Chapter 3
Cikin rashin kuzari da rashin karkashi na jiki da na zuciya ya musu sallama, kafin ya saka kansa cikin parlorn…
Maimartaba ya amsa masa fara’a fal Fuskarsa don Mahmud yana d’aya daga cikin surikansa da yake matuk’ar alfaharin aura masa y’arsa, ba don yana da dukiya ko wani abu ba, aa sai don mutunmcinsa da yarda yake girmama su tamkar su suka haifeshi, ga shi ya rik’e musu y’a cikin kulawa da sauke mata duk wani nauyinta da yake kansa wanda shari’a ta wajbta masa da ma Ihsani wanda a karan kansa ya d’orawa kansa… Anna ma da fara’ar ta tarbeshi ita kuwa Zakiyya da wani irin sauri ta fa’da jikinsa cikin wani irin murna da farin ciki. Yana murmushi ya mata masauki a k’irjinsa kafin cikin kammalalliyar muryarsa ya ce “Kiyya Ba kya girma ne? 20yrs fa ba wasa ba.” Ta turo baki ka’dan alamar shagwab’a. Sai ya ‘dan ja hancinta yana murmushi ya furta “Am joking you are still a baby….ya School yaushe aka dawo? An kammala saura Nysc ko?” Ta ‘d’aga masa kanta kafin ta ja hannunsa ta furta “Ina Jadda, I have missed her alot, Abeey Zan je gida I like to see them…” Shiru ya yi yana d’an ja ajiyar zuciya kafin ya ja hannunta su zauna gaban Maimartaba ya isar da gaisuwarsa. Ya kuma juya ya gaishe da Anna bayan amsawar Maimartaba. Anna ta amsa tana furta “Gwara da Allah ya kawo ka, wannan yarinyar fa ta kafe sai ta je gida, me kuka shirya za ku gayawa Jaddan tata? Na san dai Jadda ba zata tab’a Jin da’din hakan ba wallahi.” Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya furta “Ni kaina sai yanzu duk abin ya dame ni Anna, sai nake jin kamar ba mu kyauta wa Jaddan ba.” “Don kyautawa fa Baku kyauta ba sam Mahmud, da na san kuma baku sanar da ita ba da tun lokacin ni zan gaya mata don ba zan biye shirmenku ba, to rashin sani duk ya ja haka, abu almost 13yrs ta yaya zaa mata bayanın da zata gamsu?” Maimartaba ya furta fuskarsa a d’an tsuke don tabbas bai sani ba a sanda ya sani kuma lokaci ya k’ure. Mahmud ya ji zufa ta fara zubo masa duk da sanyin na’urar sanyaya waje da take buzawa. Duk abin yazo masa wani iri ba wadda yake ji sai Jadda, bai san irin kallon da zata yiwa abin ba, ba mamaki ta yi zaton ko don ba ita ta haife shi ba, kalmar da sam baya son ya ji ta ratsa dodon kunnensa. “I have a solution…” Maimartaba ya fa’da idonsa a kan Mahmud ‘din yana jin tausayinsa shi kansa k’arfin hali zai yi ya tari Jadda da zancen. “Ka kawo min Jadda gobe, I will explained yarda zata fahimta, ba kuma zata zargeka ba, sai dai duk yarda za’a yi ka nuna baka son zancen ba, zan saka y’ata cikin masifa na sani ba mamaki Jadda ta tsaneta amma gwara nata akan naka daga baya na san duk zata saki, naka kuwa zai mata ciwo sosai.” Mahmud da sauri ya dago yana kallon Maimartaba kafin ya furta “Ranka ya da’de kada a yi haka, ka bar shi a yarda abin yake na san zata yi fushi amma bana son a ‘dorawa Gimbiya laifin…” Maimartaba ya girgiza kai “Ba zai zama matsala ba, zan d’orawa Kai na rabin laifin, a condition ‘din da Zakiyya take ciki a lokacin hakan kawai za’ayi a ceci rayuwarta daga wa’danda suke son su ga bayanta. Ka je ka taho da ita Allah yasa mu dace.” Mahmud ya ‘daga kai yana ‘dan sakin ajiyar zuciya. Kiyya dai na gefe ba abinda ya dameta ko me ma zai faru ya faru abu guda ta sani she want to go home cikin zuri’arta take son komawa ta gaji da zaman ka’daici ita dama can mai hayaniya ce mai son mutane ce ko zamanta a England ta yi shine cikin rashin son ta don dai ba yarda zata yi ne.
