Chapter 15
by @reeeyarh
Page 15
*~reeeyarh~*
A hankali take tafiya tana zuwa zata zauna akan kujera yace sauka kasa, mamma tashi tayi ta bar musu palo, zama tayi a kasa tuni idon ta ya ciko da kwalla, yaya kayi hakuri, baki da hankali ko, ke bakisan idai kayi baki mantawa kake da lefin da suka maka ba tunda sunzo inda kake, shiru tayi, yaya I’m sorry, zanci ubanki ne, ba zaki gaida su ba.
A hankali tace yaya ina yini, yarima baiji dadin abinda yaya yayiwa du’a ba, jiki duk a sanyaye ya amsa, fatiha meeno kuyi hankali.
Yaya besting fa batayi laifi ba, fatiha ki fita daga ido na ai dama keda abbah baku ganin laifin ta, kuma ki shirya gobe Zakije gidan su fatiha.
Wani wawan kuka tasa wanda saida ya taba zuciyar yarima , shima kanshi yayan baisan zatayi irin kuka nan ba, a hankali ya dago ya kalle ta yace sister zaunan tashi tayi ta koma kusa dashi.
Stop crying kinji na daina miki fada, yaya a rayuwar sa ya tsani yaga tana kuka, shi yasa ma tasa kukan dan tasan dole ya lallashi ta, a hankali tace yaya bana son zuwa, okay shikenan bazaki je ba amma idan kin daina kuka, ba shiri ta tsayda kukan, goge mata hawayen ya fara yace toh kiyi murmushi, murmushi tayi tace yaya I’m sorry.
Yarima dai sai kallon ikon Allah yake kamar bashi ya gama mata fada ba amma kali yacce yake lallashin ta, lallai dole du’a tana iskancin ta yan gidan su son juna ya rufe musu ido.
Fatiha ce tace besting ki daina kuka, tashi tayi ta koma kusa da ita ta zauna tace besting bazan iya yiwa kowa magana ba a family mamma ba sai ke, besting dan Allah kice musu su barmu muyi rayuwar mu yace muka saba, rungume ta fatiha tayi tace besting stop crying kinji.
Komai zai huce wata rana sai labari, du’a bata ce komai ba, yarima yace fatiha taso mu tafi, tam yaya, yaya yace tun yanzu zaku tafi, akoi inda zanje, ka barsu mana idan anjima sai na kaisu gida, aa karna saka wahala , saidai naje na dawo, ok bari na fadawa mamma, tashi yayi yaje ya fada mata.
Babana ba yini kazo ba dama, aa mamma bari naje saina dawo na dauke su, tam saika dawo. tashi yayi yaya ya raka shi, koda suka fita saida yacewa yaya dan Allah ya taya shi shawo kan du’a ta amince ta karbi su hajja a mtsayin su ba matsala in sha Allah zamuyi magana da ita.
Lokacin da ya dawo suna palo, daki ya huce ya barsu, sosai du’a ta saki jiki dasu, sunyi hira har meeno, kuma su nemar wa su baffa yafiya, koda suka mata zancen murmushi kawai tayi. Bayan la’asar su dee suka dawo, nan suka zauna a palo suna hira, meeno family du’a sun burge ta sosai, bayan magariba suna zaune dee na feeding du’a dan tace ita zatayi feeding dinta su kuma sun gama cin nasu abinci.
Yarima ne ya shigo da sallama, tsayawa yayi yana kallon ikon Allah yanzu abincin ma a baki ake bata, Allah ya shirya, babana shigo mana, karaso wa yayi ya zauna, dee I’m okay wallahi na kwoshi, okay shikenan, gaisa suka sakeyi da mamma sannan yace su fatiha suzo su tafi, aa babana tun dazu jira nake ka dawo maza kaje kaci abinci, aa mamma idan naje gida zanci bana jin dadi, sai lokacin du’a ta kalle shi.
Du’a tashi kuje ki zuba mishi abinci, kinji, ba yacce ta iya dan dole ta tashi, babana tashi kuje.
Suna isa dinning area ya saki labulan da sauri du’a ta juyo ta kalle shi, sai kuma ta juya ta fara zuba mishi abinci, a hankali yace du’a laifin mai nayi, bata kula shiba, saida ta gama zuba mishi abincin tazo hucewa ya ruko hannun ta, da sauri ta juyo ta kalle shi.
Tsaya muyi magana, can you please live my hand,idan kin tsaya munyi magana ba, dan dawo tayi baya tace me hadina dakai, babu, kokarin fuzge hannun ta tayi amma bazata iya ba, janta yayi ya zaunar akan kujera shima ya zauna.
