RAYUWAR DU’A

Chapter 12

by @reeeyarh

Page 12

*~reeeyarh~*

    Yarima ne yace kodai gudun mu kake bro, sai’a lokaci fatiha ta rula da adam dake gefan yarima, ba shiri tayi kasa da kanta tace yaya adam ina yini, lafiya lau kawai yace yana mike wa.

   Nina isa ai sai fatiha ta tara mini mutane, indai ba gudumu kake ba ka zauna, adam ina zaka je, daki ina jira, aa adam kar muyi haka dakai, ba haka kace idan ka dawo anan zaku ci abinci ba, dan dole ya zauna.

   Yaya ka fasa tafiya ne, ka manta abbah na jiran ka, aa du’a yanzu zan tafi, fatiha azo amin rakiya, yayi wa su mami sallama, du’a da fatiha suka raka shi.

   Adam ya kusa fashe wa, yarima ya lura da haka, yana son yi mishi dariya amma ba hanya, mami nanan.
   Adam kuje kuci abinci, tam mami, tashi sukayi suka tafi suci.
 
   Suna isa wurin motar taga sakon da mamma ta bata ta kaiwa mami, dauko wa tayi suka koma ciki, mami ce kadai a palon, du’a ta bata sakon da mamma tace ta kawo mata, suna hira su.

   Yarima tunda aka gama zuba musu abinci yake ta tsokanar adam, wai kai kishi ko, Allah saiki, karfa yayan du’a ya kasa ka, wallahi bai isa ba, aa dai, wannan dan talikin yaron ne zai kasa ni, aiko da yayi dana sani, taya akan sister shi zan rama, dama yayi dan yaga reaction din yarima ne.

   Ai wallahi baka isa ba mai laifin du’a, can ta matse muku a tsakanin ku amma babu mai saka ta, Allah inji adam, eh din. 

  Suna zaune har su adam suka dawo suka zauna, hira suka ci gaba da ita, adam a zuciyar shi yake cewa wallahi gara ayita ta kare, danshi bazai iya rabuwa da fatiha ba. 
   
   Kamar daga sama yaji mami na cewa adam wai ku maza kuka rako duniya ne ko kuma me, shiru yayi dan yasan maganar bazata huce akan aure ba, Allah idan bakuyi wasa ba sadakar ku zanyi, murmushi yayi yace mami a kara mana lokaci, dadai ka fadi gaskiyya, malan ba ruwan ka nida mami muke maganar mu, okay mami ai ya samu wacce zai aura lokaci kawai muke jira.

   Masha Allah wacece ita, mami fa da sauri adam ya rufe baki yarima ya ja shi suka futa, fatiha kuwa da tuni tayi daki.  

  Du’a ki fada mata, inji yarima kallon ta mami ta tsaya ta nayi, ko kece aa mami fatiha ce, sai lokaci ta kula fatiha bata gurin, murmushi kawai tayi tace Allah ya sanya alkhairi, da Ameen du’a da meeno suka amsa, mami bari naje wurin fatiha, okay nima daki zan tafi. Meeno da tun dazu ta gaza sukuni ( ganin yayan du’a) ta tashi itama ta tafi daki.

   Du’a na shiga daki tace an yanka ta tashi, fatiha komai yazo karshe, mun kusa shan biki. da sauri fatiha ta juyo ta kalli du’a, murmushi tayi mata tace mami ta sani saura baffa, da gaske, eh zama tayi suka ci gaba da hirar su. 

      Sai bayan sallar la’asar suka dawo palon, abinci suka ci sannan du’a tace zataje wurin baffa, nan suka tafi da fatiha.
   Yarima da adam na wurin, gaida shi sukayi sannan suka zauna, du’a yau kece kika zo, eh baffa, ya mutanan gidan naku Alhamdulillah baffa, yau dai ta kasa sakewa dan haka tace fatiha su tafi. 

     Sallama suka mishi suka tafi shashen hajja suka tafi, bayan sun gaisa suka huce shashen ummah, umar na zaune a palon shi da aliyu da mujid da basu dade da kammala karatun su ba sunka dawo a kasar uk. Gaida su sukayi sannan fatiha tace ina ummah, futowar ta kenan daga daki, ganinan fatiha. gaida ta suka sannan suka tambayi samha, tana daki.
   