Jiki a salub’e Mahmud ya koma ZAWIYYA FAMILY MANSION. Ko part ‘d’insa bai shiga ya isa wajen JADDA a time ‘din da yake yamma ce tana cikin bedroom dinta tana Azkar ‘din yammaci. Ya yi sallama ya shiga ba tare da jiran ta amsa ba, don ya san a irin wannan lokacin da take addu’a bata katsewa ko menene sai dai a jira ta. Ya zauna gefenta yana d’an Danna counter da yake hannunsa, idonsa a kan Tv da ake hasko Tafsirin Sheikh Abdallah gadon k’aya a tashar Da’awa Tv. Sai da ta gama gaba d’aya sannan suka shafa addu’ar tare. Idanunta a zube a kansa bayan ta fahimci kamar yana cikin damuwa duk da k’ok’arin b’oye mata da yake. Ta san Mahmud gabansa da bayansa duk da bata haifeshi ba amma ta raineshi ta kuma shayar da shi daga ruwan madarar jikinta, akwai shak’uwa mai girman gaske tsakaninsu fiye da ta yaran da ta tsuguna ta haifa. “Auta me ya faru? Akwai damuwa ko?” Ta furta still idanunta na cigaba da gewaye fuskarsa, tana hango wancan Mahmud ‘din da yake yaro banda wannan da girma ya fara kama shi har da furfura da wancan ne ba mamaki da tuni ya fara hawaye cikin shagwab’a kuwa zai zayyane mata abinda ke damunsa.. Sosai ya yi k’ok’arin kawar da tsoro da damuwa da ke fuskarsa cikin farin cikin da ya aro ya ce “JADDA, akwai abin al’ajabi a can Bauchi, abin kuma ya girgiza ni, shine Maimartaba na tsorata da lamarin Ubangiji shine Maimartaba ya ce Na zo na tafi da ke akwai abinda zai nuna miki….” Jadda da kanta ya gama k’ullewa ta ce “Allah ya jishshemu alheri, don koma menene tunda ya saka damuwa to tabbas akwai wani abu..” Cak ya yi da numfashinsa yana addu’ar Allah yasa kada ta gano abinda suka shirya, a hankali ya furta Ameen ya kuma yi azamar mik’ewa ya bar ‘d’akin don baya son ta zurfafa kallonsa balle har ta hango abinda yake b’oyewa.
Sai da ya shiga parlorn Sashensa sannan wata nutsuwa tazo masa. Ya shiga yana kallon Gimbiyarsa da ta tasa Zuhair da Zuhaira a gaba tana koya musu karatun Alk’ur’ani. Farin ciki ya lullub’eshi. Ya zauna daga gefenta yana furta “Allah ya yi albarka Gimbeeya ta.” Ta ‘dan saki murmushi ka’dan kafin ta kai aya ta k’arshe cikin suratul Tauba, ta furta “Ku tashi ku je, zan saurari hadda gobe, Abeey ya dawo ban san abinda yasa ya dawo a wannan lokacin ba.” Zuhair da Zuhaira suka mik’e bayan sun mannawa Abeey ‘din kiss a gefe da gefen kumatu sun kuma furta “Welcome Abeey” ya ja hancinsu yana furta “Shukran Kids.” Suka shige can parlorn da Suka saba zama. Gimbiyar kuwa mik’ewa ta yi ta samo masa drink mai sanyi da snacks ta ajiye a gefensa sannan ta zuba masa ta kai bakinsa. Da hannunta ya ha’da ya sha idanunsa a kanta yana Jin wani irin farin ciki kamar yarda ya saba a duk sanda ya kalleta “Allah ya yi albarka Dear.” Ya ji kissing leb’enta a hankali. Murmushi Kawai ta saki tana Jan hannunsa tana matsawa cikin yanayin da ta tabbatar yana sauke masa duk wata gajiya da damuwar da ya Debo a waje. Balle yau da a cikin idanunsa ta hango damuwa. “Daga Bauchi nake, Zakiyya zata dawo gida gobe……” Wani irin juyawa hantar cikinta ta yi, ta yi saurin d’ago kai tana kallonsa ta furta “Abeey gida kuma?” Ya lumshe idonsa bayan ya saka soft hand d’insa a gefen wuyanta yana murzawa ka’dan “Zata dawo gida ta kafe tana son dawowa cikin ahalinta, and Maimartaba ya yi supporting dinta….” “Subhnallah…” ta furta a hankali tana Jin kanta yana wani irin sarawa a yanzu dai kam sam bata son Kiyya ta dawo gidan nan, tafi son idan ta yi aure ta dawo. Idan har ta dawo yanzu bata san abinda zai je ya dawo ba. “Abeey why not a Bari sai bayan ta yi aure…” Shiru ya yi yana kallon cikin idonta da suka fara tara hawayen damuwa. Bai san sanda ya jata jikinsa ba ya rungumeta sosai yana shafa bayanta a kunnenta ya ra’da mata “Just pray Gimbeeya, ba abinda zai faru In sha Allah….” Ta samu nutsuwa ka’dan daga tarin damuwar da take ciki, saboda yarda Mahmud ‘din ya dinga gaya mata kalaman da zasu kwantar mata da hankali. “
