Chapter 4
Runtse idanu Jadda ta yi kafin ta sake buɗe su ta ware a kan Zakiyyan, tana cije leɓenta don son tabbatar da ba mafarkin da ta saba bane. Jin zafin haƙoranta a saman leɓenta ya tabbatar mata Zakiyya ce ba mafarki ba. Musamman Jin Zakiyyan ta nufo wajenta ta kuma shige jikinta da sauri tana sakin wani irin kuka, Jadda hannunta na rawa ta dafa kan Zakiyyan idanunta akan na Mahmud da ya yi matuƙar ƙoƙari wajen danne zuciyarsa bai bayyana halin da yake ciki ba… Jadda bata gano komai a tare da shi da yake da alaƙa da rashin gaskiya ba, hakan yasa ta mayar da kallonta cikin idon Maimartaba da ya yi saurin janye nasa kwayar idon, kunyar Jadda yake ji, tabbas an aikata mata babban laifin da ya kamata a ji kunyarta. Muryar Jadda na rawa ta ce “Me yasa? Me yasa kuka ɓoye mini wannan al’amari mai girman gaske, ko don Zakiyya ba Jinina ba ce? Ko don bani na haifi Ubanta ba?” Ta faɗa tana wani irin kecewa da kuka. Abin da ya ɗaga hankalin Mahmud har bai san sanda ya isa ga Jaddan ba ya fara girgiza mata kai cikin murya mai bayyana tashin hankali ya furta “A'a Jadda, A'a kada wannan tunanin ya zauna a zuciyarki, kada ki min wannan horon Jadda bani da wata Uwa da ta wuce ki, Jadda ni kaina ban san da maganar nan ba, I was surprised sanda na ji labarin” ya faɗa idanunsa suna zubar da ƙwalla.
Mai martaba ya yi gyaran murya hakan yasa hankalin kowa ya koma kan shi banda Jadda, da take Jin wani irin haushin shi “Ki yi haƙuri, kamar yarda Mahmud ya sanar miki bashi da hannu akan hakan, laifinmu ne kuma mun yi hakan saboda saving rayuwar Zakiyya daga dukkan wata cutarwa, kada ki manta irin wahalar da ta sha a lokacin shi yasa muka yanke wannan shawarar muka kuma ja kunnen mahaifyarta a kan kada mu ji zancen ko a wajen Mahmud balle wani a cikin Ahalin ZAWIYYA” “Har ni ko? Saboda kuna tunanin sharri da cutarwa daga gare ni? Me na muku me yasa na cancanci hakan daga gareku? Ko saboda kuna ganin za’a iya haɗa kai da ni a cutar da ita? Kun san iya hakkına da kuka ɗauka? Kun san tun bayan rasuwar Zakiyya ban sake samun nutsuwar zuciya ba? Ban sake samun barci mai daɗi ba, mutuwa bata taɓa tsaya min a rai kamar yarda ta Kiyya ta tsaya min ba, daga ranar kuma da abin ya faru ban sake ganin farin Zayyad da iyayensa ba? A kullum baƙinsu nake gani ba don komai ba saboda jinin Mahmud aka taɓa me yasa na cancanci haka daga gareku?” “Kuskure ne Jadda, amma ki yi haƙuri don girman zatin Allah abinda kuma ya wuce ya wuce har abada don Allah. Mun san mun aikata miki ba daidai ba, muna roƙon Ubangiji ya huci zuciyarki don Allah.” Anna ta faɗa a hankali cikin muryar nutsuwa. Maimartaba Ma ya ɗora da nasa. “Kada ki bari shaiɗan ya rinjayi zuciyarki, ba wani dalili da zai saka mu yi miki kallo wanda ba na Uwar Mahmud ba, kin masa riƙo irin riƙon da sai wanda ya samu Uwa ta gari sannan yake samun irinsa, har abada Jinin Mahmud naki ne ƴaƴansa jikokinki ne, ba mu yi haka don mu nuna miki ba ki isa da Mahmud ba sai don samun masalaha don girman zatin Ubangiji ki yi