Chapter 16
by @reeeyarh
Page 16
*~reeeyarh~*
Adda kuma yaushe, zamuyi magana anjima okay, suna zaune du’a ta kuma kiran mamma lokacin har 9:00 tayi, koda mamma taga du’a ke kiran ta sai tasa wayar airplane mood.
Papa ne yace fatima yaushe mai gidan zai dawo ne, murmushi tayi tace papa yau bada wuri zai dawo ba, ai shikenan kuzo mu tafi, hajja ce tace fatima yaushe zaku zo, murmushi tayi bata ce komai ba, yaya yace zuwa wani satin in sha Allah.
Papa yaji dadin ganin yacce yaya yake yiwa mamma kamar ita ta haife shi, dukda baisan waye shi ba.
Tam Allah ya kaimu, da Ameen duk suka amsa, nan suka tashi zasu tafi mamma saida suka raka su har mota sannan suka dawo.
Suna dawowa yaya yace su dee su tafi daki, bayan sun tafi ya zauna kusa da mamma yace mamma maiya faru ina abbah, dan yasan yau abbah da wuri yake dawowa, ba musu ta fada mishi duk abinda ke faruwa, yaji haushi sosai yace zai kira du’a, aa ka barta zata dawo dan kanta rashin kiran saiya fi mata ciwo.
Tun dazu take kira naki dagawa, tam shikenan mamma Allah ya kyauta, Ameen barina shiga daki, nima dai dakin zan tafi, tare suka tashi kowa yayi dakin shi.
Du’a tunda ta kira mamma bata daga ba sai taji ba dadi, amma sai tace gobe zata sake kiran ta.
Su yarima kuwa da suka tafi a hanya papa yake tambayar su waye yaya dan ance mishi du’a ce babbar yar mamma, fatiha tace yayan du’a ne, yayan du’a kuma, mami tace ai dan dayar matar ce data rasu, okay Allah mata rahama, fatiha bata taba tunanin yaya ba dan mamma bane.
Koda suka isa gida saida yarima yakai papa sannan yakai hajja sai mami, shima ya huce part dinsa.
Washe gari around 11:00 du’a ta dauki wayar zainab ta kira mamma, koda ta daga tace mamma ina kwana, lafiya lau yasu adda, lafiya lau mamma, mamma jiya na kira ki baki daga ba, mai zaki ce mini tunda kin zabi kiyi abinda kikaga dama ai shikenan, mamma kiyi hakuri.
Hakuri du’a akan me Zakije kiyi wa abban ku karya eh, mamma dan Allah, ki rufe mini baki dan iskanci basai kice bazaki dawo ba amma sai kika ce kin mini laifi ko kinyi daidai, mamma dan Allah kiyi hakuri, du’a family nane baki so ko ba matsala kiyi rayuwar ki da family abbah ku.
Mamma dan Allah kiyi hakuri, ni bama wannan bane ya bata mini raiba karyar da kika yi, mamma kiyi hakuri bazan sake, kiyi zaman ki anan, saura idan abbah naku na kira kice ni nace karki dawo, kuma karki sake kira na saina neme ki ta kashe wayar ta.
Du’a tunda take bata taba ji mamma tayi mata fada kamar wannan ba a zuciyar ta tace duk su suka ja mini da ina rayuwa ta lafiya amma daga dawowar su har an fara samun sabani a gidan mu, tana wannan tunanin zainab ta shigo daki.
Du’a tunanin mai kike, dagowa tayi ta mata murmushi tace aunty ina kwana, lafiya lau du’a lafiya kika zo daki kika zauna, ba komai munyi waya da mamma ne. Okay tashi muje kiyi breakfast.
Tashi tayi jiki a sanyaye suka fita palo adda na zaune sai munira, mamana kin tashi kenan, eh adda ina kwana, lafiya lau kin tashi lafiya, lafiya lau adda, masha Allah, kuje kuyi breakfast, hucewa sukayi dinning area suka zauna.
Munira ce ta zuba musu abinci, suna ci suna hira, har suka kammala, palo suka dawo suka zauna suna hira.
Mamma kuwa tun jiya da abbah ya fita bata sake ganin shi ba, dan da sassafe ya fita, yaya yau zama yayi a gida dan kar mamma ta zauna cikin damuwa, mamma ki barni nayiwa du’a magana, aa yaya ka barta tunda abbah ku yace kar wanda ya mata magana, ai shikenan.
yarima kuwa sai kusan 1:00 ya fitoh part mami ya nufa koda yaje ba kowa a palon zama yayi yana jiran sakkowar wani, aiko saiga mami, tana zama ya gaida ta, bayan ta amsa tace yau kenan miskilancin ne ya motsa, murmushi kawai yayi, au baza kayi magana ba kenan, aa mami kawai dai sai kuma yayi shiru.
