RASHIN SANI

PAGE 04.

by @sumy6163

💫💫RASHIN SANI 💫💫

STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic).

Dukkan godiya ta tabbata gab Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).

Godiya mai tarin yawa tare da jinjina ga 'yan' uwa marubuta da suka karfafa mini gwiwa wurin yin wannan rubutu, Allah ya Saka musu da alkairi ya kara daukaka su.

Wannan labari kirkirarre ne, idan yayi kama da rayuwar wani ko wata, to arashi ne.

PAGE 04

Koda gari ya waye, haka ta tashi jikinta a mace, saboda rashin bacci da wuri da kuma tunanin Kamal data sawa ranta, haka dai ta gama duk aiyukanta ta shirya ta wuce makaranta, ko takan Abdul bata biba bare su Hamida iyayen latti.

Ko a class ma haka tayi wani sukuku da ita,hatta kawayen nata saida suka fahimci yau akwai wani abu, Aima dai sarkin surutu ne yau shiru haka.

Humaida ne ta tabo ta tace "nikam yau Aimana baki da lafiya ne?

Zuba mata ido tayi ba tare da ta amsa mata ba, don ita a karan kanta bata san mai zata ce yana damunta ba.

Can dai tace" ba komai Humaida,yau dai kawai na tashi wani iri ne"

"Ikon Allah, to Allah ya sauwake, haka ma ya Kamal yau ya tashi da wani kalan sakalci, ke hatta ruwan wanka yau saida aka kai masa wai stress ne yake damunsa"

Duban Hamida tayi da tayi maganar, jin ta tabo inda yake mata kaikayi tace, "Allah sarki ya Kamal ai yana fama kuwa, niko jiya yaushe ya dawo, nayi ta jiranshi da assignment na, karshe dai in gaya miki ya Abdul ne ya nuna min bayan ya gama min wulakanci san ranshi".

Dariya suka hau yi dukansu.

Hamida tace " ai kece Aimana da abun haushi kike, ya Abdul nan dai kinsan guru ne shima amma duk lokacin da yace kizo kuyi karatu sai kice bai iya ba, ai shine maganin ki, to ko nine kikewa haka sai na miki abunda yafi nashi"

"Kyaji dashi dai, kinsan dai ya Kamal na gama jarabawan nan ai shikenan, bama zai ga ko note nawa ba bare ya min wulakanci, saura 10 days ma ai su fara rubuta JAMB din, kinga daga nan na huta".

"Uhumm ai sai kiyi kuma, haka dai yace saura 10 days" cewar Hamida da take kokarin dauko littafi a jakanta.

"Allah sarki yayana Allah y bada sa'a" suka amsa da ameen.

Lokaci nata tafiya, yau ya kama randa Kamal zai rubuta JAMB nashi, fes ya fito cikin shirinsa, yasha jamfarsa ya tsaida hulannan kamar wani babban mutum, ya kuwa yi kyau ainun, koda Aimana tayi tozali dashi har kusan tuntube taci garin kallonsa.

"Yi hankali my Aima karki fadi, ki rinka kula in kina tafiya".

Murmushi tayi tace "ya Kamal ai kai nake kallo, kaga yanda kayi kyau kuwa, young alaji kenan".

"Allah ko Aimana kice yau zan bada kala".

"Sosai ma kuwa yayana,ai kaidin karshe ne"

"Kai Aimana kina fasa min Kai,to a mana addu'a"

"To yayana Allah ya bada sa'a, Allah yasa question din suyi sauki yayana, ka samu points har da Kari".

"Ameen kanwata nagode da addu'arki, and plus mata ta gari".

Tura baki tayi ta wuce ko amsa shi bata yiba.

Daga murya yayi yace " to my Aima ba sallama ne, to sai na dawo".

Ko kulashi bata yiba taci gaba da tafiyarta, a ranta take ayyana wasu matan suna can zasu ta kalle mata yayanta, bata ankara ba taji hawaye nabin fiskanta, "to wai ke ina ruwanki da masu kallonsa ne, suyita kallonsa mana", wata zuciyar ta gaya Mata.

Share hawayenta tayi taci gaba da tafiya.

Daga nesa taji ana kwala mata Kira, juyawa tayi taga su Hamida ne harda Abdul, da kamar baza ta tsaya ba sai kuma ta tsaya.

Suna isowa kuwa Abdul yace "duk saurin mutum dai gashi tare zamu isa makarantar".

"Ai don na tsaya jiranku ne shiyasa ka samu daman gaya min magana"

"Oho dai, da ni nace ki jira ni, ai da sai ki wuce abinki kiga ko baza mu karaso ba, mutum sai son sammakon zuwa makaranta, sai kace tafi kowa son karatun, anya Aimana kekam ko duty master yana riga ki zuwa makaranta kuwa?

