Blind love (Makauniyar soyayya )

Chapter 4

by @reeeyarh

Blind love 31&40
(Makauniyar soyayya❤️)

  A hankali tace aa sir oya dawo ki huce gidan ku, a hankali ta rufe kofar motar, yaja motar saida yabar layin maima  kon yabi ta street saiya zagaya ta layin baya gefen wani gida yayi packing, a hankali ta dago tace this is not our house.

  Bai kulata ba ya dawo back sit, ganin haka yasa tayi sauri zata bude motar ta fita ya ruko hannun ta, da sauri ta janye hannun nata daga nashi, mai damu ba ya rufe kofar ya danna lock.

  Sir, da izinin wa kika zo, my parents, wani janyo ta yayi wanda ta kusa fadawa jikin shi ai tuni ta fashe da kuka tace sir please I’m sorry, am I your mate dazan kafa doka ki karya, kai ta girgiza mishi.

  Look over me sir please dan Allah karka dake ni, murmushi yayi a zuciya yace wai duka yace ke yaushe rabo da a dake ki, tun ina 15 years mamaki ne ya kama shi kenan tun 15 years take tsoron duka, who beat you, daddy.

  Shiru yayi na tsawan 5 minutes sannan yace nine aljanin da kika gani a dakin ki ko, aa sir da gaske na, am I your mate zaki mini karya, aa.

  Oya kalle ni ranar wa kike harara, da sauri tace mirror, really repeat what you did the last time, wani kukan ta sake fashe dashi, a hankali yace fatima, kittt ta tsayar da kukan nata, a hankali ta dago ta kalle shi.

  Stop crying, kai ta daga mishi ta goge hawayen ta, okay let talk serious, dan Allah sir kayi hakuri, okay look at me kin dagowa tayi kawai sai jin hannun shi tayi a habar ta ya dago fuskar ta ta.

  Mai yasa baki ji, shiru nanan tayi, laifin mai kikaiwa daddy jiya, bata boye mishi komai ba, lumshe idon shi yayi data kai karshe magana sannan ya sake bude wa.

  Fatima kinsan laifi nawa kikai mini, kai ta daga mishi, nawa ne, one, no tuna dai, shiru tayi da yaga bata da niyar magana yace firstly i said karki tafi gida sai time yayi kika tafi second kin mini ihu a kai thirdly kin zo ba tare da izini naba duk da wannan dole na barki kizo amma baki sake tambaya taba still hannun shi na fuskar ta.

   Duk maganar da yake idon ta a rufe yake a hankali ta bude baki tace I’m sorry, that is what you always said, I promise not to do it again, and I promise you will do it again, kuka ta sake fashe dashi  Allah i will not, murmushi yayi ya saki fuskar ta.

   Baki son koma wa gida ko, kai ta daga mishi, murmushi yayi ya fita ya zagaya ya bude door din side dinta ya ruko hannun ta ya dawo da ita gaba sannan ya zagaya ya shiga driver sit ya fara tuki a hankali.

  Suna isa ta juyo ta kalle shi, what about the look, dama kasa gida bai tanka mata ba yace kice mamie zan shigo mu gaisa kai ta girgiza mishi murmushi yayi nan ma wa kuma kallan shi, banson kallo.

  Baki ta turo yace zaki iya tafiya tunda ramawa za kiyi dan na hana ki shiga gidan mu, da sauri ta girgiza mishi kai tace that’s not what I mean, Allah na shiga daddy will dell with me, toh yaza kiyi, let me call huda ta fada mata, okay call her.
   
  Huda na dagawa tace daddy nanan, eh ya maha wallahi karki dawo yanzu ki tafi gidan uncle dan wallahi daddy a fusace yake kin tafi yawo,a speaker wayar take yaji duk abinda ya faru, a hankali tace tam. 

  A hankali tace ka shiga ni zanje gidan uncle, ohh your uncle lives her, yes, murmushi yayi yace babu inda zaki huce mu tafi, Allah ni bazan shiga ba, kina tsoron duka, kai ta daga mishi.

 Toh mai yasa baki ji, shiru tayi anyway huce mu shiga, fita tayi tana fita tayi hanyar titi da sauri ya damko hannun ta, kuka ta fashe dashi, zo magana za muyi, kai ta girgiza mishi, janyo ta yayi yasa a back sit shima ya shiga.

   Yana shiga ya sama door din lock, juyawa tayi zata tafi taji a rufe, please sir dan Allah Allah daddy will beat me, he will not, he will ta fashe da kuka.

  Fatima keep quiet muyi magana, kai ta girgiza mishi kawai ya janyo ta jikin shi kittt taji zuciyar ta ta daina aiki, sosai yayi hugging dinta sun dau kusan two minutes a haka ganin tayi shiru yasa ya janye ta daga jikin shi yace let talk.

