Chapter 19
by @reeeyarh
Page 19
*~reeeyarh~*
Suna zaune suna hira da mamma dasu fatiha, sai kusan 2:00 ta tashi, lokacin abbah harya dawo mutane da yawa sunzo sun tafi kamar su hajiya,adda da family ta, duk dai family abbah sunzo sun tafi, sauran matan baffa ma duk sunzo sun duba ta.
Yarima kuwa shima saida yaga mami ta tafi ta kwanta sannan ya huce part dinshi, sai kusan 1:00 ya dawo mami har ta tashi ta saka an hada musu abinci, shi kuma yayi wani wankan.
Muje ka kaini asibitin, tam mami, suka tashi suka tafi.
Du’a data tashi sallah tayi ta koma kusa da fatiha ta zauna, suna hira yaya Ibrahim ya shigo, zama yayi kusa da ita ya gaida su mamma ya mata ya jiki, da sauki, Allah ya kara sauki, Ameen nagode, mamma da abbah na hirar su shi kuma ya juyo suna kallon juna shida du’a suna hira da fatiha, meeno kuwa sai faman danna waya take.
Mami ce ta fara shigowa shima ya shigo, gaida ta yaya ibrahim yayi ta amsa, sannan ta zauna, yarima kuwa kamar ya kama shi da dambe, da karya daidai ta kanshi suka gaisa.
Du’a harkin tashi, eh mami, amma dai babu zazzabin ko, babu, kema baki da lafiya, eh yaya Ibrahim amma naji sauki, Allah ya kara sauki, Ameen.
Yarima kuwa wurin ya samu ya tsaya, hira su sukaci gaba, yaya Ibrahim yace wai dazu da adda tazo ta fada miki sako na, adda kuma yaushe suka zo, au ashe fa kinyi bacci ko inaga kina bacci suka zo.
Ita dawa ita da zainab da munira, amma shine bawa tashe niba, kema kinsan adda bazata taba bari a tashe ki kina bacci ba, okay yanzu menene sakon, aa ki bari ba yanzu ba, yarima duk abinda suke yana jinsu.
Mamma barina tafi, tun yanzu, murmushi yayi kawai ya tashi yace Allah ya kara sauki, duk da ameen mutanen daki suka amsa, du’a tace barina raka ka, aa ki zauna keda baki da lafiya, aa yaya Ibrahim ai naji sauki, toh muje, tare suka fita da fatiha da adam ya kira ta a waya.
Yarima ya kusa fashe wa, mamma ce tace abbah yau bazaka je wurin akiba, tafiya zanyi gida ma.
Tashi yayi ya fita yarima yabi bayan shi wai zai raka shi, yana fita mami ta kalli mamma tace kun kama muda yawa mamma bata gane ba, tace ban gane ba ashe duk abinda yarima keyi mami na kallon shi tasan saboda du’a ya fita yanzu.
Fatima ku taimaka ku bamu dama, tame nan mami ta fahimtar da ita, mamma tace Allah sarki babana ai indai hakan gaske ne kamar ya same tane, aa indan ita kuma bata sanshi fa, toh wa zata so nidai nasan batada wani saurayi, aa gara dai mu zama yan kallo, tunda fatiha ta yaudare ni take soyayya da adam ban gane ba ai kawai ki tsaya kiga ikon Allah.
Murmushi mamma tayi tace Allah yasa hakane yafi alkairi, naga alama ya kusa fara dukan mutane akan ta, tunda daga kallon baza ai sai duka.
Hakanma bazata kasan ce ba, amma gaskiyya yarannan Allah ya shirye shi abu na cinka bazaka fadaba, bafa ki tabatar ba aunty, aa ni inada tabas dan nasan halin shi ciki da waje, ai shikenan Allah ya shirye shi, ameen.
Fatiha wurin ta samu a waje ta zauna tana waya, du’a kuwa suna tsaye ita da yaya Ibrahim yana cikin mota ita kuma tana bakin motar ta rike kofar motar suna hira, sai dariya take, a haka yazo ya same su, abbah mota ya shige ya huce.
Du’a barina tafi kije ki huta, yaya Ibrahim waisai muna cikin hira saika ce zaka tafi, ta bata fuska, du’a akoi wadda take jirana a shop ne.