     Okay bari muje, umar da tun shigowar su yake kallon du’a dan har ummah ta lura dashi, yace aliyu kuje kawai ni idan anjima zanje, ummah ce tace ina zaku, wurin papa, okay toh kai mai kake da bazaka je yanzu ba, tashi kuje kawai.

   Suna dade suna hira da samha sai bayan magriba suka koma part din mami, yarima ne zaune a gefen mami hanun shi cikin nata, adam yaje ya dawo dan yau a gidan zai kwana gobe da safe yarima zai tafi China. 

    Suna shigo wa ya bita da kallo sai faman murmushi take, har kun dawo daga yawon, mami saida mu kaje part din hajja dana ummah, na ammi fah inji mami, fatiha tace bamu je ba, dalili.
   Basai sunje ba ku huce ku tafi daki, yarima ne yayi maganar, dan suna magana akan fatiha da adam.

  Bayan sallar isha suka fitoh mami tace kuje kuci abinci, ba musu suka tafi, suna isa wurin suka tarda yarima , zama sukayi zakiha (  kuyangar mami) ta zuba musu abinci, suna ci muryar yarima ta dirar musu aka kamar wasa, auta sai bayan aure zaki ci gaba da karatun ko yaya. fatiha saida cokalin hannun ta ya fada, du’a kuwa ido ta zuba mishi.

    Baibi ta kansu ba yace mun yake shawara adam zai turo ayi magana, da sauri tace aa yaya dan Allah ba yanzu ba, toh sai yaushe idan kika ce ba yanzu ba saidai ki tafi karatu idan kin dawo , sai kuyi aure.
   Shiru tayi bata ce komai ba, kira neya shigo wayar du’a, hello yaya kazo ne, aa du’a bazan samu damar zuwa ba saidai na turo miki baba driver, aa yaya ka barshi
Zan dawo da kaina, aa du’a bari yazo ni bada wurin zan koma gida bane, sai yaushe zaka koma, sai 10:00, okay ba matsala idan na gama zan kira shi, okay, yawwa sister toh kiyi murmushi, murmushi tayi kaman yana gaban ta,

    yaya wurin aunty zahra zakaje, daidai da shigo war meeno karaf maganar ta shiga kunnan ta, ban sani ba salon yau na jini a kotun abbah yace na bar mishi diya na tafi hira, yar dariya tayi tace haba yaya na, karka damu asha soyayya lafiya, saika dawo, ta kashe wayar.

    Fatiha da tun dazu jikinta ya mutu tace du’a yaya bazai zoba, eh wurin aunty zahra zaije, okay bari na fadawa mami idan kin shirya sai tasa a kaiki, aa yanzu zan kira baba driver yazo ya dauke ni, shiru sukayi har suka kammala cin abincin.

   Shi kuma tunda du’a ta gama waya ya koma palon a zuciya yace ya samu damar kebewa da ita ko zai samu ta fahimce shi.

   Palon suka dawo nan fatiha ta fadawa mami cewa yayan du’a bazai zoba okay ba matsala sai yayan ku ya kaita, ko kanada wani abu ne, aa mami dama abinda yake so kenan. 

   Meeno ce ta fitoh ta zauna, kusa da mami yau dai tinda taga yayan du’a ta kasa sukuni, meeno da wani abune, aa mami me kika gani, shikenan ya huce, mami yaushe zamu je gidan aunty hauwa, sai end of next month. 

   Suna zaune mamma ta kira du’a, du’a kodai anan zaki kwana ne, aa mamma yanzu zan taho, tam gara dai ki taho dan abbah ku ya kusa dawowa, tam ta kashe wayar.

  Mami bari na tafi dare yayi, toh du’a yaushe zaki zo ki kwanar mana, murmushi tayi tace kwana mami, eh kiyi kamar one month, dariya fatiha tayi tace aiko da kinga ikon Allah, a abuja ma kuka ta musu, nanko da tana fita sai gida ai washe gari zata gudu, ina ruwan ki bada ke muke maganar muba mami ce tayi maganar.

  Mami zanzo amma ba kwana ba, dama na fada miki mami, okay du’a ina zuwa, daki ta shiga ta fitoh da leda a hannun ta, tace ta kaiwa mamma, tam nan sukayi sallama, shi kuma ya fita yana jiran fitoh warta, har mota fatiha ta raka ta.

