Page 12
by @sanazty
•••SANADIN MAHAIFINA•••
Wattpad@SaNaz_deeyah
Arewabooks@sanazty
Facebook@Habibtyn Habibi
YouTube: ***
Tiktok: ***
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula ta gari]
'''Shafi na 12'''
________________📲Cikin tashin hankali Ummu ta kira likitoci, aka zo aka fitar da Mommy daga ɗakin. Ta suma bata san a ina take ba.
Ummu waya ta ɗauko daga cikin jakarta ta sanarwa da Alhaji Ma'azu halin da ake ciki, ya ce ga shi nan zuwa.
1 hour later
A hankali ta buɗe idanunta, akan silin ta fara diresu kafin ta kalli mutanen da ke gefenta. Ganin Ummu da Daddy ne ya saka tayi saurin tashi zaune, dan tayi tunanin duk abinda ya faru mafarki ne, sai da ta gansu tsaye a kanta, kuma a asibiti.
Drip ɗin ta fuzge, tana ƙoƙarin sauka daga gadon. Ummu ta riƙeta tare da faɗin "Dan Allah ki bari ki samu hutu tukun"
"Hutu fa kike faɗa Hajiya Bilki? Ina naga hutu bayan yarana wanda su kaɗai na mallaka suna cikin wani hali"
Daddy ya matso jikin gadon yana faɗin "Falmata dan Allah ki nutsu, ki jira Doctor yazo domin ke ma ba cikakkiyar lafiya ne dake ba"
Ranta a ɓace ta kalleshi, sai kuma ta fashe da kuka. "Duk abinda ya sami ƴaƴana kaina sila, kaine mahaifinsu amma kuma baka son su, da kanka kayiwa ƴaƴanka baki, yanzu ga illar furucin ka nan, na tsane ka wallahi, kuma idan har na rasa ƴaƴana sai nayi shari'a da kai, domin muguwar zuciyarka ce ta jefa su ga halaka" tashi tayi da sauri ta fita ta bar ɗakin.
Daddy ya zauna kan gado tare da dafe kai.
"Wai meke faruwa ne haka da har zata ce furucina ne ya jawo?"
"A'a har yanzu ai Jannat bata farka ba, haka itama Safina tana can unconscious, bamu san abinda ya faru da Jannat ba, amma ita Safina accident ne, Hajiya Falmata ta faɗi haka ne saboda tana ganin kamar korar da kayiwa Jannat ne ya jawo mata haka, tunda Doctor ya tabbatar mana cewa fyaɗe aka mata"
"Idan korar da nayi wa Jannat ce ta jawo haka ita Safina fa? Matar da take ɗakin mijinta, wannan ƙaddara ce kawai, Allah ya basu ikon cinye jarabawarsu"
"Amin ya rabbi"
"Ina Ahmad ɗin yazo kuwa?"
"Gaskiya bamu ga Ahmad ba, ko bai sani ba, ka dai kira number tashi dan ya kamata ace ya san halin da matar shi ke ciki, nima zan kira Farhan na faɗa mata"
"A'a ki bari sai gobe kada ki tada mata hankali saboda lokaci ya ƙure ki kirata yanzu"
"To shikenan, Allah ya kaimu goben"
"Amin" ya faɗa lokacin da yake dialing number Ahmad amma a kashe.
"Wayar tashi bata shiga, bari na kira Driver sai yaje gida ya sanar masa"
"Okay ba matsala"
******
Atamfa ce a jikinta ɗinkin doguwar riga orange color, ta yafa babban mayafinta dark green wanda touch ɗin atamfar ne.
A kunyace ta sauka down stairs.
Mommyn Khalil, Hidaya da Shahina suna zaune kan kujeru.
Khalil ɗin shima yana zaune kan 1 seater.
Kanta a ƙasa ta ƙarasa gaban Mommy, har ƙasa ta kai gwiwoyinta ta gaida ta. Mommy ta ɗagota tana faɗin tashi ki zauna ƴata.
Kusa da ita ta zaunar da ita, Hidaya da Shahina suka gaidata duk da cewar sun girmeta dan Farhan is just 17.
Miƙewa tayi ta nufi kitchen. Mommy ta kalli Khalil tace "Allah ya maku albarka gaskiya Khalil kayi sa'ar mata mace mai kunya, duk da ta sanmu tun kafin auren amma kuma kunya kamar yau ta taɓa ganinmu.
Murmushi yayi, lokaci ɗaya ya tuna furucin Mommy lokacin da yana tare da Jannat.
Jannat tana da tarbiyya, kunya da kawaici, kaf cikin ƴan uwanta ta fisu nutsuwa, bata da rawar kai, shiyasa nake farin cikin kasancewarta suruka ta, Allah dai ya nuna mana ranar bikin........
"Ba ka ji na ne?" ya tsinkayi muryar Mommy" ɗagowa yayi yana murmushin yaƙe.
"Tunanin me kake haka?"
"Wallahi Mommy aiki ne yayi min yawa"
"Gaskiya ka riƙa hutawa shima stress ɗin yana haifar da matsala"
"Insha Allahu."
Farhan kuwa, sai da ta cika center table ɗin da kaya. Mommy tana ta saka mata albarka.
Da kanta ta zubawa Mommy lemo, tana ƙoƙarin zuba snacks, Mommy tace "A'a zubawa ƴan uwanki, ni lemon ma ya isa."