Kodai aunty muce tana murmushi, gidan ku du’a yaushe muka fara wannan wasan dake, kai yaya Ibrahim daga tambaya, Allah ya shirye ki, Ameen yaya na tana dariya, okay yanzu huce ki koma ciki, tam sai anjima, okay bye, ta rufe motar ta tafi.
Duk abinda suke akan idon shi yana bakin motar shi a tsaye, ta kusa zuwa inda yake wayar ta tayi kara, number ce saida ta kusan yanke wa ta daga.
Hello, hello du’a ce, eh nice waye, ajiyar zuciya yayi yace faruq ne, wana faruq, abokin sadiq, okay ina yini, kawai ji tayi an amshe wayar, dan yaji lokacin da tace wana faruq.
Wanna wana irin shirme ne tana juyowa, ganin shine yasa ta shiga hankali ta tace yaya, dawa kike waya, faruq najin haka ya kashe wayar shi.
Dan shi gaskiyya yarima ya fara kular dashi, wannan ai rainin hakali ne toh wai ma uban meya hada ta dashi yasan dai ba sister shi bace amma duk inda take yananan, jiya ma ya bashi haushi sosai amma zaiyi maganin shi.
Yaya ka bani waya ta, nace dawa kike waya, kallan shi tayi kawai tayi gaba, janyo ta yayi, yayi mota da ita, duk akan idon fatiha da ke waya da adam.
Ruhee wai meke damun abokin ka, wa kenan, dama kanada wani abokin ne banda wanda na sani, mai kika gani, labari ta bashi na komai daya faru har yanzu da yaja ta mota, kije ki tambaye shi, ni awa yaci ubana akoda yaga fishi na, murmushi tayi kawai, kin san me, aa yayan ki ya fada da yawa sai kun mishi uzuri.
Haka ma mami tace, mami kuma eh dazu ai na fada mata abinda yayi, ai shikenan amma shegen girman kan yaya ki yayi yawa kana so bazaka fada ba harsai abuya maka nisa, nima dai mamaki yake bani.
Ai dole ya baki mamaki, amma zan mishi magana, yafi dai, yanzu ya maganar zuwan ku, wallhi ni banma sani ba saina tambayi mami, wallahi teemana nayi missing dinki, yaya kazo nima nayi missing dinka, keda ko nazo ba haduwa zamuyi ba, kema da taki kunyar, zaka ganni saimu fita, da gaske.
Allah idan kazo zamu fita, okay shikenan zanzo yaushe kike so nazo gobe ko jibi, gobe, okay zaki ganni in sha Allah,yawwa my love, yanzu dai karna zo bamu haduba dan nasan halinki, Allah zamu hadu, nidai Allah ne ya hadani da mutane buyu kuma duk gida daya, yaya kamar ya, keda yayan ki mana shi miskilancin kema miskilancin, haba yaya taya zaka hadani dashi.
Toh kema da ba irin soyayyar tashi muke ba sai dakar abuya fitoh fili, amma ai garani tunda wanda muke soyayyar dashi ya sani, ai kema da kece na mijin haka zakiyi dan nasan wannan ma danni na bayyana shiyasa, aa niba halin mu daya ba, toh naji.
Suna shiga ta bata fuska, du’a dawa kike waya, ba hurimin ka bane ka tambaye ni, ko abbah yaga ina waya baya tambaya ta dawa nake waya, kallan ta yayi yace okay shikenan zan fada mishi shashancin da kike.
Kamar ya ta turo baki, murmushi yayi yace hukunci ya tabbata akan ki, tunawa tayi da maganar suta dazu, kasa tayi da kanta yace ki dago ki kalle ni muyi magana kafin na miki hukuncin ki, yaya dan Allah kayi hakuri, ai babu hakuri a wannan lamarin.
Kina jina, eh, zan fada mishi abinda kike, mai nayi, waya da saurayi around 12:00 ni kuma yaushe, idan da bakiyi jiya mai yasa aka kira ki, aka kira ni kuma, eh, toh akan me zaka daga mini waya, ra’ayi yasan bayi take ba kawai dai ya bigi cikin ta yaji ko tanada wani saurayin.