haƙuri, ga Kiyya nan mun dawo miki da ita wanda mun san a yanzu ta yi hankali, za ta iya bambance fari da baƙi zata iya bambance duk wata cutarwa da za'a mata, a yanzu mun zan zata iya kare kanta bamu da hannu wajen iko da ita, ita ɗin taki ce a tsawon shekarun nan bata da wani zance wanda ya wuce naki, da ƙyar muka samu ta manta da ZAWIYYA da ahalin cikinsa amma bata manta Jaddaty ba kullum zancenta Jaddaty don Allah ki mana afuwa” Zakiyya ta sake rungume Jadda sosai kamar wani zai kwace mata ita a hankali ta furta “Aren't no happy seeing me? (Ba ki farin ciki da gani na ba?”) Jadda ta yi murmushi tana saka yatsa ta lotsa kumatunta inda wani dimple mai kyau yake. Kiyya ce dai, Kamannin da komai suna nan ba abinda ta rage sai ma k’ari da aka samu a kan kyawunta na da. Ta girma kamar ba waccan Kiyyan tasu ba ƴar shekara goma. Sai ta saki ajiyar zuciya tana ɗan kissing ɗinta kaɗan so da ƙaunar yarinyar yana sake shiga zuciyarta, bata san me yasa tafi sonta a kaf jikokinta ba saboda tana da shiga rai sosai kuma soyayyar Mahmud sai ta shafeta… “Na yi farin ciki sosai Kiyyan Jadda, Alhamdulillah Allah Ashe mafarkan da nake yawan yi a kanki gaskiya ne? Ashen zan ga girman ki Kiyya, Ashe zan ga aurenki kamar yarda na sha gani a mafarki….” Zuciyarta ce ta buga sosai da k’arfin gaske tuna zancen auren Kiyya da ta yi? Shin lamarin kuwa mai yiwuwa ne. “Are you Okay?” Ta ji muryar Kiyya a kunnenta tana matsa hannayenta. Ajiyar zuciya ta sakar mata sai kuma ta saki murmushi tana furta “Am Okay Zakiyya, ki shirya mu tafi” Anna ta yi saurin cewa “Haba Jadda, ai da kun bari sai gobe, saboda na ji kince kina azimi Kano fa ba nan ba ce 3hours trip ne from Bauchi to Kano tunda har yanzu ba Flight da yake zuwa da an samu sauk’i.” Jadda ta girgiza kai tana k’ok’arin danne fushin da take ji a zuciyarta ta furta “Bakomai, farin cikin da nake ciki ba zai saka na ji wahalar tafiyar ba.” Ta faɗa ba wai don haka bane a cikin zuciyarta, sai don bata son zama haushin su Anna take ji, ta fi son ta yi nesa da su kafin ta gaya masu bak’ar magana” Haka şuna ji şuna gani suka ƙyalesu suka tafi har gate suka raka su. Kiyya sai wata irin fara’a take tana sallama da barorin gidan da suka ɗan saba tunda ba wani zama ta yi a gidan ba, raywuarta gaba ɗaya a England ta yi ta, gidan wani bature abokin Maimartaba shi yasa gaba ɗaya ɗabiunta irin na turawa ne.
ZAYYAD ZAWIYYA
Cikin tarin kasala da masifaffiyar gajiya ta jiki da ta zuciya yake saukowa daga matattakalar jirgin. Fuskarsa a ɗan ɗaure as usual. Ya mayar da idanunsa kan wayar da yake dannawa da alama kiran wani yake so ya yi, ko kuma ya yi haka ne don gujewa idanun jama’a da yake jin kaifinsu na yawo a jikinsa. Ba ya son kallo tun fil’azal haka yake idan aka fiye kallonsa sai ya ji sam ransa yana ɓaci. Yarda yake tafiyar zata za ka yi gayu ne ko kuma tsarabar girman kai da nuna isa, sai dai gareshi sam ba haka ba ne, yanayin zubi da tsarin halittarsa ne, a haka ya taso tun yarinta kuma still har girmansa bai canja ba.
