Chapter 13
by @reeeyarh
Page 13
*~reeeyarh~*
Bazaki daga ba, hajiya bakuwar number ce ki barta kawai kuma fa kamar ba number naija ba, toh ni ta dame ni daga kice musu wrong number ne, kai hajiya ni nama tafi daki na bar miki palon.
Koda ta shiga dakin saida aka kara kira ta kusa yanke wa ta daga, hello ba amsa sai tace can you hear me, nama ba amsa, wrong number zata kashe.
Da sauri yace aljana nine, tayi mamakin kiran shi amma sai ta basar tace amma sai magana nake kayi shiru, sorry ban jiki bane, okay ina yini, lafiya lau yasu mamma, Alhamdulillah, shiru sukayi nadan second sannan tace ina jinka.
I have two things to said, okay shima kanshi basan mai zaice ba, sai wani tunanin yazo mishi, about mamma family and fatiha marriage, kiyi tunanin.
No yet and kuma maganar fatiha nace ka tambayi sisters dinka, dan daure fuska yayi kaman yana gaban ta yace ke nayi ra’ayin tambaya, ta sautin muryar shi ta gane.
Shiru tayi, ina sauraran ki, har yanzu bata yanke hukunci ba, sai yaushe, wallahi ban sani ba amma idan ta yanke hukunci zan kira ka sai tayi saurin yin shiru, murmushi yayi yace ok ina jiran ki, ki tabbata kin sanar dani, bata da damar canza magana ta tafi tunani, wannan wana irin abu nayi toh taya zan kira shine ma, du’a baki jinane, na’am ina ji.
Dayar maganar ai ba haka mukayi dake ba, you said when you get back home zaki yanke hukunci, kawai kabar maganar.
Du’a ki zamtoh mai hakuri da yafiya and idan na dawo zanzo har gida muyi magana keba karamar yarinya bace bazai yiba kina batawa mutane rai ba koshi wanda akayiwa laifi ya yafe itama mamma ta yafe she want to be with her family du’a ki gane mana da fadafada yake maganar.
That’s my family issue ba ruwan ka, kuma wana batawa rai, when I’m back you will know, everything will be over as soon as possible. du’a bata gane kan maganar shiba, no need basai kazo ba zamu warware matsalar mu.
ni ban hana mamma zuwa wurin dangin ta ba nidai nace bazan jeba kuma non of my family will visit them kuma wannan ra’ayi nane babu wanda zai canza mini shi, SAINI…
Yar dariya tayi irin ta ranin hankali tace never, okay ki jira na dawo you most visit mamma family. Good night ya kashe wayar sa.
Du’a kanta ya kulle kodai yarima yasan dangin mamma ne tana saka tana warware wa hajiya tazo ta same ta.
Namesake dawa kike waya ko siriki nane, aa hajiya yayan fatiha ne, toh shi dinma ai zai iya zama siriki na, hajiya akan bikin fatiha muke magana fah, aa dai ki fada mini gaskiyya, wallahi ta tashi zaune.
Hajiya niko na tambaye ki wani abu, Allah yasa na sani, ai kima sani ma, okay ina jinki, hajiya wai family din mamma a wani gari suke, hajiya tayi mamaki dan du’a tun ranar da taji mamma nacewa family dinta korar ta sukayi, a lokacin batafi ten years ba tasa abin a ranta, bata san a wani gariba suke, ko maganar su bata sake bari anyi a gaban ta ba saboda lokacin mamma da kanta tace ba ita basu.
Hajiya kinyi shiru ai du’a maganar taki ce bani da amsar ta, nidai kamar a nan garin suke amma bani da tabbaci, amma mai yasa kika tambaya, ajiyar zuciya tayi sannan tace kawai inaso nasani ne shiyasa.
Nan itama ta daura tace du’a kinsan me, aa hajiya, mamman ki nasan komawa family ta amma kisan mai yasa taki koma wa, aa, saboda ke ne, tana sonki bata son bata miki rai, shiyasa’ wai kowa sai yace saboda ni ne, murmushi manya hajiya tayi tace kina so a daina cewa soboda ke ne, hajiya ni wallahi ban hana mamma zuwa gidan suba kawai dai nace nida family na bazamu je ba.