Abinci fa kaci, aa mami ba yanzu ba, sai yaushe, anjima,okay ai shikenan, mami bari naje wurin baffa, tam.
Yana isa fada nan ya gaida mutanan fada, babana sai yanzu, murmushi yayi yace mai martaba banajin dadi ne, Allah ya kara sauki duk mutanan fada suka amsa da ameen, kaje ka huta, tam mai martaba, tashi yayi ya koma part din mami, fatiha ta fitoh lokacin.
Zama yayi yace mami kunyi waya da mamma, aa, ya akai, ba komai kawai dai naga jiya kamar bata jin dadi, aa bamu yi magana ba koda wani abune, mami jiya da rana naje gidan nan ya bata labarin duk abinda ya faru, tab Allah yasa dai fatima basu samu matsala da mijin ta ba.
mami wallahi saura kadan naci uban ta ita bata da hankali ne, aa karka sake dan wallahi ka taba musu diya ba ruwana kuma abun sabo zai dawo.
Amma mami wannan ai shashanci ne dan nasan yanzu haka wani abun abbah yayi wa mamma dan dana kirata da yamma naji kamar kuka take, kaidai kubi abin a hankali, nan suka dauko wata maganar.
Bayan baffa ya gama zaman fada yarima ya koma, murmushi yayi yace aa babana ya jikin kaida nace kaje ka huta, baffa ai na huta, zama yayi suka gaisa sannan suka fara hira, anan yace ya kira mishi du’a dan jiya hajja tace da suka je bata nan, kiranta yayi badan ya san zata daga ba, yana kira na biyu, aiko sai gashi ta amsa.
Lokacin daya kira suna zaune a palo ita dasu zainab, zainab ce tasa ta daga dan dole, tace taje daki ta daga.
Hello, ina yini, lafiya lau, mai kuma yanzu, bayan kun hana mamma kulani toh mai zan muku, ni shiyasa nace banson family mamma sai tasa kuka taci gabada cewa tunda nake mamma bata taba cewa karna kara kiran taba kuma karna koma gida, ni ban taba ganin iyaye na sunyi fada ba amma daga zuwan su shine zasu ce mamma ta daina kulani.
Tsawa yayi mata yace rufe min baki, ganain tsawar da yayi mata yasa baffa cewa babana mai yasa zaka mata tsawa bani wayar malama zakuyi magana da baffa saura naji wani shirman mika wa baffa wayar yayi yana magana kasa kasa.
Da sauri ta goge hawayen ta kamar tana ganan shi, yana daga wa tace baffa ina yini, lafiya lau du’a, kin koma gida ne, aa mamma sai tayi shiru, aa ba yanzu ba, okay du’a, na’am baffa, inaso muyi magana, tam baffa ina jinka, du’a ki zamtoh mai hakuri da yafiya kamar maman ki, tam baffa, ba tam kawai zaki ce ba inaso na ganki a gidan nan, baffa bazan iya zuwa ba yanzu, okay sai yaushe, ranar da Allah yayi,Allah ya nuna mana ranar, ameen baffa, yanzu dai naga kin batawa yayan ki rai ki nemi yafiya, in sha Allah baffa, yawwa sai anjima.
Amsar wayar yayi ya kashe, nan suka ci gabada hirar su da baffa, babana mai yasa zaka mata fada, baffa yarinyar nan shegen taurin kaine da ita, baffa sai kace ita aka taba yiwa laifi dan taga kuna barin tane shi yasa amma yanzu ai zata shiga haiyacin ta tunda mamma tace karta sake kiran ta, fatima ce tace mata haka, eh baffa dan Allah karku mata magana saboda indai ba haka aka mata ba baza ta taba canza wa bah, ai shikenan Allah ya kyauta,ameen saida sukayi har sallar isha sannan ya tafi, part din mami yaje ya mata saida safe ya huce nashi.
Du’a tunda suka gama waya ta koma palo, suna zaune bayan isha sadiq yazo, palon babansu aka kaishi, bayan sun gaisa saiga du’a ta kawo musu drinks yauma tare da faruq suke, gaida su tayi zata tafi sadiq yace du’a ki zauna mana.
Aa bacci nake ji, haba du’a bacci yanzu just sit for 30 minutes zainab ta kalla ta daga mata kai, zama tayi faruq yake cewa du’a ina yayan ki, murmushi tayi tace yana gida, shi kuma fa dayan yayan naki daya takura mini fah, dagowa tayi tace wa, junaid mana, zaro ido tayi tace yaya kuma mai ya hada su, murmushi yayi yace ya huce, suna hira sadiq na tsokanar du’a tana dariya, nan faruq yayi mata hotoh yayi posting a story sa yasa mar’atul Salina.