“Ina tsoro Gimbiya, ina tsoron Jadda ta kasa fahimtata ta juya min baya…” ya furta yana kallon Gimbiyar tasa bayan sun kammala cin abinci. Ta kalli yaransu tana furta a je a yi wanka a saka sleeping dress kowa ya tafi d’akinsa, ku kwanta ku yi barci a yi addu’a.” Suka mik’e şuna furta “Lailatan sa’eedan Abeey, Lailatan sa’eedan Mameey.” Shafa musu kai Suka yi Suka musu addu’a duk da sun fara girma har yau a k’ark’ashin kulawarsu suke. Suna wucewa ta juya tana kama hannayen Mahmud bayan ta shige jikinsa sosai, so take duk abinda zata gaya masa ya shiga zuciyarsa ya zauna don haka ta shiga murza hannunsa tana kallon cikin kwayar idanunsa. Full attention d’insa ya bata. “Ka nuna baka san komai ba Abeey, hakan shine kawai abinda zai saka Jadda ba zata ji haushinka ba, zan jingina laifin a kai na, na amince na ‘dau duk wani hukuncin Jadda akan na ga Jadda tana maka wani kallo daban….” Ta fa’da tana cigaba da murza hannunsa. Cikin mamaki ya dinga kallonta yana tunanin me yasa tunaninsu yazo ‘daya da na Maimartaba. Kasa shiru ya yi ya ce “Me yasa? Me yasa zaki jinginawa kanki laifi? Bayan da ni aka shirya komai?” Murmushi ta yi tana sake shiga jikinsa ta kwanta kamar mage kafin a hankali ta furta “Fushin da Jadda zata yi da kai zai fi muni akan wanda za ta yi da ni, Jadda zata kullaceka ta yi tunanin don ba ita ta haifeka ba ne shi yasa ka b’oye mata, kada ka manta irin tashin hankalin da ta shiga sanda aka sanar da ita mutuwar Zakiyya. Don haka ka nuna kawai baka san komai ba, just pretend as if kaima yanzu ka sani pls Habibi…” ya saki ajiyar zuciya yana manne bakinsa da nata hakan kawai zai yi ya huta da zazzafar k’aunarta da take keta masa jiki a hankali ya furta “Allah ya miki albarka Yar baiwa….” “Farin cikinka shine nawa Zaki na.”
****ZAYYAD ZAWIYYA****
Da wani irin hanzari yake zuba kayansa a jaka shekarunsa Uku rabonsa da Nigeria, haka kawai baya son zuwa tun bayan faruwar lamarin sai ya da’de bai je ba, kunyar mahaifinta da ya zame masa Uba bango yake ji har yau ya kasa daina dana sanin abinda ya aikata. Yana da k’arfin gwiwar tunkararsu a yanzu tun bayan da fahimci lallai Zakiyya na nan da rai dole ya je a tsananta bincike wajen gano Zakiyya da inda take koda zai rasa komai nasa a rayuwa. Tsaf ya shirya don surprising ‘dinsu yake son yi bai sanar da kowa zai koma Nigerian ba…
***BAUCHI****
Tunda suka shigo gidan Jadda take jin k’irjinta na bugawa ka’dan, hakan yasa ta dage wajen karanta addu’ar yaye tsoro da fargaba. Gaisuwa sosai suka yi da Maimartaba, aka kuma gabatar mata da duk wani kayan ciye ciye, sai dai ta sanar da su a rana irin ta ta yau Alhamis tana azimi. Maimartaba ya jinjina kai yana furta “Allah ya bada lada, mun miki laifi Hajiya, sai dai a yau muna son mu gyara Kuskuren da muka aikata, hakan bai afku ba saboda son zuciya sai dai neman masalaha, ku yi hak’uri mun b’oye muku ZAKIYYA NA DA RAI, tsawon wannan lokacin……” Cak numfashin Jadda yaso d’aukewa bayan da ta yi ido biyu da Kiyyan ta da take tsaye idanunta cike da k’walla ta zuba mata ido. Lab’banta na rawa ta furta “JADDATY….”
'Yan uwa
Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS,
duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su
Sandal flakes
Hawee
Gabgab
Halut
Dorot
Coconut chips
Dufr(farce)
Black khumra
Brown khumra
White khumra
Oil perfumes da
Body sprays
Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku.
Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka
Call/WhatsApp
***
Location:Gonan Ganye,zaria
Kaduna state
Nationwide Delivery.
JIKAR NASHE✍🏽