RAYUWAR DU’A

Chapter 17

by @reeeyarh

Page 17

*~reeeyarh~*

   Masarauta kuwa tunda su baffa suka fita kowa kai sonji make faruwa amma ba dama.

      Lokacin dasu fatiha suka koma duk dakin ummah suka huce, ummah na palo ita da samha.

    Suna shigo wa umma tace daga ina, yaya umar ne yace daga asibiti muke, asibiti kuma waye ba lafiya tare da su papa kuka fita, eh ummah inji meeno.

   Nan suka ce mata mamma ce batada lafiya, tayi mamaki meke damun ta, muma bamu sani ba amma sosai batada lafiya. 

     Allah ya bata lafiya duk da Ameen suka amsa, zezee da taji duk abinda ya faru taje ta sanar wa uwar ta.

   Nan ummah tasa aka hada musu abinci mai rai da lafiya, bayan la’asar tace umar yaje ya kai musu fatiha tace zata amma ya hana ta yace kinsan halin junaid tunda yace ku dawo gara karki koma.

  Yaya kuwa suna tafiya a hanya hajiya take cewa wai tun yaushe fatima ta fara rashin lafiya, hajiya kusa kwanan ta uku bata da lafiya kuma du’a bata gida abbah ma baya zama a gida sai dare sosai yake dawowa, mai yasa nan ya fada mata duk abinda ke faruwa, tayi fada sosai tace zaizo ya same ta.

     Saida ya kaita sannan yakai ammu tayi tayi ya zauna yaci abinci amma yace shi ya koshi, okay anjima su mufida zasu kawo musu abinci. Yana shigowa yaga du’a na jijiga mamma kasa motsi yayi saida ta janyo shi…
  

    Tashi sukayi daidai shigowar doctor yace su fita za’a shirya ta, nan du’a tace ba inda zata ta rike hannun mamma, yarima ne yazo zai janye ta amma abin mamaki sai yaga mamma ta rike hannun ta, kallan shi tayi tace yaya na fada maka mamma bazata tafi ta barni ba ka gani ta rike ni, duk juyowa sukayi suna kallon ta, rungume ta yarima yayi yace, mamma bata mutu ba.

   Doctor ne yace su basu guri zasu duba ta, da kar aka cire hannun du’a daga na mamma, yarima ya jata suka fita, baffa yaja yaya, papa kuma shi da abbu da abbah, sai mami da hajja.

    Bayan kusan 20 minutes doctor ya fitoh, Alhamdulillah ta farfado amma ba wanda zai shiga, sai nan da 1 hour. 

   Okay shikenan zamu jira ta, wani dakin aka basu suka zauna, abbah mota ya huce ya zauna, du’a koda ta lura babu abbah sai tace ita wurin shi zata tafi, yaya yace bari su tafi tare, yarima ne ya taya su neman shi, suka shiga mota shi kuma ya koma wurin su baffa. 

  Wai dama haka suke inji papa duk juyowa sukayi suka kalle shi, yau da fatima ta rasu ai shi uban nasu sai asibitin mahaukata, duk dariya suka saki, hajja tace gaskiyya mun shiga hakin yaran nan, sosai hajja inji baffa, kiji wai suzo suje su dafa mata abinci kafin ta tashi, galadima ne yace ai baku ga sauran bane da yau kunga ikon Allah. Ni wani abun nasu har mamaki yake bani

    Ranar da mukaje gidan ya mata fada tana fara kuka saiya fara bata hakuri, Allah ya kyauta, ameen, amma wannan rayuwa tasu akoi kallo..

  Abbah mamma bazata tafi ta barmu ba ko, in sha Allah mamana, zata tashi tayi mana alkawari, duk murmushi sukayi abbah yace muje mu hada mata abinci ko, eh gida suka tafi yaya yayi drive du’a na baya.

    Koda suka je abinci suka daura, favorite food din mamma suka dafa, bayan sun gama sukayi wanka kowa ya shirya kusan tare suka fitoh palon, abincin suka dauka suka nufi asibiti.

   Tun dazu yarima yake neman su amma bai gansu ba gashi wayar du’a na hannun sa abbah kuma bai daga ba. 