Uncle bari na tafi bacci nake ji, tam shikenan saida safe, faruq ta kalla tace mishi saida safe, Allah ya kaimu, Ameen tace ta huce.
Tana isa daki kiran yarima ta fara cin karo dashi, har kusan 4misscall kafin ta karsa dubawa saiga wani kiran ya shigo, kamar bazata daga ba sai kuma tace kar naje wani abune, tana daga taji yace, ke baki da hankali ko abinda bakiyi a gidan ku shine dan baki gida kike yi ko, kanta ya kulle dan bata san mai tayi ba, ba magana nake miki ba, me nayi, ban sani bah, ki hau online yanzu.
Online ta hau taga ya turo mata hotoh, tana shiga ta ganta, abin ya daure mata kai dan ita ta manta ko mayafi bata saka ba gashi rigar tadan kama ta, kayan munira tasa tadan fi munira ciki shi yasa kayan suka kama ta, tana wannan tunanin kiran shi ya shigo, daga tayi tace wallahi bansan anyi ba, dan Allah kodan ina zaki sani kinje gurin gardawa duk kaya sun matse ki ko mayafi ko.
Allah na manta munira ce tace dan Allah na kai musu drinks ita tayi shirin bacci , shine fa dana je uncle sadiq yace na zauna muyi hira, kuma ai ban dade ba, ai shi sadiq din kanin abbah ne ko, shiru tayi yace wallahi du’a ki guji haduwar mu dan naga abin naki gaba yake karawa, ni zaki yiwa rashin kunya dazu ko, bata ce komai ba dan yanzu shakkar shi take sosai, ba magana nake miki ba, Allah nabar wurin su fa, aa ki tashi ki koma kinji, su muharaman kine dazaki zauna kina washe musu baki har wani yana daukar ki yana mar’atul saliha ko, da kyau, kuka ta fara tace waini ya kuke so nayi yaya yaki daga waya ta mamma haka kai kuma sai fada kake mini, tsaki yayi yace damuwar ki ya kashe wayar shi.
Kukan ta taci gaba dayi har zainab ta dawo, tana shigowa taga tana kuka dan a dakin ta take kwana, du’a lafiya mai ya faru, fada mata tayi abinda yarima ya mata, dariya tayi tace shine kike kuka, aunty idan banyi kuka ba mai zanyi sai kace ubana yayi ta mini fada, du’a ai ke kika ja tunda ance ki karbi family mamma kinki.
Aunty bafa akan wannan yake mini fada ba, wannan fadan nashi na kishi ne karki damu amma du’a ina baki shawara ki karbi family mamma kinji, in sha Allah aunty amma saina koma gida, yawwa sister Allah ya barku da yarima, baki ta turo tace tab wallahi bazan iya zama dashi ba, du’a Allah guy din nan na sonki da yawa, haba aunty Allah ba sona yake ba, tam na yarda idan lokaci yayi ma gani, tashi ki canza kaya ki kwanta, tam.
Yau kwanan du’a biyar a gidan adda yarima bai sake kiran ta ba mamma ma, ko ta kira mamma bata dagawa, yaya ma haka, abbah kadai take waya dashi dan fatiha ma yarima ya hanata waya da du’a,
tana zaune bayan isha ta turawa fatiha messages.
Fatiha ki turomin number baffa, lokacin yarima bai dade da dawowa daga gidan mamma ba dan bata jin dadi, nuna mishi tayi yace karki kulata, amma yaya, kindai ji abinda nace ko, tam ta ajiye wayar, du’a taga ba amsa ta kira bata daga ba, abin ya fara damun ta dan haka ta yanke shawarar ta kira yarima dan tasan duk shi yake hada wannan abun. Kiran shi tayi sai’a kira na biyu ya daga,
Hello yaya ina yini, ya akai, yaya dama gida nake so na koma, ina ruwa na, kuka ta sa mishi mai sosa rai tace yaya dan Allah kayiwa mamma magana idan na fadawa abbah fada zasu kara yi, dama shima yayi missing dinta dan kullun da ita yake kwana da ita yake tashi, ba ruwana, ya tashi yabar palon part dinshi ya huce, yaya dan Allah.
Kije umar ya shawo miki kanta mana, yaya ba maganar sa bace maganar family mu ce, mai kika ce, sabon kuka ta saka, you mean idan ba maganar family bace zaki saka shi, yaya nifa bani da hadi dashi Allah, okay mubar wannan maganar yanzu kin yarda zaki zo gurin su hajja kenan, eh yaya, du’a bazaki maidani yaro ba, idan na yiwa mamma magana ki canza Allah da gaske na yafe musu.