Dan Allah ka kale ni, du’a way are you always hurting me, kamar ya, du’a mai nayi da bazaki mini magana ba baki san kina cutar dani ba, mtssss, tsaki tayi ta tashi tabar wurin, saida yaja lokaci kafin ya fara cin abinci, bayan ya gama har lokacin sallar isha yayi, tare da yaya suka tafi masallaci.
Du’a kuwa ita haushi yarima ke bata, sai yanzu taji ta tsane shi duk abinda ya mata na baya ya dawo mata musamman marin daya mata, tan zaune wayar ta tayi kara, hello, hello du’a kinaji na, eh inaji, dan Allah fitoh kofar gidan ku, waye nan yace faruq ne abokin sadiq, sai yanzu ta gane mai magana, mamma na daki, satar hanya tayi tace wa fatiha bari naje na dawo.
Ina zaki, kofar gida yanzu zan dawo, tana fita ta ganshi a bakin mota, yace su shiga mota tace aa sauri take mamma bata san ta fitoh ba, okay du’a dama saiga yarima da yaya sun dawo, yaya ne ya fara zuwa gurin dan yaga du’a yace ke uban me kike anan, yarima na zuwa yayi suman tsaye saida faruq yace Ahmad kaine, murmushi yayi suka gaisa, nan yake tambayar shi dama yasan du’a, eh cousin dina ce, okay yaya ne yace huce mu tafi.
Faruq ne yace haba yayan mu ka bamu two minutes yanzu zata dawo, aa umar kaga abbah ta ya hanata fitoh wa bada izinin shiba, okay shikenan, du’a zamuyi magana, okay sai anjima, saida ya tafi sannan suka shiga gida, ke a gidan uban wa kika san shi, friend din saurayi aunty zainab ne, toh uwar surutu, shima surutu kika je kina mishi shine ya biyo ki ko, mamma tasan kin fitoh, aa.
Sannu toh muje ki mata baya ni, yaya sallah take lokacin shi yasa, oho ke kika sani dan Allah yaya kayi hakuri Allah bazan kara ba, wallahi duk ranar da na kuma ganin ki a waje Allah saina fadawa abbah, wallahi bazan sake ba Allah, a haka suka shiga palon, har kun dawo, eh mamma ke kuma fa, aa yanzu nace tazo ta bude mana gida, okay.
Yarima kallon shi kawai yayi a zuciya yace Allah ya shirye ku da wannan shege san junan shikenan wani bazai bari a yiwa wani fada ba, meeno ku tashi mu tafi, meeno dai bata ji dadin zuwa gidan nan ba inji yaya, murmushi kawai tayi, fatiha tace inji wa, naga she’s too silent, aa naji dadi mana, kuma zan kara zuwa in sha Allah, kin tabbata eh tace tana mike wa, saida suka raka su har mota sannan suka dawo gida. koda suka koma zama sukayi suna hira har abbah ya dawo.
Yau abbah shi kadai yaci abinci dan duk sunci, sunnu dade suna hira su dee suna bawa abbah labarin su fatiha, har kusan 10:00, abbah ne yace su tashi su tafi su kwanta, dee da teema sukayi dakin su, du’a ma tayi nata, baffa ma ya tafi nashi dakin, yaya bai tafi ba.
Abbah dan Allah ka taimaka ka yiwa du’a magana, akan mai? mai tayi. abbah akan family mamma mana yau kaga iskancin da tayi nan ya bawa abbah labari, mamma najin su ba tace komai ba, yaya ka daina mata fada she is still young, mamma mace tayi murmushi yake tace hmmmm ta tashi tabar palon.
Abbah Allah du’a ba yarinya bace yanzu she’s 18 fah, kuma Allah abbah mamma bataji dadi ba, karka damu zan yiwa du’a magana kaji yaya, yanzu kaje ka kwanta, tam abbah saida safe, Allah ya kaimu.
Su fatiha tunda suka tafi suke suke hira da meeno, yaya kaga yacce du’a take fushi da kai, ni kuma, eh Wlh yaya tace wai ka sani amma baka fada mata ba, fatiha yaushe kukayi haka da ita, da muka shiga kicin, okay.
Toh yanzu fatiha ni mai nawa a ciki, nima fa haka akace karna fada, amma zamuyi magana da ita, a haka suka je gida, mami na zaune da kuyangun ta.