Toh ai kinga dalilin nan taya tayi wannan uban shekarun ta koma gida ita kadai, du’a idan kika yi hakuri kuka je tare sai tafi jin dadi, kuma tace bazata koma ba tare da yaran taba, du’a ki taimaki rayuwar bawar Allah nan, itama fa yar wani ce, kiji a ranki idan abbah ya kore ki zakiyi fushi dashi, aa hajiya zanna zuwa gida har saiya yafe mini, toh kin gani itama da kanta ta fada mini iyayen ta sun nemi yafiyar ta, amma tace bazata je ba, soboda ke. yaushe sukayi hakan, lokacin kina gidan hafsa(ammi), shiru tayi.
Du’a ki yafe musu kinji, hajiya mu bar maganar zanyi tunanin akai. bari nayi alwala dan naga lokaci sallar magriba yayi, hajiya da kallo ta bita, a zuciyar ta tana tunani wannan yarinyar halinta daya da uban ta shiyasa tasu tazo daya, dan shima saida akayi dashi kafin ya manta maganar, mutun sai shegiyar kafiya Allah ya shirye ku dake da uban naki. hmmm gaskiyya uwart ce tace bazata yarda ba gashi kuwa na gani, amma zamuci gaba da kokari har Allah yasa muyi nasara, gashi shi uban nata yaki mata magana nasan da tuni wani zancen ake ba wannan ba.
Ranar da mamma tazo lokacin du’a na abuja saida ta zayane mata komai na halin du’a da abbah dukda hajiya tasan halinsu amma ita abunna bata mamaki shegen taurin kai na uba da yarshi, hajiya tace karki damu badai mun gama da uban nata ba itama zata sauko ne, tam hajiya dan Allah kota tambaye ki family na kice baki sansu ba, kuma hajiya kiyiwa abbah magana kar du’a tasan naje gida, kamar ya waishi saiya fada mata, hajiya har yanzu baki fahimci halin da nake ciki ba akan wannan uban da yarshi, wani abun fa saidai naji a bakin shi idan nashi ne saidai naji a bakin ta. karki damu zan mishi magana.
Hajiya anfa idar da sallah tun dazu sai magana nake amma baki jina, hajiya thinking is not good for your health.
Wa yace miki tunanin nake, gashi na gani, kinga bari nayi sallah yau bakin dare zanyi, baki kuma hajiya, eh ko karasu zone uwar rashin son mutane aa hajiya suzo abinsu, ni ina gama a gidan nan zan kwana, bari na fadawa abbah saiya fadawa mamma, a zuciya hajiya tace ako gashi abuya tabbata tunda anyi a gabana wai ta fadawa abbah ya fadawa mamma.
Ke idai bazaki kira mamma ki fada mata da kanki ba bazaki kwanar mini a gida ba, du’a shiru tayi tana kallon hajiya, sai kuma tasa dariya kaga mai suruka, hajiya gaskiyya kinaji da wannan surukar taki Allah ya bani suruka irin ki, kedai kika sani ki kirata ki fada mata, tam. hajiya tayi hucewar ta.
Shi kuma lokacin daya kirata yayi shirin bacci da suka gama wayar har 12:00pm yayi, yana tunanin bacci yayi gaba dashi,
Hello mamma, ina jinki, mamma dama sai tayi shiru, dama mai, mamma zan kwana a gidan hajiya, oh da shine kika tsaya kina inda inda, shiru tayi bata ce komai ba, toh ki kira yaya ki fada mishi basai yazo daukar ki ba. Tam mamma sai gobe, ummhim…..
Yaya ta kira ta fada mishi, okay shikenan, ta kira abbah shima ta fada mishi, nan yake tambayar ta kodai laifi kika yiwa mamma, aa wallahi abbah kawai ina son kwana a gidan hajiya ne, ai shikenan bye, okay dad sai gobe…
Palon ta fitoh, taje gefan hajiya ta zauna, hajiya na fada mata, yawwa, kije kici abinci, kefa na koshi dinning area ta huce taje ta zuba abinci ta dawo palo wai anan zata ci.
Bayan sallar isha tana kwance kanta a kan cinyar hajiya, akayi sallama bata tashi ba, taci gaba da danna wayar ta, wasu samari ne su buyu sai mace daya a gaban su.
Hajiya kice yau bakuwa mukayi inji maccen, da sauri du’a ta tashi tace la aunty na kece, kar kizo inda nake keda baki ziyara, haba aunty na, hajiya ce tace wa samarin su zauna mana, suna zama itama ta zauna du’a kusa da ita taje ta zauna, matashiya ce wace baza ta huce 25years ba mai suna zainab sister yaya Ibrahim.