Bai gayawa kowa zai zo ba, don haka Bolt ya yi kansa tsaye don isa gida. Akwatinsa guda cal shi ya riƙe a hannunsa sauran kuma da zarar sun iso zai aiko a ɗauka, don ya san bai isa ya ƙi yin tsaraba ba, idan ba so yake Jadda ta isheshi da mita ba “Ihsani ko ya ya yake yana da daɗi Zayyadu, idan aka maka Ihsani duk arzikinka kana jin farin ciki musamman idan ya fito daga hannun jininka, yana kuma ƙarfafa zumunci ya kuma ƙulla wata irin alaƙa da duk ƙulalliyar soyayya ka ji son ɗan uwanka yana sake gauraya da jininka don haka kada ka fasa alheri komai kashinsa” Ya jiyo irin furucinta a cikin kunnuwansa, dole zai haddace irin nasihohin Jadda don bata fasa jaddada su a kullum. Sai kawai ya samu kansa da sakin murmushi yana cusa hannayensa a cikin gashin kansa da gaske Jadda wata irin baiwar Allah ce da Samun irinta a cikin duniyar nan sai an daɗe ana bincike. Duk da ta san mai laifi ne shi a wajenta tun bayan wancan lamari da ya faru tsakaninsa da Kiyya bata fasa yi masa uziri ba, bata fasa gaya masa tana taya shi neman gafara a wajen Ubangiji ba.
Da wannan tunanin ya isa mahaifarsa. Gidan da lokutan baya babu wani waje da ya fi shi saka shi farin ciki. Amma tun bayan faruwar komai ya ji gidan ya fice masa a rai, banda a yau da kuma yanzu da yake jin wani irin tarin farin ciki da annashuwa şuna fusgar zuciyarsa wajen son shiga gidan, bai san meye dalili ba? Amma ya alaƙanta hakan da murna da zakwaɗin son zuwa ya sanar musu Zakiyya na raye!
Da sauri ɗaya daga cikin masu yiwa gidan hidima ya taso yana ware ido cike da farin cikin ganin Zayyad, don mutum ne shi mai alheri garesu, bai kuma san wani abu wai shi wulaƙanta Ɗan'Adam ba, sau tari idan har yana gida ya kan fito ya zauna a wajen su su yi hira. Zayyad na murmushi ya miƙ’a masa hannu, yana furta
“Yaya dai Alaramma? Kana mamakin gani na ne?” ya ce a nutse.
"Sosai ma kuwa"
Alaramma ya furta yana jijjiga kai. “Amma dai al’ummar ZAWIYYA basu san da zuwanka ba ko? Don ko kaɗan ban ji ana zancen ba, don da sun sani bana jin Jadda zata fita ta tafi Bauchi yau.” “Bauchi?” Zayyad ya furta yana jin sunan a tsakiyar ƙirjinsa ko sunan garin ya ji hankalinsa na tashi balle ya tuna Anna da take masa kallon tsana ko gaisuwarsa bata amsa wa. “Me ya faru a Bauchin suka tafi?” Ya samu kansa da jefawa Alaramma tambaya. Girgiza Kai ya yi ya ce “Nan fa ɗaya, ka San Jadda ba zata taɓa yi mana bayanin abinda ya faru ba, tafiya ce suka yi ta da Abba
Ƙarami. Amma dai yallaɓai da ka sanar ai mun je an taroka daga airport ɗin tunda a motar haya fa naga ka iso nan..,” Kafin Zayyad ya bashi amsa a saki wani horn da ƙarfi daga waje. Kallon juna suka yi şuna murmushi don in dai aka ji haka a san waye. Zayyad ya girgiza kai yana furta “Abba ƙarami” Sai ya lumshe ido yana jin wani sururi a ransa yana fatan Zakiyya ta zama da gaske tana da rai, ko bakomai zai goge tabon laifinsa a wajen Abban nasa. Gefe ya koma ya yi folding hannayensa a ƙirji yana kallon motarsu Abba Mahmud ɗin da take shigowa kamar walƙiya, dama haka ya saba tuƙinsa kuma ko Jadda ta masa magana baya fasawa har ta haƙura ta ƙyaleshi. Basu lura da shi ba, har zuwa sanda suka fara fitowa daga cikin motar idonsa ya faɗa kan Zakiyya sanye cikin wasu irin English wears, şumar kanta a waje kamar baturiya. Numfashinsa ne ya yi season ya zuba mata ido baya ko ƙiftawa yana jin yarda zuciyarsa ke bugu da ƙarfin gaske so da gaske Kiyya tana raye she is still alive?” Ya ji bakinsa ya furta, bai san a fili ya yi furucin ba bai kuma san da isowarta wajensa ba saboda idonsa a rufe yake, sai ji ya yi ta furta “Yes Am still alive Yaya Zayyad, ban mutu ba as you wished………..”
JIKAR NASHE✍🏽