Bayan sun gaida su suka tashi suka bar palon, nan suka yiwa mami Sannu da hutawa, yawwa sunnun ku, sun danyi hira sannan yace ya tafi part dinshi, okay saida safe. Yaya kayi magana da du’a kaji, tam mama fatiha ya huce.
Mami tace wani abu ya faru ne, nan fatiha ta bata labarin abunda ya faru, sosai mami tayi mamaki tace kuma bata ce zata yafe musu ba, bata ce komai ba, ai shikenan kuje ku huta.
Koda ya shiga daki wanka yayi, yayi shirin bacci, yana kwance ya dauko wayar shi ya kirata harta yanke ba amsa, kira na biyu ma haka, message ya tura mata.
Du’a na kwance taga kira, hmmm wallahi bazan daga ba, saida message din ya shigo sannan ta duba, du’a kiyi picking call din akoi maganar da zamuyi, kira ya shigo, bata daga ba harya yanke.
Saida ya kuma kira ta daga, hello, batayi magana ba yace du’a ba magana nake ba, ina jinka, okay I’m not talking about mamma family inaso zamuyi magana, okay inaji, du’a ki cire ni a cikin fadan ku babu ruwana, toh mai hadina da kai, dan Allah ka barni nayi rayuwa ta, dama ai bamu da hadi fatiha ce hadin mu ko dan haka itace friend dina not you understood.
Yes I know but kawai yaji an kashe wayar, kira ya karayi amma bata daga ba, bai kuma kiran ta ba.
Washe gari around 12:00 yaje gidan, da sallama ya shiga palon, du’a ce kadai tana kwance a kan kujera, bata amsa ba dan bata jishi ba, ganin mutun a kusa da ita yasa tayi saurin tashi, zama yayi a kusa da ita.
Tashi tayi zata bar wurin yayi saurin rukota ya zaunar da ita saura kadan ta fada kansa, ka sake mini hannu, I will not.
Jiya mai yasa kika kashe mini waya, shiru tayi ba amsa, hannu yasa ya dago fuskar ta, yi magana, ya matsa hannun ta, nika sakeni kar mamma ta fito, sai kin amsa mini. Bacci nayi, dayan hannun yasa ya dan bigi goshin ta yace karya ba kyau, da gaske nake ka sake ni.
No we have to talk, toh dole ne ai ni bana da hadi da kai, canza fuska yayi yace ba wasa nazo ba, magana nazo muyi, du’a tadan ji tsoron shi, tace akan mai, ina mamma, tana daki, okay jeki kirata, tam tashi tayi taje dakin koda taje mamma na bacci.
Dawowa tayi tace bacci take, okay zanci abinci, kai ta daga ta kalle shi, suka hada ido, ya daga mata kai alamar eh, a zuciya tace anya bazata ce mishi babu ba kar kuma mamma ta fitoh ya tambaye ta, aljana ko baza ki zubo mini bane, halima ce ta fitoh tace du’a wai abincin ne bazaki ciba koya.
Aunty halima banji yinwa, sai lokaci halima taga yarima , gaida shi tayi sannan ta shiga ta dakko mishi drinks, aunty halima ina abincin, yana dinning, okay, sai kuma ta kalle shi tace muje kaci abinci, okay halima daki ta shiga, su kuma suka nufi dinning.
Koda ta zuba mishi abincin tashi tayi zata tafi, ina zaki, zan jira ka a palo, no zauna kici abinci, I’m okay, sit nace zama tayi, oya zuba, Allah da gaske bana jin yunwa, nidai nace kici, dan dole ta zuba abinci ta fara ci.
Du’a abbah na nan, aa, yaya fah, shima bainan, okay.
Du’a mai yasa baza ki yafewa su papa ba, bata ce komai ba, soboda basu san abbah ko, toh yanzu suna sonshi, kuma sunce idan anjima zasu zo su nemi yafiyar shi, murmushi yake tayi tace Allah ya kawo su, Ameen, a zuciya tace suzo baza su ganni ba.
Kamar daga sama yaji tace da gaske baka da lafiya, dagowa yayi ya kalle ta kamar ba ita tayi maganar ba, inji wa, a takaice tace inji mami, wacce mami, mami nawa ka sani.
Ajiyar zuciya yayi yace yaushe ta fada miki, dazu naji suna waya da mamma.
Du’a idan ma bani da lafiya mai naki a ciki kin manta kince baki da hadi dani, wai akan wannan matar ce, wace mata, wacce kake so, murmushi yayi bai bata amsa ba, zan fadawa mami, akan mai baki da hadi dani fa. dan haka babu ruwan ki da rayuwa ta.