"Bansani ba dan rainin wayo, ai dai naga sammakon ba a banza ba tunda ana gani a kasa.

Su Hamida sai dariyan fadansu suke yi, shiyasa suke son hada hanya dasu, don zasu kwashi nishadi, saidai abun burgewa kuwa duk fadansu baka isa ka taba dayansu ba, don lokacin zasu nuna maka 'yan'uwa ne su.

Haka suka karasa makarantan Aimana tana ta fushi, da zaran ta tuno Kamal yana can enmata na kallonsa sai taji bacin randa bata san daga ina yake zuwa ba.

Kamal sunyi exam nasu lafiya sauran jiran sakamako, tun jiya ya lura Aimana take fushi dashi ya rasa dalili.

Itako daga ta tuno matan da suka ganshi jiya sai taji ranta ya sake baci, kila ma har murmushi yayi ta musu da wadannan kyawawan hakoran nasa, duk abun duniya ya taru ya ishe ta, ita tama rasa me yake faruwa da ita ne wai,wai meyasa ta dauki al'amarin ya Kamal so serious haka ne, meyasa bata damuwa da al'amarin Abdul kamar na Kamal ne, kuma shima ai yayanta ne, shine ma yafi kusa da ita, ya kamata tafi damuwa da al'amarin sa ma fiye dana Kamal, to amma meyasa?

Wadannan tambayoyi su take yawan yiwa kanta, kuma bata da amsan su a yanxu.

Washegari kuwa aka saki result, Kamal yaje cafe ya dubo nashi, kuma Alhamdulillahi ya samu 260 points, murna kamar zaiyi me, da sassarfa ya isa gida, yaje ya nunawa ummah result nasa, ta kuwa tayasa murna hade da sa masa albarka.

"Bari naje na nunawa Aimana, wai ina su Hamida ne" ya tambaya.

"Ka manta suna makaranta ne,irin wannan zumudin haka ai dai ka hakura su dawo ko, Aimana ma bata nan yanzu tunda tare zasu taso, al'amarinka da Aimana sai Allah kamalu, Allah dai yasa tarayyarku ta zama alkhairi".

" Ameen ummah" ya amsa cike da farin ciki, don shi baima fahimci inda maganar umma ta dosa ba, tunda shi hankalinsa baikai can ba tukun.

Koda Aimana ta dawo basu hadu da Kamal ba kasancewar suna tafiya islamiya karfe biyu, wanka kawai tayi, tayi sallah suka ci abinci suka wuce.

Kamal bai samu ganinta ba har sai karfe biyar bayan dawowarsu islamiya, da murnansa yazo ya nuna mata result nashi.

Tsalle tayi cike da farinciki tana taya shi murna"ya Kamal na taya ka murna, ai dama na gaya make,this time around you will make it, and see, you did it" daga masa dan yatsa tayi alamun yayi kokari.

Hira suka cigaba dayi cike da farinciki, Aimana kamar ba itace take fushi dashi kwana biyu da suka wuce ba.

A cikin hiran yake ce Mata "yanxu dai kinga Aima nan da wata shida ko bakwai zan fara zuwa makaranta, indai na samu admission, sai kiyi ta saka ni a addu'a Allah ya bani sa'a, kinsan jami'a fa akwai wahala, musamman ma course danake so".

To ya Kamal, insha'Allah zanta maka addu'a zakayi nasara,ni nasan yayan nawa ba daga nan ba, our future doctor, Dr Kamal Muhammad" ta karashe cike da zolaya.

"Aikuwa kina da kyauta na musamman saboda wannan addu'a taki,fadi duk abunda kike so".

"Yanzu dai ya Kamal ba abunda nake so,amma tunda kayi niyya ka barshi a matsayin alkawari, duk randa na ga abunda nake so zan gaya maka".

"To shikenan Aima, na miki alkawari duk randa kika tuna abunda kike so ki gaya mini, nikuma inhar baifi karfi na ba zan nemo miki shi a duk inda yake a fadin duniyar nan insha'Allah".

"Promise fa ya Kamal"

"Yess promise my sweet sister"

Hiransu suka cigaba dayi har saida suka ji Kiran sallah, da hanzari Aima ta mike tana cewa" na bani, yau Mama sai tayi kulikulin kubra dani, Allah ya Kamal duk laifinka ne da ka cikani da surutu".

Hamida tasa dariya tace" kuka cika mu da surutu dai ai zaki yiwa Mama bayani ne".

Ummah dake jinsu tace "kinga rabu dasu Aimana, ba abunda Mama zata miki ai tasan bakya wuce nan".

"To ummah nidai bari nayi sauri na wuce kar in kara laifi, Allah kuma ya Kamal kazo Ka rakani ka gaya wa Mama ina nan ba tsokana na tsaya yiba".