Okay shikenan tunda ra’ayi ne ai ka gani ko tam bani waya ta, bazan bayar ba, juyawa tayi zata fita taji ya janyo ta yace ina zaki baki amshi hukuncin kiba, tuni ido ya raina fata, yaya kayi, ai kafin ta karasa taji ya matso da ita jikin shi sosai hanun shi a wrist dinta, tuni jikin ta ya fara kirma.
Yaya ka bari bana so, a kunne yace what did you said i should do bata bashi amsa ba yace what ever I want, amma yaya ai, shiru ba abinda zan miki just wait karki sake magana, shima kanshi baisan mai yake cewa ba dan tuni ya fada wata duniyar, shiru tayi taga iya kacin gudun ruwan shi.
Rungume ta yayi sosai kamar zai maida ta ciki, can kuma sai ya dagota ya kalli fuskar ta yace wana punishment zan miki, yaya kayi hakuri, no bazan hakura ba, Allah i promise bazan sake ba, idan kika sake fa, shiru tayi dan ita indai irin wannan punishment dinne gara karta amsa, in sha Allah bazan sake ba.
Kin tabbata, kai ta daga mishi, okay shikenan, gara dankolin ki, tam ta gara sannan yace ma zaki fadawa abbah, sirine, about what, girgiza mai kai tayi, shi kuma kallon ta kawai yake, tsakani na dashi ne, anyway kar naji suna na, murmushi tayi tace in sha Allah ba zaka jiba, okay let’s go.
Suna fita har lokacin fatiha bata gama wayar ba, suna isa inda take yace ke kashe wayar nan, bata musa ba ta kashe, aiko ran adam ya baci a lokacin ya kirashi.
Ku huce ku tafi ina zuwa, yana dagawa adam da fada yace malan mai hadinka da rayuwar mu bana san irin wannan abin, meya faru bana sani ba ai kasan dani take waya zaka wani ceta kashe, sorry wallahi na manta, adam ya kulu ya kashe wayar shi.
Kiran shi yarima ya kuma yi amma ya ki dagawa, har sau uku yana kiran shi amma yaki dagawa, a ranshi ya jin jina sonda adam ke yiwa fatiha dan ba karamin abu bane yake sawa adam ya ki daga wayar shi ba saida baya kusa, amma yasan yanzu yana kusa.
Du’a wai mai yaya yace miki a mota, ina ruwan ki, babu, toh kuma suna hira har suka karasa dakin, suna shiga mamma tace kuzo kuci abinci, du’a tace saidai fatiha nina koshi, fatiha zuba abinci tayi ta fara ci, ita kuma ta zauna ta hau online dan raban tada online tun jiya a gidan adda, reply takewa mutane ya shigo.
Babana ka dawo, eh mamma, kaima zoka ci abinci, du’a tashi ki zuba mishi, ba musu ta tashi, kusa da mami yaje ya zauna, koda du’a ta kawo mishi abinci, cewa yayi wai mami ta bashi a baki, bata musa mishi ba soboda san yaranta yayi yawa.
Aunty gaskiyya ki sangar ta babana da yawa, ai tunda ya furta idan ban bashi ba bazai ciba, du’a kallo daya tayi mishi a zuciya tace toh karya ci mana cikin wa, kawai ji tayi yace shi mutun Allah kadai yasan irin nashi iskanci gara ni mami ke bani abinci amma wata young sister ta tasa a gaba take bata.
Da sauri ta zaro ido dan ita harga Allah a tunanin ta a zuciya tayi maganar, dariya su mami suke musu sosai, mamma tace ai kema yanzu da za’ace a baki ci zakiyi, haba dai mamma ai na girma.
Gaskiyya dai kam yarinya ta ta girma tabar su yaya suna shagoba, maga yace zakayi zaman gidan aure da ba kocce macece zata dauki halinka ba.
Mami ni bani abinci na zanci da kaina, ai tunda na fara saina karasa.
Du’a koma wa tayi taci gaba da abinda take, murmushi tayi tace mamma yanzu zakiyi baki surikan ki zasu zo, wani tari yarima ya fara ba shiri, da karya tsaya, duk sunbi sun rude, make damun ka, kaiya girgiza yace na koshi.
Okay sannan duk sannan suka mishi, shidai babban burin shi yaji suwaye zasu zo.