A tare suka futoh daga dinning area din, daidai lokacin mamma ke fitowa daga daki, suna isa palon ya gaida ta, ta amsa tace babana yaushe kazo, mamma ai nadan jima, shine ba’a kirani ba, du’a tace bacci kike, ai saiki tashe ni ko. Haba mamma taya zan tashe ki kina bacci kawai dan yazo.
Murmushi yayi yace gaskiyya dai kam bai dace ba, amma idan ra'ayinki ne ai kina tashi na ko, toh mamma ai, rufe mini baki. tashi tayi zata tafi daki mamma tace kizo na aikeki gidan adda, da sauri ta dawo dama neman yacce zata fita take.
Mamma yanzu eh, okay bari naje na shirya, daki ta tafi tana ta murna.
Gara zama yayi yace mamma yau su hajja zasu zo ko, eh, kuma du’a zata fita, yanzu zata dawo, okay barina kaita, Allah yasa ta yarda, zata yarda in sha Allah.
Tana fitowa mamma ta bata wasu kaya ta kaiwa aunty zainab, karba tayi tace mamma baba driver ne zai kaini, aa muje na kaiki, kallon shi tayi tace mamma kudin mota, kije daki ki dauka kizo babana ya kaiki, aa mamma saina kaita na dawo da ita, aa ka barshi zan iya zuwa, babana ka kaita kawai sai ta dawo.
Mamma zan iya jiran ta, okay muje tace mamma saina dawo, tam, suka fita, nan ta bashi address din gidan, tunda suka tafi ba wanda yayi magana.
Suna zuwa yace kiyi sauri ki fitoh, saida ta tabbata ta fita daga motar ta rufe sannan ta loko ta window tace ka tafi sai gobe zan dawo idan baffa yazo ka gaida shi, ban gane ba, hausa fana maka I mean yau bazan kwana a gida ba, because ban bukatar wasu baki ka gane.
Amma ai baki fadawa mamma ba, ina ruwan ka tana juyawa tace bye tana daga mishi hannu, shi tsabar mamaki ya kasa kuma cewa komai, harta shiga sannan ya dawo cikin hankalin shi, mamma ya kira ya fada mata yacce sukayi, okay bari na kirata.
Koda ta kira wayar bata daga ba sai ta kira wayar zainab, mamma ina yini, lafiya lau zainab ina du’a, tunda ta shigo ta shiga bayi wai bata jin dadi har yanzu bata fitoh ba, zainab kice ta fitoh, dakin ta nufa ta ganta a zaune bakin gado, harkin fitoh kenan, eh aunty zainab gashi mamma na miki magana.
Dan zaro ido tayi sannan ta amsa, mamma, ki mini shiru yana jiran ki, tam tace ta kashe wayar, nan zainab tace meke faruwa, bata boye mata komai ba ta fada mata, nasiha zainab ta mata sannan tace taje su gaisa da adda ta tafi, ba musu tace tam, koda suka gaisa nan tace ta tafi, aa dama ba yini kika zo mana ba, zan dawo wata rana, tam ki gaida mamma taki, tam adda.
Zainab da munira ne suka raka ta har bakin mota, yarima ya fitoh suka gaisa, suna zuwa du’a tayi gefe ta kira abbah, hello abbah, na’am mom, abbah dama nayiwa mamma laifi na tafi gidan adda, laifin mai, nan duk suka juyo suna kallon ta, abbah dama na sai tayi shiru dan ta tasa karyar da zatayi, okay shikenan ki zauna da daddare zanzo na dauke ki, aa abbah ni kwana zanyi, bari naje gidan zan kiraki, tam ta kashe wayar ta.
Kallon shi tayi tace abbah yace na kwana, a tsawace yace aiko bazaki kwana ba, ok saimu gani ta juya zata tafi, zainab tace du’a mai yasa zakiyi karya, toh aunty dole ne saisun zo mana gida, ai ita mamma tace zata je, du’a that’s not a reason mamma baza taji dadi ba, zan kira ta na bata hakuri.
Yarima kuwa tuni yayi zuciya ya shiga mota ya tafi.
Koda suka koma adda tace yanagan ki, nan zainab tace adda muje daki, nan ta fada mata komai, jeki kira ta, adda ta mata fada sosai da nasiha amma tace ita wallahi yau bazata kwana a gida ba, naji amma dole ki hakura ki karbe su, tam adda amma ba yanzu ba.
Suna zaune bayan la’asar ta kira mamma, bata daga ba, dan tun bayan wayar du’a da abbah ya koma gida.
