fa, eh nasani basai naje ba, okay barina jira idan tazo saina tafi, damuwar ka, adam neya hango su dan dama bai shiga ba sun hadu da umar suna hira, umar bari naje wurin mutane can.
Juyawa umar yayi ganin du’a yasa yace muje na gaisa da junaid
Du’a har kun dawo, yaya adam ni wallahi bazan iya zuwa ba mutane sunyi yawa, ai shiyasa nace bazan jeba.
Ina yini ta gaida umar, umar da tundazu ita yake kallo yace lafiya lau, ya kike, lafiya, sai kuma ya gaisa da yarima.
Tsayuwar me kuke anan, ina jiran fatiha ta dawo sai mu shiga na gaida mami na tafi, ki tafi ina, gida.
Mai yasa zaki tafi gida da wuri, yaya adam banson hayaniya da yawa, yarima ya lura umar du’a kawai yake kallo dan haka yace du’a muje part dina ki zauna idan fatiha ta dawo sai kuje.
Aa zan jira ta anan, aa du’a muje kinji adam ne yayi maganar. bazata iya yiwa adam musu ba dan haka dole ta hakura.
umar kuma ya musu sallama ya tafi.
Suna shiga suka zauna, adam yace du’a did you need something, no yaya adam I’m ok.
Yarima tashi yayi ya shiga daki dan ya rage kayan jikin shi, du’a na’am yaya, kinga kawar ki nace mu fadawa mami amma taki yarda, nima saida nace haka,
Ya kamata ace mami ta sani, okay ke zaki iya fada mata, eh zaniya , okay dan Allah bayan biki ki fada mata, wai ita tsoron junaid take, toh yaya idan ba’a fada ba shi zai aure tane, ni bana son abin haushi.
Yarima ne ya fitoh, sannu dama naga kokari ka na zama da kayan nan, ina ruwan ka, du’a ko kallan shi batayi ba.
Suna zaine suna hirar su yarima yace Sannu miji fatiha, da sauri ya daga kai ya kalli du’a da itama kallon shi take, adam baiyi tunanin du’a ce ta fada mishi ba, a tunanin shi hirar da suke yaji.
Ya dai kake kallon yar mutane bafa du’a nace ba fatiha nace, kai kuma abinda ka fara kenan yar labe, toh idan ma kaji saime, garani ansan budurwar kuma aure ta zanyi kaifa.
Eh naji ba komai andai ji kunya, ace da wannan yar abar kake soyayya, toh kai kayi da yar abar mana, tashi yayi zai fita, ina zaka, ban sani bah, kodai ita take kiran ka, yaya ina zaka, zan dakko su fatiha a wurin makeup, kuma karki ce zaki bini, yaya adam dan Allah, aa du’a ki zauna yanzu zamu dawo, ba ita kadai bace. Du’a kodai wani abu ya faru tsakanin ki da junaid, aa yaya adam meka gani. ba komai shikenan.
Yana fita du’a ta tashi zata fita, da sauri yarima yazo gaban ta ya tsaya, malan lafiya, dan Allah du’a karki fita wallahi kina fita adam zai gane, ki zauna ni saina fita na bar miki palo.
Tausayi ya bata, saita koma ta zauna, zai fita tace ina zaka, zan jira a waje ne, mai yasa Kazo ka zauna.
Du’a, ya akai, inaso na canza, wani muskilin murmushi tayi tace da gaske, eh du’a ya zanyi, kana so ka canza ba laillai ka iya ba. mai yasa kika ce haka. Ba komai, wallahi inaso na canza just tell me mai zanyi.
Ka fara aure ziyada, a zuciya yace yarinyar nan tana son sani a hanyar da bazata bulle ba, du’a idan na auri ziyada itama halin tane, okay saika sata daina.
Bazata daina ba saboda ziyada shu’uma ce, kaima haka. Murmushi yayi yace na sani amma kuma wannan shu’umin ne yake so ya dawo mutumin kirki. Okay Allah ya taimaka yasa ka shiryu. Ameen du’a nagode.
Dan Allah zanna kiran ki ki bani shawara, bata ce mishi komai ba.
Adam yana fita fatiha ya kira, teema na kina ina, ina wurin makeup, an gama miki, eh su samha nake jira, okay ina son muyi magana bari nazo, amma fatiha we need to talk, okay sai kazo, yasan wurin da suke zuwa makeup.