Toh kukan me kike, yaya taya zanyi rayuwa ba mamma, yaya, fatiha duk basu kulani. da gaske, eh, ni kenan zaki iya rayuwa bani, shiru tayi, magana nake dake, aa yaya tam shikenan yanzu ki daina kuka kinji, tam zaka yiwa mamma magana, eh gobe zanzo Mu tafi, tam Allah ya kaimu.
Mamma tunda abunan ya faru bata jin dadi ciwon zuciyar ta ya tashi, shi yasa ma bata daga wayar du’a dan karta gane, su dee kuwa idan suka tafi school sai yamma suke dawo teema ke kula dasu dan taga kamar mamma bata jin dadi, abbah iya kacin su gaisuwa.
Yau bayan yarima ya tafi su dee sunje gidan fatima sister abbah, abbah ya shiga dakin ta, ganin ta yayi a kwance tana numfashi da kar, da sauri ya karasa wurin, fatima kina lafiya, murmushi tayi mishi tace lafiya ta kalau, kinsan me kike cewa kuwa, fatima meke damun ki, abbah ko yanzua na mutu na godewa Allah amma takaici na daya shine halinku kaida du’a.
Ban gane ba kinga ba abinda zai same ki tashi tashi muje asibiti, aa ka barni kawai ba fushi kake dani ba, haba fatima kinsan bazan taba fushi dake ba, dan Allah ki tashi muje asibiti, hijabi ya dauko mata tasa ya kama ta suka tafi asibiti, koda suka tafi a hanya sai cewa take ya kula mata da yaran ta, abbah ya gama gigicewa sai cewa yake fatima bazaki tafi ba kiyi hakuri zamu canza in sha Allah.
A haka suka isa asibiti, suna zuwa likitoci suka karbe ta, duba ta sukayi sannan suka mata alular bacci, nan suka ja abbah suka tafi masallaci sukayi sallar isha.
Bayan sun dawo likitan yace anan zasu kwana, ammu ya kira yace su teema su kwana anan ya fada mata mamma batada lafiya amma karta fada musu, toh yaya dawa zata kwana, dani karki damu karki fadawa kowa kinga dare ne, tam shikenan, yana kashewa ya kira yaya yace karyaje dakko su teema acan zasu kwana, kuma kazo asibiti ini jiran ka, asibiti kuma abbah, eh nan ya fada mishi number daki.
Koda yazo baiji dadin ganin halin da mamma ke ciki ba, har kuka yayi, toh yanzu kukan ne zai sa ta samu lafiya ko ya, aa abbah kayi hakuri, okay kaje gidan hajiya ka kwana amma karka fada mata abinda ke faruwa, amma abbah kai kadai zaka kwana, eh ka bari sai 10:00 saika tafi lokacin hajiya tayi bacci, tam, zama sukayi suna jinyar ta sai around 9:40 yaya ya tafi.
Mamma sai kusan 11:00 ta farka, koda ta farka abbah na zaune akan kujerar gaban gado, ya kifa kansa akan gadon, hannun tasa tana shafa kansa a hankali ya dago yace fatima kin tashi, ya jikin naki, murmushi tayi tace da sauki, Allah ya kara sauki, abincin da yaya ya dauko musu a gida ya zuba mata, cewa tayi ta koshi, da kar abbah ya bata abinci a baki har saida taci da dan yawa sannan ya bata magani tasha.
Nan ya zauna suna ta hira har kusan 1:00 abbah bazaka kwanta ba, aa fatima banjin bacci a yanzu lafiyar ki tafi komai, murmushi tayi tace amma ba anan zaka kwana ba ko, a ina zan kwana, kaje gida da safe saika dawo, fatima kinsan karfe nawa yanzu kuwa 1:00 fa tayi, ai shikenan nidai barina kwanta saida safe, shidai bai tashi ba yana zaune ya rike hannun ta, har tayi bacci, bawai bata jin jiki bane kawai dai daure wa take, shima koma wa yayi kan kujera ya kwanta.
Washe gari tun 7:00 yaya yazo lokacin ta farka amma jikin nata yayi tsanani, zama yayi bakin gadon yana mata kuka kamar karamin yaro, dukda haka mamma murmushi take musu, abbah shima daure wa yake dan dada dama kukan zaiyi, da kar likitoci suka mata alurar bacci, sukace abbah yaje gida ya dawo, yace ba inda zaije, sai kusan 10:00 yaya yace bari yaje gida ya dawo, wayar shi ce tayi kara.
Hello ammu ina kwana, lafiya yaya ya jikin mamma, da sauki, kuna asibiti ne, eh, okay bari yanzu zanzo, tam ammu ni yanzu zanje gida na dawo, okay hajiya ta sani, aa babu wanda ya sani, ya kamata a fada mata, ammu ki barta karta tashi hankalin ta, tam Allah ya kara sauki Ameen. Lokacin teema ta shigo dakin,ammu dan Allah na tambaye ki wani abu, ina jinki teema, ammu mamma ce bata da lafiya ko.