Yana shiga ta mishi Sannu da zuwa, bayan ya amsa tace mishi ga abinci, yana cikin cin abinci yace fatima niko mai du’a ta miki dan ta kira ni tace ta miki laifi wai a gidan adda zata kwana.
Shi yasa kenan naga har yanzu bata dawo ba, masha Allah zata zo ta same ni, mai tayi nan ta fada mishi komai, tunda bata so ki barta mana.
Kaifa naga kamar baka son na koma gida ko, kamar ya, karfa ka manta sufa iyaye nane kuma ina buka tarsu a halin yanzu, badan komai ba saidan na rabu dasu lafiya, anzo wurin kin fara ai ni bance karki koma ba kije Allah ya kiyaye, kuma zan miki magana ta karshe karki kara mini maganar mutuwa tunda likitocin ba suke bada lafiya ba, kuma kar wanda ya sake takurawa diya ta tunda tace bata buka ta kin gane.
Ai ba yar ka bace kai kadai nima diya tace, damuwar ku nace karku fusata ni amma saida kuka kaini bango, bance ku bata sati daya ba, sai kuje ku saka ta karbe su, kar wanda ya sake yiwa diya ta wannan maganar, yaa fuce.
Mamma tayi kuka sosai koda yarima ya kira ta saida ya gane tana cikin damuwa, mamma wani abuya faru ne, aa babana, kawai bari nace su fasa zuwa sai wani lokacin, aa ka barsu suzo kawai, tam shikenan sai anjima, tam babana sai kunzo, mamma bada ni zasu zo, mai yasa, kawai mamma, kazo kaji, tam.
Haka ta sake kira amma baa amsa, a zuciya tace bata huce ba kenan bari na bari zuwa anjima.
Bayan isha su hajja suka zo da mami sai papa da fatiha, yarima koda suka zo hannu biyu mamma ta karbe su, amma kana ganin alamun ta zaka gane tayi kuka dan kusan wuni mamma tayi tana kuka koda su dee suka dawo tace teema ta shirya su, su zauna suyi kallo karsu takura mata.
Bayan sun gaisa tace su yafe mata, ai mun yafe miki fatima muma ki yafe mana, ba komai papa, wai ina du’a inji mami dan duk abinda ke faruwa yarima bai fada mata ba, aunty safiyya du’a bata nan taje gidan yayar abbah su, kana ganin mamma zaka gane halinda take ciki dan taji zafin maganar abbah kuma tasan kafin ya huce za’a dade.
Okay, fatiha jeki kira su dee, tashi fatiha tayi taje dakin teema da gudu dee ta rungume ta tace aunty fatiha tare kuke da aunty du’a, aa dee ai aunty du’a na gidan adda, yanzu dai kuzo muje mamma na kiran ku, hannun dee ta rike suka fita tare.
Teema na ganin bakin fuska ta canza yanayi, bayan sun gaisa tace zata tafi daki, mamma kallon ta tayi tace teema zo, kusa da mamma taje ta zauna, hannun ta ta rike tace teema kema bazaki kula family naba ko saboda yayar ki ta hana ki, tana magana hawaye na bin fuskar ta, daidai shigo war yaya da sauri yazo gaban ta ya tsugunna yace mamma way are you crying mai aka miki.
Papa ne yace fatima waye wannan, sai lokacin ya kula dasu, ajiyar zuciya yayi sannan ya gaida su dan yasan sune dalilin kukan nata, amsawa sukayi sannan yace mamma dan Allah ki daina kuka kinji, ya fara goge mata hawaye, teema da tuni jikin ta yayi sanyi tace mamma kiyi hakuri wallahi ba haka nake nufi ba, murmushi tayi tace toh kije ku gaisa ga mamana hajja ga papa babana sai kuma mami maman fatiha, ga kuma yayan ku ai kin san shi, daga kai tayi, papa yace zo kusa dani, tashi teema tayi ta koma kusa dashi ta zauna, baffa na gefen yarima , mamma barina shiga ciki.
Aa yaya ka zauna mana, mamma na gaji da yawa yau tun safe na fita, fatiha ce tace yaya ka zauna muyi hira kaji, sai lokacin ya karewa palon kallo yaga babu du’a, kasa yayi da murya yace mamma ina du’a, murmushi takaici tayi tace tana gidan adda.
Mu hadu a kashi na gaba.😊❤️❤️
Domin neman ci gaban wannan litafin zaku iya following Instagram page dina Reeeyarh ko kumin dm ta WhatsApp ***.
Nagode
*~Book by Reeeyarh~*