Hello teema ina jiran ki, fitoh wa tayi, ta shiga motar, bayan sun gaisa tace yaya any problem, teema your brother has already no, what tana zaro ido, I’m your boyfriend, why did you tell him,nan ya fada mata abinda ya faru, but, but what bazai miki komai ba, yanzu mu tafi du’a na jiran ki. Su samha ta kira tace ita ta tafi saisun taho, ke dawa, yaya adam du’a na jira na, okay sai mun taho, zezee ce tace ita dawa, adam, okay.
Suna isa shashen yarima suka nufa, suna zaune yace ya tafi ya barshi.
Besting kinyi kyau sosai inji du’a, da gaske , eh, yaya ina yini, lafiya lau fatiha. Bai nuna mata wani abuba, du’a ce ta tashi tace, muje na gaida mami, dan tafiya nake son yi, ai ance mini saida kika yi kuka kafin ki taho, wata harara ta mata, adam ne yace kuka kuma, eh yaya adam wai sai mamma tazo su tafi.
Kai du’a yanzu kuka kika yi, yaya ni karya take mini, wallahi da gaske nake, nayi din kuma tafiya zanyi.
Du’a karki kulata kije ki gaida mami kizo na kaiki gida, yarima bece musu komai ba, suna tafiya adam ya zauna a kusa dashi.
Junaid wai meke damun ka , ka fada mini, adam me kagani, kana cikin damuwa, haka kuke gani amma ni banda damuwa. Okay ai shikenan, ya maganar aiki nan, next week in sha Allah zanje, ok Allah ya kaimu, Ameen.
Hirar su suka ci gaba kai nifa aure zanyi, dariya yarima ya fara wai ita fatiha zaka aura, aa kai zan aura, dan Allah ka fada mini yaushe aka fara soyayya nan ake boye mini, ban sani bah, aa lailai na fadawa mami ta shirya tanada wani bikin, bikin auta zamu sha shagali sai munyi sati buyu muna biki.
Kaga ni bakai na wakilta ba du’a ce zata fada mata, wallahi nizan fada yau ma kuwa, Junaid wallahi karka fada mata, kana fada yau zan tafi gida, aa mai yayi zafi, na fasa fada.
Du’a kuma suna fita shashen mami suka tafi da suka gaisa, fatiha kuje ku gaida hajja, tam, suka tafi suna tafiya fatiha tace du’a ashe yaya ya san yaya adam saurayi nane, eh yasa ni, kinga shikenan yanzu zamu sha biki, du’a nifa ba yanzu zanyi aure ba, mai yasa, du’a duk sauran yan uwana basuyi aure ba saini, toh mai a ciki, ba hafsee da meeno da siyah ( Safiyyah) ne kawai ba sai samha , Zezee eh haka ne.
Suna isa shashen hajja suka gaisa, hajja mami ce tace tazo ta ku gaisa tace nace miki yar fatima ce, da gaske, a Masha Allah, ya sunan ki, du’a basu wani dade ba a shashen suka tafi.
Du’a dan Allah ki zauna, fatiha wallahi kawai bana son hayaniya, kuma kinga banason takura miki gara ki shiga cikin yan uwan ki, shashen yarima suka tafi.
Har kun dawo, du’a ce tace eh, amma kin fasa tafiyar, aa tafiya zanyi, okay muje na kaiki, yarima ne yace zanje, ina wurin mamma, okay muje, suna zuwa wurin motar yace bazan zauna a gaba ba, dalili, shigewa motar yayi, fatiha ko zaki jene, kai ta daga mishi, shigo gaba ki barsu can da halinsu na miskilanci, du’a shiga tayi suka tafi.
Sati nawa zakayi a china, daya, okay, ya jingina da baya ya daga kanshi sama, kamar mai bacci amma ba bacci yake ba idon shi na kan du’a, hurar su suke ita da adam da fatiha, wai shida kowa a gidan su yake tsoron shi wannan yarinyar take raina wa hankali, dama ban santa a duniya ba. ni yazan yi.
Suna zuwa suka shiga mamma na daki aunty halima ce a zaune ita da teema, aunty du’a harkin dawo, ba mamma tace karki dawo gidan nan basai magariba, dan ubanki tashi kibar palon nan, ke baki da hankali bakiga da baki nazo ba.
Sai a lokacin teema taga su yarima.
Gaida su tayi tace aunty du’a kiyi hakuri.
Halima suka gaida, aunty halima ina mamma, tana daki, abbah ya dawo, aa yaya fah, shima bai dawo ba. ke wai bacewa nayi kibar palon nan ba, tashi teema tayi ta tafi daki, halima ta tashi ta dauko musu drinks.