   Sunci kusan 2 hours dan har mamma ta farfado sosai taji dadin jikin ta dan har zama yanzu take, tana zaune suna hira da papa yana bata labarin abinda ya faru, sai dariya take.

     Shigowa sukayi da kayan abinci, yan dakin duk kallon su suke, du’a da sauri taje ta ajiye kayan tazo ta rungume ta, mamma kin tashi, eh my daughter tana dago ta tace amma kinsan banda lafiya kike kokarin danne ni, sorry sweet mom, ga abinci mun miki.

   Yaya ya fara zuba mata abincin, sannan yace a baki zai bata, abbah kuwa tunda ya mata Sannu yaje ya samu wurin ya zauna. yaya saida yaga ta cinye abincin daya zuba mata sannan hakalin shi ya konta. 

   Papa ne yace su tashi suje suyi sallar la’asar, suma su hajja duk sukayi tasu, bayan sun dawo basu dade da zama ba saiga teema da mufida, bayan sun gaisa suka je sukawa mamma ya jiki, amsawa tayi.

    Teema kusa da mamma taje ta tsaya wai ita sai wani a cikin yaya da du’a ya tashi ta zauna, duk suka ce bazasu tashi ba, ba wanda ya iya musu magana, abbah ne yace mom zoki zauna kusa dani. 

    Tashi du’a tayi ta koma inda yake, mufida mana kusa dashi, a hankali suke hira su uku.

        Mamma ce ta kalle su tace du’a kuzo ku tafi gida, da sauri du’a ta daga kanta tace aa mamma ai anan zamu kwana ko abbah, yaya yace ku zaku tafi mu kuma mu kwana ko abbah, murmushi abbah yayi yace aa duk tafiya zakuyi ni zan kwana na kula da ita.

    Su dai su baffa sai kallon ikon Allah suke wannan wace irin drama ce, papa ne yace aa Ahmad kaje ka huta tun jiya kake nan, murmushi yayi yace aa ni basai na huta ba, mamma ce ta musu alamar su barsu.

    
Umar ne ya shigo da kayan abinci nan ya sake gaida mutanan wurin, mamma ce ta mishi Sannu da kokari.

 Tunda ya shigo idon shi nakan du’a amma du’a bata shi take ba.
 Bai wani dade ba yace zai tafi tare da abbu suka tafi, ance hajja da papa su tafi sunce ba yanzu ba.
    
     Bayan magriba yaya ya maida su teema gida, ance du’a taje tace ita ba inda zata anan zata kwana.
   Hajiya ce tazo bayan isha ta kawo musu abinci, around 9:00 hajiya tace wazai kwana a asibitin, du’a da abbah da yaya har hada baki suke wajen cewa ni.

    Wani kallo hajiya ta musu wanda suka sha jinin jikin su, hajja ce tace ita zata kwana, baffa yace ta barshi mami ta kwana ita mami tace eh hajja ta tafi gida zata kwana.
 
     Abbah budar bakin sa sai yace zai iya kwana da ita, hajiya ce ta kalle shi tace tashi ka tafi gida kaida iyalin ka, hajiya dan Allah, na gama magana.

    Dan dole ya tashi yace yaya da du’a su tashi su tafi, du’a kuwa tace wallahi ba inda zata, tasa musu kuka, abbah da kanshi yacewa hajiya dan Allah ta barta, da kar hajiya ta barta tace tare zasu tafi.

   Bayan su abbah sun tafi su baffa ma suka tashi zasu tafi, sunyi wa hajiya godiya sosai sannan suka tafi, yarima yace zai taho daga baya.

   Hajiya da tazo tafiya ta rasa du’a sama da kasa a dakin nan dan dole ta tafi yarima ya raka ta mota, har yanzu 
hajiya na driveing da kanta tazo.
   
       Tana ganin hajiya ta tafi ta dawo zata  shiga dakin taji an janyo ta, ihu tayi yayi saurin rufe mata baki, muryar shi taji yace daga ina kike, tsabar tsoro ido ta rufe ta kasa cewa komai sai girgiza mishi kai take.