Saida dakin yayi shiru mamma tace Zahra ce zata zo, eh mamma, mami tace wace zahra, fatiha ce tace budurwar yaya ce, okay Allah ya kawo ta, yarima sai yanzu yaji daidai.
Babana baza kuje gida ba ku huta, ai kawai ki barsu dan babu inda zasu, shima na gidan ba dan naje ya ganni da tuni yana nan kuma ma dan papa nanan, aunty dama ki nada wani dan bayan babana, eh mana jiya ai sunzo, aiko zanso na ganshi dan ban gane shiba.
Karki damu zaizo yau da dadare yace ai naji suna cewa gida zan tafi dama nima banson zaman asibiti nan, Allah yasa toh, Ameen suka ci gaba da hirar su.
Mamma wai kinji yaya su bari sai gobe suzo, ina ruwan ki ba tare kika gansu ba, eh mamma, kuma, doctor neya shigo, du’a ya kalla yace mai tsoron alura kiyi hakuri nadan dade ga maganin, aa ni nama bar maka, ba’ayi haka ba gashi yana hucewa dan yakai mata, kawo, duk juyowa sukayi suna kallon shi, doctor mika mishi yayi ya duba mamma yace zuwa yamma idan ruwan ya kare zasu iya tafiya, tam mun gode, yace ba komai Allah ya kira sauki, Ameen suka ce ya tafi.
Kizo kici abinci kisha magani inji mamma, nifa mamma banjin yunwa, Allah bazaki sani surutu cikin dare ba gara kisha maganin ki, tam mamma.
Tashi tayi taje ta amshi maganin ta koma kusa da mamma ta zauna, yaya ne ya shigo bayan su gaisa dasu mamma ya kara mata ya jiki, sannan suka gaisa da yarima , su fatiha suka gaida shi, ke kuma mai zakiyi da magani, ba komai, da dai kin fadi gaskiyya inma dura miki zaiyi yayi, mamma batada lafiya, eh, zama yayi kusa da ita ya meke damun ki.
Yaya kawai fa jiki nane yayi zafi kuma dazu nasha magani wai shine yanzu ma saina sha.
Toh kinci abinci ne da zaki sha magani, mamma tace yau ni fatima naga ikon Allah yanzu zamu hanata abinci ne, ai garama daka zo sai taci a gaban ka, kallan ta kawai yayi sai ganinta nayi tana zuba abinci, zonan taje da abincin.
Bani ta mika mishi, yana dakko wa zai bata tace ai ita da kanta zataci, fatiha mai zatayi badda dariya, akin banza dama abinda mutun yake so kenan idan ma zakici abincin ki kici ni ina ruwana dake, duk yan dakin saida sukayi dariya.
Yaya dai bai gane meke faruwa ba, yace ta bude baki saida ta cinye duka sannan ya bata maganin, kije ki kwanta ki huta, yaya ban dade da tashi daga bacci ba, ok Allah ya kara sauki, kai kaci abincin ne, dan sosa keya yayi yace dama.
Allah ya shirye ka du’a zobo mishi abincin, aa mamma ni ba yanzu zanci ba saina yi sallah la’asar, okay shikenan.
Meeno tunda ya shigo gaba daya hankalin ta ya koma kanshi, ita wallahi komai nashi burgeta yake, kamar ma sanshi take gashi yana da budurwa, zata so taga wannan zahra da ake cewa, murya shi taji yace meeno kedai baki magana ko, murmushi tayi tace aa.
Ai yaya na fada maka duk yaran mami babu wanda yakai ta surutu inji fatiha, kai fatiha banson sharri, Allah yaya da gaske nake, meeno wai haka ne, aa nan suka fara hira har aka kira sallar la’asar, tashi sukayi suka tafi masallaci su kuma sukayi tasu sallar.
Koda suka dawo tun kafi yayi magana du’a ta zuba mishi abinci, bayan ya gama mamma tace suje su dakko su dee su huce gida, aa mamma yaya ya dakko su kinga ni saimu tafi tare, rankoshin ta yayi yace uwar wayo toh tare zamu je.
Aa yaya dan Allah kaje ka dakko su, okay amma da sharadi, inaji gobe zaki tatara baban ki ya tafi wurin aiki da wuri kuma karya dawo da wuri, mai yasa, ban sani bah ai kin san dalilin.