Fatiha kije ki kira mamma inji du’a, ke bazaki je ba, wallahi naje fada zata mini, dee ce ta fitoh da gudu, aunty du’a kinga yaya zai dake ni, wallahi baffa zanci uban ka, da sauri ta rufe baki, baffa bar wurin nan, dee zo, bazaka tafi ba, tafiya yayi, me kika mishi, dukan shi nayi, baffa zo inji yarima , tsayawa yaro yayi yana kallon du’a, kaje mana, dee kina jina, eh aunty du’a, kije ki cewa mamma tayi baki amma karki ce mata dani a ciki, tafiya tayi.
Baffa zuwa yayi kusa da yarima ya zauna, gaida su yayi, lafiya lau baffa ya kake, lafiya lau.
Dee ce ta fitoh tace aunty du’a wai mamma tace kije bata gane bakin ba, da sauri du’a ta juya ta kalle ta, dee zonan mai kika cewa mamma, haka nace wai kince tayi baki amma badda ke, innalillahi, tashi muje, adam da fatiha sai dariya suke mata, fatiha dan Allah idan ta fitoh kice mata kaina ke ciwo, yarima kawai kallon ta yake, dakin mamma tafi.
Mai ya dawo dake, mamma kaina ke ciwo, kuma su fatiha sunzo gaida ki, okay ganinan zuwa, da sauri ta fita dan kar mamma tace mata wani abun.
Yarima ya tambayi baffa ya sunan sa na gaskiyya , Ahmad Ahmad Yusuf, ok wana class kake primary three, masha Allah.
Du’a ce ta fitoh ta samu wurin ta zauna, baffa teema ta gara mini dakin, eh aunty du’a nina taya tama, yawwa, aikin kenan sai aje a kwanta, wallahi fatiha ko.
Mamma ce ta fitoh suka gaisa, hala kuka taje tana muku ko, kai mamma kuka kuma sai kace wata dee, da bakiyi ba za’a fada , wallahi yaya adam ka rabani da fatiha. Ai kwarama dee bata kukan banza, keko ko fita zanyi sai kinyi kuka.
Ya sauki jiki, jiki da sauki mamma, Allah ya kara sauki, Ameen mamma dama abinci nazo ci, murmushi tayi tace toh babana, du’a hada musu abinci ki kawo.
Adam da fatiha suka tsaya ganin ikon Allah wai abinci zai ci, du’a tashi tayi tana turo baki, ta nufi kicin, tana shiga aunty halima tace du’a lafiya, wai abinci zai ci, waye yayan fatiha, okay kije zan kawo musu.
Yana ganki haka, mamma aunty halima tace zata kawo, mamma ce tace bari naje daki idan kun gama saiki kira ni baffa tashi ka tafi daki , ba’a dade ba halima ta kawo musu abincin.
Dan dole du’a ta tashi zata zuba musu abinci, da sauri ya tashi yace ba wanda zai taba abinci, shi kadai zaici, adam ne yace du’a barshi ya cinye mu gani ko zai iya,
Ko kula shi batayi ba zata tashi yace dan zuba mini, danshi baisan yace zai zuba abinci ba. tam zubawa tayi da sauri ta tashi zata kaiwa adam ya ruko ta, ina zaki, juyowa tayi ta kalle shi, yace bani abinci na, ai ba kai kadai aka ce kaci ba. Ka sake ni, dan dole ya sakar mata kwanan.
Komawa tayi ta zauna, du’a nima ki zuba mini abincin, gashi nan a gaban ka, bazan iya ba, tashi tayi ta zuba mishi,
Ta kara zubawa ta mikawa fatiha, bari naje na dawo, daki ta tafi ta canza kaya, ta dawo.
Adam ne yace du’a ke bazaki ci abincin ba, eh yaya adam I’m okay, du’a zoki kara mini, tashi tayi taje ta kara mishi, a hankali yace saboda nine baza kici ba, aa banjin yunwa. Please dan Allah kici, enjoy your self I’m ok.
fatiha yaushe sultana zata tafi, kije ki tambaye ta, aa mai yayi zafi, suna hirar su suka gama cin abincin.
Adam ne yace tunda kaci abincin zamu iya tafiya, eh, du’a kice wa mamma zamu tafi inji adam, tashi tayi taje ta fada mata.