  Ba magana nake miki ba, dama dama, huce mu tafi yau a gidan mu zaki kwana, ai tuni ta fara kuka, yaya Allah bazan iya kwana ba, give me a reason, yaya dan Allah kayi hakuri, mai yasa kika tafi yawo, bana son tafiya, zakiyi bayani muje ciki.

   Hannun ta yaja suka shiga dakin, mami na zaune gaban gadon suna hira da mamma, suna shigowa yace mami bari mu tafi saida safe.

    Du’a kallon shi tayi ya galla mata harara. Mami kice mishi ya barni na kwana.
  Mami yanzu naji doctors na complain akan kwana mutun biyu mami kinga kuma ku baza su muku magana ba, amma mutane sai suce dan ku wasu ne, ni bana son irin wannan rayuwa kara abi doka a zauna lafiya.

    Mamma ce tace yana da gaskiyya du’a kije ya kaiki gida, mamma dan Allah ki barini na kwana, aa su tafi gida mana saisu kwana da fatiha idan kuma ita kaida zata kwana kasa a gara mata daki, du’a da taga ba sarki sai Allah sai tace ita toh gidan su zata tafi.

    Okay muje na kaiki, aa ni kadai zan tafi idan  na bika wayo zaka mini, murmushi yayi yace da gaske zan kaiki gida.

   Sallama sukayi har sunje bakin kofa mamma tace du’a baza ki canza ba ko, da sauri  ta juyo tace mamma mai nayi, kije gidan su ki kwana, har zata musa kawai sai tace tam mamma amma kice gobe ya kawo ni da wuri, gaki gashi ki fada mishi, turo baki tayi tace ai kona fada bazai kawo ni ba.

   Saida safe huce mu tafi, kana binta a hankali mana inji mami,tam suka tafi.

    Su abbah tunda suka tafi saida suka biya suka siyi abinci, koda suka je gida suna gama cin abinci suka kwanta,bacci rabi da rabi sukayi.

   Su baffa suna komawa mutane suka dinga zuwa har saida yace shi bacci zaiyi ya sallami kowa,

   Papa kuwa zama sukayi shida hajja suna maida zance, fatiha ta shigo, tana gaida su ta zauna, hajja ina mami papa ne yace mun saida ta, kamar zatayi kuka tace haba papa ai kaima baka saida mami ba, hajja ce tace tana asibiti acan zata kwana.

   Bata wani dade ba tace bari ta tafi saida safe, fatiha ki kwana anan mana, aa hajja meeno na jira na zamu kwana mu biyu, aa kuzo ku kwana nan, hajja zamu iya kwana saida safe, Allah ya tashe mu lafiya, ameen tace ta tafi, nan ta fadawa meeno yace suka yi da su hajja. 

   Kowa dakin ta ta nufa amma sai sukaji gida ba dadi, kamar sunyi shekara bata nan, rashin uwa ba dadi.

    Hajiya kuwa da taje gida mama na palo tana jiran ta, hajiya ya jikin nata, da sauki, Allah ya kara sauki, Ameen basu wani jima ba suna hira mama ta tafi part dinta.

  Suna fita yayi gaba tana binshi a baya, ganin ya danyi nesa da ita yasa ya tsaya, saida tazo daidai shi sannan yace lafiya ki klau, eh tana kokarin kuka dan ita harga Allah bata so tafiya ba.

    Ko bacci kije ji, aa, yinwa, aa toh mai, ba komai, okay huce mu tafi, suna isa inda mota take suka shiga, suna tafiya a hanya tayi tunanin kiran abbah amma sai ta tuna bata san inda wayar ta take ba, a fili ta furta ina waya ta, kallon ta yayi ya juya.

   Juyawa tayi tana kallon waje, kawai yaji shashekar kukan ta, juyowa yayi ya mata tsawa ki rufe mini baki a gidan namu cinye mutane ake, tsawar ta shige ta da sauri ta girgiza mishi kai, okay iskanci ne kenan, a hankali tace abbah.

   Mai abbah yayi, inaso na mishi magana, toh waya hana ki, na manta waya ta, a ina, asibiti, kallon ta kawai yayi yayi tsaki.