    Suna tafiya a hanya ya juyo ya kalle ta, tayi shiru kamar bata motar, mai makon su tafi gida saiya bi waya hanyar, dan juyowa tayi tace ina zaka kaini, bai kulata ba yayi hanyar gidan su ziyada.

   Bata san wace ziyada ba ita dai taga ya shiga gidan governor da ita, suna zuwa wurin ya samu yayi packing ya kira ta yace ina jiran ki. 

   Tun dazu da yasan shi zaikai du’a gida ya kira ziyada yace zaizo, ziyada sai murna take Ahmad zaizo wurin ta, koda ta karaso inda motar take bude baya tayi ta shiga a tunanin ta yana bayan motar, driver ne ya kawo shi, tana shiga tayi tozali da du’a.

   Tana kokarin bude motar ta fita ya daka mata tsawa dan har du’a saida ta tsora ta, dalla malama dawo, zama tayi saida ya muri ya murmure sannan ya kalli du’a da tuni jikin ta yayi sanyi, a hankali ya furta du’a, dan dagowa tayi ta kalle shi ya sakar mata murmushi, itafa al’amarin yarima na bata mamaki kamar bashi ya gama masifa yanzu ba.

   Hannun yasa ya rike hannun ta, babu damar fizge wa dan ita tsoron shima take yanzu, kin san wace wannan, kai ta girgiza mai, banson haka ki bude baki kiyi magana, aa kanta a kasa.

  Juya ki kalle ta, juyawa tayi ta kalli ziyada da tayi suman zaune dan ita cewa tayi anya du’a yar nigeria ce. 

   Kin ganta kai ta daga sai kuma tayi saurin cewa eh, ki kalle ta tun daga sama har kasa, juyawa ta sake yi ta kalle ta, yace baki santa ba ko, eh.

   Ziyada ce da sauri ta daga kai ta kalle shi, kai ya daga mata alamar eh itace, sai ta kuma juyawa ta kalle ta a zuciya tace toh ina cikin, matsa hannun ta yayi yace ta nuna miki dan ita bata san maganar ta fitoh ba.

    Kuma kallo shi tayi, ya sakar mata murmushi yace tambaye ta yana ina, tuni ziyada gumi ya ciki mata fuska, tsawa ya mata yace yau idan baki nuna mata cikin nan ba saina ci uban ki wallahi.

   Ita dai du’a tsoron lamarin yarima ke bata, ziyada kuwa tuni ta fara bashi hakuri, dan girman Allah kayi hakuri, du’a wallahi karya nake bani da ciki, Allah karya nake, dan ubanki saikin nuna mata shi.

Du’a ita tausayi ma ta bata, amma bata ce komai ba, ziyada ki nuna mata cikin nace, da kar ta danne tsoron ta tace babu, babu kin tabba ta, eh wallahi babu ok fitar mini a mota, idan na dawo zanzo na miki hukunci ko kuma nasa adam ya miki, aa dan ALLAH ka mini da kanka karka turo adam.

   futa nace da sauri ta fuce, shi kuma yaja motar shi yayi hanyar gidan su du'a har suka je gida ba wanda yayi magana, nagode tayi kokarin bude kofa taji kofar a rufe, kasa juyowa tayi, yarima kuwa ya lura du'a ta fara tsoron shi dan haka shima baice mata komai ba ya dan kwantar da kanshi jikin kujera.

    a hankali tace motar a rufe, murmushi yayi kana ya dago ya kalle ta, juyo muyi magana bata musaba ta juyo, suka hada ido da sauri ta sauke kanta kasa dan gani tayi yarima ya mata korjini.

      hannu yasa ya daga fuskar ta yace idan kin shiga ki gaida mamma, kai ta daga mishi, sai kuma tace tam. 
 Du’a gobe zan tafi china ki tayani da adu’a ko na samu abinda ya kaini, in sha Allah. 

 Unlocking din door din yayi yace zaki iya tafiya, a tunanin shi ya fita daga zargin amma ya matan yafa amsa mata ya aikata.
   Tana shiga mamma na zaune a palo, mamma sanu da hutawa, yawwa du’a kin dawo, eh abban ya dawo, aa amma yana hanya dawowa. Okay bari naje na canza kaya.

  Kaya ta canza ta dawo, mai zan gani, a hankali ta karasa palon, abbah sannu da zuwa, yawwa du’a, zama tayi tana kallon shi, du’a ashe babana ne ya kawo ki shine ko kice ya shigo, baki ta turo tace ai baice zai shigo ba, murmushi yayi yace mamma tana da gaskiyya bance zan shigo ba.