Sallama sukayi mata yarima yace sai na dawo gobe, Allah ya kaimu. Ameen suka tafi, du’a saida ta raka su har bakin mota, sannan ta koma ciki.
Bayan sun dawo fatiha suka fara shirya shirya kai amarya, aunty siyama ce kadai za,a kaita yau saboda a cikin gari ne, aunty maryam sokoto, aunty hauwa kuma abuja su sai gobe za’a kaisu,
Yarima na zaune yasa aka kira mishi su dukan su amaren, yayi musu fada sosai da nasiha, kuma sun karba sannan yace su tashi su tafi.
Du’a tunda suka tafi ta koma daki, mamma ce ta shigo, du’a mai yasa bakiji bance ki bari sai anjima ki dawo ba, mamma kaina ke ciwo, du’a ni na haife ki nasan halin ki, ki fada mini ko an miki wani abune a gidan, aa mamma mai zasu yimin, okay ai shikenan amma ki daina abin da kike kina ganin yarinyar nan yace take sonki ita idan tazo gidan ku saita dade, amma ke ko hour uku bakiyi ba kika dawo.
Mamma zan gara in sha Allah, nan kusa ma bayan biki zanje na yini, yawwa haka nake so, ta fita.
Bayan abbah ya dawo sukaci abinci, sun dade suna hira sai kusa 10:00 abbah yace suje su kwanta.
Tana shiga daki miss call din fatiha ta gani dana yarima , fatiha ta kira sun dade suna hira, tana kashewa kira yarima ya shigo.
Hello, sai tace salamu alaikum, sorry slm, Wslm ya kike, Alhamdulillah, shiru sukayi nadan wani lokaci kafi yace, how can I change, ka koma ga Allah, okay, sai gobe, bai musa mata ba yace Allah ya kaimu.
Bacci ta tayi shi kuwa yana can yana tunanin, ya dade kafin baci yayi awan gaba dashi.
Bayan sati daya du’a na zaune bata dade da tashi daga bacci ba, mamma ce ta shigo daki tace mata zata aike ta wurin mami zata kai mata sako, tam, shirya wa tayi ta fitoh mamma na palo tana jiran ta.
Mamma na shirya, okay yaya zai kaiki da daddare zaizo ya dauke ki, bata musaba dan tayi missing din besting ta, leda mamma ta bata ta kaiwa mami.
Suna tafiya suna hira ita da yayan ta, koda suka isa gidan shiga sukayi dan ansan da zuwa su.
Yarima na kokarin fita mota yaga ta fitoh daga mota, adam ne yace wacce ba du’a bace, ita ce “ amma waye wance yayan tane okay, bari muje mu gaisa.
Suna isa wurin adam ya mika mishi hannu suka gaisa shima yarima suka gaisa dashi, gaida su du’a tayi, bayan sun amsa adam yace du’a kin guje mu ko munyi laifi ne. Haba yaya adam ai baka laifi.
Du’a bari na tafi, haba yaya bafa ku taba gaisawa da mami ba, kazo muje ku gaisa kaji, toh yar abbah muje, yawwa yaya na.
Tare suka tafi shashen mami har su adam dama nan zasu je, meeno ce kwance kan cinyar mami, koda suka shiga bata tashi ba zama sukayi, yaya ya gaida mami, adam ma suka gaisa.
Sai lokacin da taji muryar adam ta tashi dan tasan tabbas tare da yarima suke, tana dagowa suka ido hudu da yaya, gaida su tayi, tadan kalli yarima wata uwar harara ya mata wace tasa ta yin kasa dakai.
Fatiha ta fitoh da tata rigimar, mami ni yunwa nake ji tana turo baki, idan ta ya sauka akan yaya, murmushi tayi tace la yaya kaine, dan ita bataga su adam ba.
Nine rigima ashe dai duk kwawar ja ce haline yazo daya shiyasa baku ganin laifin juna, murmushi tayi tace yaya du’a ta fini, duk haka kuke inji mami, kuba yara ba.
Ai mami gara fatiha ace itace auta amma du’a ita iskanci ne, dariya sukayi badda adam daya daure fuska, saboda kishi.
Kai yaya, I’m sorry yar abbah bari na tafi, tun yanzu son, murmushi yayi yace mami fita zanyi shi yasa.
Mu hadu a kashi na gaba.😊❤️❤️
Domin neman ci gaban wannan litafin zaku iya following Instagram page dina Reeeyarh ko kumin dm ta WhatsApp ***.
Nagode
*~Book by Reeeyarh~*