  Can kuma sai yace gashi, tana juyowa taga yana miko mata wayar ta, da sauri ta amsa, abbah ta kira lokacin harya shiga daki.

   Hello abbah, na’am du’a ya jikin mamma, abbah nima bana asibitin, okay kardai ki zauna kiyi ta yiwa mutane kuka, abbah bazan ba in sha Allah, amma hawaye ne ke fitowa daga idan ta, abbah ne yace du’a nasan yanzu ma kuka kike, da sauri tace aa abbah ba kuka nake ba.

  Du’a idan baki son kwana saina zo na dauke ki, aa abbah basai kazo ba bana gidan hajja, kina ina, abbah dama sai ta daga kai ta kalli yarima ido suka hada,tayi saurin dauke kanta, ina gidan su fatiha, okay shikenan, tam abban kunci abinci, eh du’a kefa, nima naci, tam ki kulada kanki, tam abbah saida safe, don’t cry, murmushi tayi tace in sha Allah,kashe wayar yayi.
       Na kaiki gida ne, aa, tam bansan na kuma ganin kina kuka, in sha Allah, mai zaki ci, ba komai, you have to eat something. Allah da gaske banjin yunwa.

      Har suka karasa ba wanda yayi magana, suna isa shashen mami ya huce, koda sukaje kowa yayi bacci kuyangu duk sun tafi shashen su, gashi yunwa yake ji, suna shiga palon suka zauna saidan yi kamar 5 min ya dauko wayar shi ya kira ta  mami.

    Hello mami, ya akai, longobe fuska yayi kamar small boy yace mami yunwa nake ji, toh kaci abinci mana, mami ba kowa ai duk sun kwanta, Allah ya shirye ka matar ka ta shiga uku sai ka kwanta a haka saida safe, a speaker yasa wayar ya ajiye ta a gefan shi, da sauri ya dauki wayar ya fara mata shagoba wai shi yunwa yake ji.

   Mamma ce tace du’a ta dafa maka mana, kallon ta yayi itama ta daga kai ta kalle shi, mamma sai dai ki fada mata, aa ka fada mata ai kai yayan tane duk abinda kasata zatayi, ai tuni ta fara turo bakin nan nata tana magana ciki ciki.

     Mami ce tace aa yabar ta ta huta mana barina kira azo a dafa maka, aa karki kira zata iya dafa mishi, ai iskancin  kane da tsawon daran nan kasan zaka ci abinci baka tsaya ka siya ba toh wallahi banson wannan shegen iyayi naka duk abinda ta dafa kaci. Tam mami saida safe.
   
      Yana gamawa ya juyo ya kalle ta, tashi muje, daga kai tayi ta kalle shi idon ta duk ya ciko da kwolla, bazaki iya bane, kai ta girgiza mishi, banson wannan abin kin sani, tashi tayi tace aa, shima tashi yayi yayi gaba tabi bayan shi, suna isa kitchen din ya tsaya.

    Mai zaka ci, komai ma, gashi bata san kan kitchen dinba juyowa tayi ta kalle shi, hannu ya daga mata alamar meye, mai za’a dafa kuma ina kayan dafa war, nima ban sani ba, kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace toh wai mai zai hana ka sha tea, aa ni abinci nake so, ai ba’a san cin abinci idan za’a kwanta.

   Doctor du’a ai bance miki kwanciya zanyi ba, toh mai zakayi, ina ruwan ki, turo baki tayi, kallon ta yayi.

  A hankali ya fara takawa zuwa inda take baya ta fara yi har saida suka je jikin bango, ta rufe idon ta, tsayawa yayi yana kallan kyakyawar fuskar ta, ta fara motsi da lips dinta zatayi magana, taji ya saka hannu ya murde mata su ai tuni tasa kuka tsabar azaba.

    A hankali yace idan ina miki magana kina turo baki ko yayi kofa ya sake mata lips din, mai zan gani aiko yana saki ta kara turo su, sabo turken wawa.

   Akan idon sa, murmushi mugunta yayi ya kara matsowa ya kara murde lips din, wani sabon kuka ta saki, saida ya tabbata ya murde su sosai sannan ya sake ta.

    Ki hado mini tea da akoi cake ki taho mini dashi ya fice.