Inji wa, nasan itace kawai dai bakuso mu sani ne ammu bazan fadawa kowa ba, eh teema itace amma karki damu ance yau za’a sallame su karki fadawa kowa kinji, tam ammu, kuma karki saka kanki a damuwa har yan uwan ki su gane, in sha Allah.
Du’a koda ta tashi saida ta kira abbah amma baiyi picking, ta cewa adda idan anjima yarima zaizo ya dauke ta, ako suna zaune kusan 10:00 ya kirata yace tazo su tafi, nan tayiwa su adda sallama zainab da munira suka raka ta, bayan sun gaisa dashi suka koma gida, bazaki shiga bane, shiga tayi suka tafi.
A hanya yayi mata nasiha sosai, kuma ta amsa, suna isa gidan yaya yana fitoh wa zai koma asibiti, du’a kallo daya ta mishi tasan yayi kuka, yarima ta kalla tace yaya kukan me yayi, sai lokacin ya tsaya ya kalle shi sosai, saboda yaya koda yazo gida kuka yayi sosai dan har zuciyar shi yake jin jinyar mamma.
Da sauri ta fita daga motar, yana kokarin shiga, tace yaya, juyowa yayi ya kalle ta sai zuciyar shi takara karaya, ta karasa zuwa gaban shi tace yaya mai aka maka kake kuka, lokaci guda yaji wani sabon kukan, rungume ta yayi dan karta ga zubar hawayen shi yace I miss you my sister, yarima ta bayan ta yaje yake mishi alama da hannun maiya faru.
Murmushi yayi kawai, du’a tace yaya kukan me kake, muje gidan waya taba ka mamma ko abbah, dagota yayi yace ba kowa a gidan ai, ji tayi gaban ta ya fadi, kamar ya inasu mamma, su dee suna gidan ammu, mamma kuma taje ta dawo yanzu ma wurin ta zanje.
Yarima ne yace du’a shiga mota ki jira mu sai muje tare, matar shi ta koma, nan yace wa yaya meke faruwa, yaya bai boye mishi komai ba, okay yanzu ka maida motar sai muje a tawa, aa muje kawai saiku biyo baya na, kana wannan halin taya zakayi tuki, karka damu zan iya.
Mota ya shiga yaya yayi gaba suka bi bayan shi, a hanya take tambayar shi ina zasu je, idan munje zaki gani.
Suna isa gate din asibiti ta juyo ta kalle shi, waye baida lafiya, ki mini shiru, mamma ce bata da lafiya, du’a kiyi shiru nace, ai tuni ta fara rera kuka, wuri ya samu yayi packing sannan ya juyo ya kalle ta, banson kuka kiyi shiru, bata saurare shiba ta ci gaba da kukan ta.
Hannun ta ya ruko yace du’a please kiyi shiru mana, saboda nine ko, akayi mai, mamma batada lafiya, kinji nace miki batada lafiya, aa toh fitoh muje, a tare suka fita, tare da yaya suka je har dakin, suna shiga lokacin mamma bata dade da tashi ba, ammu da abbah ne kawai a dakin, ta gudu du’a ta shiga daki tana kuka, sosai ta rungume mamma tana kukan itama mamma nayi.
Abbah ne ya kalli yaya yace mai yasa yazo da ita, fada mishi abinda ya faru yayi, da kar abbah ya raba su yace su daina kuka, zaunar da ita yayi a kusa dashi, nan suka gaisa da abbah da ammu, wayar galadima ce tayi ringing, yana dubawa yaga mami, dagawa yayi.
Kana inane mami ina asibiti, da sauri abbah ya mishi alamar karya fada, asibiti kuma, abbah ai gara su sani, mami naji yace abbah jikin ta ya bata mamma ce bata da lafiya, mamma ce tace ya bata wayar muka mata yayi, hello aunty safiyya ina kwana, lafiya lau fatima ya jikin, da sauki, Allah ya kara sauki, Ameen.
Aunty safiyya dan Allah Kuzo, tam shikenan yanzu zanzo harsu hajja da yaya, tam an gama, karba wayar yarima yayi ya fita, mami ki barta karku zo, aa gara muzo ya jikin nata yake, sosai batada lafiya, kaga tunda tace muzo kara muzo, tam saikun zo.
Koda ya koma ciki mamma tace badai hanasu zuwa kayi ba ko, aa mamma yanzu zasu zo, suna zaune mai makon jikin yayi sauki amma karuwa yake, yarima da yaya suka koma palo, mamma tace abbah a kawo mata su dee, du’a ta gama rikice wa, saban kuka ta fara, mamma dan Allah ki daina wannan maganar bazaki tafi ki barmu ba idan kika tafi muma zamu biyo ki, murmushi dole kawai take.