Sun ɗan taɓa hira ita dai Farhan bata cewa komai. Sai da Shahina ta tashi tace "Farhan muje ɗaki muyi hira mubar Mommy da Yaya"
Su ukun suka nufi bedroom ɗin Farhan. Anan kuwa ta saki jiki tana ta hira dasu duk da cewar lokacin kafin ta auri yayansu basu wani shiri sosai amma yanzu dole ta saka.
Sai gaf da magrib suka tafi, Farhan kuwa kewarsu sosai taji.
*****
Tana zaune kan gadon asibitin, idanunta na zubar da hawaye, ta dafe fuskarta da dukkanin hannayenta. Sallamar da taji ne ya saka ta ɗago tare da goge hawayen ganin Ummu da Daddy.
Ƙwayar idonta ta sauke ƙasa tana jin zugi a cikin zuciyarta.
Ummu ta zauna gefen gadon sannan ta saka hannu ta goge mata gutun hawayen.
"Ki bar kuka, zaki ƙarawa kanki ciwo, ki ɗauki wannan a matsayin jarabawa, Allah ya baki lafiya"
"Ya jikin naki?" taji muryar Daddy ta dirar mata. Ɗago ido tayi ta kalleshi suka haɗa ido sannan ta mayar da ƙwayar idonta ƙasa tare da cije leɓe.
"Ummu ina son ganin Mommy"
"Za ta shigo yanzu, taje gurin likita ne"
Hawaye masu zafi za su zuba a kuncinta ta saka hannu ta goge cikin shashsheƙa.
****
Tana tsaye jikin gadon da Safina take tana hawaye. Nurse dake tsaye tare da likita suna ta bata haƙuri kan ta kwantar da hankalinta komai zai dai-daita.
Wayata ta ɗaga ta kira number Ahmad amma a kashe. Bayan likita ya gama rubutu a file ya kalli Mommy ya ce idan jinin da aka jona ya ƙare ta kira nurses, ta gyaɗa kai kawai.
Farhan na bedroom tana gyara gashinta Khalil ya faɗo ɗakin a gigice, da mamaki ta kalleshi "Yaya Khalil lafiya?" da kyar ya iya dai-daita nutsuwarsa. "Ki tashi ki saka mayafin ki zaki raka ni unguwa" "Unguwa haka ba sanarwa lafiya kuwa" "Ba komai karki damu, yi sauri ki shirya" "To" ta furta sannan ta faɗa bathroom, wanka tayi ta fito anan tsaye ta same shi yana duba agogo. Ganin haka ya saka ta shirya a gurguje suka fita.
Kai tsaye asibitin suka nufa, hankalinta a tashe ganin su a ƙofar asibiti. "Yaya Khalil lafiya kuwa?" ta furta a sanyaye gabanta na faɗuwa. "Kada ki damu dubiya zamuyi." kai kawai ta gyaɗa suka shiga, da ledojin fruits a hannunsa wanda suka tsaya a hanya suka saya.
Suna turo ƙofar Farhan ta saka salati, da sauri ta ƙarasa jikin gadon da Jannat ke kwance. Ummu tana daga zaune kan kujera ita kaɗai ce a gurinta a lokacin. "Mene ya sameki, Jannat lafiya na ganki haka?" Farhan ta furta tana hawaye. Itama Jannat riƙo hannun Farhan ɗin tayi ta ce "Sis...." kuka ya hanata ƙarasa maganar.
Khalil ya gaisa da Ummu, Sam ya kasa haɗa ido da Jannat duk da cewar itace ta masa laifi. "Ummu ina Mommy da Safina?" Farhan ta faɗa tana goge hawaye. "Mommy tana ɗakin da aka kwantar da Safina"
Jannat a hankali ta miƙe zaune cikin tashin hankali ta ce "Ummu mene ya samu Safina?" "Jannat ki kwantar da hankalinki, Zazzaɓi ne take" cikin kuka ta ce "Ina son ganin Safina dan Allah."
******
"Dukkansu ƴaƴana ne kuma ni ce kaɗai wadda zan iya jinyarsu, dan Allah likita ka haɗa min su ɗaki ɗaya" Mommy ta furta tana goge hawaye. Likita ya ƙara kallonta ya ce "Hajiya kiyi haƙuri, bama yin haka a wannan asibitin domin cutarsu ba iri ɗaya bace, ki samu wanda zai miki jinyar ɗaya daga cikin su, domin ita ɗayar zamu turata asibitin masu yoyon fitsari." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
******
Jannat ta miƙo hannu ta riƙe Farhan tana hawaye. "Ina son ganin Safina please Farhan" Cikin kuka Farhan ta saka hannu ta goge mata hawaye "Kiyi haƙuri Jannat, kin ga baki jindaɗi idan kin warware sai ki ganta." kuka ta cigaba da yi da ƙyar Ummu ta rarrasheta ta daina kukan. Khalil na nan tsaye idanunsa tuni sun canza launi, ya kasa kuka amma yana jin raɗaɗi sosai a ran shi.
*****
Likita zan tausasa murya cikin rarrashi ya ce "Kiyi haƙuri Hajiya, in sha Allah za su samu lafiya, amma gaskiya bama zai yuwu a haɗasu ɗaki ɗaya ba" Mommy za tayi magana kenan, aka turo ƙofar da ƙarfi aka shigo a gigice. Nurse ɗin ya kalla, Mommy kuwa tuni ta miƙe tsaye. "Doctor Patient ɗin tamu ta rasu" zare idanu Mommy tayi da tashi hankali ta ce "Wace pa......." bata ƙarasa maganar ba ta zube a gurin ta suma.
To wace ta rasu?
Jannat ko Safina?
Ku biyoni a kashi na gaba
SaNaz Ce✌️