  Ita dai bata ce komai ba sai sauraran shi, a hankali ya fara magana yace fatima yanzu ki bari mu shiga zan bawa daddy hakuri kuma yanzu idan kika tafi gidan uncle din ku ai kin karawa kanki laifi, babu abinda zai miki kinji ita dai bata ce uffan ba harya fita ya bude door din.

  Ganin taki fitowa ya ruko hannun ta ya fitoh da ita sukai hanyar shiga gate din sai da suka iso bakin gate din ya sake mata hannun, yace lets go shiya fara shiga tana bayan shi.

   Daddy dake zaune ya taso tini tayi hanyar fita waje jin an rike hannun ta yasa ta kasa motsi, a hankali ya jata suka je suka zauna, daddy ma ya zauna, gaida daddy yayi ya amsa.

   A hankali ta karasa wurin daddy ta rike kafar shi tana kuka tana rokon shi yayi hakuri, kuka take sosai ganin hakan yasa daddy ya dagota saman kujerar ya zaunar da ita yace tayi shiru.

  Shiru tayi yace maha mai yasa baki ji, daddy Allah ruwa naje siyowa, inma yawo zaki tafi basai ki tafi ke kadai ba amma ki dau yar mutane kin tafi da ita kin daga musu hankali, daddy zan basu hakuri Allah, mtssss yace huce kije ki huta.

   Daki ta huce daddy kuma yace wa AA suyi hakuri please yarinyar bata ji, ai babu komai dama cewa nayi bara na kawo ta sai mu gaisa da mamie.

  Okay bara a kira ta, a waya ya kira ta ta fitoh suka gaisa nan itama ta basu hakuri, babu komai wallahi ai duk daya ne, daga haka ya musu sallama ya tafi, daga daddy har mamie babu wanda yabi ta kanta.

  Sai after isha huda takai mata abinci kadan taci ta kwanta.

  Tunda ya koma gida mom ta tambaye shi ina maha yace ya maida ta gidan su nan yace wai maman ta tace kuyi hakuri, ai babu komai yanzu kazo kaci abinci, not now mom ya tashi ya huce daki.

  Saida ya kwanta yaji duk kamshin ta ya cika mishi hanci dan dole ya tashi ya cire kayan, but how did this happen mai kamshin turaren ta kayi a kayan shi lokaci daya ya tuno da yayi hugging nata dazu fa ashe, ajiyar zuciya ya sauke dan sanda yayi hugging nata shi kadai yasan abinda yaji.

  Yau two days kenan maha babu inda taje tun washe garin ranar data bawa daddy hakuri kuma ta mishi promise baza ta sake ba ta daina fita ko palo saidai abu tazo dauka, ba tsoron fita take ba AA ne bata son haduwa da.

  AA tun ranar yake baza ido dan yagan ta amma babu ita babu labarin ta harya hakura gashi yaji munawwar na cewa gobe zasu tafi.

   Aiko washe gari suka tafi da safe, tunda suka sauka nigeria taji sanyi a ranta, waka tayi tana zaune dakin gado huda ta shigo ta fada mata daddy na neman ta, koda taje nasiha ya mata sosai yace ta daina abinda take yanzu fa ta girma.

  Nan ya ringa janta da hira har saida ta sake,har akai sallar magriba. 

   Haka rayuwa taci gaba yau monday ta shiya ta tafi office abin ta dan tayi alkawarin ta daina rashin ji, tana zaune aka bude kofar office din daga kan daza tai sukai ido hudu.

   Bai taba tsamanin ganin ta a office din ba, shiga yayi ya zauna a hankali tace good morning, sai daya dau second sannan yace morning daga nan babu wanda ya kuma magana.

   Ana tashi ta huce gida abinta, haka suka ci gaba da rayuwa bata rashin ji kuma ta daina shiga harkar AA tun ranar daya yi hugging dinta dan bata yarda da shi ba yanzu, yanzu zuwa office din dadi ya mata dan yayi tafiya kusan two month back.

  Kamar kullun yau sunday suna zaune a palo suna hira akai sallama da sauri ta daga kai jin muryar mai sallamar, tashi tayi ta taro su ta basu wurin suka zauna, mom munawwar ta gaida munawwar ta gaida ta itama.

   Nan ta tafi ta dauko musu drinks koda ta ajiye mamie ta tafi kira, da fara’a mamie ta sauko suka gaisa, mom munawwar tace mamie gata nan ta takura mini wai a kawo ta wurin maha da huda, murmushi mamie tayi tace gaskiyya ne kinyi abin arziki da kika kawo ta amma yini kuka zo mana.
  
   Aa nidai mamie tafiya zanyi anjima azo a dauke ta dama haka nace barina zo mu gaisa, toh nagode kuwa Allah yayi albarka bata jima ba ta tafi.