Du’a zo, tashi tayi taje zama tayi a kan gadon, hannun ta mamma ta rike tace du’a ki kula da kanki da abban ki da yan uwan ki, du’a idan na mutu ku kadai yan uwana zasu kalla su tunani, kai kawai du’a ke girgiza mata, juyawa tayi ta kalli abbah tace abbah kace mata baza ta mutu ba.
Tashi yayi yaje inda suke yace fatima ki daina wannan maganar, fati zoki tafi da du’a waje, aa ka barta magana zamuyi ka kawo mini su dee inaso na gansu.
Ammu zuwa tayi taja hannun du’a suka fita da kar, suna fitoh wa tana kuka, yaya da yarima suka taso da sauri, ammu itama kuka take.
Ammu meke faruwa, kai ta girgiza mishi zai shiga tace karka shiga suna magana da abbah ne, du’a ce tace yaya ka fada mata bazata mutu ba.
Yarima ne yazo ya ja hannun ta suka bar wajen.
Mami na kashe wayar ta kira hajja tace ta shirya gatanan zuwa zasu je wani wuri, ta tura meeno gurin baffa tace tana son magana dashi yanzu yanzu, papa kuma fatiha ta aika tace suje ita da baba driver su dauko shi.
Meeno na zuwa aka mata iso, nana tace baffa mami ce ta aikoni, duk futa mutanan sukayi, sannan tace wai tana son ganin ka yanzu, mai yake faruwa, baffa bata fada mini ba amma kamar mamma ce batada lafiya suna asibiti,
wacce mamma, maman du’a, mai taya, ina zuwa yanzu nan, tashi tayi ta tafi.
Fatiha kida sukaje dauko papa, suna zaune shida abbu da yaya mujid da ya umar sai ya aliyu, tana zuwa suka gaisa, tace papa ga mota inji mami wai zaku fita, fita kuma fatiha, eh haka tace mini, ina zamu je, papa kamar mamma ce batada lafiya, ba shiri ya tashi, muje fatiha, abbu ne yace shima zaije, papa bai musa mishi ba, muta suka hau su yaya umar sukace zasuje, fatiha da papa suka shiga mota sukayi part din, mami.
Baffa ma sanar wa yayi yau an gama zaman fada yasa sarkin mota ya dauko mishi mota, suka huce part din mami, sun riga su papa karasowa, nan mami ta jadda da mishi fatima nason ganin su, yanzu kuje nida hajja zamu taho, aa kizo muje kawai saimu dakko ta suna fitowa matar su papa ta karaso, basu sakko ba suka huce, part din hajja wani driver yaje ya dakko ta, mota biyar sukayi suka tafi.
Yarima tunda yaja hannun du’a mota ya nufa da ita, bayan motar ya bude ta shiga sannan ya shiga.
Bata daina kuka ba saida yace du’a sannan ta dago ta kalle shi, duk fustar ta tayi ja.
Hannun yasa ya fara goge mata hawayen yace ya isa haka kukan yayi yawa, yaya mamma fa tace mutuwa zatayi, ta kara fashewa da kuka, shi kanshi baisan ya rungume ta ba, a hankali yace baza ta mutu ba ki daina kuka.
A hankali yake shafa bayan ta yana lallashin ta, saida ta tsayar da kukan sannan ya rabata da jikin shi, yace kina so mamma karta tafi, kai ta daga mishi, yace saikin daina kuka kuma kice mata duk abinda ta saki zakiyi.
Yaya na fada mata fa, still hawaye na zubowa daga idon ta, ai baki daina kukan ba, wayar shice tayi kara, da yaga adam ne saiya daga, hello adam ya kake, lafiya lau Junaid ya gida, Alhamdulillah, wai ina ka shiga kwana biyu ne, kaidai bari wallahi matsaloli ne suka mini yawa, wai du’a ta koma gida
Aa wallahi kagan mu a asibiti mamma ba lafiya, meke damun ta, wallahi ban sani ba, ina du’a, gata nan sai kuka takewa mutane, ta barmu muji da rashi lafiyar mana, bata wayar, mika mata yayi.
Hello yaya adam ina yini, lafiya du’a yamai jiki, Alhamdulillah, nan ya mata nasiha sosai sannan ya musu sallama yace zasuyi waya anjima.
Kukan ya ragu, dan haka ya ce ta zauna a mota tadan huta, jin gina tayi da kujera, hannun shi yasa ya daura kanta a kafadar shi, ya rike mata hannu.
Yaya kuwa zama sukayi shida ammu, ammu tace ya kamata mu sanar wa hajiya, eh ammu tun jiya nace zan fada mata amma abbah ya hanani.