  Mamma saida safe ni bacci zanyi, toh Allah ya kaimu, mamma nima bari na tafi, tun yanzu, dare yayi shiyasa. Okay saida safe ka gaida mami, du’a ba rakiya inji abbah, abbah ka barta bacci zatayi.

   Abbah saida ya raka shi har mota sannan ya dawo, aa ina bacci, abbah na tuna yaya zai kawo mini abu, ai shikenan.
   Sun dade suna hira sannan yaya ya dawo, kamar ya san maganar da sukayi da du’a da abbah sai gashi da ice cream, mamma Sannu ku da hutawa, da yawwa suka amsa mishi, du’a tayi mishi Sannu da zuwa, ledar ya mika mata ta amsa ta mishi godiya.

   Abbah bai kawo komai a ranshi ba itama mamma ko magana basu mata ba, itama taji dadin hakan, dama saboda yarima ne tace bacci zatayi kuma daya tafi saita fasa tace yaya take jira.

   Abbah bismillar ku, aa mun gode dama ai ba’a so musha ba shiyasa aka kawo miki ke kadai, yayi maganar da zolaya.
Aa abbah ai ita tace tana so shiyasa na kawo mata kuma harda nasu dee a ciki, ai sunyi bacci saina sha duka, duk kallon ta sukayi da mamaki wai tasha duka, idan zaki iya maza shanye, inji mamma, murmushi tayi tace aa mamma da wasa nake, bari na ajiye musu gobe sun sha Basu dade ba kowa ya kama gaban sa.

   Yarima kuwa tunda ya tafi gida ya nufa, adam na zaune a palon sa yazo ya same shi, malan daga ina haka, na kai du’a gida ne, okay yayan nata bai zoba kenan, murmushi yarima yai yace eh yaje wurin budurwar shi siya sa. da sauri adam ya juyo ya kalle shi, majewa yayi kamar bashi yayi maganar ba.

   Da gaske yana da budurwa, ka tambayi sister shi, ko ita mosoyiyar taka. Bai kuma cewa komai ba ya tashi yayi hanyar daki har yakai baki kofa yace a ina zaka kwanta, a nan, shige wa yayi ya bar shi. 
Adam sun dade suna waya da fatiha sannan ya shiga dayan daki, ya rufe.

  Yarima kuwa tunda ya shiga dakin ya kasa bacci tunanin du’a kawai yake, ko yanzu ta gane shiba fasiki bane, can kuma sai yayi tunanin ai ba lallai ta fahimta ba bariya kira ta ya fahimtar da ita. 

   Kamar bazata daga ba saida kira na biyu ya kusan yankewa ta daga, da sallama a bakin ta, amsa mata yayi kana yace ya kike, lafiya lau Alhamdulillah, shiru sukayi nadan wasu minute kafi tace inada abunyi, murmushi yake yayi yace ohw sorry, dama, ita dai har yanzu a tsoroce take dashi.

  Dama na manta waya ta ne idan kin ganta ki ajiye mini inna dawo zan karba, okay saida safe, ai ban gama magana ba. Fatiha ta fada miki ra’ayin ta akan auren ne, tace wai sai meeno tayi aure zatayi.
    Meeno kuma, eh haka tace, sai kuma me tace, ba komai, okay inaso kija hankalin ta ta amince ayi kawai a huce wurin. 

   Shi yaya adam din yace yanzu zaiyi aure ne, aa, toh ka barsu zasu yanke hukunci da kansu, duk abinda nace zasuyi su duka biyun, amma ai baka san zuciyar su ba, sufa zasuyi rayuwa ba kaiba, gara su fahimci juna su yanke shawara da kansu mu duk yan kallo ne. 
    Amma ai, rayuwar aure fa zasuyi su suke da iko da kansu ba wani ba, a zuciya yace kuma fa tana da gaskiyya, okay shikenan duk hukuncin da suka yanke ki fada mini dan nasan adam ba fada mini zaiba baran tana ita, amma ai ba hurumi na bane, you can ask one of your sister or mami.