Du’a dauko wa bakina drinks inji hajiya, tashi tayi da sauri taje ta dauka ta dawo ta zauna kusa da zainab, aunty ina munnira mai yasa bakuzo tare ba, idan kina son ganin ta kije gida ki ganta mana, aunty zanje fa lokaci ne ban samu ba, okay bari dai yanzu idan anjima mayi magana, aunty anan zaki kwana, dan Allah ki kwana, aa gida zan tafi saida kizo mu tafi, eh zan biki, toh yar aunty ba inda zaki kina nan gidan inji hajiya da ta gama gaisawa da samarin.
Turo baki tayi, hajiya ko gaisawa bamu yi ba yar nan ta dame ni, nan suka gaisa,
Daya daga cikin samarin tunda suka zo yake kallon du’a, ita tama manta da wasu a palon, a hankali zainab tace mata du’a baki gaida su bafa, wanda zan aura ne, la aunty da gaske ni banma lura dasu ba.
Dagowa tayi ta gaida su suka amsa, nan suka hau hira dasu da hajiya, abinka da yan boko su basu san wani abu waishi surika ko suriki ba, wayar du’a ce tayi kara, zainab ta kalle ta tace kodai kani nane yake kira, du’a bata gane mai zainab ke nufiba tace yaya abbi wai ni yashe rabo da muyi magana dashi, hajiya wannan jikar taki ba komai take fahimta ba, murmushi manya hajiya tayi.
Du’a ina nufin saurayin ki, haba aunty fatiha ce, ki fadi gaskiyya kullun saidai kina fatiha ce, Allah aunty kin gani ta nuna mata screen din wayar, okay na gani.
Tashi tayi ta tafi daki, hello besting, na’am Ykk, lafiya lau, masha Allah yasu mami, Alhamdulillah ina mamma, mamma na gida, okay baki gida kenan, eh wallahi naje gidan hajiya, okay besting mami na neman ki, dan Allah kizo. meya faru, dama inaso ki fada mata mun yanke shawara za’a kawo kudi nanda next year sai ayi bikin,
kinga maganar bata waya bace, eh haka ne yanzu dai ina gidan hajiya zan mata kwana biyu, idan na dawo zuwa ranar Wednesday sai nazo, okay shikenan, hira sukaci gaba har saida zainab tazo tace mata zata tafi sannan sukayi sallama.
Da sauri tabi bayan zainab tana cewa aunty dan Allah ki kwana dan Allah aunty, ke kibar yar mutane ta tafi dare yanayi, kamar zatayi kuka tace haba aunty na, daya daga cikin samarin yace haba matar aboki ki kwana mana, ka barta iskanci ne idan tana son ganina tazo gida mana.
Wayar tace tayi kara, hello adda daga can bangaran akace kin taho ne, aa adda, kinga dare yayi kawai ki kwana anan, okay shikenan saida safe ta kashe wayar.
Kinga Allah ya taimake ki adda tace na kwana, rungume ta tayi tana murna, okay mu bari mu tafi inji wanda zata aura sunan shi sadiq dan gidan governor gahar kano ne ( yayan ziyada). Sai abokin shi faruq dan manager center bank of nigeria ne.
Okay du’a muje mu raka su ko, a tare suka je suka raka su, sadiq ne ya mikowa du’a kudi, aa nagode, faruq yace ai ba’a maida hannu kyauta baya dan Allah ki karba, kin karba tayi sai zainab yaba yace ta bata, daga nan suka tafi.
A hanya faruq yake cewa nifa wannan tamin dan Allah a taimaka mini, aboki karka damu ka bari zanyi wa wife magana, murmushi yayi yace yawwa my man.
Koda suka koma ciki a tsaye suka ga hajiya, ta tashi zata kwashe kayan taga kudi bandir din yan 1000 har guda biyu, zainaba kiga abinda yarannan sukayi ai dana gani basa ajiye ba, murmushi zainab tayi tace hajiya kenan, nima wallahi ban kula ba, kuma gashi wannan yaba du’a, itama bandir din 1000 guda 1.
Mai yasa kuka karbo, hajiya dama niban karba ba, hajiya wallahi haka yace saimun amsa, ai shikenan kuje kuyi shirin bacci naga dare yayi, a wana daki zaku kwana, hajiya wai ina abokiyar zaman ki(mama). Dazu taje babura gobe zata dawo in sha Allah. Nan suka huce sama suka shiga wani daki, gidan ba wani babba bane part biyu ne, ko wana part yana da daki hudu palo biyu sama da kasa ne, hajiya daya mama daya.
Washe gari suka tashi koda suka sauko an gama komai na gara da girki hajiya nada yan aiki biyu, dayar batafi shekara 20 ba dayar kuma 16, yar 20years din sunan ta rabi, dayar kuma Fauziyya.