Mamma ce tace bamai korar mini miji wallahi saina tona muku asiri, haba mamma dan Allah kiyi hakuri, wallahi zahra tace tsoron abbah take, sosai ya bawa yan dakin dariya, toh haka za’ayi auren tana tsoron haduwa da sirikin ta.
Mamma dan Allah, shikenan an gama ai kai ne karka damu ni kaina saina kora shi, yawwa mamma na. bari naje na dakko su, tam saika dawo, amma mamma dawa zaku dawo, abbah zaizo ya dauke mu.
Aa ai sai mun kaiki gida muda tafiya sai dare inji mami, amma ai motar bazata ishe kuba, du’a kizo mu tafi, du’a tace ita ba inda zata, fatiha ma tace yaya karma ka kira sunana saidai ku tafi da meeno.
Yarima baice komai ba dan karya saka baki a tafi da star girl dinshi, mami ce tace meeno kije ku tafi muma yanzu zamu zo kinji, tam mami ta tashi suka tafi.
Suna fita yarima yace ku kuma saidai ku hau adedeta, fatiha ce tace yaya adedeta kuma, eh ita, dan Allah kayi hakuri, tsaki yayi yaci gaba da danna wayar shi.
Abbah ne ya kira du’a, tace mishi ai yanzu zasu tafi, okay bari nazo, aa abbah basai kazo ba, aa du’a akoi maganin da zan siya dazu na manta ban siya ba , ai zan iya, kin tabbata, eh abbah, okay ki karbi ATM a wurin mamma kije kiyi komai barda shirme, tam abbah saika dawo.
Tana kashe wa tace mamma ina ATM din abbah, gashi can me zakiyi, ba komai yanzu zan dawo, har takai bakin kofa taji ance idan kika dawo kika ga bama nan kin taho, kamar ba zatayi magana sai kuma tace wani magani zan siyo fah,
Wana magani, mamma abbah yace dazu ya manta bai suyo ba yace naje zai turomin sunan maganin, okay kiyi sauri, mami ce tace fatiha kije ki raka ta, tam ta tashi suka je suka siyo, suna dawowa taji ance du’a juyawa tayi.
Uncle faruq ina yini, lafiya lau fatiha ma ta gaida shi, me kike a asibiti, dama sai tayi shiru, waye ba lafiya, mama nace bata jin dadi, kuma tana asibitin eh, toh muje na duba ta.
Suna tafiya a hanya yace dazu muna waya naji shiru, ita sai yanzu ma ta tuna dazu sunyi waya da sauri ta kalle shi, yadai, ba komai wallahi akasi aka samu, a zuciya tace Allah yasa baiji komai ba.
Ba komai du’a nasan waye ya karbi wayar amma karki damu zamuyi magana dashi, murmushi kawai tayi har suka je dakin ba wanda ya sake magana, a bakin kofa ya tsaya suka shiga, mamma za’a shigo duba ki, waye, idan ya tafi zan fada miki yanzu yana kofar dakin, okay ya shigo inji mami.
Koma tayi tace ya shigo, yarima kasa motsi yayi ganin faruq, mai ya kawo shi, faruq har kasa ya tsugunna ya gaida su mami, mami tace zauna mana mami tayi mamakin ganin faruq, yana zama yace yamai jiki, da sauki, Allah ya kara sauki, Ameen mu gode. Yarima dai bai iya masa magana ba.
Du’a ce tace yaya ga abokin ka fa, sannan yace ai na ganshi, gaisawa sukayi, faruq kamar yayi dariya saboda yadda yarima yayi, barina tafi Allah ya kara sauki yasa hannu a aljihu, tuni yarima ya tashi ya daura hannun a kafadar shi sukayi waje.
Du’a tashi tayi tabi bayan su, mami tace wai wannan yaron meke damun shi, ki barshi aunty yarinta ce.
Suna fita yace no need thank you, ya juya zai komai, du’a ceta fitoh.
Mu hadu a kashi na gaba.😊❤️❤️
Domin neman ci gaban wannan litafin zaku iya following Instagram page dina Reeeyarh ko kumin dm ta WhatsApp ***
Nagode
*~Book by Reeeyarh~*