   Nan su munawwar sukayi daki labarai kala kala suka ringa dawo juna dan ita maha babu ruwan ta data girme ka koma waye zata zauna tayi hira dashi.

   Kasar uk kuwa yana zaune ne amma kwata kwata bai jin dadi zaman ya rasa maike damun shi sometimes he just wants to see maha but know way, basai meke damun shiba dan wani lokacin haushin kanshi yake ji, kamar kullun yana zaune a office din shi jazz ya kira shi.

  Hello jazz ya kake, I’m good AA and you, Alhamdulillah, Masha Allah shiru ne ya biyo baya sannan jazz yace amm AA when are you coming back kasan fa yarinyar nan ta kusa gama abinda ya kawo ta, which girl, my student.

   Shiru yayi dan shi ya manta da abunda ya kawo ta kwata kwata a tunanin shi she will be there forever, AA, sorry jazzz I will be back soon, okay Allah ya dawo da kai lafiya nan suka dauko wata hirar.

    Koda ya gama waya da jazz gida ya huce yana tunanin abinda jazz yace mishi, wai yanzu tafiya zatai da gaske, toh yaushe tazo ma da, ohhh but I need her closer to me haka yayi ta tunanin har yaje gida.

   Ranar sunday ya dawo nigeria shida su samir mom munawwar ce ta taro su kusan mota takwas sukai nan ya ringa makale wa mom.

 Duk da suka tambayi mom munawwar ina munawwar tace ai tun safe ta kai ta gidan su maha, jin an kira sunan maha yasa ya dago shi yanzu tunanin shi ina zai ganta a zuciya yace toh idan na ganta mai zan mata mtssss.

  Sai dare mom munawwar tazo ta dauke ta suka tafi gida nan take cewa ai su samir sun dawo, sosai munawwar tayi farin ciki dan kamar yayanin suke a wurin ta idan basa kasar bata jin dadin zama ita kadai ce a gidan su.

   Yau ma kamar kullun tun 7:40 taje office din, tana zaune wurin 10:00 taji an bude door din, rubutun da take yasa bata dago ba tana zaune kan sofe ganin shirun yayi yawa bata ji anyi magana ba yasa ta dago.

  Tunda ya shigo kallan ta yake yacce take zaune da yacce take rubutun duk saiya sa jikin shi yayi sanyi yayi nisa cikin kallon ta yaga ta dago.

   Da sauri ta tashi tace good morning sir, bai amsa ba sai takowa gaban ta da yayi, dab da ita ya tsaya wanda kadan ya rage ya shige jikin ta kasa tayi da kanta ta juya zata bar wurin kawai taji ya rike hannun ta.

  Da sauri ta juyo zatai magana yasa dan yatsa daya daga dayan hannun shi yace shiiiii, tuni idon ta sun ciko da kwalla, tana rufe su kuwa sai gashi kwallar ta zubo.

  Shi dai kallan ta kawai yake ya kasa dauke kai gani kukan take da gaske yasa yayi hugging din ta, nan ta fara kokarin barin jikin shi amma ta kasa because they is different between girls and boys.

   A hankali yace fatima, shiru tayi dajin sunan daya kira ta dashi, stop crying please kinji, cikin muryar kuka tace I don’t want this, murmushi yayi yace the hug kai ta daga mishi, yace okay shikenan a hankali ya raba ta da jikin shi.

  Yana rike da kafadar ta yace is that okay, kai ta girgiza mishi cire hannun shi yayi yace is this okay, kai ta daga mishi, okay shikenan I don’t want to see those tears, a hankali ta fara goge hawayen.

  Hucewa yayi ya zauna a site din shi yana kallan ta, saida ta dau minute san ta juya ta huce site din ta ta juya mishi baya, shi dai kallan ta kawai yake.

  Daura kanta tayi kan table din kusan 30 minutes kawai yaji saukar agiyar zuciya da alama bacci take, bari yayi saida ta kara minutes sannan yaje ya dauke ta kamar baby ya kwantar akan sofe din office din.

  Fita yayi yace wa PA din shi kar wanda ya shigar mai office, bayan kusan two hours ya dawo har lokacin bata tashi ba, zama yayi yana kallan yace take bacci kamar baby.

  Saida ya kara kusan 20 minutes sannan yaga ta fara motsi da sauri yaje gaban sofe din ya tsugunna dan tsaf zata iya fadowa aiko tana kuma juyi taji ta a jikin mutun.

  Wani kara ta saki wanda yasa shi rufe idon shi da sauri ta tashi zaune ta fashe da kuka, jin kukan na shigar mishi kai ne yasa ya zauna gefen ta ya ruko hannun ta.

