RASHIN SANI

TSAKURE

by @sumy6163

💫RASHIN SANI... 💫

STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic).

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).

Godiya mai tarin yawa tare da jinjina ga 'yan' uwa marubuta da suka karfafa mini gwiwa wurin yin wannan rubutu, Allah ya Saka musu da alkairi ya kara daukaka su.

Wannan labari kirkirarre ne, idan yayi kama da rayuwar wani ko wata, to arashi ne.

TSAKURE.

Yini ne mai cike da rana mai tsananin zafi,wanda alamu suke nuni da gaf ake da samun ruwan sama duba da yanayin garin. kasancewa ana cikin farko-farkon damuna.

Tafe suke tana rike dashi a wahalce cike da gajiya yunwa gami da ƙishirwa ga kuma nauyin shi da ya sakar mata, wani numfashi taja tare da tunanin ya kamata su dan huta, wuri ta samu kasan wata bishiya ta ajiye shi don su dan huta kafin su ci gaba da tafi ya, ta samu gefen shi ta zauna tana sauke numfashi a gajiye.

Juyawa tayi ta kalli gefen da yake kwance a take hawayen tausayin shi da kanta ya shiga zubo mata, hannu ta daga sama tana mai addu'an Allah ya kawo musu agaji cikin gaggawa.

Duba gabas da yamma ta yi ko zata hango inda zata samu ruwa amma bata ga alama ba, a take ta yanke hukuncin bari ta dan zaga ko Allah zai sa ta samo ruwan ko dan wani abu da zata ci.

A hankali ta juya gefen da yake kwance ta dube shi bai ma san inda kanshi yake ba,sai ta mike tare da fadin.

"Allah ga amanan bawanka nan na bar maka ka kular min dashi, ka tsare shi da tsarewarka ya Allah har in dawo."

Tana gama addu'ar ta ta juya ta fara tafiya.

Sai da ta yi tafiya mai nisa bata ga alamun akwai inda zata samu ruwa ba har ta gaji, tayi tunanin bari ta dawo kawai sanin a halin da ta barshi.

Ta na kan hanyar dawowa ne taci karo da bishiyar magarya ta zuba 'ya'ya, tsayawa ta yi ta tsinta ta zuba a ɗankwalin ta, ta ci gaba da tafiya har ta dawo inda ta barshi, yanda ta barshi kuwa haka ta same shi a kwance, shafa fuskan shi tayi tare da fadin.

"Allah ya baka lafiya."

Magaryan nan ta dauka ta fara ci duk da babu ruwa haka tayi ta turawa har sanda taji ya isheta tukun ta ajiye sauran, gefen shi ta samu ta dan kwanta tana mai kallon kyakkyawan fuskan shi, tana haka har wani baccin wahala ya dauke ta a wurin ba tare da ta sani ba.

~~~~~~~~~~

Wata hamshakiyar mata ce a zaune cikin wani kayataccen parlour, kai da gani kasan kudi sunyi kuka a nan,dika-dika baza ta wuce irin shekara 35 ba don ba wata babba bace, sanye take cikin wani tsadajjen leshi, a yayin da wuyan ta da kunnuwanta kuma sun sha setin gold hade da hannun ta na dama, dayan hannun kuma wani agogo ne mai tsada na silver,tana cikin matan dake da matsakaici kyau, gefen ta fruit ne a cikin wani bowl mai kyau tana dauka da fork tana ci lokaci zuwa lokaci, rike take da wayanta a dayan hannun tana daddannawa, ta kusa minti shabiyar kafin ta kammala abunda take yi ta dago tare da gyara zaman ta.

Duban ta takai zuwa kan wasu samudawa dake tsaye a parlour masu mummunan kama, da ganin su babu digon imani a zuciyar su, magana tayi wa dayan wanda da alama shine shugaban su.

"kai Tijara me kake fada ne don ban fahimce ka ba,"

"Allah ya taimaki hajiya aikin nan gaskiya bai yiwu ba don ko a sanda muka shiga gidan ba kowa, amma dai da alama sun bi ta kofar baya ne suka gudu."

"To uban wa ya hanaku bin kofar bayan ku cin musu ku kaddamar musu a a can!,"

Ta yi sauri. katse shi cikin tsawa kamar mai magana da d'anta,rusunar da kai yayi tare da fadin,

"Allah ya huci ran hajiya, mun bisu amma bamu same su ba sakamakon sawun su ya bace,"

"kar ka gaya min maganan banza,"

Ta sake fadi a tsawace,

"Abu daya nake da bukata, duk inda suka shiga ku nemo min su, ko a mace ko a raye, ku fice ku ban wuri."

"Allah ya huci zuciyan ki ranki shi dade, zamu kokarta"

Ya fada tare da ficewa sauran yaran shi suna take masa baya.

~~~~~~~~~

A nutse dattijuwar take zaune saman abun sallah, hannayenta ta daga sama tana addu'a tare da zubda kwalla da ganin ta kasan tana cikin damuwa.

"Ya Allah kaine ubangijin mu mai share mana kukan mu, ya Allah bani da wani gata sai kai, kai kace mu roke ka zaka amsa mana, ya Allah ga baiwarka nan mai yawan zunubai, na gurfana a gaban ka ina mai kaskantar da kai ya Allah 'ya' yana, ya Allah ka tsare su a duk inda suke, Allah ka kare su da kariyar ka ya Arrahmaan, ka tsare su daga sharrin duk wani abu mai cutarwa, Allah ka zama gatan su a duk inda suke, ya Allah ka sanya hijabi a tsakanin su da duk makiyan su, Allah ka tozarta duk mai hannu a cikin wannan lamari.

Fashewa tayi da kuka mai ban tausayi kafin taci gaba da jero addu'o'in ta, daga karshe ta shafa, ta dauko Al'qur'anin ta ta fara karantawa har zuwa lokacin da aka kira sallah, tashi tayi tayi nafilfili tare da raka'atanil fajr, kafin a tada sallah, ita ma tayi nata sallan, koda ta idar bata tashi a wurin ba har sai da ta gama azkar ɗinta na safe tare da addu'o'in ta kafin ta mike, fita waje tayi ta samu almajirai da kananan yara ta raba musu sadaka sannan ta dawo cikin gida.......