"To muje,ai ke dince har yanxu kinki ki daina rigima, zanga randa zaki gane kin fara girma Aima, ke ba yar fari bare ace, kuma ke ba auta ba, amma sai rigiman da neman fada, Allah dai ya taro mana ke Aimana".

Daidai nan suka iso kofar gidan su Aimana, sallama sukayi aka amsa musu, suna shiga suke iske Mama na alwala a bakin famfo.

Tsuru Aimana tayi, don batayi tsammanin samun Mama a tsakar gida ba yanzu,tunda mafi yawan lokuta a toilet na daki take alwalanta, bata san kuwa yau sabida ita Mama ta tsaya yi a tsakar gida ba don ta ga da wacce zata shigo.

Kamal ne ya fara gaisheta " Mama an wuni lfy"

"Lafiya qalau Kamal ya umman taku?

"Lafiyanta qalau Mama, tama ce in gaishe ki"

"Masha Allah,ina amsawa, yaya sakamakon jarabawa naji ance an saki ko?

"Eh Mama sakamako Alhamdulillahi an samu abunda ake so, har ma da kari".

"Wai wai Masha Allah,ai haka akeso sai a kara dagewa kuma, Allah ya taimaka".

Aimana dai na tsaye bata ce komai ba, dubanta Kamal yayi yaga tayi wani tsuru a wurin kamar wata ta kirki, dariya ne yaso kubce masa ya daure, kallo Mama yayi data idar da alwalanta ta mike zata shiga daki bata ko kula da Aimana dake tsaye kamar wata munafika ba.

Cewa yayi" to Mama bara naje masallaci naji ana kokarin tada sallah".

"To Kamal gara kayi hanzari kam ka samu jam'i, kasan shi sallah a jam'i ba karamin lada ne dashi ba, Allah ya kara shirya mana Ku".

Ameen mama, ga Aimana nan, ummah tace in rakota, tun dawowarsu muna tare muna ta murnar result nane, bamu ankara ba kawai sai kiran sallah mukaji, don Allah Mama ayi mana afuwa".

"Kajika Kamal, gidanku ai ba wani unguwa bane, kawai dai banason magariba yayi tana waje ne, don ba mutuncin ya mace bane ana magariba bata gida, kuma na gaya mata ta rika sanar dani in zata guri amma Aimana sai addu'a, ai da sai ta shigo ta gaya min tana gidanku da shikenan".

Haka ne Mama,ayi hakuri zamu kiyaye insha'Allah".

"To Allah yasa i maza kaga an shiga sallah muna ta surutu".

Da hanzari kuwa ya fice, Mama ko tayi falonta don gabatar da sallanta.

Aimana na ganin haka tayi wuff ta fada dakin Dada,don baza tayi gangancin tunkarar Mama a yanzu ba.

Bayi ta wuce ta dauro alwala itama ta gabatar da nata sallan.

A yan kwanakinnan Kamal ba inda yake zuwa, hakan kuwa sai yayiwa Aimana dadi, don da ta dawo islamiya zata dauki littafi tayi gidansu ko bata da assignment, dake yana musu extra lesson a gida tare dasu Hamida, ranarda ba islamiya kuwa a can take tarewa suyi karatu suyi hira,ba karamin dadin hakan takeji ba, ita dai gata ga Kamal tana kallonsa to fa bawani matsala.

Mama ta lura sosai da yawan zuwan Aimana gidansu Kamal da sunan karatu, abun ya wuce gona da iri.

Ranar kuwa ta dauko littafi tazo ta sallami Mama zata tafi, kiranta mama tayi tace " nikam Aimana wani irin karatu ne kukeyi haka kullum awa da awanni eye? harna manta yaushe rabonda ki zauna a gidannan na awa daya in ba dare ba".

"Mama extra lesson ne ya Kamal yake mana dasu Hamida,in muna da assignment kuma sai ya koya mana, bakiga ba yanda muke ganewa sosai,yanzu fa ko a class kokarinmu daban ne,har fa ce mana ake top 3".

"Nikam ya isheni surutun haka, jeki sai kin dawo kuma ki tabbatar biyar ta miki a cikin gidannan".

"Mama ai shida muke tashi"

"Nidai na gaya miki biyar ta miki a cikin gidannan,tunda ai ba makaranta bane bare ace sai lokacin tashi yayi, in kuma ba haka ba sai ki hakura da zuwa gabadaya".

Mama na kaiwa nan a maganarta taci gaba da abunda takeyi, Aimana ko haka ta hakura ta tafin, don idan ta tsaya rokon Mama ma hana ta zuwa zatayi gaba daya, tayi biyu babu kenan.

Haka kuwa akayi, tun hudu da arba'in ta musu sallama tace zata koma gida.