  Stop crying please ni babu abinda na miki i see zaki fadi ne shine na tare ki maha babu abinda na miki fa, kai ta girgiza mishi, what’s it, ni wurin mamie zanje, kawai kallan ta yake nayan second sannan yace okay Zakije amma in kin daina kuka.

  Kai ta daga mishi alamar ta dai, saida ya dau wasu lokaci sannan ya tashi yace I’m waiting for you outside, no baba zan kira, dawo wa yayi ya zauna, sai tayi saurin matsawa daga kusa dashi.

  Tashi yayi ya tashe ta a kausassar murya yace pack your things now, haka ta hada kayan ta yaja hannun ta ya fice a office din, ganin mutane na kallan su yasa tace sir please live my hand, a hankali yace wallahi idan baki mini shiru ba i will pick you up.

  Sir, I mean it try me and see, ganin yacce yayi maganar tasan zai aikata dan haka tayi shiru koda suka sauko idon mutane duk a kansu haka ya jata har packing space, suna isa aka bude musu motar suka shiga.

   Direct gida yasa aka kaita yace tawa mamie magana zai shigo su gaisa, saida ta fita ta leko ta window tace ai ba gidan ku bane tayi saurin shegewa palon,tana shiga ma’ash na kokarin fitoh wa.

  Ke daga ina, work ta huce sama direct daki ta tafi ta kulle, ta huce toilet dan tayi wanka because of kamshin turaren shi daya dame ta.

  Tunda ta tafi yabi ta da kallo harta shige bai daina kallan door din ba kamar zai ganta a ciki saiga ma’ash ya fitoh da yake window din a bude yake yasa ma’ash ganin shi da sauri yazo suka gaisa.

  Big bro dama tare kuke, kai ya daga mishi, shine ta barka a waje, no ni nace bazan shiga ba, aa gaskiyya ya kamata ka shigo ai please kaji, murmushi yayi yace tam.

  Nan ma’ash yace mishi masallaci zaije shi sai lokacin ya tino shima bai sallar ba, tare suka je sukai salla suka dawo.

  Maha koda ta fitoh daga wanka wasu riga da wando ta saka dan yau daddy bai nan, aiko tana fitowa taga mamie a zaune a palo nan taje ta kwanta akan cinyar ta.

  Mamie tace yaushe kika dawo, yanzu tana turo baki tace mamie Allah kaina na ciwo kuma na gaji da kitson nan, sabule hular kanta mamie tayi tace ki tsefe anjima kuje saloon idan huda ta dawo.

  Turo baki tayi tace ni mamie Allah bazan iya ba daidai shigowar ma’ash da AA,taji karar bude kofar duk a tunanin ta ma’ash ne idon ta a rufe ta sake turo baki tace ya ma’ash zaka tsefe mini kai ko.

  Ban sani ba, baki ta turo tana tashi tsaye tace toh shikenan ni maganar ta ta tsaya lokacin data ga AA a tsaye yana kallan ta, ai da gudu ta huce sama.

  Mtssss mamie tayi tsaki, tace Allah ya shirye ki maha ta kalli AA da yayi kasa da kanshi tace son ka zauna mana, zama yayi yana gaida ta ta amsa da fara’a nan ta tambaye shi yaushe ya dawo dan maha ta fada mata bai nan.
 
  Yace ai jiya suka dawo dasu samir, okay Allah sarki, maha ta taso ka rana tsaka ko, murmushi yayi yace ba komai mamie ai tace kanta ke ciwo, eh haka tace mini, ma’ash yace iskanci dai kawai bata son zaman office dinne.

  Nan suka danyi hira nan mamie ta zaunar dashi tace saiya ci abinci, ganin yaki sakewa tacewa ma’ash suje part dinsu yanzu zata bawa maha ta kawo, nan suka tafi.

  Saida ta hade abinci sannan taje ta kira maha tace ta kaiwa ma’ash abinci, dauka tayi ta tafi tana mita toh akan me bazai ci acan ba aikin banza kawai salon asa mutun aiki.

  Batai knocking ba ta shiga tana cewa ya ma’ash yanzu tsakani da Allah yau maiya hana ka cin abinci a part din mamie salan kawai nazo kawo maka abinci na hadu da wannan mugun yayan naka.

  Wallahi babu ruwana yana daki yana jinki, toh ni ga abincin tana turo baki, ai ba nawa bane na ogan kine kije kiyi serving nashi, mtssss wana ogan kuma ya ma’ash.

  AA ya nuna mata da hannun wanda tunda ta shigo yake kallan ta harta kai abinci dinning area ta dawo, kittt taji zuciyar ta ta tsaya, maganar da ma’ash ke mata ne ya dawo mata da hankalin ta.