   Okay tam shikenan saida safe, Allah ya tashe mu lafiya, Ameen har zai aje wayar yaji tana magana, Allah ya kiyaye, yaji dadin adu’ar tata Ameen nagode, ya kashe wayar.  tunani ya shiga yi kodai du’a ta gane gaskiyya har bacci yayi awan gaba dashi, itama tana tunanin tayi bacci, 
Kawaii dai ta mishi adu’a ne badan komai ba saidan ya sanar da ita zaiyi tafiya.

  Washe gari da sassafe adam ya raka yarima airport musali 6:00AM shima daga nan yahau wani jirgin yayi abuja.

    Du’a koda ta tashi da safe bayan tayi wanka taci abinci ta koma daki, fatiha ta kira sun dade suna wayar, fatiha yanzu mai kika tsara auren ko karatu, daga can bangaran tace wallahi basan yazan yiba
besting, nidai a ganina gara kiyi auren, amma, amma me, besting mai zaki jira tunda Allah ya baki mujin aure mutumin kirki, nasan ko karatun kika ce zakiyi bazai hanaki ba. 

   Wallahi besting yaya adam mutumin kirki ne, yana matukar sanki, du’a i already no that amma wallahi banson aure a wannan age din, okay saikin kai 30years zakiyi aure kenan, dan dariya fatiha tayi kafin tace ba haka nake nufi ba.

   Oho dai ke kika sani amma a matsayi na na besting ki gaskiyya nake fada miki. nifa so nake kamar nanda one year sai a saka ranar. Okay saiki fada mishi ai Allah ya taimaka. Ameen ina dee, suna school, okay sai anjima ki gaida mami zataji in sha Allah.

   Koda lokacin lunch yayi tana gamawa ta koma daki, wunin ranar a haka tayi shi a daki.
  
**************

A kasar china kuwa sai kusan 1:00 jirgin su ya sauka, koda ya sauka taxi ya sayar direct gidan su nacan ya sauka, tunda ya shiga daki yayi sallah yayi wanka sai bacci. 

  Sai bayan la’asar ya farka yayi sallah ya kira mami sun dade suna waya sannan sukayi sallama, fita yayi ya samo abinci da zaici, bayan ya kammala ya dauko wayar shi.
    
    Kallon hotan yake ko kiftawa  da alama lokacin da aka dauki hoton bata sani ba, sanye take da atamfa mai kyau  ba wata kaliya tayi ba amma tayi kyau sosai sai faman dariya take dimple dinnan ya loma itada friends dinta, daga gani wurin biki ne.

   Sosai ya shagala da kallon hotan dan gani yake kamar itace a gaban shi ranar dinner ne a abuja yayi mata hotan wani video ya kunna sai faman turo baki take ita a lallai an mata laifi lokacin da taje asibiti duba shi mamma tace ta jira mami.

     Screen din wayar ya shafa a hankali ya furta my aljana tsiwa, ya danyi murmushi yace ga shagoba. 
    Yana nan yana ta faman kallon hotunan ta wasu tasani wasu kuma bata san dasu ba, sallar magriba aka kira, murmushi ya karayi sannan yace i miss you my aljana.

   Toilet ya shiga yayi alwala ya huce masallaci, estate din da ya sauka kusan rabin su musulmai ne suna da masallaci a ciki, bayan an idan nan suka hau gaisawa da abokan arziki suna hirar yaushe rabo.

   Sai bayan isha ya koma gidan abinci yayi order, bayan an kawo mishi yaci ya koshi sannan suka hau waya da adam, sun dade suna wayar sai kusan 11:00 suka gama.

    Koda suka gama shirin bacci yayi, yana gado yana tunanin kodai ya kira ta, da wannan tunanin bacci barawo ya sace shi.

Washe gari ya fara aikin daya kawo shi yayi tunanin aikin zai dau lokaci sai yaga sabanin haka a ranar suka kammala komai.  yayi farin ciki da hakan da shi dama dole ce ta kawo shi aiko sati daya yace zaiyi ya koma.  

************* 
Washe gari du’a ta shirya tace ita gidan hajiya zataje, yaya ne ya kaita yace zai dawo ya dauke ta, anan ta yini tana zaune bayan la’asar kusan karfe biyar taji wayar ta na ringin, ko takan ta bata biba saida hajiya tace ba wayar ki bace, sannan ta duba.

Mu hadu a kashi na gaba.😊❤️❤️


Domin neman ci gaban wannan litafin zaku iya following Instagram page dina Reeeyarh ko kumin dm ta WhatsApp ***.

   Nagode 
*~Book by Reeeyarh~*