Zama sukayi suka ci abinci har yan aikin a dinning dan sai kayi tunanin yaran gidan ne, hajiya tana kula dasu sosai kanar yaran ta, suna gamawa suka koma palo fauziyya da rabi kuma suka gara wurin.
Zainab ce ke waya da sadiq, har yake fada mata wai faruq yace yana kamun du’a, murmushi tayi tace tam bari mu goda, amma she’s still young, suna cikin waya ziyada ta shigo, nan tace saita gaisa da zainab, du’a na gefan zainab, taji zainab na cewa ziyada ya kike, da sairi ta juyo ta kalle ta, zainab ta rula da kallon da du’a ke mata.
Bayan ta gama wayar tace du’a wannan kallon fa, ba komai aunty kawai dai, kawai dai me, aunty dan Allah na tambaye ki, ina jinki, uncle sadiq a ina yake da zama, murmushi tayi tace anan garin mana, dan waye shi, zainab tayi mamaki maganar du’a dan saida ta tsaya tana kallon ta.
Aunty dan Allah kiyi hakuri bai kama ta na miki wannan tambayar ba, kawai sunan da kika ambata ne yasa na tambaye ki, akoi wace na sani mai irin sunan, nasan ma ba ita bace, murmushi tayi tace fada mini wacce ita toh, aunty abar maganar.
Aa du’a ki fada mini, shiru tayi tana tunanin can ta sauke ajiyar zuciya tace aunty, na’am, uncle sadiq dan governor garin nanne, taya kika sani, ji tayi gaban ta ya fadi tayi saurin dagowa ta kalle zainab.
Du’a kinyi shiru meya faru ki fada mini, aunty amana ce bai kama ta na fada miki ba, amana kuma du’a, eh aunty zan fada miki amma karki fadawa kowa okay ina jinki, aunty dama lokacin dana je gidan ammi, nan ta fada mata komai har sanda taje gidan su galadima, tayi mamaki tace du’a yanzu ke wana kallo kike mishi, aunty baya ce halin shi bane.
du’a you’re still young girl, ya kamata ki gane, taya zaki zargi babban mutun haka, du’a ba halin shi bane, amma ai shi yace halin shine, shiyasa nace ke yarinya ce, du’a yarima na sonki shiyasa ya kasa gaya faki gaskiyya, haba aunty nidin,
du’a ki tsaya kiyi tunanin da kyau ba kince baya son abokin shi yasani ba, eh haka yace baisan yana yiba, yarima yasan halin abokin shi yana da zafi soboda son da yake miki baya son adam ya miki fada shi yasa, amma tabbas ba halin shi bane so ne yaja mishi. Allah aunty ba sona yake ba yayan fatiha ne fah. toh shi yayan fatiha ba mutun bane.
Ni kawai abar maganar, tam naji amma ki yarda dani yarima ba fasiki bane, tam aunty na yarda, amma dan Allah karki fadawa kowa, kinga siri ne, an gama.
Yau mada da daddare saida ya kira du’a, yau yawo ya fita yaje yaga gari da magariba wani abokin shi yazo wanda sukayi makaranta tare.
Suna zaune a palo, mama bata dade da dawo wa ba, du’a ba wayar ki ake kira ba, eh tawa ce, dan iskanci sai ana kiran mutun bazai daga ba jiya ma haka kika mini, wallahi zan karbe wayar na kashe ta, zainab tace du’a ki dauka mana, a hankali tace nace mishi mai, waye, yayan fatiha ne, murmushi zainab tayi tace kije kiji mai zaice miki kinji, tashi tayi ta tafi daki.
Hello, hello aljana ya kike, ina yini, lafiya lau ya gida, Alhamdulillah, sai kuma shiru ya biyo baya, du’a, na’am, ziyada ta kara kiran ki, aa” okay, a zuciya tace bari na goda shi, amma taya akayi da muka je banga cikin ba, ba tare muka jeba, ai kinji me tace.
Eh kuma kace kayi mata cikin, ajiyar zuciya ya sauke a zuciya yace komai ya kusa zuwa karshe, du’a ai tun farko na fada miki gaskiyya amma naga kina zargi na shiyasa nace nayi, shiru tayi, sai kuma tace toh ka taba yiwa wata cikin ne, maganar taso bashi dariya sai ya basar yace, du’a taya zanyi wa yar wani cikin kuma naje lahira nace mai, tunma kafi aje lahira da wana ido zan kalli baffa da mami.