  Kije kiyi servin nashi bara naje na dawo, ya ai kafin ta karasa ya shige daki,mike wa yayi yazo gaban ta a hankali yace ai ba gidan ku bane ko yayi murmushi yace ko abincin ma bana gidan mu bane.

  Ni fa bada kai nake ba, toh muje kiyi serving dina I’m hungry, baki ta turo tace ban iya ba, hannun ta yaja yayi dinning area din, mamie, kai maha I’m your mate mutane zaki tara mini.

  Baki ta murguda mishi, ohh yau a gabana kike murguda min baki ko i will punish you zaki zo gidan mu muma, shiru tayi bata kula shiba yaje ya zauna.

  Sai da taji dama sannan ta zuba mishi abinci shidai kallan ta kawai yake, tana gama zuba mishi ta juya zata tafi, janyo ta yayi sai gata a kan cinyar shi zata saka mishi ihu ya toshe bakin.

  Ido ta zaro tana girgiza mishi kai, hade fuska yayi yace haka ake bawa bako abinci, kai ta girgiza hannun shi ya cire da sauri tace sir please Allah ya ma’ash zai fitoh, and so.

  Kokarin tashi tayi ya sa hannun shi ta wrist dinta ya rike ta sosai, sir please dan Allah wallahi bazan sake ba, kin mini laifi ne, kai ta daga, what it’s, nace ba gidan ku bane, ummhmm, Allah shikenan, kin tabbata, eh.

  I want to punish you, dan Allah kayi hakuri please, last time ba kince kinyi promises baza ki sake ba, kuka ta fara kasa kasa, banson kukan nan fa it hurts me.

  Please kayi hakuri sir, okay stop crying lets eat the lunch, sir I’m not hungry bacci zanyi,yanzun kai ta daga mishi, oya stand up tashi tayi daga kanshi sannan yace have a sit yana nuna mata kujerar gefan shi, zama tayi.

  Abincin shi yake ci hankali kwance, ita dai bata ce komai ba ma’ash ne ya shigo yana cewa ai kina nan kina mishi surutu ko, murmushi yayi yace aa ai sister ka bata son mini magana, kaiii maha dama duk surutun naki na banza ne.

  Baki ta turo tace ya ma’ash a shagobe, na’am baby maha autar mamie nima zuba min abinci, hannuna ciwo yake ta murguda mishi baki, murmushi yayi yace sorry zan taya ki tsifar, promise, yes.

  Tashi tayi ta zuba mishi abincin sannan tace ta tafi, baza ki tsaya ki taya mu hira ba, ya zanyi bacci, ai kin kenan juyawa tayi ta tafi abin ta.

   Koda ta koma mamie tace mai na zuwa ki zauna, mamie fa kinga huce ki bani wurin ni bansan sanda za kiyi hankali ba wallahi kuma daga yau karna sake ganin ki da shigar dazu you not a small girl maha yanzu gashi kinji kunya a gaban mutane kuma mai ma kon ki gara zaman ki sai kika kwasa a guje wai nikam yaushe za kiyi hankali maha.

 Ke gudu bai miki wuya kodan kin ganki yar kucila eh maha you’re know 22 fa haba maha behave like a girl mana maha please ki daina inba haka ba i will tell daddy, mamie Allah zafi ne yasa nayi haka amma bazan sake ba in sha Allah.

  Inma za kiyi kije can dakin ki kiyi ko ance dole sai kin fitoh ne, aa mamie AC nane ya lalace fa, ohh baki san AC ya lalace ba sai yau, Allah mamie, naji huce ki bani wuri, tam mamie naje dakin ki, ban sani bah da da kike zuwa tambaya ta kike.

  Hucewa tayi ta tafi dakin mamie ta kwanta abin ta, sai bayan la’asar huda tazo ta tashe ta, ya maha ki tashi kiyi sallah muje kitson, tashi tayi tayi sallah taci abinci.

   Mamie sukai wa sallah sannan tace suje ma’ash ya kaisu, tafiya sukai huda taco barina jira ki a can, knocking daya aka bata izinin shigowa.

   Da sallama ta shiga ma’ash ne da samir da AA sai sa’ad gaida su tayi sa’ad yace ya akai, baki ta turo tace ni fah ba wurin ka nazo ba ya ma’ash mamie tace ka kaimu saloon, tsifar fa, idan naje za’a mini.

  Ina hudan, tana waje, baza ki iya kaiku ba, daddy ya hana ni driving, ai ba yawo zaki ba huce ki dauko key din akan mirror, hucewa tayi ta dauko.

  Samir ne yace dama ta iya driving, eh mana, AA shi mamaki abin ya bashi yanzu wannan mai rawar kan zai bawa key kuma bayan tace daddy ya hana ta.