    Saida tayi kukan ta mai isarta sannan ta daura ruwan zafi tasa a tea plastic sannan ta dauko cake din koda ta fita yana dinning area yana danna wayar sa.

   Tana zuwa ya dago ya kalle ta fuskar ta duk tayi ja, a hankali yace kukan me kike waya taba ki, kallan shi tayi a zuciya tace anya yarima bashi da aljanu kodan lafiya shi kalau rainin hakali ne, magana nake miki, murmushi tayi tace ba komai, na jin dadi ne kenan, eh tace a takai ce.

   Tea ta hada mishi ta juya zata tafi, zonan, dawowa tayi yace zauna, ba musu ta zauna dan har zuciyar ta tsoran yarima take.

   Hada tea ki sha, na koshi, kallan ta yayi wanda yasa tayi saurin tashi ta hada ta koma ta zauna tana kallan cup din.

   Bai mata magana ba saida ya gama, tasowa yayi ya dawo kusa da ita, ai tun kafi yayi magana tace yaya dan Allah kayi hakuri Allah bazan iya sha ba, dalili, lips dina na mini zafi, da gaske, eh, maiya same su, tayi kokarin turo baki sai tayi sauri fasa wa , a zuciyar shi yake mamakin wannan shegiyar tsiwar ta ta.

   Matsawa yayi da kujerar ya dauki cup din, ya dauko tea a spoon yaji har lokacin da dan zafi, kara dauko wa yayi yakai bakin ta amma taki budewa hararar ta yayi ta bude duk da zafin da take ji haka ta daure, saida yaga babu komai a cikin cup din sannan ya dauko cake din shima ya fara bata, guda biyu taci tace ta koshi, bai musa mata ba ya barta.

   Tashi muje ki kwanta, tashi tayi suna isa  palon yace a ina zaki kwana, bari naje dakin fatiha kallon ta yake har saida ta bace mishi .

   Koda taje dakin a rufe, dawowa tayi yana inda ta bar shi.

   Ya akai, dakin a rufe, okay muje ki kwana a wani dakin, ni kadai, aa ni dake,ido ta zaro,yace maida idon nan a gida ke dawa kuke kwana, ni kadai, kuma, amma ai sai tayi shiru, amma me, ba komai, a hankali ya fara kusan toh ta yace amma me, Allah ba komai, rankoshin ta yayi yace matsoraciya kawai.

   Wani daki ya kaita,but you have to change your clothes, bata ce mishi komai ba,fatiha have to wake up, aa ka barta zan kwanta da wannan, no muje dakin meeno saikin dauki kaya, aa tayi bacci fa, and so muje, a hankali suke tafiya sai kuma ya tina bai dace ya shiga daki ba.

    Hucewa yayi dakin hauwa, itama tabi bayan shi suna isa inda clothe set yace ta dauki kaya, ita dai tsayawa tayi tana kallon kayan, hannun shi ta gani ya shafi face nata ya dauko wata gown, oya take this.

    Kallon rigar ta tsaya tana yi, daura mata yayi a kafadar ta ya huce ya kashe hasken daki, yar kara tayi sai jin mutun kusa da ita, a hankali ta fara yin baya suna isa bango ta rufe idon ta, a daidai kunnan ta yace change your clothe kije ki kwanta dare yayi sosai.

   A hankali tace dakin duhu, okay mu tafi yaja hannun ta.

   Suna isa daidai dakin da zata kwanta ya tsaya, kanta ya dago da dayan hannun yayi mata kiss a goshi sannan ya saki hannun ta yace good night, ya huce.

   Dakin ta shiga ta canza kayan ta kwanta, cikin dare zazzabi ya rufe ta, saboda bata taba shan wahala irin ta yau ba ga muguntar yarima .

    Shi kuma bai koma part dinshi ba dakin shi na part din mami ya huce, zai shiga yaga waya na haske, yana zuwa yaga wayar ta ce.


Mu hadu a kashi na gaba.😊❤️❤️


Domin neman ci gaban wannan litafin zaku iya following Instagram page dina Reeeyarh ko kumin dm ta WhatsApp ***.

   Nagode 
*~Book by Reeeyarh~*