"To yau kuma lafiya Aima da wuri zaki koma gida" Hamida ta tambaya cike da mamaki, don wataran in shidan tayi ma haushi takeji, ta rinka korafin shidan ma da wuri takeyi, dakyar take yadda ta tafi, shima kuma don tana tsoron fadan Mama ne.

"Eh Hamida,yau da wuri zan koma, Mama ce tace in dawo da wuri, bansani ba watakila akwai abunda zan mata ne".

Aimana bata iya karya ba shiyasa kai tsaye ta gaya musu Mama ce tace ta dawo da wuri yau.

"To shikenan Aima, sai gobe kenan, ki gaida min hajja Dada", Humaida ce ta amsa ta wannan karon.

"Oh wato baza ma kice in gaida Mama ba, sai tsohuwar nan ko, to dai zataji, bara na tafi kar inyita bata lokaci, sai gobe".

"To Allah ya kaimu", suka fada a tare,taje tayiwa Ummah sallama ta fito.

"Ya Kamal baza ka raka ni ba?".

"Jeki abinki Aima, kinsan yanzu idan na rakaki sai muyi ta surutu har ki kasa karasawa gida da wurin, sai gobe kinji, ki gaida min Mama".

"To ya Kamal zataji insha'Allah, Allah ya kaimu".

Ta fita ta tafi badon haka taso ba.

Da sallama ta shiga gidan, ba kowa a tsakar gidan, sai kawai ta nufi dakin Dada,bata nan ko ina tayi oho,zama tayi zugum ta hau tunanin, can kuma ta mike tayi wurin Mama, bata san meyasa tace ta dawo da wuri ba maybe aiki zata mata,tazo tayi zamanta a nan.

Da sallama ta shiga, Mama dake zaune tana duba abu a wayarta, ta amsa tare da dagowa.

"Yanzu ne karfe biyar din ko Aimana"

"A'a Mama, tun dazu na dawo, ina dakin Dada ne, naga ma bata nan, akwai abunda zan miki ne Mama, kince in dawo da wuri".

"Ba abunda zaki min Aimana, ina son dai kawai ki rika zama ne a gida wasu lokuta.

Gyara zamanta tayi ta dubi Aimana tace "kinga dai yanzu kin fara girma, sannan Kamal namiji ne ba mace ba, bana son yawan shige masa da kike yin nan, Aimana mace da kamun Kai, da rike mutunci aka Santa, kar kiga ke yarinya ce, mace ana so ta kasance mai girmama kanta da kare mutunci da martabarta tun da karancin shekarunta, ta haka ne koda ta girma zata kasance da wadannan dabi'u, mace ba ita ke bibiyar namiji ba, saidai shi yazo inda take, Aimana yanzu bazaki fahimci mai nake nufi ba sai zuwa gaba,duk da karatu kike zuwa wurin Kamal, amma ki daina zakewa, ke komai sai Kamal ne, ba ga nan yayanki a gida ba, meyasa shi bazai koya miki ba sai Kamal, Aimana kiyi hankali, ke daya Allah ya barmini a cikin 'ya'ya takwas da na Haifa, bazan so ganin wani abunda zai taba rayuwaki ba, ba kuma zanso ki kasance daga cikin wadanda suke azabtuwa saboda zuciyar su ba, kar kiga kamar ina yawan takura miki, ina son ganin rayuwarki ta gaba tayi inganci ne koda bana nan, ba lallai ki gane duk abunda nake nufi a yanzu ba, amma gaba zaki gane, Allah ya miki albarka Aimana, Allah ya tsare ki daga sharrin dakkan abin halitta, Allah kuma ya hadaki da abokin zama na kwara"i.

Sosai jikin Aimana yayi sanyi, duk da kasancewar wasu daga cikin zantukan Mama duk ba ganesu tayi ba, duk wani haushin da take ji na dawowa da wuri da Mama ta sa tayi sai taji duk ya gushe.

Zuwa tayi ta kwanta a cinyar Mama,tace" ameen Mamata, Allah ya barmin ke har tsufa ta, kina nan insha'Allah"

Murmushi Mama tayi tana shafa kanta tace" to Aimana in hakan alkhairi ne a garemu, Allah ya sa, in kuma ba alkhairi bane, Allah ya zaba mana abunda yafi alkhairi.

"Ameen Mama"

Daga haka suka cigaba da hiransu na ya da uwa, Mama tana dada nusar da ita wasu abubuwan cikin hikima, bata duba karancin shekarunta, takance idan bata gaya mata tun yanzu ba, to gaba in ta fada mata wahalar dauka zai Mata, kuma bata san ko Allah zai ara mata rayuwarta har zuwa gaban ba,amma idan yana kwakwalwarta tun yanzun, gaba aiki dashi bazai mata wahala ba.

Tun daga ranar wasu abubuwa suka canza.....