  Yana wannan tunanin yaji tace ya ma’ash bye, samir yace shi kadai kika sani, aa ya samir bye, ma’ash yace su kuma big bros fa, ko kallan su batai ba tace ya ma’ash, na’am.

  Shiru tayi, maye, kazo kaji, no zoki fada mini, zuwa tayi daidai kunnan shi, mtssss saikin tambaye ni kije ki dauka mana, murmushi tayi tace thank you my lovely brother, sa’ad yace haka dai abu kamar pencil.

  Ya sa’ad Allah daddy yace ka daina ce mini pencil, murmushi yayi kawai dakin ta koma ta fitoh ta tafi.

  Koda suka dawo su samir sun tafi nan mamie tace kin samu mota shine kika tafi yawo ko, aa mamie kawai shopping muka je, ai shikenan.

  Koda ya ma’ash ya dawo ta bashi key din shi da ATM dinshi ta mishi godiya.

  Washe gari ta tashi da ciwon mara dan ko aiki bata iya zuwa ba the next day ma haka bata jeba sai ranar alhamis ta koma babu yacce mamie batai da ita ba akan karta je dan bata da lafiya amma tace ita ta gaji da zaman gida, da wuri taje lokacin baizo ba. 

  He was really missing her but he doesn’t way, baizo office din ba sai around 9:40 shiga yayi kai tsaye dan bai taba tsamma nin zuwan taba daidai lokacin da take gara veil dinta rabin gashin ta daya sha gara a bude.

  Da sauri taja veil din ta rufe kan ta, sai ta daga kai taga waye ya shigo, ba shiru tayi kasa da kanta ganin kallon da yake mata saida ya dau minuets yana kallon ta sannan ya taki cikin office din.

  Ganin gurin ta yayi yasa gaban ta faduwa har ya kara so idon shi a kan ta, a hankali tace good morning, bai amsa mata ba saima hannun shi daya kai ya cire veil din kanta, nan bugun zuciyar ta ya karu.

  Saida ya kallan kan yace yaga dama sannan yace mai yasa baki zuwa work yana rufe mata gashin, a hankali tace I’m having headache, really, kai ta daga mishi, but baki fada mini ba ai.

  Shiru tayi ganin bata da niyar magana yace tun yaushe baki da lafiya, the day you came home, have you visit doctor, kai ta girgiza mishi, way, I’m okay, no you have to.

  Sir I’m ok, let’s go, shiru tayi taki tashi, hannun shi yakai zai taba ta ta fashe da kuka sir Allah I’m okay idan naje allura zasu mini shiru yayi yana kallan ta can yace kina tsoron allura, aa, oya let’s go.
  
   Sir please Allah i take drugs, zama yayi kan table din yana kallan ta sannan yace okay shikenan it’s okay, kai ta daga mishi still hawaye na bun fuskar ta, what about the tears kai ta girgiza mishi.

  Ya dau minutes sannan yace as from today idan kinzo office I’m not here kina sa key a door din, kallan shi tayi alamar mai yasa, yanzu da wanine ya shigo kina gara veil din fa, shiru tayi, do as i say, kai ta daga mishi.
 
   Okay let’s go we’re having meeting, tashi tayi yaga tadan tsaya, are you okay, kai ta daga mishi, no you’re not ya rike hannun ta ya jata suka huce kan sofe suka zauna, tell me meke miki ciwo, kai ta girgiza, no say it i will not take you anyway i promise.

  Kai ta girgiza mishi ganin yacce tasa hannun ta a gefen cikin ta yasa ya gane nan ke mata ciwo a hankali ya kai hannun shi kan nata yace it pains you, shiru tayi, answer me, kai ta daga mishi, let’s visit doctor fatima.

  No banso, baza a miki allura ba fa, sir Allah i take drugs, okay let’s get back home, aa, way, it pains me more they, kallan ta yayi tace when I get home nasan kwanciya zanyi and it can cause fever.

  Da hannun ya matsa wurin ta rufe idon ta tace ashh, it hurts you, kai ta da mishi, let’s me get some water for you, ruwa ya dauko a frige mai sanyi ya kawo mata, kai ta girgiza tace i can’t take it it’s too cold.

   Kallan ta yayi na seconds sannan yace are you on your period, shiru tayi murmushi yayi sannan yake tunanin tambayar daya mata juyawa yayi ya hado mata coffee ya kawo mata bata karba ba ya zauna yace have it.

 Gannin zata bata mishi lokaci ga meeting dazai shiga yasa ya kamo hannun ta yasa a ciki yace mata ya tafi meeting yana fita PA dinshi ya turo ta dauko mishi takardun shi ta kai mai.

  Koda suka fitoh a kwance yazo ya same ta direct inda take yayi a tunanin shi bacci take sai yaga tana kuka, tsugunnawa yayi a hankali yace it still pain you, shiru tayi gannin haka yasa ya kira driver sa yace yazo da mota daidai kofar shigowa.