Wayar ta tasa ta kira ta, bayan sun gaisa tace mata mamma ce batada lafiya jiya a asibiti ta kwana, au shine baku fada mini ba sai yanzu, hajiya abun ne ba dadi, okay ganinan zuwa, tam hajiya saikin zo.
Su mami yarima suka kira ya tura musu address din wurin, koda suka zo mutane sunga ikon Allah wanda bai taba ganin mai martaba ba yau ya ganshi.
Tare suka fitoh daga motar ya rike hannun ta, suka nufi inda su mami suke, kana ganin ta zaka gane tasha kuka.
Gaida su tayi suka amsa, mami ce tace tazo, kusa da mami ta je, kawai sai ta sake fashe wada kuka tace su papa su yafe mata, dan Allah kuce mamma karta tafi ta barmu, rungume ta mami tayi tana lallashin ta, muje ciki inji yarima , hannun ta ya ruko yace mu tafi, har daki suka je.
Har lokacin abbah na dakin, suna zuwa papa ya shiga, mai zai gani abbah ne zaune akan kujera kanshi a kan gado ya rike hannun mamma duk suna kuka.
Sosai jikin papa yayi sanyi ganin yace abbah da girman shi yana kuka, gaskiyya ba karamin so abbah kewa mamma ba, kanshi ta shafa tace abbah ga papa yazo dan baiji shigor su ba, tashi yayi lokacin baffa da hajja da abbu sun shigo, har kasa ya gaida papa da hajja , amsawa sukayi sannan ya gaisa dasu baffa , hanyar fita yayi sai yaji muryar ta tace ina zaka je, juyowa yayi ya mata murmushi yace yanzu zan dawo, papa ne yace aa ka dawo ka zauna.
Yarima yaki sakin du’a saida mami tace tazo, nan su fatiha suke mata ya mai jiki, da sauki, Allah ya kara sauki, a daidai lokacin hajiya tazo, ganin da mutane yasa ta kira ammu a waya tace suna ina, tashi ammu tayi taje ta shigo da ita, nan duk suka gaida ta. bayan ta amsa tace ina fatima, tana daki, daki ta shiga, ganin halin da mamma take ya hargitsa ta,
haba Ahmad ya zaka mini haka, yanzu daka hana a fada mini lafiya ka bata, ita bata san dasu hajja a dakin ba. A hankali abbah yace hajiya gasu hajja ku gaisa, sai lokacin taga mutane, itama kanta taji wani iri, gaisawa sukayi sannan tayiwa mamma ya jiki, da sauki hajiya, Allah ya kara sauki, bari na tafi, Allah ya baki lafiya fatima.
Mamma da zaulaya tace haba hajiya bakiji kunya taba saita iyaye na ki zauna mana ko kun saba dasu, duk yan dakin saida suka murmusa, aa fatima ku zauna abun ku gara naje gida na huta, kinga sunan zasu kula dake, aa hajiya ki zauna komai ya faru a gaban ki, yawwa hajiya kice yasa a kawo sauran yarannan, fatima mai zasuyi a asibiti kema yau zaki koma in sha Allah, murmushi tayi tace Allah yasa, duk da Ameen suka amsa.
Papa ina aunty safiyya, tana waje, baffa ta kalla sai kuma ta kalli abbu tace baza ku mini magana ba, murmushi suka mata abbu yace aa autar papa, ya jikin, da sauki yaya, baffa kusa da ita yaje ya ce fatima ki yafe mini, haba yaya mai ka mini, kanta ya shafa yace har yanzu baki canza ba ko, yanzu fada mini meke damun ki.
Murmushi tayi tace yaya mutuwa zanyi, kamar daga sama taji muryar abbah yace fatima kin mini alkawari bazaki sake cewa zaki mutu ba, murmushi ta sake yi tace hakane, yaya bani da lafiya, menene yake damun ki, ciwon zuciya, duka yan dakin ido suka zuba mata har hajiya dan bata taba sani ba, tun yaushe, tunda nabar gida, yaya inason abbah bazan iya rabuwa dashi ba, amma kunka sa ganewa.
Amma karku damu bashine silar cuta ta ba, shima ba yacce ya iya dan saida yace nazo ku yafe mini amma naki zuwa, kuma duk da haka bai taba cutar dani ba, ya kula dani kamar shine ya haife ni, yaya karku masa mumunar fasara mutumin kirki ne, koyau na mutu komai nawa ya cika, tunda baza ku zarge shiba.
Hannun baffa yasa yana goge mata hawaye yace, auta ku yafe mana, abbah tashi yayi ya fita daga dakin dan bazai iya jurewa ba, ba komai yaya mun yafe muku kaji, yanzu dai ku kula mini da yara na, ai ba inda zaki muna tare in sha Allah.