Du’a inadai na bata yar wani nima sai anyi akan daughter ta kinga kuwa wana uba ne zaiso yarshi ta baci ta dalilin shi.
A hankali tace kayi hakuri, akan me, na zarge ka akan abinda bakayi ba, ka yafe mini, murmushi yayi yace du’a ya huce kema kiyi hakuri kinji, sharin shedan ne yasani taba macen daba maharamata ba.
Yaya ya huce, amma karka kara, murmushi yayi wanda har saida taji sautin yace in sha Allah, yaya karka fadawa yaya adam, du’a mai yasa kike tsoron adam da yawwa haka, ni bana so ya mini fada, du’a idan na fada mishi ai ni zai fara yiwa fada kafin ke.
Tam shikenan yanzu dai komai ya huce ko aljana, murmushi tayi tace eh, sai anjima, haba aljana ki bari muyi hira mana yawwa ranar wednesday zanje gidan ku, gidan mu kuma mai zakiyi, dama zan fadawa mami yaya adam yace zai kawo kudi sai nanda 1year sai ayi auren, okay ai shikenan tunda haka suka zaba, ai yafi dama nima hakan ya mini.
Dama zaki ce ya miki mana tunda zabin besting ki ne, murmushi tayi, ita wallahi ta gaji da wayar kawai so take ya kashe, du’a kinyi shiru, emmm, da alamu dai kin gaji ko, aa, ina mamma, tana gida, ina kika je, ina gidan hajiya, okay yau zaki koma gida ne, aa sai gobe, yau ziyara kika je kenan, ai tun jiya nazo.
Kinyi abin arziki saura gidan su mamma, gidan su mamma kuma ai mamma bata da kowa, murmushi yayi a zuciya yace wannan yar Allah ya shirye ta, a fili kuma yace inji wa, ni, okay muje a haka ina dawowa komai zai zo karshe, yaya kasan family mamma ne, eh, su waye, idan na dawo zan fada miki, okay Allah ya dawo dakai lafiya, Ameen my aljana good night. Okay night.
Yana kashe wayar ya shiga duniyar tunanin, yayi farin ciki da du’a ta gane gaskiyya a haka yayi bacci.
Ita kuma palo ta fitoh ta zauna kusa da zainab, du’a kina lafiya, lafiya lau mai kika gani, aa ba komai ya kuka yi dashi nan ta fada mata yace sukayi da yarima , toh shi yasan family din mamma ne eh yace ya sani, okay ai shikenan amma du’a guy dinnan na sonki sosai ki fahimta, aunty ni ki daina cewa yana sona, Allah ba sona yake bah, tam tashi muje muyi sallah.
Bayan sunyi sallah du’a take tambayar ta amma ba yau zata tafi bah, yau zan tafi mana, idan anjima yaya Ibrahim zaizo mu tafi, du’a bata son tafiyar zainab, zainab na son du’a sosai sun shaku, kamar ciki daya suka futoh, aunty, na’am sister, next week in sha Allah zanzo, okay Allah ya kaimu, Ameen.
Sai bayan isha yaya Ibrahim yazo, sun danyi hira kafin su tafi, koda suka tafi du’a sai taji gidan ba dadi, da wuri tayi bacci.
Washe gari da yamma yaya yazo ya dauke ta, tana shiga ta fada kan mamma tace mamma wallahi nayi missing dinki, ji tayi ance karya ta zakiyi ne ko ya, bazata manta muryar ba, juye juye ta fata taji daga ina sautin yake, sai a lokacin ta kula da laptop din dake gaban mamma, sanye yake cikin jallabiya fara gashin nan yayi lumai ya kwanta.
Tashi a kanta madam, a hankali ta tashi ta zauna a gefen ta, yaya ina yini, lafiya lau kamar wata yarinya kin hau kanta, kai dai bari babana haka nake fama da ita.
Ai mamma ke kika barta take wannan abun, Allah ya shirye ki baki ta turo ta tashi tabar palon, daki ta huce ta canza kaya tana canza kaya tana tunanin mai galadima yake cewa mamma, ita fa lamarin shi yana bata tsoro, koda ta dawo har lokacin basu gama wayar ba.
Zama tayi kusa da mamma, mamma yaya fah, yana daki abokin shine yazo, okay, wayar mamma ce tayi kara tace du’a zo ku gaisa bari naje na dawo.
Mu hadu a kashi na gaba.😊❤️❤️
Domin neman ci gaban wannan litafin zaku iya following Instagram page dina Reeeyarh ko kumin dm ta WhatsApp ***.
Nagode
*~Book by Reeeyarh~*