  Dawowa inda take yayi yace let’s go, sir please kafin ta karasa taji ya daga ta, kai ta fara girgiza mishi baibi ta kanta ba ya kama hannun ta suka fice nan yace PA din shi ta dauko mishi bag and phone nata.

  Lokacin da suka sauko driver nazo dan haka ya bude musu motar suka shiga, PA din shi na kawo kayan suka huce asibiti, har suka je bai saki hannun ta ba ita kadai tasan abinda ke mata ciwo.

  Suna isa aka fara duba ta bai bari doctor namiji ya taba taba yana cikin room din, madam za’a miki wannan allurar zata sa ciwon ya ragu, no ki bani magani, bata da magana allura ce kawai, ku banni da ciwo na.

  Ganin da gaske take yasa ya matsa wurin, sir kace you promise baza’a mini allura ba fa, hannun rigar ta ya nanna de yace wa nurse din tazo ta mata, sir please no dan Allah sir please, rungumai ta yayi ya rike hannun sosai hakan ya bawa nurse din damar mata allurar.

  Tana gamawa ta fice abinta sosai take kuka shiru yayi bai sake ta ba kuma bai hana ta kukan ba, saida ta dau minute tana kuka sannan ya raba ta da jikin shi ya zauna gefen ta.

  A hankali yace fatima I’m sorry i don’t have choice but it’s good for your health please stop crying ya fara goge mata hawayen, cikin kuka tace I want to go home, okay but sai doctor sun gama duba ki kinji, shiru tayi kukan ma ta daina.

  Suna zaune a haka likitan data duba ta ta shigo, kallan ta yayi alamar meke damun ta, sir she needs blood cause nata yayi kasa da yawa, okay ba matsala you can have mine it’s O- okay bara na shirya wurin ta fita.

  Doctor din na fita tace wallahi she’s lied i don’t need any blood ni banso, murmushi yayi yace blood dinne baki so ko kuma nawa ne baki so, shiru tayi, baki son nawa ko, yana kallan ta yaji doctor din tace sir are you ready, bai bata amsa ba sai tashi da yayi ta fice yabi bayan ta.

  Koda aka dauka saida ya huta kusan one hour sannan ya tafi dakin da take bacci take hankali ta kwance ta kudun dine da alama sanyi take ji, zuwa yayi ya rufe ta da bargon dake kan gadon yaja kujera ya zauna yana kallan ta.

  Sai yanzu yaga yar ramar da tayi gashi tayi wani fari sosai,yana cikin kallan ta yaji wayan shi na ringing kallo daya ya mata ya daga yasa ta a speaker, hello ya AA, yes samir, amm dama wai maha ce ake ta neman ta kuma ana ta kiran wayar ta bata daga ba.

  Shiru yayi baice komai ba, kuma mamie tace bata da lafiya shine tace a tambaye ka ko tazo office, yes she’s here with me muna hospital, hospital ya wane hospital, i will send the address and ka turo mini number mamie, okay bara na fada mata dan tun dazu a rude take.

  Mom dake gefen samir taji duk abinda ya faru kawai dai tace Allah ya bata lafiya ta huce daki, samir ma’ash ya kira ya fada mishi sannan ya turawa AA number mamie.

  Yana gannin number ya kira, da sallama ta daga, saida ya daidai ta kansa sannan yace mamie ina yini, lafiya lau, amm mamie AA ne, okay Allah sarki ya aiki, Alhamdulillah mamie dan Allah kiyi hakuri ban kira na sanar daku ba har kuka tashi hankalin ku, murmushi manya tayi tace ba komai AA ai kaima maha kwanwa kace.

  Yaji dadin hakan nan yace tam mamie na gode Allah ya kara girma, Ameen ai samir ya turo mana address din yanzu zanzo in sha Allah, aa mamie basai kunzo ba yanzu zamu dawo dama jini ne aka saka mata, what jini kuma sai tayi shiru.

  Eh mamie dan Allah basai kinzo ba yanzu   zai kare saina kawo ta, amma AA ai wahalar tayi yawa, aa mamie ba komai wallahi, tam shikenan yanzu tana ina, mamie bacci take, okay sai kun dawo.

Ko 30m bata kara ba ta tashi, a hankali take bude idon ta ta sauke su akan shi ya jingi na da kujera idon shi a rufe, tabe baki tayi a shagobe sai kuma ta kalli ledar jinin sai tayi kamar za tayi kuka.

  Duk abinda take yana kallan ta ta kasan ido, a hankali take kokarin tashi dan haka ya bude idon shi a kanta, ganin kallon da yake mata yasa ta fasa tashi ta juya mishi baya, murmushi yayi ya tashi ya daga ta zaune, ashh tace.