Abbah koda ya fita yaya yace yaje ya dakko su dee, nan suka gaisa da mami su fatiha suka gaida shi.
Du’a kawai tsintar kanta tayi a cikin daki dan tunda taga abbah ya fitoh a haka tasan ba lafiya, shigar ta daidai lokacin da mamma tace wa baffa su kula mata da yaran ta, du’a tsugunna wa tayi a bakin gadon tace mamma dan Allah kiyi hakuri karki tafi ki barmu.
Baffa ne yazo ya daga ta yace du’a daina kuka ba inda zata kinji, mamma kawai kalan su take ita kadai tasan zafi da take ji.
Yaya karku damu kuje gida, aa auta, toh ina aunty safiyya, du’a da baffa suka fita yace karsu sake barin ta ta shiga dakin sannan yace mami tazo.
Yarima yace wa yaya karya dauko su dee, sannan yace su fatiha suzo su tafi gida, yaya bamu duba ta ba, okay ina zuwa, shiga yayi yace bari suzo su duba ta su tafi, su yaya umar ne suka fara shiga, sunga ikon Allah, sosai mamma ke kamada baffa, suka duba ta, sannan su fatiha suka duba ta.
Tare da fatiha da su ya umar suka tafi, sai yaya yace wa ammu koya kaita gida, gida ya kaisu ita da hajiya, sannan ya dawo.
Tunda suka tafi yarima suna zaune shida du’a, du’a muje kici abinci kinji, aa tare da mamma zamuci, okay muje kiyi sallah, a ina, gidan sister baffa ba nisa. tam nan suka tafi gidan aunty sa,ada suna isa, suka huce palo, bayan sun gaisa tace babana ina ka samu wannan yarinyar mai kamada fatima, murmushi yayi yace yarta ce, da gaske kake ko wasa dan ita duk abinda ke faruwa bata sani ba, Allah aunty ba wasa nake ba.
Kenan fatima ta dawo gida, yanzu dai aunty ina noor tazo ta raka ta tayi sallah, noor ta kira tasa takai du’a daki tayi sallah, nan yarima ya bata labarin komai dan matar nada a kirki,amma ni a wanda ya fada mini, ai aunty ba kowa bane ya sani. shima sallar yaje yayi, koda ya dawo du’a tadan saki jiki da noor dake kusan sa’ani ne.
Mu tafi ko, aa ku zauna kuci abinci tukun saiku tafi, du’a tace ta koshi shi kuma dan ita yace zaici tazo suci ko kadan ne, bata wani ci sosai ba tace ta koshi.
Bayan sun gama suka koma asibitin suna isa suka ga an ruko abbah yana fuzge wa, ashe tunda suka tafi jikin ya kara rikice wa, suna kara sawa taji abbah na cewa karya ne wallahi fatima bata mutu ba, ai a guje ta shige dakin ganin mamma an rufe mata fuska yasa ta karasa da gudu ta janye bedsheet din.
A hankali ta furta mamma mamma ki tashi, dan Allah mamma, mami ce ta rike ta amma ta fuzge ta fara jijiga ta, tana wallahi saikin tashi, mamma ki tashi, daidai lokacin yaya ya shigo, da sauri du’a taje inda yake ta ruko hannun sa tace yaya kace ta tashi, shima kawai hawaye yake, tsugunna wa yayi a gaban gadon.
Mamma ba haka mukayi da keba mamma kince zaki kula dani har karshe rayuwa ta baza ki taba barina nayi mairai ciba, mamma dan Allah ki tashi, daga kai yayi ya kalli abbah da ya dawo yace abbah kace mata ba’a wasa da mutuwa ta tashi, du’a tace abbah mamma bata magana, abbah kace muma su mana allura mu tafi tare.
Shima tsugunna wa yayi ya rungume su, ku daina kuka bacci take kunji ku tashi muje mu hada mata abinda zata ci idan ta tashi.
Su baffa kawai kallon ikon Allah suke, dan basu taba tunanin haka abbah yake sonta ba dan da alama abbah mutuwar ta zarar dashi.
Papa ne yaje inda suke ya ruko hannun abbah yace haba Ahmad yanzu kaida zaka lallashe su amma har kai aka kukan,kuyi hakuri mana kullu nafsin za’ikatul maut, Ahmad ku tashi ba kuka take bukata ba, dagowa abbah yayi da jajayen idanun shi yace, bafa mutuwa tayi ba bacci take ku tashi kunji banson kukan ku.
Mu hadu a kashi na gaba.😊❤️❤️
Domin neman ci gaban wannan litafin zaku iya following Instagram page dina Reeeyarh ko kumin dm ta WhatsApp ***.
Nagode
*~Book by Reeeyarh~*