  Kallan ta yayi yace raguwa kawai, baki ta turo tace water, banza yayi da ita ya zauna, ganin baza ta sake tambaya ba yasa ya tashi dan kanshi ya dauko mata ruwan ya mika mata, ko kallan shi batai ba budewa yayi yace have it.

  Baki ta turo tace banso, murmushi yayi yace sorry beauty have it kinji, ganin da gaske take baza tasha ba yasa ya dawo inda ta juya fuskar ta yace I’m sorry, zata juya ya rike fuskar yace fatima i said I’m sorry, duk abinda suke akan idon samir dake musu video tun sanda ya tashi dan ya bata ruwa.

  Baki ta bude a hankali tace ya samir da sauri ya juya amma baiga kowa ba dan tuni samir ya fice,juyowa yayi yace way did you see samir, shiru tayi,gorar ruwan yakai bakin ta yace take it.

  A hankali tasha ruwan saida ta girgiza mishi kai sannan ya dauke robar ruwan, sir kace su cire mini, mai yasa, baki ta turo, jinin nawa za’a zubar, banza ta mishi tashe yayi zai fita tace sir i want to use toilet, bai amsa mata ba ya fice.

  Wata nurse ya turo ta cire mata sannan ya huce masallaci koda aka idar da salla mota yaje ya dauko mata wayar ta sannan ya dawo lokacin an maida mata da sallama ya shigo.

  Bata kula shiba har yazo ya zauna a gaban ta, karan da wayar ta yayi yasa ta juyo ta kalle shi, wayar ya kurawa ido ganin mai kiran da alama boyfriend dinta ne tayi saving da soulmate.
 
  Bata kula shiba ta juya dan kanshi ya miko mata wayar bata daga ba itama kira aka kuma yi a hankali yace pick the call, shiru tayi mishi dan haka ya karbi wayar yayi picking yasa a speaker.

  Baby please I’m sorry dan Allah maha wallahi i can’t life with out you na gane kuskure na baby kiyi magana please kusan one week ina kiran ki amma baki picking dan Allah maha.

   Bata ce komai ba sai kallan wayar da take hawaye na bin fuskar ta shi kuma ita yake kallo, maha aka fada daga cikin wayar, naji nayi kuskure kuma na gane dan Allah kiyi magana wallahi i will not tread your brother like that again i promise.

  Maha wallahi i love you and I will call ma’ash and apologize maha wallahi i have change kittt ya kashe wayar, juyawa tayi tasa kuka mai cin rai, saida tadau minutes tana kukan sannan ya tashi ya dawo side din data juya kanta yana kallan ta.

  A hankali yace mu tafi gida, kai ta daga mishi okay daina kuka, nan ma kai ta daga mishi, goge mata hawayen yayi yace sit, zama tayi ya zauna gefen ta ya rike hannun ta saida ya kalle ta na second sannan yace way are you always crying fatima.

   Shiru tayi, rigima ko shi yasa komai aka miki kina kuka and you know it’s not good for your health, nan ma shiru tayi, okay yanzu fada mini who’s he your boyfriend, fatima I’m talking to you.

  Kai ta daga mishi, kina son shi kai ta girgiza mishi, way, he was a bad guy, waya fada miki, ya ma’ash, how did he know, a school dinsu yake daga nan aka koro shi, mai yayi, yana shan drugs and alcohol kuma yayi raped a girl.

  Kallan ta yayi ganin hawayen da yake zubo mata yace fatima you love him, kai ta girgiza, before, kai ta daga, okay is okay daina kuka Allah will replace him with a better person in sha Allah.

  A hankali tace thank you sir, banson sir call me AA, shiru tayi, let me call the nurse ya mike ya fita, bai jima ba ya dawo da nurse din, sai ai bai kare ba saura kadan, just remove it, okay sir.

  Tana cirewa yace ta kira doctor din, inda take yazo ya tsaya da inda yake miki ciwo, a hankali tace aa, yana tsaye yana kallan ta fuskar ta duk tayi ja sosai a haka doctor din ta shigo.

  Duba ta tayi ta mata tambayoyi sannan ta rubuta mata magani tace shikenan babu wata matsala zasu iya tafiya, doctor din ce ta kama ta har mota yana biye dasu sannan ta koma bayan ya bata abin arziki.

   Samir yana komawa gida direct dakin mom ya tafi tana zaune ita da basma da sara sai kuyangar ta mom mom yake ta kiran ta, samir what it’s, murmushi yayi Yana zama gefen ta yace mom your son is in love.
  
   Duk kallan shi sukai da mamaki mom tace lallai samir abun naka gaba yake ni zaka zo kana cewa you’re in love, mom not me fa i mean ya  AA, what duk suka ce video ya kunna mata suka gani.